Showing 12001 words to 15000 words out of 38755 words

Chapter 5 - Mummunan Zato Book 3 Complete Halina Mashi

09 Jul 2025

2073

ce ko shi ke gare ki? Ta ɗaga kai. Ya miƙe da sauri ina ki ka samo shi? Jin furucin shi yasa
ƴan hanjinta juyawa me Uncle ke nufi? Bata ankara ba sai ta ji ya cakumi wuyan rigarta, abinda za ki min
kenan ko A'isha ya ɗan tausasa murya,kin dai san zuwana gurinki na ƙarshe kina haila ko? Muryarta tana
rawa ta ce eh, amma bai san sanda ya ɗauke ta da wani wawan mari ba,amma me? Ya hankaɗata kan
gado kin cuceni don ina neman ƴaƴa ido rufe shi kenan sai a kawo min shege? A'isha kin yi kuskure
yanzun so nake ki gayan uban da ya yi miki cikin? Kuka take yi sosai tamkar ranta zai fita, ina ma ta mutu
ta huta da wannan baƙin cikin? Ya ce zaki gaya min ko sai ranki ya yi mugun ɓaci? Jin shi yake tamkar ya
shaƙe ta ta mutu ya huta, ya dubeta a zafafe,kiji nan kafin da safe kiyi ƙoƙarin sanar da ni kowanene ya yi
miki wannan cikin,ya juya fuu ya fita tare da bugo ƙofar.

Ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un,wane irin mummunan zato ne wannan Uncle za ya yi min? Ta ci
gaba da kuka,ya ma ƙi ya saurare na, yau shi ne har da marinta,to ko dai ya daina sonta ne? Shin dama

haka ne maza ke yi? To in haka sukeyi me yasa Abbanta ba ya yi wa Ummanta haka? Ta tsorata da lamarin
Uncle bata san me zai mata ba washegari cikin kishiyoyi,gara ta san nayi tun yanzun.

Fitar Uncle Tabawa ta miƙe cikin motoci domin tana laɓe tana sauraron duk hidimar da ake yi,jin Uncle
zai fito ta ruga ta ɓoye,da gudu ta nufi Hadiza tana faɗin. "Antina zo ki ji." Ta shiga rattafo mata duk
yanda ta ji, ta ce matar so har da mari ta sha,kin san ta dai dai wundon su na uwar ɗakin na maƙale, ciki
tayo can a makaranta an zo a yaudareshi sai kuma Allah yasa ya gane. Hadiza ta ce kai Tabawa? Tabawa
ta ce na taɓa kawo miki wani labari daga baya ki kaga ba haka ba ne? Hadiza ta dafa ta,ko sau ɗaya ba'a
taɓa haka ba . Tabawa lallai ki ce lokacin fitar wannan matsiyaciyar matar ya yi,dama nafi jin haushinta
sai inji da waccan guzumar ta bar gani yanzun tana jan zare na barta da ma in gama da wannan ne kai
naji daɗin wannan labarin Tabawa zan baki goro da safe amma yanzun bari in je gurinta a zuwan na zo in
yi mata sannu da zuwa ne, Tabawa ta ce kin yi daidai tama san an sani.

Lokacin da Hadiza ta shigo ta same ta tana kuka da sauri ta ƙaraso, lafiya A'isha? A'isha ba taji shigowar
Hadiza ba sai dai ta ji magana akan ta, ta ce cikina ke ciwo. Hadiza ta ce assha to bari in kira Alhajin a
waya. A'isha ta ce ai ya sani ya tafi ya zo min da Likita,harara Hadizan ta sakar mata shi ne zai je yazo da
Likitan? A'isha ta ɗaga kai, Hadiza ta ce, Allah ya sawaƙe ta fita. Ta je gurin Tabawa tana cewa Tabawa
gaske ne kuwa labarin da ki ka bani? Tabawa ta ce me ki ka gani ke? Hadiza ta bata labarin yanda suka yi,
Tabawa ta ce to ke da kin zauna ne ta faɗa miki? Ko ance miki kowa ma irin ki ne? Hadiza ta ce ƴar iska ni
zata yi wa bariki,ai muna cikin gidan ma ga yanda za a ƙwashe.

Shi kam fitarshi ke da wuya ya nufi sasan Jummai,tana zaune tana tunanin kada dai ta tura shi yaje kuma
komai ya daidaita tsakaninsu? Kai ina ba zai yiwu ba, domin ta yarda da Malam ɗari bisa ɗari. Sai ko ga
Alhaji ya shigo tamkar wani bijimin zaki, da sauri ta miƙe Alhajina lafiya? Ya zauna yana huci, ta ce kayi
haƙuri ko mene ne ya ce wane haƙuri zan yi? Ya ci gaba, wallahi ba zan haƙura da cikin da ba nawa ba,
Jummai ta zaro idanu tare da dafa ƙirji ban gane ciki ba? Ya ce A'isha mana yarinyar nan zuwana na
ƙarshe gurinta fashin sallah na samu tana yi, yanzun sai gata ta zo min da uban ciki don ina neman
haihuwa shi kenan sai a kawo min shege? Zufa ce ta shiga keto ma Jummai,domin tana tsoron kada a
juya a sake juyawa cikin ya zama na shi,ai ko da ta shiga uku.

Ta juyo tamkar ta zuga shi, amma Malam ya ce mata babu wannan aikin ta ba zai tafi da zuga ba sai da
kissa ta daure ta ce to Alhaji ko dai zuwan naka na ƙarshen ne ta samu cikin? Ya dubeta ta tana hailar ne
za ta samu cikin? Jummai ta kuma jan dogon numfashi,ka dai a hankali, ya ce ke ni fa ba batun hankali
cikin wannan lamarin, ta ce to ni bana sone ka ce zaka rabu da ita,ga mamakinta sai ta ji ya ce babu
batun rabuwa amma sai na ji uban da ya yi mata wannan cikin,shiru Hajiya Jummai ta yi ilahirin jikinta
kuwa rawa yake yi. Ta daure ta ce in ka samu wanda ya yi cikin tunda mu musulmai ne sai ka tuntuɓi

malamai, ya dube ta ke ce kika fini sanin yanda zanyi? Ta ce a'a ya ce ki bar ni ya miƙe ya nufi gefenshi.
Da kallo ta bi shi,takan rasa gane kanshi wasu lokutan itama ɗaki ta shiga ta kira Karima Aminiyarta, don
jin wane mataki ya kamata ta ɗauka don cikin nan ba ƙaramin firgita ta ya yi ba.

Tsam, ta miƙe ko jakar ratayawa bata ɗauka ba domin tasan babu ko taro ciki, ta nufi barin gidan tun
kafin gari ya waye ya yi mata tijara, gidan Anty Nafisa ta yi nufin zuwa saboda yanzun dare ne.

Da safe sai ta amshi kuɗin mota a hannunta ta nufi garinsu. Kafin ma ta iso babban titi ta samu mai
mashin cikin mintuna suka isa gidan Nafisa sai da ya jira ta shiga ta amso mishi kuɗin. Mamakin ganin
A'isha ya hana Nafisa zama har A'ishan ta dawo daga gurin mai mashin ɗin in da suka shiga ɗakin
baccinta suka zauna bakin gado, Nafisa ta zuba ma A'isha idanu lafiya kuwa? A'isha ta nisa hawayen yana
zuba daga idanunta,ta shiga rattafo ma Nafisa halin da take ciki da kuma wanda ta shiga yanzun nan,baki
Nafisa ta saki tana kallon ta, lamarin kamar almara, ta ce shi da kansa Brother ya ce ba cikinsa ba ne?
A'isha ta ce wallahi ya ma ƙi ya tsaya ya saurareni, balle ma yasan ga yanda Ubangiji ya juya lamarin cikin.
Nafisa ta ce ni ko naji mamaki, amma yanzun yanda za'ayi bari in kira Anty Fatima ba zaki tafi gida ba,nan
take ta shiga kiran layin Anty Fatima ko gaisawa ba su yi ba ta shiga sanar da ita abinda ya faru, cikin
tsananin mamaki Anty Fatima ta ce,kada ki bar ta ta tafi zan zo da safe.

Ranar dai A'isha bata runtsa ba,ƙwana ta yi kan sallaya tana me zubar da hawaye, tare da sanar da Allahu
matsalolinta. Ko kusa bata so ta tsani Uncle shi yasa take yawan ba shi uzuri, yanzu da haka zuciyarta na
bata tabbacin in yaji yanda lamarin ya kasance za ya yarda da ita,ƙila ma ya bata haƙuri.

Shida daidai na sai ga Anty Fatima, ta tausayawa A'isha matuƙa yanda taga yarinyar ta ƙare ta fita daga
hayyacinta. Nan Fatima ta shiga faɗa tana cewa, lallai Brother irin tsirfar da ya kama kenan Nafisa ta ce
kin san ba haka yake ba,ni dai na ce ba haka aka barshi ba. Fatima ta ce shi dai ya sani yanzun dai ki tashi
muje gidan Hajiyarmu ke Nafisa tunda mijinki ba ya nan ki zauna duk yanda aka yi zaki ji. Nafisa ta ce
muje kurum babu wata matsala zan masa waya ai baya gari ne. Fatima ta ce shikenan mu je, cikin matar
Anty Fatima suka tafi. Hajiyarmu ko tashi daga kan sallaya bata yi ba,ta ji sallama ta ɗago idanu ta dube
su, suka zauna kan kafet suka jira har ta shafa, sannan ta dubesu ta ce lafiya? Nafisa ta ce da sauƙi,
Hajiyarmu kallon A'isha kurum take yi. Anty Fatima ta ce wallahi Hajiyarmu Brother ne ya taso A'isha fa,
gidan Nafisa ta ƙwana,jiya,-jiya daga dawowarta daga makaranta har an soma tsiya. Nan ta shiga rattafo
ma Hajiyarmu Nafisa tana ƙara bayani, Hajiyarmu tayi shiru ɗakin ya yi tsit suna sauraron hukuncin da
zata yanke. Ranta ɓace amma ba kasafai mutane suka cika gane ɓacin ran nata ba sai ƴaƴanta, ta dube su
Nafisa ke da Fatima ku tashi ku koma gidajenku ita A'isha ku barta nan suka ce to, suka miƙe suka fito
bayan sun yi musu sallama.

A'isha tana can maƙale gefe, Uwani ta shigo ɗauke da karin kumallon Hajiyarmu, ta dire a gaban Hajiyar,
Hajiyarmu ta ce A'isha me ki ke son ci?

A'isha ta ce, sai anjima yanzun bana jin yunwa, to kurum Hajiyarmu ta ce bayan fitar Uwani, Hajiyan ta ce
A'isha ki zama jaruma ba ki ga komai ba game da halin namiji,in zaki bincika duk matan duniya komai
matsayin mace komai mulkin ta zata sanar da ke cewa ta yi kuka saboda namiji,wata ta yi shi a fili wata
kuma ta yi shi a ɓoye, ta share hawayenta ta zauna a ɗakinta kema ina so ki saba na sani kina da haƙuri,
to ki ƙara. Sannan ki dage da addu'a wata rana za ki ci ribar haƙurin ki, da addu'o'inki bana so ki sama
ranki cewa an mishi asiri ne da sauransu,ki yarda a ranki cewa jarabta ce daga Allah, sannan ko a waya
bana son mahaifanki su san ga halin da ki ke ciki,ki zama mai ɓoye sirrinki zaya kasance ki sanar da su
hankalinsu ya tashi ke kuma nan ku zo ku shirya da shi kin ji duk abinda na faɗa? Kan A'isha yana ƙasa ta
ce,eh insha Allah zan kiyaye. Hajiyarmu ta ce na gode yanzun ina son ki ci abinci kinga ba ke kaɗai ba ce,
sannan ki yi wanka,matso nan ki zuba abinda ranki ke so, sannan ta miƙe in kin gama kiyi wanka bari in
hau gurin Alhaji, A'isha ta ce to.

Cikin natsuwa ta yi wa Alhajinmu bayanin komai,shiru ya yi na tsawon lokaci, can ya nisa ya ce "Shikenan
ki barta a nan kada a neme shi." Hajiyarmu ta ce, "Ni lamarin shi yanzun yana bani mamaki, haka kurum
duk ya bi ya ruɗa kanshi, ya hana kan shi sukuni." Alhajinmu ya ce,ki bar ni dashi kawai wannan karon,
zan taka mishi birki, Hajiyarmu ta ce bari in shirya maka abin kari, ya ce inda tuwon nan nafi son shi, ta ce
da akwai bari inje in ɗumama maka,ta fita shi kuma ya ci gaba da nazarin matsalar ɗan nasu,ko
harkokinshi yanzun ba kamar da yake tafi da su ba,lallai dole ne ya zauna da yaronnan in har yana da
wata matsala ne mu sani.

Daren Alhaji Saddiƙ bai runtsa ba,ya yi duk iyaka nazarin da ya kamata ya yi amma zuciyarshi ta ƙi yarda
cewa A'isha zata aikata wata alfasha,ya tambayi kanshi cewa to ko cikin ruwa tasha? Domin dai ya
tabbata zuwanshi na ƙarshe tana Haila. Hajiya Jummai ta so ta lallasheshi amma ya dakatar da ita kan
cewa ta barshi ba ya so a dame shi.


**** ***** *****

Yana dawowa daga sallar Asubahi, gefanta ya nufa dole ne ta mishi bayanin inda ta roro wannan ciki? Ko
tana nufin taje jami'a ne idanunta sun buɗe? Da wannan tambayar ya tura ƙofar ko ina ya duba bai ganta
ba don haka sai ya za ci tana bayi,shirun da ya ji ya yi yawa ne yasa shi duba bayin,bata ba dalilinta, ya

tsaya shiru sai kuma ya fita gurin Baba maigadi ya nufa,bai amsa gaisuwar da Baba maigadin ke masa ba,
tambaya kurum yake masa,Baba ko kaga fitar Beby? Baba maigadi ya ce gaskiya ba wanda ya fita yau, sai
dai kuma jiya da dare Hajiyar da ta dawo ta fita, amma bata dawo ba, ya ce ita nake faɗa,tun jiya kenan
ta fita? Baba ya ce,ƙwarai kuwa ya juya cikin sasan Jummai zuciyarshi tana harbawa, to ina wannan
yarinyar ta nufa? Me take nufi? Ya zauna bakin gadonshi ya lalubo wayarshi ba za ya iya tuna rana ta
ƙarshe da ya kira wayarta ba,nan ya lalubo lambarta ya shiga kira, sai ta yi tayi har ta yanke ba'a ɗaga ba,
shi bai ma san bata ɗauki wayar ba ya fito ya shiga mota sai da ya hau titi sannan ya soma tunanin ina ma
zaya nufa ne yanzun? Ya kira Nafisa don yasan yanda suke,ya ce mata sister ko A'isha ta zo? Nafisa ta ce,
a'a ta dawo ne? Ba tare da ya bata amsa ba ya katse wayar, gidansu Hajiyarmu ya nufa babu kowa cikin
falon kai tsaye ya nufi ɗakin Hajiyarmu daidai lokacin da A'isha ke shan wani ɗan kunun gyaɗa da ta tarfa
cikin kofi don dai kada Hajiyarmu ta ce bata ji maganar ta ba,yana ganin ta sai ya ji wani sabon ɓacin ran.

Ke me ya kawo ki nan gidan? Kina zaton za'a tursasa ni ne in amshi cikin da ban san daga ina yake ba? Ta
zuba mishi idanu, muryarta na rawa ta ce, "Uncle da ace zaka saurareni da ka gano yanda Ubangiji ya zo
da al'amarin. Ba zan saurari shirme ba, kuma ina so kiyi maza ki fita daga nan gidan, muryar Hajiyarmu ta
katse shi gidan ai bana zaton naka ne ko? Ya juya da sauri, kada ku yarda da dukkan abin da yarinyar nan
zata gaya muku."

Hajiyarmu ta ce, "to ubana." Jin haka yasa shi yin shiru tare da kauce mata daga hanya. Ta nuna ƙofa sai
anjima ko? Zai yi magana ta haɗe fuska,sai ya fita domin babu shaƙuwa tsakanin su ko in ce suna jin
nauyin juna.

Saman Alhajinmu ya wuce, Alhajin yana cin tuwanshi, Uncle ɗin ya shigo da sallama,kan kafet ya zube ya
dubi Alhajinmu ga mamakin shi sai yaga fuskar Alhajinmu tamkar hadarin mangariba murtuk, iya tsawon
rayuwarshi bai taɓa ganin Alhajin cikin wannan yanayin ba,nan take fargaba gami da tsoro suka shige shi
cikin sanyin jiki ya zauna kan kafet ya soma da gaida Alhajin a dake kuma ba tare da ya dube shi ba ya
amsa zai tashi Alhajin ya dakatar dashi da hannu.



######
[12/20, 23:02] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 7*

Ya koma ya zauna cike da tunanin me zai biyo baya,ya san Alhaji tamkar yunwar cikinsa, dattijo ne mai
sauƙin kai mai zafi kuma ga wanda ya taɓa shi, sai da ya gama karyawar shi tsaf sannan ya dube shi jeka
ɗauki matarka kuje gurin Doctor gani nan zuwa,za ya yi magana Alhajin ya katse shi da cewa, kada ka ce
min komai bana son ji, Uncle ya miƙe ba tare da cewa ƙala ba, ya fito yana tunanin shin me yarinyar nan
ta faɗa ma mahaifansa ne da zafi irin haka? Na shi ganin ai ita ce da laifi,laifin ma mai girma.

Ɗakin Hajiyarmu ya koma shima ranshi a ɗaure ya ce ke taso, Hajiyarmu ba ta ce ƙala ba, ganin haka sai
A'isha ta miƙe ba tare da tasan inda za suje ba,ko cikin mota ƙala bai ce mata ba ita kuma ba tace mishi
ba, sai dai taga sun tsaya asibiti. Tun kafin su iso Likitan yasan da zuwansu don sun yi waya da Alhajinmu,
don haka suna zuwa Likitan ya shiga yiwa A'isha tambayoyi.

Tun yaushe rabonki da al'ada? Uncle ya zuba mata idanu yayinda shi kuma Likitan yake ƴan
rubuce-rubuce, ta ce yau ƙwana shida kenan, Likitan ya ajiye biron hannunshi ya ɗora hannuwanshi kan
teburin shi tare da maida hankalinshi kacokan gurinta,kina nufin duk wata kina al'ada? Ta ce eh, cikin ya
shiga ne bayan wanda ya fita anan watanni bakwai da suka wuce? Babu wanda ya ji takun sawun
Alhajinmu sai kaɗai muryarshi suka ji ya ce ai cikinne bai zube ba, dukkan su suka juya suka dubeshi,ya
ƙaraso yana ce ma Likitan shi yasa na ce ka ciro fayal ɗin ta ka duba sannan ka duba ta, Likitan ya bashi
gurin zama sannan ya ci gaba da aikinshi, Uncle kuwa jinsu kurum yake yi yanzunne ya gano zancan da ta
shirya wa tsofaffin nashi suka hau kai suka zauna, bayan tambayoyi da bincike gami da aune-aune sai
kuma ya kira wani Likitan daban shi kuma (scan) ya yi mata sai da ya fitar da sakamakon sannan ya ba
Doctor ya fita nan dai Doctor ya tattara bayanai ya tabbatar musu cikin nan shi ne dai bai faɗi ba, sannan
yana cikin ƙoshin lafiya. Uncle ya yi zaraf ya ce, "Likita dama in mata suna da ciki suna fashin sallah ne?"
Likitan ya zauna ya yi mishi dogon bayani tare da tabbatar mishi cewa akwai matan, kuma itama hakanne
ya faru gareta, duk da yanda yake jin tsanarta cikin ranshi amma wani sashen na zuciyarshi na murna da
wannan labari.

Ƙwarai ya so ya tafi da ita gida, amma sai Alhajinmu ya ce ya kai ta gidanshi can gurin Hajiyarmu, duk da
ba taga canjin komai daga gare shi ba,ta ji daɗin yanda ya amince da cikin koda suka dawo har yanzun
Hajiyarmu bata sakar mishi fuska ba, ya fito ya nufi gida.

Hajiya Jummai ta ƙosa ya shigo domin ta ji me yake faruwa, da kanta ta taka har gefen A'isha, amma bata
nan lamari fa zaya jagule mata in bata yi Sa'a ba,ga Hadiza kuwa murna ce fal zuciyarta,tasan ƙarshen
A'isha ne ya zo,wa ya sani ma ko tun jiyan ya danƙara mata saki? Inji Tabawa, Hadiza ta ce Allah yasa
hakanne. Lokacin da maigidan ya dawo bai ce komai ba, Jummai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0