Showing 27001 words to 30000 words out of 38755 words

Chapter 10 - Mummunan Zato Book 3 Complete Halina Mashi

09 Jul 2025

2075

Jamila ne, da taimakon ƴan aiki ya samu ya dannata kan
gado zuwa wani lokaci yana tofa mata addu'o'i sannan ta lafa sai kuma kuka tana faɗin na shiga uku ni
Jummai. Ya ce me yake faruwa ne ki min magana mana ta ce su Jamila ne zasu kashe ni suna ta bina, ya
ce wacece Jamila? Matanka mana da suka mutu, shiru ya yi ya zuba mata idanu, cikin zuciyarshi kuwa
tunani yake yi me zasu ɗauki fansa yake nufi? Amma sai ya dubeta ya ce to kici gaba da addu'a ya miƙe
ya fita cikin ɗaurewar kai,baya son zargi don haka sai kawai ya shafe batun daga zuciyarshi sannu a
hankali mafarkin ya zamo wa Hajiya Jummai ƙa'ida in dai har zata rufe idanu da sunan ko gyangyaɗi ne
ba ma bacci ba,tuni ƴan aikinta kunnuwansu sun soma sabawa da jin ihun Hajiya Jummai cikin dare da

rana, ita kuwa tuni rashin bacci ya yi biji-biji da ita tamkar zautacciya ta dawo ko yaushe tana surutai
waɗanda in ka saurare su asirin ta kawai take tonawa,ko yaushe tana faɗin kada ku kashe ni sun ce zasu
rama na shiga uku na kuyi haƙuri wannan yasa Alhaji tsare Jummai da son jin me ke faruwa ne? Kuma me
zasu rama? Cikin kuka ta ce ka taimake ni nice na kashe su dukkansu nan ta zayyane mishi duk yanda
komai ya faru,kuka da hawaye Alhaji Saddiƙ ya yi sannan ya je yazo da Alhajinshi don jima kunnanshi
shima, Alhajinmu kasa magana ya yi sai da yaje gida sannan ya iya furta ma Hajiyarmu labarin itama
girgiza mahaifan Jummai sun yi baƙin cikin jin wannan zancan, Alhaji Saddiƙ ya samu mahaifan nashi don
son sanin menene mafita shi dai ta gefen shi ya gama zama da ita, ashe duk ita ce silar da jama'a suke
mishi mummunan zato kai Allah ya isa Jummai na tsane ki har abada, mahaifinshi dai ya ce in yaga
bazaya iya zama da ita a haka ba to ya sauwaƙe mata domin kam dan cutarwa an cutar da shi Hajiyarmu
kuwa shawartar shi ta yi da cewa in ya saketa to don Allah yabar ta a muhallinta wato gidan shi kenan, ya
amince da hakan don haka yana shiga gidan ɗakinta ya nufa zaune ya sameta gefenta Hajiya Kari ce tana
cewa, haba Jummai yaya zaki saki baki ki yi ta tona ma kanki asiri? Alhajin da basu san da shigowar shi ba
ya ce ko bata fada ba dole ne wata rana asirin ya karye, domin ta ɗauki rayukansu ba tare da haƙƙinsu
ba,shawarata gare ku ke da ita in kuna son samun sauƙi gobe kiyama ku kai kanku kotun musulunci
domin a zartar muku da hukuncin da ya dace da laifukanku,in kuma kun fi son Allah ya yi muku nasa
hukuncin da kansa to kuyi shiru ya ja numfashi sannan ya ci gaba da cewa Jummai am sorry to say na
sake ki saki biyu in kina so za ki ci gaba da zama cikin gidan nan sai dai ni yazama dole in barshi.

Wani irin ihu ta saki mai ƙarfi tana cewa ka taimake ni kai ne kaɗai ka rage min saboda sonka ɗin ne fa na
aikata duk waɗannan laifukan shi ne yanzun za kayi min haka? Ya ce ke kika zaɓo hakan, wacece ke da
zaki ce ba za'ayi miki kishiya ba saboda kin ƙwashe kayan ki daga gaban Manzo,ya dubi Karima ku saurari
ƙarshenku yana zuwa. Yasa kai ya fita abinshi, Jummai an shiga sabon ruɗu, hauka hauka ne ya sameta
nan take. Lamari fa ya ta'azzara su Jummai yau gashi an kai ga rufe mata ƙofa domin zabura take zata
gudu tana faɗin ga sunan baƙin wani kashi da ke jikin Jummai tuni ta yi mishi fizgar kaza,ya zama abinci
sai dai a kulla ƙwano da igiya a tura mata Alhaji Saddiƙ tuni ya tattara su Hadiza da wasu daga cikin ƴan
aikin gidan suka koma wani gidan shi da ke can cikin G.R.A. Hadiza a baɗini murna take amma a fili kuka
rurus ta ringa yi wai ita dole nan me imani, shi ko Alhaji tuni ya dawo rakiyar su shi dai tsoron lamarin
mata yake bashi domin bai taɓa zaton Jummai zata iya kashe koda ƙiya shi ba bare mutum. Shine dalilin
da ya ji mata sun fita ranshi, hatta A'isha da bata san ma meke faruwa ba duk yasa su gefe shi ne dalilin
da hankalin A'isha ya yi matuƙar tashi ga zatonta abinda ya faru ƙwana kin baya ne zai kuma faruwa cikin
sauri ta kira Nafisa da kukanta tana cewa Uncle ya yi watsi da ita kota kirashi ba ya ɗaga wayarta,nan take
Nafisa ta ce daina kuka mijinki yana cikin ruɗani ne sannan ta sanar da ita dukkan abinda ya faru. A'isha
tasha mamaki lallai dole ne maigidan nasu ya shiga rudani.

Karima kuwa taje tazo da bokansu don ya yiwa Jummai magana,suna shiga inda take ta riƙe shi fatar
jikinshi ta shiga yaga tana surutai Karima ta yi baya da gudu,tana fita mashin ya yi ciki da ita nan take
wuyanta ya karye shi ko boka da ƙyar ya ƙwaci kanshi ya fito jina-jina ya fita da gudu, ganin ƙofa buɗe
itama Jummai ta yi ficewarta ta shiga gari tana fallasa dukkan abinda ta yi anyi watanni kusan uku kafin

Alhaji Saddiƙ ya gano kanshi, ya zaunar da Hadiza ya yi mata nasiha tare da nuna mata cewar ta dauki
ishara daga abinda ya faru kan Jummai, ta nutsu ta dawo cikin hankalinta domin itama zai iya kasancewa
da ita, Hadiza kam ta ɗan yi nazari game da batun maigidan nata lallai haka zancan yake. Amma Hajiyarta
har yanzun tana nuna mata cewa aikin da suke yi ne nasara ta samu, sannan ta ƙara miƙe ƙafa gidan miji
ya zama nata, haka nan kada ta damu da zancan A'isha ita ma data dawo za su saukar mata da nata aikin
don haka sai hankalinta ya kasu gida biyu, amma wata safiyar asabar da Hadiza ta nufi gidansu don duba
jikin mahaifinta,taga Jummai wasu ƙarti suna dambe zasu saka ta a mota don kai ta gidanta gefe kuma ga
mijin nasu da alama shi ne ya bada umurni sai ta ƙara tsorata don haka ranar da kukanta ta dinga roƙon
mijin nasu wai ya yafe mata insha Allahu ta daina kuma zata zauna da shi fisabilillah, to kun ji Allah yasa
gaske ne.

Tun zuwan farko da ya yi gurin su A'isha bai sake samun sukunin zuwa ba sai wannan karon ita ko taso
hakan saboda dama tana tsoron ciki, zuwan ba zata ya yi mata dawowarta kenan daga lecture ta samu
Uwani tana tuƙa tuwon shinkafa, cikin jin daɗi ta ce Allah sarki Uwani,ke da kanki? Uwani ta ce ƴan nan
na gaji da cin shinkafar nan tuwan semo ɗin nan naku baya ɗaukana shi yasa na ce bari dai ki gani, cikin
dariya A'isha ta ce nima fa ƙuiya ce dani ina son cin tuwon wace miyar ki kayi mana? Ta ce a'a ga dai
tumatur ɗin nan yana dahuwa. dama kiyi mana miyar ganyan nan me ƙara jini, ta ce ogun? Uwani ta ce
shi kuwa, A'isha ta shiga haɗa miyar ji suka yi ana ƙwanƙwasa ƙofa,Tani ce ta buɗe su Hafsat Sulaiman
ne, suna ganin tuwo suka ce sun zo a Sa'a. Uwani tana ta musu tsiya da cewa sai yau ƴaƴan nan ƙwana
biyu kun mana yaji har dake uwata, ta ce ma Hauwa'u. Hauwa'u ta ce karatune ya yi zafi Uwani,sunan
mahaiyarta ne Hauwa'u, A'isha kuwa sunan ƴarta ne ta fari ƴar ma ta rasu amma bata faɗa don kara,kai
dai dai da laraba bata cewa saboda a ranar Laraba ne ta haifi ƴar sai dai ta ce ranar samu.

Duk sun zube a falo suna ƙwasar tuwo, A'isha ko ta ce sai ta yi wanka wai warin zufa take, mai kurum ta
murza ta zuro doguwar riga baƙa ta zauna tana shayar da Abulkhairi sai kuma suka kuma jin ƙwanƙwasa
gida, A'isha ta ce maƙotana ne suma su shigo mu ƙara yawa yau gidana ya yi albarka, na gode da Uwani
ta yi tuwon nan mai yawa,tuni Tani ta je ta buɗe ƙofa tun kafin ya iso falon ƙamshin sa ya shigo da sauri
ta miƙe har ta tsorata ƙawayan nata tare da cewa Uncle da sauri ta fita, suka kalli juna fuskarshi tana
ɗauke da murmushi ta ɗan sakar mishi irin hararar nan ta masoya cikin shagwaɓa ta ce Uncle ba notis?
Ya ƙaraso ya cafki yaronshi cikin jin daɗi, sannan ya ce bana so in kira ki ce min karatu ya yi yawa gashi
ina cike da kewarku,kin san saboda sauri ban zo da Jabiru ba, jirgi na biyo, ta ce sannu da zuwa Uncle
shigo,yana shiga ya samu ɗakin da jama'a sai ya ce muna da baƙi kenan? Ta ce eh,ƙawayena ne ta
gabatar mishi da su da kuma sunayensu, sannan su kuma ta ce musu ga Uncle ɗina dai yau kun ganshi
suka ce lallai kam suka tashi wai za su tafi ya yi ciki tare da cewa suyi zamansu ganin yanda A'isha ta hana
kanta sukuni yi wannan yi wancan Hafsatu ta ce kai Hauwa'u ina zaton Uncle ɗin nan nata shi ne mijinta
baki ga kamar su da yaron ba? Ta ce na lura kuma fa haka ne don yanzun haka ma ta kan ce wa mazan su
kai amma A'isha ta samu cikin ƙwali da harmun kama Hafsa ta ce sosai kuwa, amma fa tayi dace
mutumin ya haɗu Allah da Uncle ɗin ta ne na gaske sai na ce don Allah ta haɗa mu, suna cikin hirar sai
gata za ta je kicin Hauwa'u ta ce ji mana A'isha Musty ta zo tana dariya Hauwa'u ta ce Uncle ɗin ki ya yi

kasuwa Hafsa ta ce ki shigar da ita, A'isha ta ce wuu ba zai ƙara ba, matan shi sun ishe shi, cikin dariya
Hafsat ta ce ƴar wulaƙanci dama Uncle ɗin ne Abban Abulkhairi shi ne kike ta samu cikin ƙwali ko? A'isha
ta juya tana dariya ganin sun harbo jirgin ta.

Ta yi murmushi ganin yanda yake cin tuwon hannu da baka hannu ƙwarya, ta ce Uncle da alama ka jima
ba ka ci tuwo ba ko? Ya dubeta "Beby ba ma tuwo ba,na jima ban ci abinci ba, tun da matsalolin Jummai
suka tsananta wata rana ma yini nake ban sha ko ruwa ba, lamarin ya girgiza ni sai tayi tamkar bata ji
labarin ba ta ce jikinta ne ya yi tsanani? Ya dubeta kina nufin baki san me ke faruwa ba? Ta ce, "Uncle ina
zan samu labarin Katsina, ina Sokoto?" Ya ce na zaci Nafisa ta tsegunta miki, ta ce muna waya amma ba
ta ce min ga wata matsala ba, ya yi shiru can ya girgiza kai Beby na ƙara tsorata da lamarin mata, kuma
na amince sharri tare da kaidin mata ya ɗarar ma na sheɗan, kazalika dole ne su fi yawa a wuta." A'isha
ta ce "haba Uncle ya ya ka ke wannan zantuka ba duka aka taru aka zama ɗaya ba,wai ma duk me ya
kawo wannan batun? Nan ya bata labarin komai, duk da cewa Nafisa ta bata labarin da take jin shi
yanzun sai da ya girgiza ta, ta zuba tagumi cikin hawaye shi kam nasiha ya shiga yi mata da cewa A'isha na
sani ke cikin mata daban ki ke,kin samu tarbiyya tare da yin gadon halayen mahaifanki, amma ina so ki
ƙara zama cikin mata salihai,abin koyi kada ki amince ruɗin duniya ya ja ki ga halaka, duk duniyar guda
nawa ce? Duk sonka da ita wata rana sai ka barta, tare da duk abinda ka tara daga kai sai halin ka zaka
tafi, abinda Jummai ta kasa ganewa kenan, yanzun wa gari ya waya? Mai sammako inji ƴan magana,
A'isha ta nisa ta ce to yanzun tana ina? Ya ce tana nan gidan sai dai ba a buɗe ta don ƙwanaki da ta
ƙwace sati huɗu ana nemanta sai da ƙyar aka ganta hauka tuburan fa. A'isha ta ce, Allah ya bata lafiya,
sannan don Allah ina roƙon mata arziƙin ka yafe mata ta ji da na sauran,ya tsura mata idanu sannan ya yi
murmushi, A'isha ina son halayan ki to har zuciyata ta ci albarkacin ki na yafe mata nawa laifin, shi
kenan? Ta ɗaga gira suka yi ƴar dariya.

Kafin ya dawo sai da A'isha ta tabbatar da cewa babu sauran wata damuwa cikin zuciyarshi na shi ganin
har wata ƴar ƙiba yayi, A'isha kuwa dariya ta ringa yi mishi lokacin da ya iso gida Hadiza ta tare shi da
nata salon tarairayar.

Yau da gobe lokaci yana tafiya,ƙwanaki na shuɗewa haka satittika da kuma watanni har su A'isha sun
sami ɗan hutu suna ƙarshen shekara, sun iso gida cike da ɗokin ganin ƴan'uwa.



#######

[12/22, 23:34] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 13*




Uwani garin su zata wuce don duba dangi haka ma Tani, Aisha kuwa gidan su da suka koma aka wuce da
ita,tsarin gidan yafi nasu na da, haka nan kowace da gefenta babu abinda zai haɗa wata da wata, komai
sabo ya zuba mata, Hadiza har da yin girki don taran A'isha. Tabawa kuwa ta turo baki ta ce in dai kishiya
ce fa baza kiyi gwaninta ba, Hadiza ta ce don Allah Tabawa ki ƙyaleni,ni na gaji da halinku, Tabawa ta
kuma taɓa baki,nan gaba za ki kuma neman mu,kin kama tashar daji in dai kishiya ce,ta fita waje.


Cikin ƙwanakin suna zaman lafiya da juna, Hadiza ko yaushe tana shigowa gurin A'isha musamman in ba
ita ce da miji ba, sai dai ganin yanda A'isha ke kula da mijinta da yanda shi kanshi ke ji dasu ita da ɗan ta
sai ta kasa daure ma zuciyarta,in ta koma gurinta sai ta yi ta ƙunci wannan damar Tabawa ta sake samu ta
dinga zuga Hadiza tare da cewa in fa Aisha na gidannan ta bar Samun soyayyar mijinta har abada, sai dai
ƙunci ya kashe ta, Hadiza ta ce bana son in koma gurin maƙaryatan Malaman nan ne,sun jima suna ce
min A'isha zata fita ba zata haihu ba menene, menene,sai gashi duk babu abin da ya faru,a ƙarshe ma ita
ce ta haihu. Tabawa ta ce tuni da kin yarda tun dawowarta da tuni mun soma shirya mata kissa, tunda ba
ki son Malaman, Hadiza ta ce kada ki shirya min ramin da zan rufta, Tabawa ta ce kajiki da wani tunani,
duk abubuwan da muka shirya can baya wanne ne ki ka rufta? Hadiza ta ce shikenan.

A'isha tana kallon su tana dariya, Uncle ne shi da ɗan shi suke rigima, ya rarrafa ya janyowa Uncle ɗin
waya daga chaji ya jefar sannan ya hau kan kujera ya zauna kan laptop ya hana Uncle ɗin aiki, ya dubi
A'isha Beby zo ki ɗauki yaron ki ya hanani aiki, A'isha ta ce tayaka fa zaya yi Uncle, ya dubi yaron Babana
je ka gurin Mominka, A'isha tana tasowa yaron ya ƙanƙame uban ta koma tana musu dariya, ya ce kina
dariya ne ma ko kin ƙi ɗauke shi in gama ko? Shima ya yi ƴar dariya tare da rungume yaron dama muna
magana ne kan tafiyar ki aikin hajji, tunda ba zaki riƙe shi mu gama ba shi kenan. Asha wasa ko yaron
Baba?" Da sauri A'isha ta tashi ta cafke yaron zo kada kasa in ga samu in ga rashi, ta zauna kusa da shi
tare da dafashi gaske ne Uncle ɗina? Ya ce kalli ki gani lis ɗin sunayan waɗanda zasu tafi aikin hajji ne
sunan waye farko? Ta kalli screen ɗin laptop ɗin, Beby ta gani farko cikin murna ta ƙwantar da kanta a
kafaɗarshi tana cewa na ji daɗi bari na gani su waye sauran nayi musu albishir koda in samu tukuici, daga
sunanta sai nashi ta dubeshi kai fa duk shekara sai ka je ya ɗora yatsanshi kan leɓanta ke zan raka ta ci
gaba da dubawa, sai sunan mahaifanta biyu da yayanta Abdulrahman sai Nafisa da Uwani mai aikinta
sauran kuwa bata san ko su waye ba,ƙila cikin danginsu ne. Ta dube shi ban san da wane baki zan maka

godiya ba Uncle, ya ce kawo kunnanki ki ji dame za ki bani tukuici, ta miƙa kunne ya raɗa mata, dariya ta
shiga yi sannan ta ce ka samu ban ga Hadiza ba, ya ce kin san dai ance Hajji kiran Allah ko? Ta ɗaga kai ya
ce to Allah bai kira ta ba, A'isha ta ce to Allah yasa tana da rabo nan gaba, ya ce Amin.

In kin je me zaki roƙa? Ta ce Sa'a a karatuna sai kuma gamawa lafiya, tare da samun ƙyaƙƙyawan ƙarshe.
Ya ce ni duk shekara haihuwa nake roƙo, ta dubi Abulkhairi da ke bacci a jikinsu, sannan ta ce Uncle ba
gashi ka samu ba, ya ce ni da nike son dozin biyu Beby kina da sauran aiki fa, ta ce wai ba zan iya ba ana
shan wuya fa sosai,ni dai wannan ya isheni, ya zuba mata ido, Beby ba ki yin tsarin iyalin nan ko? Ta ce
me yasa ka ce haka? Na gane shiru, ta ce Allah tunda ka ce baka so an wuce gurin, ya ce shi kenan. Ta
miƙe da yaron a kafaɗarta bari in shinfiɗar da shi ka ƙarasa ina zuwa yau zaka sha tukuici, murmushi ya yi
tare da cewa Beby.

Tabawa wadda ke maƙe tana kallo tare da sauraron duk abinda ke faruwa tsakanin ma'auratan, ta riƙe
baki sannan saɗaf-saɗaf ta bar gurin tana tafe tana tafa hannu gami da riƙe haɓa, irin na wanda ya ji ko
ya ga abin mamaki, har Hadiza ta soma bacci Tabawa ta tashe ta,tashi-tashi Antyna wato ma bacci ki ke yi
ke,ni ina can gurin neman zaman lafiyarki. Ta ce Tabawa na ƙi bacci tunda ke kin je kin yi zamanki?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0