Showing 18001 words to 21000 words out of 38755 words

Chapter 7 - Mummunan Zato Book 3 Complete Halina Mashi

09 Jul 2025

2068

ta zauna tana ƴan mitoci
gaskiya Alhaji baka ƙyautawa.

Hajiyarmu ta gama waya, Jummai ta ce Hajiyarmu ya kamata a yiwa Alhaji magana baya ganin ba ita
kaɗai ba ce? A'isha bata da matsala ya ya zaya ringa matsa mata? Hajiyarmu ta ce ya yi dai mu gani,
rayuwa ce amma cikin ran Jummai dam da murna sannan tafi kowa sanin dalilin da yake wannan abin ga
A'isha ita dai burinta shi ne A'isha ta haihu gabanta ko daga ita sai ita,ta samu mahaifa ta ida tarwatsa
rayuwar yarinyar.

Tana gama waya da su Ummanta, ta kishingiɗa. Allah sarki! Su Abbanta sun zata har yanzu tana cikin
ƙwanciyar hankali ne,sai dai tasha alwashin ba zata taɓa sanar da su ba, domin ko me zata ce Abbanta ba
zai yarda ba,ƙila ma reshe ya juye da mujiya,wato laifin ya dawo kan ta. Cikin wannan tunanin ne taji

tamkar an mintsine ta a baya,dama duk ƙwanakin a zaune take ƙwana in zata iya kuma ta yi ƴan nafilfili a
haka ta yi sallar isha'i. Hajiyarmu ta shigo tana ce mata,kin ci abinci? A'isha ta ce,na ci zan ma ƙwanta ne.
Hajiyarmu ta ce kina jin daɗin jikinki kuwa? A'isha ta ce eh babu damuwa Hajiya, fitar Hajiyan ke da wuya
ciwo ya dawo sabo, ita kaɗai ta dinga kai kawo sam bata za ci haihuwa ba ce,ga nata zaton irin ciwon dai
da ta saba ji ne yau da kullum,ya yi ya lafa,ya yi ya lafa cikin dare,biji-biji tayi zuwa lokacin ta gama yanke
hukunci mutuwa zata yi,taso ace Uncle yana kusa ko zaya tausaya ya yafe mata laifin da ta mishi wani irin
ciwo take ji wanda bata taɓa jin ko labarin shi ba,nishi yazo mata ta ji tana nishi mai tsanani tare da salati
sai taji tamkar ana buɗe ta sai kurum wani ruwa tare da yaro jim kaɗan sai ga wani abu shima ya faɗo
ashe mahaifa ce. Yaro ya shiga yanka ihu ita kuma ta koma gefe tana nishi.

Cikin bacci Hajiyarmu ta yi mafarkin wai ga A'isha an banƙare ta za'a yanka mata ciki, ta farka da salati
dama duk dare tana zuwa duba A'isha kusan sau uku,ta kan ganta zaune ko kuma tana nafila,tana nufo
ɗakin ta ji kukan baƙon duniya, da sauri ta shiga tana cewa ni ƴasu ke ƴan nan shi ne kina naƙuda ba zaki
yi magana ba? Gashi ni yau sai Allah ya sauko min da bacci sannu kin ji? Ina kayan haihuwar? Ta nuna
mata inda suke inda Nafisa ta ajiye su ko da yaushe tazo gidan tana shaidawa A'isha cewa tana jin burin
ɗin ciwo to ga kayan da zata ɗauka nan,reza ta ciro ta yanke cibi sannan ta sa zani ta ɗauki jaririn lokacin
da take karanto addu'ar da zata tofa ma yaron, idanu ta zuba mishi gabanta ne ya faɗi domin yaron
tamkar mahaifinshi lokacin da ta haife shi,kamannin ya yi yawa sosai,nan kuma sai ta samu kanta da jin
nauyin yaron,don haka sai ta matso ta ba A'isha shi a inda take cikin jin nauyi. A'isha ta amshe shi nan da
nan Hajiyarmu ta tashi duk ƴan gidan suka shiga aiki, Uwani ita ce ta wanke yaro tas yayin da Baraka ta
shiga gyara gurin Hajiyarmu kuwa gurin Alhajinmu ta nufa,kan sallaya ta same shi. Ya kalli agogo na jira ki
sai naji shiru, shi ne na ce Hajiyar gidan nan yau batayi da ni, ya yi maganar cikin tsokana, ta ce Allah
sarki,ba haka ba ne ɗan bacci ne ya sace ni ba farka ba sai da nayi wani ɗan mafarki haka ina tashi sai
kukan jariri na ji,yarinyar nan ashe naƙuda take yi ba ta faɗa ba, ita kaɗai ta haihu, da sauri ya miƙe
A'isha? Ta ce eh,nan ya shiga murna yana cewa alhamdulillah,ya so zuwa ɗakin Hajiyarmu ta ce ana gyara
su ne.

Zuwa wayewar gari ko'ina labari ya je ban da gidan Uncle,domin daga Alhajin har Hajiyar babu wanda ya
sanar dashi,su Nafisa kuwa an zo ana ta murna da ko tuno shi ba su yi ba, maijego tamkar ba ita ba,ta
shirya tsaf asibiti za su je don Likita ya duba su . Ita da Nafisa suka nufi asibitin. Likitan ya duba su kuma
ya tabbatar da lafiya suke. Aka yi wa yaron (Bcg) suka dawo,Likitanne ya kira shi lokacin yana shirin fita
zuwa Office,suna gaisawa Likitan ya yi mishi barka,nan take Alhaji ya shiga tambayar Likitan ta haihu ne?
Cikin mamaki Likitan ya ce ba ka sani ba kenan? Shi yasa banga ka biyo su ba? Ya ce Likita suna nan ne?
Doctor ya ce a'a sun zo na duba sune gida ta haihu ko da ya gama shirinsa sai ya sake shiga bayinsa ya yo
alwalla, nafila ce ya yi raka'a biyu yana yiwa Allah godiya, fuskarshi fal annuri ya fito ya dubi Hajiya
Jummai Beby ta haihu,jin zancan ta yi tamkar saukar aradu, amma ta dake ta ce me ta haifa ne? Ya ce
ban sani ba sai naje zan ji, ta shiga ɗakinta da gudu ta janyo gyalenta muje tare. A zuciyarta kuwa cewa
take Allah ya bata Sa'a ta ɗauko mahaifa.

Sun samu ɗakin cike da jama'a ƴan barka, Uncle ya shiga mutane suna mishi barka, Hajiya Jummai cikin
nuna zumuɗinta ta shiga ina ɗan nawa? Allah sarki,ko ƴa ce? Aka ce mata ɗa ne, Nafisa ta ce gashi nan
mai kama da mahaifinshi,yaron na hannun Jummai Uncle ya tsura mishi idanu,wani farin ciki yake ji
tamkar yau aka haife shi,ya miƙa hannu Jummai ta ɗora mishi yaron,nan take ya yi wa yaron huɗuba tare
da addu'o'i,ko Nafisa ba ta furta ba lallai yaron hotonshi ne ji yayi tamkar kada ya bada yaron ya zauna
yana ta kallonshi kawai, kaɗan-kaɗan mutane suka ringa fita har su Nafisa. Yana ɗago kai tuni sun watse
sai matan nashi kurum, ya dubi A'isha a ranshi yana so ne ya yi mata sannu amma yana kallonta sai ya ji
tamkar ya ɗauke ta da mari, Nan take fuskarshi ta canza ya kuma juya mata baya, zuciyar A'isha ta sosu
amma sai ta danne, ta ce Uncle Ina ƙwana? Da ƙurar kuma can ƙasan maƙoshi ya amsa,ta ce ka faɗa ma
su Abbana? Hajiya Jummai ta ce sai dai yanzu ya faɗa,mu ma ba yanzun muka ji haihuwar ba,wai tun
yaushe ne haihuwar? Kan A'isha yana ƙasa ta ce da dare ne. Uncle ya ce to kin ji abu da dare amma an
kasa sanar dani. Hajiya Jummai ta ce Alhaji sai ka amshi mahaifar mu je gida ka rufe ko? Ya ce haka ake
yi? Ta ce eh mana,ai ba'a wasa da ita,ya dubi A'isha sannan ya kauda kai, ina mahaifar? Ta ce sai dai a
tambayi Hajiyarmu, Jummai ba ta san sanda ta furta Allah yasa ba su rufe ba, sai kuma ta riƙe bakinta
saboda katoɓarar da ta yi, ya dubeta in an rufe a nan laifi ne? Ni fa bana son canfi,ta ce a'a ina fa laifi wai
mu ma muce an taɓa rufewa a gidanmu.

Ya nuna murnarshi sosai a gaban mahaifan nashi da ƙannanshi, in da har yake tambayar ƙannan nashi
me ake buƙata game da jariri da mamanshi? Nan take Nafisa ta shiga lissafi har da na tsiya, lokacin da
Uncle ya sanar da mahaifanta sun yi murna sosai, Abbanta ya ce Friend na tayaka murna sosai, Allah ya
raya mana ya ce Amin friend,na gode ina fatan za ku zo kada ka ce min don A'isha tana ƴarka ba za ka zo
ba, dariya Abban ya yi kafin ya ce ban ɗaukar maka alƙawarin zuwa ba, sai dai ko bayan suna zan zo insha
Allah. Dangin A'isha suma labari ya karaɗe ko'ina,ba labarin ciki sai na haihuwa, lokacin da labarin ya
samu Hadiza tamkar zata suma don itama da yawa Malaman nasu sun sheda mata cewa duk wadda ta
haihu cikin su shi kenan ita ce kurum zata yi ta haihuwa, kuma ta yi rantsuwa kan cewar in dai ba ita ce
zata haihu ba, to sai dai kowa ya rasa cikin da yake cewa ba na shi ba ne shine zai amsa? In ko haka ne
itama sai ta nemo shi wajen ai ba an fi su sanin kan bariki ba ne.





#########
[12/21, 18:37] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 9*

Hajiya Jummai ita dai damuwarta ta samu mahaifa, don haka lokacin da Alhaji zai fita bin shi ta yi gurin
mota, faɗi take shin Alhaji ka amshi mahaifar? Ya dubeta,au Ina zuwa,ya koma ciki sai dai ya kasa
tambayar mahaifiyarshi saboda nauyin da ke tsakaninsu,ya ce Nafisa zo mana,a gefe ya ke cewa ta
tambaya mishi ina mahaifar don ya je ya rufe. Lokacin da ta yiwa Hajiyarmu batun sai ta bata amsa da
cewa zasu yi ta ajiyar mahaifa ne ba za su rufe ba har zuwa yanzun? In kuma ya fi son ya rufe da kanshi to
sai ya jira mahaifin nasu in ya shigo sai ya ce ya tono mishi yana son ya rufe da kanshi ne,yana jin lokacin
da take faɗa wa Nafisa wannan batun,don haka sai ya juya kurum yasan har yanzun mahaifiyar tashi tana
ciki da shi.

Jummai ta dube shi ka amso ne? Ya ce sun rufe tuni, ta zaro ido har ma ya tsaya yana kallonta, sun rufe?
Ta ɗora hannu akai tare da cewa kash! Ta dubeshi ɗan jira ni in ɓari inzo muje gida, da sauri ta suri
gyalenta ko sallama ba ta yi wa mutane ba ta wuce. Yana ƙoƙarin tada mota ta fito, sannan abinda ya
dinga ba shi mamaki yanda duk surutun da yake yi bata san ma yana yi ba,ga uwar zufa da take zabgawa
sai ka ce wadda ta haɗiye kunama. Suna isa gida tun kafin ya gama parking ta buɗe mota kaɗan ya rage
ta faɗo, ta fita da sauri sauri gudu-gudu tana shiga falonta suna cin karo da Aminiyarta Hajiya Kari, ta ce
Jummai tunda na samu labarin haihuwar matar mijinki na ce bari in zo kada kiyi sakaci, Jummai cikin
wani huci mai tsanani ta ce na nawa kuma,ai an riga an gama sun rufe ta. Karima ta yi saurin cewa, sannu
Alhaji dan ganin ya riga ya shigo kuma ga Jummai da shegen ɓarin baki, sannan ta yi mishi barka,cike da
murna ya amsa tare da godiya, ya kalli Jummai ya ce, wani abu na damunki ne? Ta share zufa ta ce me ka
gani? Ya ce duk kin canza irin kamar kina cikin mawuyacin hali? Ta kuma share wata zufar haba dai mu
yau da muke cikin farin ciki? Ta yi ƴar dariyar yaƙe,ai mu yau dai babu bacci, ya tsura mata idanu Jummai
wannan zufar fa? Ta ce tsabar farin ciki ne, sai ta soma matso hawaye shekaru nawa ba mu taɓa jin kukan
ɗa ba cikin gidan nan sai bana, dole in yi zufa, Karima ta ce haba Jummai ai godiya zamu yi wa Allah ba
kuka ba, Alhajin ya dafa kafaɗarta, Jummai na san dole ne kiyi murna, sannan ina miki albishir da zaran
an tashi ya ye shi ke ce zaki ɗauke shi kiyi rainonsa har abada, ta dubeshi cikin muryar kuka tana cewa na
gode Alhaji ni dama nasan ɗan ka ɗana ne Allah ya raya mana shi, suka ce amin ya ce bari in je in ɗauki
wasu takardu ina da baƙi a Office suka ce to ya fita. Hajiya Jummai ta ɗora hannu a kai zata zunduma ihu
Karima ta saka tafin hannunta ta rufe ma Jummai baki, sannan ta ci gaba da cewa kina hauka ne? Na kula
garin taɓargazarki wata rana za ki tona kanki,ɗazun kin ƙwaci kanki yanzun in yaji ihunki ya dawo me za ki
ce?

Cikin kuka Jummai ta ke faɗin na shiga uku ni Juma, yanzun shi kenan ni ko me nayi babu nasara
cikinshi,na fi wata ina zirya gidan su Hajiyarmu na ringa daure zuciyata ina zama tare da tsinanniyar
yarinyar nan ina kashe ma tsinanen cikinta kuɗi duk don in samu mahaifar nan amma haƙana bai cimma

ruwa ba, Kari ta ce naji yi shiru ki shirya yanzun da ya fita muma sai mu nufi gurin Malam mu ji ta
bakinshi.

Ya dubeta kin isa a yi miki jaje, domin in baki dage ba ƙila lokacin rushewar al'amuranki sun zo,yarinyar
nan ita ce zata yi ta haihuwa dama kin yi nasara ne haƙiƙa da kin dace, cikin jimami ta dubeshi to ni
yanzun yaya zanyi? Ya ce sai mun bincika ta ce yanzun in je in zura idanu kenan? Ya ce in kina da wata
dabara sai ki je ki ƙwatanta, kafin mu mu binciko. Tamkar zata yi hauka ta baro gidan Malamin, Karima
tana tausarta tare da lallashinta, tana nuna mata cewa ta yi a hankali kada mutane su gane halin da take
ciki.
Gidan masu jego kuwa, al'umma sai tantsowa suke yi, wasu ma ba a san su ba,ƙwananta uku ƴan Jigawa
suka iso, murna gurinta ba a magana har da su Jafar da Munnir aka zo,sai da Hajiya Lanti da Tabawa suka
taushi Hadiza sannan ta zo barka, Hajiya Jummai ma ta cije ta sake zuwa ana gobe suna, yanda taga ana
sauke kayan ciye-ciye da shaye-shaye ga gidan ya cika da jama'a sai hankalinta ya kuma dungunzuma ta
bar gidan suna. Tafe a mota direba na janta tana surutai ita kaɗai.

Ranar suna yaro ya ci suna Usman,waton sunan Alhajinmu, labarta yanda sunan ya kasance ma ƙauyanci
ne. Sun samu alkhairi mai yawa daga abokan Uncle har da masu ba shi motar zuwa makaranta. Hadiza
dai babu wanda yasan tafiyarta. Jummai ma tunda ta yi arba da maijego tun daga ƙasa har sama take
kallon A'isha kaya ƙarshen tsada ga gwala-gwalai tun daga yatsun ƙafa har zuwa na hannu,na wuya kam
ai ba a magana, sai ta juya gida. Taro ya tashi lafiya danginta sun koma gida suna sambarka, haka suka ci
da wankansu, A'isha tana matuƙar mamakin yanda dangin Uncle suke tsananin son yaron wanda Nafisa
ta yi wa laƙabi da Abbul khairi, Hajiyarmu ce kurum ke karantawa bata ɗaukarshi, hakan ne ma yasa
A'isha sam in Hajiyarmu tana ciki bata ɗaukar yaron ta bashi nono, sai ta dinga kara itama musamman
tun bayan suna Alhajinmu ya ce su A'isha su dawo ɗakin Hajiyarmu. Matsalar A'isha ɗaya, Uncle wanda
har yanzun bata cikin ƴan kayan shi duk da cewa wani lokacin abun yana damunshi, A'isha har ta soma
ƙyau ta ci tasha duk abinda ranta ke so kuma Hajiyarmu ta ce kada ta damu da matsalar Uncle tana
zaune za ya zo ya kawo kanshi.

Misalin ƙarfe huɗu saura ya fito daga sallar la'asar ya shiga gidan mahaifan nashi don yaga Abbul khairi.
Yana shiga gefen Hajiyarmu sai ya soma jin kukan yaron, da sauri ya nufi ɗakin domin ji ya yi tamkar an
watsa mishi ruwan zafi, kuma ƙila ɗakin babu kowa, amma ga mamakin shi yana shiga sai ya samu A'isha
tana zaune tana cin abinci, Hajiyarmu kuwa tana sallah daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallon A'isha,ji ya yi
tamkar ya shiga ya hau ta da duka, waton tana zaune ma tana cin abinci? Ta bar yaro,ya ɗauki yaron ya
fita a falo ya tsaya yana jijjiga yaron, zuciyarshi na ce mishi A'isha bata son yaron kamar yanda Hajiyarmu
bata so shi ba lokacin yana yaro kai har zuwa yanzun a fili ya ce tab in dai haka ne gara ya kai ɗan shi

gidan raino. Hajiyarmu ba ta tsaya doguwar addu'a ba,ta dubi A'isha,amso shi ki bashi ya sha, ta dubi
Hajiyarmu tamkar ta ce a'a amma bata iya jan musu da Hajiyarmu, ta miƙe ta fita yasa kai zai fita daga
falon zuwa inda zuciyarshi ta raya mishi watan gidan rainon yara sai ya ji muryar A'isha, Uncle ya juyo wai
ka kawo shi in ji Hajiyarmu, ya zuba mata harara,ai dama nasan ba son shi ki ke ba, in dai irin rainon da
Hajiyarmu ta yi mun ne zaki mishi gara na kai shi gidan rainon jarirai. Ta zaro idanu, yi haƙuri Uncle don
Allah, ya dube ta ba zan amince da nufinku ba, duk cikin al'adun Hausa Fulani wannan al'adar ce bata yi
min ba,babu hadisi ko aya da ta nuna cewa iyaye su dinga jin kunyar ƴaƴansu, tun ina ƙarami babu irin
wuyar da ban sha ba,dan kawai ina ɗan fari da kaina na dinga addu'a Allah yasa mahaifina ya sake
aure,ƙila matar zata kula dani,gara na kaishi in da zan zuba kuɗina a luran min dashi.

Dukan su ba suji shigowar Hajiyarmu ba, sai kurum suka ji ta ce A'isha koma ciki barshi ya kai shi ta kama
hannun A'isha tamkar ta ƙwace, amma ba zata iya bijirewa ba, ta bi ta suka shiga ciki, A'isha tana zama
bakin gado yana shigowa ya miƙa mata shi. Ta kalli Hajiyarmu sai tayi mata alama da kai,don haka sai ta
amshe shi shi ko ya fita. Hajiyarmu ta dubeta kada ki dinga barin shi yana kuka, mijinki za ya iya raba ki da
ɗanki, domin nasan da zaran ya sanar da mahaifinshi wannan matsala za ya gaya masa,baya kan
ƙudirinshi,kin ga ku, ƴan zamani ne ki kula da ɗanki kin ji ko? A'isha ta ce to haka suka ci gaba da wankan
su.

Satin su shida suka soma fita asibiti suka soma zuwa sannan gidan Anty Sadiya sai gidan su Fatima da
kuma su Nafisa. Ranar da suka je gidan Anty Nafisa cewa ta yi to A'isha an gama wanka lafiya yanzun
kuma sai azo a soma shirin gyaran jiki, A'isha ta taɓa baki um wane gyaran jiki bayan har yanzun Uncle
yana fushi da ni? Nafisa ta ce ni fa nawa ganin tsakanin ku aka shiga, A'isha ta ce Anty Nafisa wanene
zaya shiga tsakaninmu? Ni dai nafi zaton cewa na mishi wani laifi ne. Anty Nafisa tunda kuna shiri don
Allah ki same shi ki tambayan min shi mana? Nafisa ta ce kada ki damu, insha Allah komai zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0