Showing 24001 words to 27000 words out of 38755 words

Chapter 9 - Mummunan Zato Book 3 Complete Halina Mashi

09 Jul 2025

2069

yi mata
hakan ba, ya ce Beby ɗazun na ce yaushe zaki dawo ba ki ce min komai ba, ta ce Uncle ka manta ne? Na
ce sai dai ka tambayi su Hajiyarmu, ya ce kin dai san in dan ta su ne zaki yi ta zama ne ba zasu dawo min
da ke ba, ta yi guntun murmushi a ranta ta ce kuji Uncle da wani zan ce mutumin da ke guduna. A fili
kuwa sai ta ce, sun ga baka buƙaci hakan ba ne shi yasa ya ce Beby kenan cikin ruwan sanyi ki ke dafa
mutum ni dai ki dawo gida kawai,ta tashi zaune Uncle jibi ne fa zan koma makaranta to menene ma zai sa
in dawo tunda ba zama zan yi ba, ya yi shiru can ya ce ni fa don dai kawai su Hajiyarmu ne amma Allah da
ba zaki koma yanzun ba sai yarona ya yi wayo bana son aje baa luran min dashi. Shiru ta yi mishi ya ce to
in zaki shiga aji dawa zaki dinga barin shi? Ta dube shi da Uwani zamu tafi har ma da wata yarinya saboda
aikin gida, ya ɗan taɓa baki da bana gari ma da sai dai in dawo in samu kin tafi abinki, ta ce Uncle naga
kamar kafi buƙatar hakan ne shi yasa tunda tuni ka fitar da kanka daga cikin lamarina, ta sunkuyar da kai,
wallahi a shekarar da ta wuce in wani ya ce min zan tsinci zuciyata cikin garari ba zan amince ba, domin
na san uban goyona mai amana ne da halin dattako kuma zaya jure duk wasu laifuka da ƙuruciya zata
aikata matsawar ba alfasha ba ce, sai gashi yana zarginta da alfasha wanda ke ɓata aure, ya ɗaga mata
hannu, zuciyata bata zargeki ba Bebyna ko da baki ya furta zuciya ta ƙi amincewa, Beby an wuce gurin
bana son ki dawo da hannun agogo baya, kuma kamar yanda nike fada koda yaushe ni baki yi min laifin
komai ba....

######
[12/22, 12:13] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 11*



Amma da mamaki ace don jin daɗin kanka ka juya baya gareni,kafin ya ce wani abu sai kurum suka ji
muryar Hajiyarmu tana cewa in nan zaka ƙwana mu kulle ƙofa ya dubi agogon hannunshi sha biyu
saura,lallai lokaci ba wuya ko kuwa don yana tare da masoyanshi guda biyun ne?.

Bayan fitarshi ne Hajiyarmu ta kalleta sanyinki ya yi yawa A'isha,me zai sa ki saurareshi shi da ya nuna
baya ƙaunarki? Kanta a ƙasa ta ce Hajiyarmu in ma na ɗauki zafi dole in sauke domin daga gare shi zan
samu aljanna, Hajiyarmu tana mamakin A'isha in da mata da yawa za su ɗauki halin A'isha haƙiƙa za su
zauna lafiya da mazajansu kuma su ci ribar aure, ta ce haka ne amma mazan ku na yanzun sai kuna ɗan
nuna musu kuskurensu,na ce baki sakir mishi fuska yanzun ba nan gaba zaya ji shakkar yi miki irin haka.
Ta ce haka ne sai dai yana da ƙyau in bashi uzuri kasancewar bai taɓa aikata min ƙwatanƙwacin haka ba,
sai wannan karon, sannan yana da ƙimar da ba zan iya rama abinda ya yi min ba, Hajiyarmu ta ji zuciyarta
ta ƙara ƙaunar A'isha, ta ce to Allah ya daidaita ku,mu dai addu'armu kenan, sannan in ya yi ba daidai ba
mu tsawata, sannan ki lura da ɗan ki kin ji ko. A'isha ta ce, to ta lura tana matuƙar son jikanta nata tana
da kara ne.

Tafiya ta kama shi ranar da A'isha zata koma,bai so haka ba,ya so ƙwarai ya zama cikin masu rakiya in
yaso ya ƙara wanke kanshi gurin Bebyn tashi, ya dai yi sallama da su kan cewa sai ya zo insha Allahu da
zaran ya dawo daga Egypt. Nafisa ta zo da safe dan su yi sallama A'isha ke cewa ina son ki zo ki sha labari
don ba za ya yiwu ta waya ba, Nafisa ta ce bani labari. A'isha ta labarta mata yanda suka yi da Uncle ɗin
ta, nan Nafisa ta yi murna sai dai itama ta yi wa A'isha tsiyar cewa ta cika son miji daga sakar mata fuska
shi kenan ta shiga wage mishi baki, A'isha ta ce to ni ya zan yi? Anty Nafisa kin san Uncle ya wuce wasa a
gurina, domin sai fa ya ɗaga ƙafa sannan zan shiga aljanna,ya zan yi wasa da dama ta? Nafisa ta yi dariya
kina burge ni A'isha Allah ya sani ma in gwada irin halinki. Itama A'isha dariya ta yi.

Yana ƙwance yana nazarin yarinyar ya sani sarai cikin ruwan sanyi A'isha magana ta gaya mishi, ita
kowace irin mutum ce bata fushi? Gaskiya ba zaya gaji da godewa Allah ba,muryar Hadiza ce ta katse shi.
Gaskiya ni na gaji, kullum sai ka tafi gurin A'isha ka raba dare ko ka je asibiti ni ce ban san haƙƙina ba don
kaga ina haƙuri? In zata dawo ne A'ishan ba gwara ta dawo ba, amma sai a dinga shiga cikin haƙƙina
ranar girkinta da ranar da ba tata ba.

Ya miƙe zaune to tunda kin gaji sanar dani yanzun me ki ke son in miki? Ta zunɓuro baki ta dawo a raba
ƙwana mana, ya ce na ƙi ta dawo ɗin sai ya ya kuma kike so? Ta kalleshi,ai ni banida alfarmar da zan faɗi
abinda ni ke so ayi wannan sai A'isha. Ya ce ƙwarai kuwa domin bata da san kai a rayuwa in kuma abinda
ya kawo ki kenan to fita ba ni da lokacin ɓacin rai yanzun ya juya bayanshi, tunda ta wanke gaba ta baka a
zoɓo kuma ta haihu ai gare ka babu kamarta, murmushi ya yi a fili kuwa ya ce mahaukaciya kawai, ta fita
tana ƙunƙunai.
Haka lokaci ya yi ta tafiya A'isha tuni tana makaranta kuma ta dage ma karatunta, yayinda Uwani ke lura
da Abulkhairi, kullum kuma tana ɗaga wayar Uncle ɗin nata a ƙalla sau huɗu a rana ko fi ma,don haka
hankalinta ƙawance ta murmure gwanin sha'awa da ita, ranar suna waya da Nafisa take cewa Anty Nafisa
Uncle yana son kawo min ziyara ina dakatar da shi da cewa karatunmu ya ɗau zafi in ya zo bazai samu
kulawarmu sosai ba, sai nace ki bani kayan nan na gyaran jikin kafin ya zo, gefe kuma ina tsoron kada na
kuma ɗaukar wani cikin ga Abulkhairi ga karatuna, Nafisa ta ce zan tura miki da kaya ta tasha gobe, akwai
na sha sunanshi hurul'in da na matsi sannan turarukan shafawa da na tsuguno sai man gyaran jiki da
sabulun shi sannan lalle na wanka da kuma haɗi na musamman irin wanda ta ke yi don Amare duk nasa
ta haɗo min su, zaki gan su kawanne da sunanshi wanda baki gane ba ki kirani ko ki kira Hajiya Aliya zan
turo miki lambarta, batun ciki kuwa a sakar ma ɗan uwana jiki ya huta haihuwa muke buƙata kema kin
sani, A'isha ta ce haba Anty Nafisa baki tausayin Babanki? Abulkhairi bai yi ƙwari ba Nafisa ta ce za ya yi
ne ma suka sa dariya sannan suka yi sallama.

Hajiya jummai kuwa yau in ciwo ya lafa gobe zai tashi domin ta kasa ƙwantar da hankalinta guri ɗaya, shi
kanshi Likitan ya gaji da ita don haka yana ganin ta ɗan samu sauƙi sai kawai ya sallame ta ya ce zaya
dinga zuwa gida yana duba ta,Indo ma tayi murna don tana so ta tafi, kuma halin ƴar uwarta ya isheta a
gidan ma a daddafe ta yi sati ta haɗa yanata yana ta tayi tafiyarta sai ƴan aiki da kuma ƙawayanta da ke
tururuwa suna cika gidan kullum kuma abin takaici har yau ba su daina ƙalla banza ƙwance wofi
ba,burinsu wai su fitar da A'isha kuma wai A'ishan asiri ta yi mata wannan ciwon nata wai Hadiza ma tana
jeho mata asirai kin ji fa.

A'isha suna hanyar su ta zuwa aji ita da wasu abokan karatunta, suna tafe suna hirar Abulkhairi ne, Hafsa
Sulaiman tana cewa yaron ya fi ki ƙyau sam bai yi kama da ke ba. A'isha ta ce Abbanshi ya biyo sun yi

kama sosai,Hauwa'u Hamza ta ce to kuwa Baban nashi yana da ƙyau kenan,don nima bana gajiya da
yaron, kafin ta yi magana sai wayar Uncle ɗin ta ta shigo ringin ɗin shi na musamman ne don haka cikin
sauri ta soma lalubo inda wayar take,cike da kissa ta ce Hello Uncle ɗina,ya gyara zama Bebyna, suka
gaisa yana tambayar ina Babanshi ta ce suna gida tare da Uwani yanzunni ina hanyar zuwa aji ne ya
jingina da kujera,na kasa komai Beby ina cike da kewarki ke kuma na kula baki son in zo inda ku ke, ta ce
wacece ni Uncle da zan hanaka zuwa gurin mu ya ce in gaske ne in zo yau? Ta ce Uncle kaɗai shigo week
end duk ƙwanakin nan bama samun lokacin kanmu, ya ce shi kenan zan dai samu tarba ta musamman
ko? Don maƙogwarona ya bushe da yawa ina jin ƙishi, ta ce faɗi duk me ka ke so zan maka ya ce ke
kurum kin wadatar dani, ta ce Uncle dama ni ai taka ce ko yaushe sai dai in kai ne ka ƙi hakan ya ce
Bebyna kenan kin dai warware ni a hankali to kaina dai bisa wuya, sai na zo ta ce to shi kenan muna
kallon hanya.

Hafsat ta ce A'isha Musty dawa ki ke waya haka kina faman salo sai ka ce kina gabansa cikin dariya ta ce
yanzun don Allah har wani salona yi? Da Uncle ɗina fa nake waya, Hauwa'u ta ce kai wannan salon ina jin
dai da Abban Abulkhairi ki ke wayar, ta ce au baku yarda ba cewa da Uncle ɗina nike yi ba? Hafsat ta ce
Uncle ɗin nan da kike kira yana ji dake kema haka, A'isha ta ce haka ne baki faɗi ƙarya ba Uncle yana ji
dani tamkar rai, Hauwa'u ta ce yana da mata? A'isha ta ce matansa uku ɗan sa ɗaya. Hafsat ta ce aiko in
bakin ci Sa'a ba matansa sai sun tsaneki, cikin dariya ganin ta shigar da su sun shiga ta ce suma ji dani
suke yi, suka ce lallai,kin dace nan dai suka ƙarasa ajinsu don ɗaukar darasi, A'isha kenan tunda saƙon da
Nafisa ta aiko mata dashi ya shigo hannunta ta soma amfani da su cikin ƙwana uku ta canza ta zama
tamkar wata amarya abokanan karatunta kuwa kowacce sai ta dinga ce mata ana karatu ana rama ke
kuma kina ƙara ƙyau dan Allah menene sirrin? Dariya kurum take musu tare da cewa suna dai zolayarta
ne. Hatta Anty Maimuna ƙawar Anty Nafisa sai da ta dinga yiwa A'isha nacin son ta san man da take
shafawa ta ce sunanshi Zahra Global in kina so zan yiwa Anty Nafisa magana.

Tunda ya yi waya cewa yana hanya duk ta rasa sukuni, ta ƙosa su fito daga lap,tana shiga gida kuwa yau
ko ta kan Abulkhairi bata bi ba suka shiga aiki su da Tani mai aikinta,girka wannan sauke wancan har suka
gama, ta haɗa mishi mutumin nashi wato zoɓo sannan ta shiga wanka.

Ƙwalliya sosai ta zauna gaban madubi ta yi tare da saka turarukan jiki masu ƙamshin daɗi. Atamfa ce ƴar
Holand ja ɗinkin riga da siket sun zauna dam a jikinta tamkar a jikin nata aka ɗinka su. Hatta Uwani sai da
ta ce kin yi ƙyau ƴannan wannan kaya sun karɓe ki, tana cikin shirya Abulkhairi ta ji ana ƙwanƙwasa gida.
Kafin ta yi magana ta jiyo Uwani tana cewa Tani taje ta duba,don haka ta ci gaba da saka mishi
kaya,ƙamshin shi ta ji ta amince shi ne ya iso cikin sauri ta ƙarasa tana cewa Abulkhairi kayi ƙyau babana"
juyowannan da zata yi sai suka haɗa ido da Uncle ɗin nata yana tsaye yana kallonsu cike da sha'awarsu,
A'isha ta ce la Uncle har ka shigo? Ya iso gabanta na iso Beby ya ɗauki Abulkhairi ya ɗaya shi sama yana
mishi wasa ita kuwa tuni ta shiga gyara mishi gurin da zai zauna don cin abinci, ta amshi Abulkhairi, Uncle
kawo shi kaci abinci bari in kai shi gurin Uwani ya ce a'a barshi nan abincinma nan za'a kawo min,nan

take ta baza capet ta shiga jera mishi kuloli sai da ya zauna kafin ya fara cin abinci ta shiga gaishe shi tare
da tambayar jikin Hajiya Jummai,su Hajiyarmu da sauran jama'a ya ce duk suna lafiya, Jummai dai jikin
nata sai a hankali, da zoɓon ya soma sannan ya shiga cin abincin ya ma rasa me zai ci duk ranshi yana so
rabon da ya yi ci irin wannan har ya manta, ya ce Beby kin ga kin sani yau har na wuce ƙa'ida,na ci na
kasa tashi, ta yi murmushi Uncle kenan to ai ni nafi son haka.

Taƙwas da rabi daidai lokacin da ya dawo daga masallaci sallar Isha'i, ya ce Beby ba zan ƙwana a nan ba
shi yasa muna isowa nasa Jabiru ya je ya kama min masauki ta ce don me? Ya ce ga su Uwani ko ba haka
bama kin san ba ni son cikin makaranta, ta ce to ya za'ayi yanzun? Tashi zakiyi mu tafi, ta ce da
Abulkhairi? Ya ce eh mana, ta ce can zan ƙwana kenan? Ya ce to ya ya kike nufi da? Ya ci gaba,kina nufin
ni kaɗai zaki bari inje in ƙwana? Ta ɗan yi taƙwa-taƙwa da fuska haba Uncle gidannan fa dasu Uwani shi
kenan sai nabi ka can da safe kuma idan na dawo da wane ido zan kallesi? Ya ɗaure fuska koda nan na
ƙwana abin da kike gudun su kalle ki dashi in kin bini dashi dai zasu kalleki,kin gane? Beby duk mace mai
miji in dai tana tare da shi an san me suke yi, balle ni da na ɗan ƙwana biyu ban abinnan ba, ya ƙarasa da
ƴar tsokana ta ce Allah Uncle gaske nake faɗa zan ji kunya, ya ɗauki Abulkhairi muna jiranki cikin mota ki
zo muku da duk abinda za ku buƙata, zuwa gobe.

Ta bisu da kallo ɗan murmushi ta yi sannan ta shiga haɗa musu kayan bacci da sauransu, ta kunna tiraran
tsugunno ta yi tare da ƙara kimtsa jikinta, ta saɓa jaka tare da zura hijabi ta fito, Uwani suna kallon T.V su
da Tani ta fito ta ce Uwani zamu in nan cikin gari kome sunan unguwar? Gidan dai wani ko abokinshi ne?
Ku dai kulle gidan in mun dawo to sai mu buga. Uwani ta ce to ƴan nan a sanyin nan? Da kun bar Alhaji
nan tunda shi bashi da rigima, ta ce yama riga ya fita da shi sai dai mun dawo. Tani ma ta ce sai sun
dawo.
Cikin mota ta same su yana ta mishi wasa, ta shiga tare da tura baki Uncle ka sani zula ƙarya, ya ce kin so
ne me ki kace? Ta sanar da shi yace in suka zauna jiranki fa? Ta ce shi ne ai ko in koma ince mun fasa sai
ka shigo mu ƙwana ciki kawai, kafin ta rufe baki ya tada motar.

Cikin Reception suka ga Jabiru yana zaune yana kallon ƙwallo cikin T.V, ya tare su tare da amsar
Abulkhairi, shi ne ya yi musu jagora zuwa ɗakin daga bakin ƙofa suka yi sallama tare da miƙa musu yaron.

A'isha tasha mamakin yanda Uncle ya ke ta rawar jiki tamkar yau ya soma sanin mace, ta dai sha wuya
sosai shi ko sai kace bame mata biyu ba, haka ƙiri-ƙiri ya ƙi su tafi gida ranar tana ji tana gani dole ta kira
wayar Uwani ta ce mata sun yi wata ƴar tafiya kada su ji shiru, cikin satin da lahadin wata rayuwa suka yi
mai tsayawa cikin zukatansu, ranar Lahadin ma sai dare sannan ya kawo su gida shi kam Asubanci zasu yi

don komawa KT,lokacin da zasu yi sallama ta kuma maimaita mishi batun da ta ringa mishi naci tun da
suka je hotel ɗin bai ce mata ƙala ba.

Ta ce don Allah Uncle kaga Abulkhairi be yi ƙwari ba, kuma ga karatuna. Nan take ya gumtse fuska Beby
na fi son in kin faɗi abu nayi shiru ki ringa ƙyale ni, ke kina ganin ko'ina shaye-shaye zan yarda da wani
tsarin iyali? Ki kalleni fa ki gani a shekaru na sai yanzun Allah ya bani ɗan fari, amma har in soma butulce
ma Allah? Please bana son in kuma jin makamancin wannan zancan, kanta na ƙasa ta ce to, sallamar ma
ba cikin daɗi sosai suka yi ta ba,in ba dan A'isha ba ce ma ƙila da wata ce tazo mishi da wannan batun sai
ya mugun saɓa mata yanda ta kula da irin ɓacin ran da ya nuna cikin dare sai da ta kuma kiranshi ta bashi
haƙuri kan cewa ya yi haƙuri ta ga ranshi ya ɓaci da batun da tazo masa dashi, ya ce ya wuce shi bai ƙima
ace yanzun tana da wani cikin ba, dariya kurum ta yi amma cikin zuciyarta cewa take yi Allah ka tsare ni.




#######
[12/22, 20:35] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 12*



Tana ta gudu gyale a hannu takalmi a hannu tana zunduma ihu cikin ƙungurmin dajin mai tsananin
duhu,yaran ta ke gani cikin wani muguwar kama mai ban tsoro, dukkan su suna furta mata kalmar fansa!
Fansa!! Ko'ina cikin dajin amsawa yake yi, gudu take yi tun ƙarfinta duk ta gaji sai ta hangi wani rami nan
take yi ta yanke shawarar tsundumawa cikin, tana faɗawa sai taji ta kan macizai da kunamu, ihu ta saki
mai tsanani sai ta farka a tsorace ta tashi zata gudu Alhaji Saddiƙ ya riƙe ta da ƙarfi yana cewa Jummai
lafiya? Masu aiki ma suka shigo da gudu saboda ihun da suka jiyo,faɗi take gasu nan,su murja ne da
Hafsatu zasu kashe ni wai zasu ɗauki fansa su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0