Showing 6001 words to 9000 words out of 38755 words
Chapter 3 - Mummunan Zato Book 3 Complete Halina Mashi
ki Hajjaju? Ina
fatan dai aikin naki ya yi ƙyau, ta ce fiye ma da yanda na zata, shine dalilin da yasa na kawo Aminiyata
domin tata matsalar ta doke tawa,Malam ya jinjina kai ya miƙa ma Jummai ƙaton carbi tare da cewa
gashi ki ɗauki ɗaya, har sau uku tana zaɓa sannan ya bubbuga charbin a ƙasa ya riƙe shi jim ya ce Hajiya
kina da abokan zama, kuma ba ƙya buƙatar zama da su ko? Ta gyara zama, hakane, ya ce ya ya
sunannasu? Ya jawo tiren ƙasar gabanshi ta ce "Malam Hadiza da A'isha, amma nafi son komai ya fara
takan A'isha,don tafi shige min gaba,na tsani yarinyar sosai. Ita ce ta soma karya min gwiwata, ta karya
min shirina a cikin kishiyoyin da ake min ita ce ta fara kai labari har ma ta buɗe fagen da aka ƙara min
wata kishiyar, cikin zafin rai ta ke maganar. Malam ya ɗaga mata hannu ya ce, bari mu bincike su mu gani,
ya ɗan jima yana zane zananshi da ƙasa cikin farantin, ya yi ya share,yana girgiza kai har ya gama, ya ɗago
kai ya dube su, dukkan su sun ƙagauta da son jin sakamakon. Ya yi gyaran murya ya zuba musu idanu tare
da fara yi musu bayani kamar haka.
"Wato ita wannan A'ishan da ki ke faɗa ta banbanta da sauran mata da yawa, tauraronta yasha banban,
wani tauraro gare ta mai ƙarfi wanda yana wahala in kin tara mata dubu da wuya ki samu ɗaya mai irin
shi, duk wadda ta kasance tana da wannan tauraron yana wuya ayi mata sihiri ya kamata, sannan duk
inda ta shiga zata kasance mutane na sonta don zata kasance mai ƙwarjini,kin ga ke nan dole ta fi ku
samun shiga gurin maigidaku,da ma danginsa." Jummai ta soma share zufa, "to yanzun Malam ya ya
za'ayi mata?" Ta ci gaba, "shi yasa nike ta tafka asarar kuɗina?" Malam ya ce, wannan shine gaskiyar
magana, batun abinda zamuyi mata kuwa sai dai mu haɗa da maigidan naku in muka biyo mata ta bayan
gida zai fi mana sauƙi, ita ko waccan yanzun zamu duba muku ita." Jummai ta yi karaf ta ce, "Malam ita
ce muka ga sun fito daga nan ita da Hajiya Lanti." Ya zuba mata idanu, "kina nufin Hadizar Lanti ce ɗayar
kishiyar taki?" Ta ce "Eh." Ya yi ɗan murmushi, "wannan nasan kowace ce bana buƙatar duba komai
kanta."
Hajiya Kari ta ce," To amma hakan ba zaya hana ayi mana aiki ba dai ko?" Ya yi ɗan murmushi, "Sam illa
dai wadda tafi ƙin jakarta aikinta ya tafi dai dai,in ko mutum ya so jakarshi nima in riƙe aikina." Jummai ta
buɗe jakarta ta ciro ɗaurin ƴan dubu-dubu ɗai-ɗai ta dire gabanshi,sannan ta ce Malam me ya kawo
Hadiza? Ina nufin da wace buƙata ta zo?" Duk da ba tace kuɗin na shi ba ne ya saka hannu ya ɗauki kuɗin
ya juya su, sannan ya aje gefenshi ya ce,ta zo ne da buƙatar korarku,burinta shi ne ta mallake gidan da
maigidan da dukkan abinda ya mallaka." Jummai ta yi murmushi, sannan ta ce, "Ni ko banƙi ace duk sun
rasa rayukansu ba, amma yanzun Malam na baka zaɓi me ka ke ganin za'ayi musu? Sannan ina son duk
aikinta kar a mata cikin da ta ce tana da shi a zubar, sannan in ta zo da wani bayani in sani, kullum a dinga
yi min binciken kome suke ciki." Malam ya ciro kuɗin da ya ajiye a gefe ya ce duk a wannan kuɗin? Ta ciro
irin su ta aje mishi sannan ta ce, "Me za ka bani in soma dashi yanzun?" Hajiya Kari ta ce, "Malam ka
mata wanda zata san kai me yi ne ba irin waɗanda da an ce ga buƙatar da ake so sai su hau cewa Allah ya
ce ba, yayi wata dariya sannan ya nuna Karima ya ce, "Ai ke kin sanni, wata roba ya ciro fara cikinta wata
ƙatuwar tsoka ce gata nan kamar zuciya,ya miƙa mata kin san wannan? Ta girgiza kai,zuciyar mutum ce ta
zaro idanu ya ce riƙe da ƙyau aikin wani da zan yi shi ne na fasa zan baki nasa a ciro min wata." Ta ce "a
jikin mutanan ake cirowa? Ya ce to da ina za'a samu? Ta tsorata Malam da sassan jiki ka ke aiki? Kari ta
katse ta tsoron me zaki ji bayan ke kanki rai nawa ki ka salwantar? Jummai ta ce amma ban taɓa amfani
da sassan jikin mutum ba,Malam ya miƙa mata hannu bani in kina ganin ba zaki iya ba ne, ta ce, "zan iya
Malam, yi haƙuri." Ya miƙo mata wata leda tare da cewa, "buɗe ki gani."
Wasu allurai ne cunkus cikin wani gari baƙi, ya ce " Guda ɗari ne da ɗaya, kullum ki dinga tsira ɗaya jikin
wannan zuciyar,in zaki tsira ki ambaci sunan maigidanku sannan cikin zuciyarki ki ƙudurce cewa aikin yi
ci, kada kiyi wasi-wasi da zaran kin yi wasi-wasi aikin ba zai ci ba, sannan aikin za ya yi tasiri ne kan
maigidanku, duk wadda ki ka soma tsira alluran da nufinta cikin kishiyoyin to ita kaɗai ce zata samu
matsala da mijin naku.
Sannan aikin mutum ɗaya ne,ɗayar za'a mata nata daban, ta ce to wannan na A'isha ne? Ya ce
shikenan,in kun dawo zan baki na ɗayar, sannan kada ki ƙagara fa, don yanda kike soka allurar nan da
ƙaɗan-kadan haka aikin zaya dinga ci da kaɗan-kaɗan,ta ce shi kenan, sannan kada ki ajiye inda za'a gani
fa, ta ce to.
A'isha tana ƙwance sai zabga Game take yi, cikin wayarta sam bata ji shigowar Uncle ba,sai...
#######
[12/19, 15:33] Ummi Tandamaí ½í¸‡: *í ½í³”í ½í³” Page 4*
Sai da ta ji an ja mata yatsa da sauri ta tashi tana faɗin Hasbunallahu wani'imal wakil" Ganin Uncle yana
mata dariya sai ta tashi tana dariya, ya ce,"Beby kin cika shegen tsoro." Ta miƙa mishi kofin ruwan cikin
risinawa tare da ladabi ya amsa cikin farin ciki sannan ya zauna a hannun kujera yana sha,ta zuba mishi
idanu, komai na Uncle birge ta yake yi, ya ɗago idanu ya kalleta ta yi murmushi shima yana murmushin
ya ce kin san dame nazo miki? Ta girgiza kai, ya buɗe jakarshi ta Office ya fiddo takardu ya miƙa mata,sai
ki zaɓi garin da ya yi miki, duk dai makarantun suna da ƙyau, cikin murna ta shiga dubawa ta dube shi
cikin ɗoki Uncle zaɓa min Kano ko Sokoto,ko A.B.U za ni? Ya dinga yi mata dariya, kafin ya ce ke wacce ya
fi ƙwanta miki cikin su? A'isha ta yi shiru alamun tunani,can ta ce Sokoto ko Maiduguri, ya ce gara ma
Sokoto, amma Maiduguri ya yi nisa sosai, daga nan. To shikenan Uncle na gode, cewar A'isha kenan.
Cikin abinda bai fi sati biyu ba, Uncle ya ɗauki A'isha, Jabir ne ke jan su sai Sokoto.
Masauki ya kama musu cikin wani shahararren Hotel. Suna sama Jabir kuma a ƙasa, ya kama mishi
ƙwana biyu suka gama amma yanda Uncle ke samun kulawa gurin Bebyn tashi, sai ya kasance tamkar
kada su dawo,don haka suka ƙara ƙwana uku ita kanta A'isha ta rubuta waɗannan ƙwanakin cikin
zuciyarta.
Bayan sun dawo sai kuma aka shiga shirin tafiya makaranta, sannan ta ziyarci Jigawa ƙwananta biyu su
Hajiyarmu da su Anty Fati duk tayi musu yini,nan ne ma Nafisa ta bata lambobin wasu ƙawayanta,kan
cewa zata haɗa su ƴa Sokoto ne, kuma duk ba su da nisa daga makaranta. A'isha ta ji daɗi,dama bata san
kowa ba, Nafisa ta sake tabbatar mata cewa zata ji daɗin zaman makaranta,don ita ma nan ta gama,ta ce
mata waɗannan ƙawayan nawa wayayyu ne musamman harkar riƙe miji,ba ma kamar Maimuna ɗin nan ,
A'isha ta yi godiya tare da shan alwashin neman su, A'isha ka bata wasa da duk hanyar da ta ji an ce in
tabi zata ƙara samun kusanta da mijinta matsawar ba hanyar saɓon Ubangiji ba ce.
Komai na ƴan gata Uncle ya haɗa mata, wani gatan ma sai da suka isa garin Sokoto,dama gida ya kama
mata, cikin makaranta ƙwanansu biyu a hotel yasa ana ta gyaran gidan sai ka ce gidanshi,kaya yasa aka
siyo aka shirya gidan tamkar sabuwar amarya ya zuba mata komai sabo ga kayan wuta har da laptop ɗin
ta sabo, ya shirge mata abinci, shima sai da ya ƙwana a gidan sannan suka je ya buɗe mata account,
tamkar kada su rabu lokacin da zai tafi, A'isha har da kuka.
Ya samu dai ya lallasheta, tare da yi mata nasihohi, sannan ya tafi. Ta koma ciki tana kallon falon, yanda
ya tsaru ta shiga bedroom ɗin ta faɗa kan gado,duk kewar Uncle ta dame ta,ita dai a rayuwa ta gode ma
Allah,don bata isa ta ce ga abinda Uncle ya yi mata ba a tsawon rayuwarta a gidanshi,ta sani Uncle
rainonta yake burinshi kullum ya faranta ranta,ya ji da ita daɗi, ya fidda ta tsara cikin ƙawayanta, Uncle
koda wasa bai taɓa yunƙurin ɓata mata rai ba,ko ta ko'ina abinda take so shi zata ci shi zata sha shi zata
sa hannun iyayanta. Ta kula ko gurin auratayyane burinshi yaga ta shiga nishaɗi, shi yasa itama ko yaushe
ba ta da burin da ya wuce mishi biyayya tare da neman hanyoyin ji da shi daɗi daga ni'imar da Allah ya yi
mata. Kafin ya isa gida sun yi waya kusan sau goma, shi ya kira itama ta kira,shi kanshi bai san ya yi
kewarta haka ba sai da ya yi ƙwana biyun shi na sauran matan da ace tana nan da yau ita ce da shi,a
zuciyarshi A'isha daban ce yana sonta,tana kula da shi tana da baiwar da ba duk mata ba,in yana kusa da
ita ya kan manta da duk wata ƴa mace a duniya. Addu'a kullum yake mata, Allah yasa da ta da
rahamarshi duniya da lahira. Haka dai ta dangana ta rungumi karatun ta ka'in da na'in.
Jummai da Hadiza kuwa, duk sun miƙa lamarinsu ga boka, ko in ce ɗan tsibbu. Jummai kam yanzun ta
yarda Malamin nan zai share mata hawaye da A'isha ta jima tana sa ta zubarwa,ta gane hakanne lokacin
da ta tinkari Alhajin da maganar son ya yi mata ginin da ya jima yana son mata a cikin gidan, daga baya ya
share zancan. Alhajin bai Musa ba, ya ce zai sa a auna gurin duk dai da cikin gidanne. Malamin ya ce ta
haɗa da ladabi da biyayya, don haka yanzun wani sabon ladabi ta samo.
Hadiza kam tafi ga magungunan mata irin waɗanda ke saka maza fitina, gashi ta ƙware gurin iya jan
hankalin namiji,takan zuba mishi cikin ruwa ko abinci in ya ci kuma ta zo da salon tana jan hankali. Ba za
ya iya haƙura ba,don haka sai ta sara mishi kuɗi haka zaya bata sannan ta yarda suyi auratayya
wa'iyazubillah. Hadiza ba wai ƙyaƙƙyawa ba ce, amma irin matannan ne waɗanda suka san kan shawo
kan maza,ta hanyar fizgar hankalinsu ta iya ƙwarƙwasa sosai, shi kan shi ya so ace A'isha ce ke mishi irin
salon jan hankalin da Hadizan ke mishi.
Tuni an soma ginin Hajiya Jummai, gini ne za'ayi shi me tsari, shi kan shi ba zai ce ga dalilin da yasa ya
ƙuƙe kan cewa sai an yi ginin cikin ƙanƙanin lokaci ba. Hadiza ta dame shi da son sanin wanda zai shiga
ginin sai ya ce mata me rabo.
Yau kimanin ƙwana sha huɗu kenan A'isha ta yi a makaranta, har yau bata saba da kowa ba, kasancewar
ta mara saurin sabo,gata miskila bata cika sakin fuska ba,ran da ta cika ƙwana huɗu ranar ta nemi
Maimuna ƙawa Anty Nafisa izuwa yanzun sun saba sosai,in bata da lakca can takan je ta yi hirarta,
Maimuna wayayyiyar ce ta gaske,tana ganin A'isha ta ga cewa A'isha ta yi mata,tana koyar da ita
salo-salon yanda zata da kanta da mijinta,kai har da yarda zata dinga yiwa mijinta magana, tafiya da dai
sauransu. Wani kunun Aya,dabino da cukwi da take bata mara suga sai madara,ga wata gumba da take
dama ta da madarar shanu, A'isha da kanta ta ji tana sha'awar mijinta. Yau kam da ta je ƙin sha tayi ta ce,
Anty Maimuna Uncle ba ya kusa gashi kina ta bani waɗannan abubuwan sai su dame ni fa, Maimuna ta
ce ke baki san yanda zaki jawo hankalinshi ya zo gareki ba ko? Nan ta shiga tsara mata yanda zata yi,
sannan ta bata garin bagaruwa ta ce ta ringa tsarki dashi in taji ranar zuwan nashi kafin ya iso.
yanzun haka da take ƙwance kan gadonta kusan ƙarfe goma tasan yanzun yana gida gaban laptop domin
lokacin ƙwanciyarshi bai yi ba. Ta shiga murza wayarta shi take nema,jim kaɗan layin ya shiga ta juya
rigingine, muryarshi ce ya ce "Beby" ta ce na'am Uncle ya ya ka ke? Ya ce lafiya lau ke fa? Ta ɗan runtse
idanu ta buɗe sannan ta ce ina cike da kewar ka,ya cire gilashin idonshi tare da matsar da laptop ɗin,
A'isha nima haka,ta ce,kai ai kana da wasu matan, ya ce, Beby basa min rainon da ki ke min, ba tonon
asiri ba ne ko yi dasu,ke daban ce wancan satin fa da kin ganni al'amura ne suka yi min yawa, da kuma
tunanin kada ki ce wannan Uncle ɗin ya nace min. Ta yi ƴar dariya cikin kissa sannan ta ce "Uncle ɗina
kenan,kana ganin in da zaka zo kullum zaka gundure ni ne?" Cikin mamakin ta ya ce, Beby sai ina ga
tamkar ba ke ba, Beby da ba ki iya gaya min yanda ki ka damu da ni ba, da zaran abubuwa sun yi sauƙi za
ki ganni." Ta ce, to sai da safe, ya ce zan zo miki cikin mafarki kinji, ta ce sai na ganka. Sai ta samu kanta
da sumbatar wayar tare da saurin kashe wayar. Sautin kiss ɗin ya daki dodon kunnanshi ya ratsa dukkan
jikinshi. Haƙiƙa ta saukar mishi da kasala,yana jin ba za ya iya ci gaba da aikin gabanshi ba, dole ya rufe
komai ya tashi. Ita kuwa juyi ta yi tana jinjina ma ƙoƙarin da tayi tasan in a gabanshi ne duk da Anty
Maimuna tana bata ƙarfin gwiwar ta ringa mishi hakan ba zata iya ba.
Washegari wuraren ƙarfe shida lokacin ta fito daga lakca don ranar uku da mintuna suka shiga, ta buɗe
gidanta ta shiga dama ta riga ta yi abincinta, magriba kawai zata yi sannan ta ci. Zaman ta kenan sai ta ji
ana ƙwanƙwasa mata gida ta je ta buɗe. Wasu ƴammata ta gani su uku, suka nuna mata wani gida kusa
da nata,ga gidan mu nan munce ne bari mu shigo mu gaisa, cikin fara'a A'isha ta ce ku shigo ta matsa
suka shiga.
Abinka da wayayyun ƴan boko,nan suka sake, ita dai taje tayo sallah ta basu abinci suka ci har suna santi,
nan suka sanar da ita sunayensu. Saliha da Amina,Kiristar kuma Linda ƴar kaduna ce,su kuma biyun nan
Sokoto suke,suma course ɗin da take yi shi suke yi. Tana zaune dai ta ma kasa cin abincin don bata sake
da su sosai ba,su ne dai sukayi tamkar dama sun santa, sai ta ji ana bugun gida, ta kalli agogo cikin
zuciyarta ta ce to ko wanene kuma, ƙarfe baƙwai da rabi,ta fita tun kafin ta buɗe ta ji ƙamshinsa, cikin
hanzari ta buɗe tare da cewa, Uncle tafiyar dare? Jawo ta ya yi zuwa jikinshi ya rungume, tare da faɗin I
miss You Beby, ta amshi Jakar hannunsa "zo mu je Uncle kai kaɗai ne? Ya ce ni da Jabiru ne, sai da na kai
shi masauki sannan nayo nan. Anan nayi magriba da isha'i, suna shiga falon ya yi turus yana kallon ƴan
matan da ke zaune, fuskarshi da alamun tambaya, ta ce maƙotana ne suka shigo don mu saba,ta dube su
ga Uncle ɗina, nan suka shiga gaishe shi kafin suka miƙe suka ce sai da safe A'isha Mustapha, ta ce na
gode. Ya zauna nan ta shiga rawar jikin kawo mishi wannan da wancan,shi kam duk in da tabi kallonta
kawai yake yi yana sonta.
Yana cin abincin suna hira tana mishi mitar zuwan ba zatan da ya yi mata, gashi bata mishi wani abu na
musamman ba, ya ce shi ai ita ce ta musamman ɗin shi, cikin ƙwanaki ukun da ya yi a Sokoto ya kuma
yarda A'isha ce kurum ta dace da rayuwarsa. Haka ya taho da kewar ta itama tana kewarshi, haka
abubuwa suka yi ta faruwa lokaci ya dinga zuwa yana wucewa, Uncle yana ziyartar A'isha duk bayan
mako ɗaya ko biyu.
Ƙwatsam! Wannan zuwa ya sameta ta tana fashin sallah, kuma ranar ta fara, da ƙyar ta lallasheshi ya yi
ƙwana biyu tare da gamsar dashi ta hanyar wasu ƴan dubarun nata.
Wani sabon al'amari tun daga lokacin sati na huɗu kenan rabonshi da Sokoto, sannan wayar ma yanzun
ba kamar da ba, kullum uzurin yake bata wai abubuwa sun mishi yawa gashi ana gyaran gida, daga baya
ma in ba ita ce ta kira shi ba shi kam baya da lokaci. Abin ya soma ba wa A'isha tsoro,nan gefe kuma ga
wata matsala da ke damunta. Motsi cikinta ke yi,ta sa rai ya zo ta sheda mishi, amma shiru suna daf da
fara jarabawa abin ya matsa mata don haka ta kira Nafisa ta sheda mata,Anty Nafisa ta ce baki gaya ma
Uncle ɗin ki ba? A'isha bata son saurin tona cikinta nata ganin gaske ne uzuri ya yi wa Uncle yawa ne, shi
yasa har yanzun bai zo ba,ba zata yi saurin kai ƙararshi ba, ta ce abubuwa sun yi ma Uncle yawa bana son
na gaya mishi zaya tada hankalinshi, ya ce zai bar aikin gabanshi ya taho. Nafisa ta ja tsaki,wane abubuwa
ne suka mishi yawa baya ga komai da ya tsaida, Ya shiga harkar yiwa Jummai gini. Gabanta ya faɗi