Showing 3001 words to 6000 words out of 38755 words
Chapter 2 - Mummunan Zato Book 3 Complete Halina Mashi
ce, "Kada ki manta fa mijinki wayayyen ɗan boko ne,za ya iya gane
mu gurin magani, amma ki bar ni dashi." Ta kashe wayar ta shiga kiran ɗan Autanta Baba Sule,wai ya zo
ya sayo mata zoɓo a maƙota.
Bayan sun gaisa sai ya sheda mata saƙon Hadiza sai ta ce kai wannan yarinya da shiririta take, maganin fa
yana nan cikin durowarta ta gefen gado na kuma gaya mata shi ne zata taso ka don iya shege." Ya ce
"Cikin ne ya matsa mata shi ne ma yasa nazo da kaina." Hajiya Lanti ta soma latsa waya "bari in kira ta
mashiririciya." Ta kira ta ce"Hadiza kin manta na ce miki yana cikin durowa?" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce
"A to ni dai nasan na faɗa miki." Ta dube shi tana kashe wayar, "kaji wai sai bayan da ka taho ne sannan
ta tuna, kuma ta sha ya faɗa ciwon cikin." Ya ce "Ai shikenan." Ta buɗe fridge ta ciro zoɓon ta tsiyaya
cikin kofi. "Gashi ni muna ta magana ko ruwa ban baka ba." Tamkar kada yasha, amma sai ya ji ranshi na
so,ya amshi na kofin ya ɗan sha,sam bai kai na Beby daɗi ba,ya dai daure ya sha kusan rabin kofin,ta yi
murnar shan da ya yi don an ce ko ya ya yasha,matsalarta ɗaya ya yi bismilla.
A'isha tana shiga gida falonsu ta samu Hadiza da Tabawa suna tsaye, Hadiza da waya a hannunta,ganin
A'isha ta shigo sai ta hau yin wayar ƙarya. Ta ce, "Hello ka wuce Darling? Yauwa amma don Allah kada ka
je da wannan sarkin nacin,ok kama wuce kai kaɗai? To sai ka dawo mijina." A'isha duk tana jin ta, kuma
ta yarda wayar suke yi,tana ta kici-kicin buɗe ƙofarta. Hadiza suka kalleta suka sheƙe da dariya, ita dai ta
shiga ɗakinta ta faɗa kan gado, Uncle bai taɓa mata haka ba kuma bata taɓa zaton wata rana zata zo da
Uncle zaya yi mata haka ba,ta jawo jakarta ta ciro wayarta. Nafisa ta kira,tana ɗagawa ta ce, "A'isha kun
iso ne?" A'isha ta ciji leɓenta ta gefe, "Nafisa sai dai wani lokacin yau ba zan samu damar zuwa ba."
Nafisa ta ce, "Saboda me A'isha, har kin sani jin haushi da ina ta murna zan samu abokiyar hira,wai ma
me ya hana ki zuwa?" A'isha ta ce "Ba komai, da har mun fito da Uncle ya ce bari ya amso ma Hadiza
magani." Nafisa ta ce "wai da gaske ne Hadiza tana da ciki?" A'isha ta ce "Gaske ne mana ana ƙaryar ciki
ne?" Nafisa ta ce "A'isha kenan,baki san waye Hajiya Lanti da ƴarta Hadiza ba ne shi yasa ke ko Hajiyarmu
bata amince cewa Hadiza ciki gare ta ba, amma ciki ɗan duma ne,yaɗo yake in ya fito ma ganshi." A'isha
ta ce "Haka ne, yanzun dai ki min haƙuri, sai wani jiƙon." Nafisa ta ce, "Allah ya kai mu." Suna yin sallama
Uncle yana turo ƙofa,ƙin kallon shi ta yi ya iso gaban gadonta, "Beby tashi muje."
Yana magana yana kallon agogon hannunshi,ji ta yi tamkar ta juyo ta ce ba zani ba, amma tana kallonshi
sai ƙwarjininshi ya hana,ƙimarshi gareta ta wuce nan, cikin sanyin murya ta ce , "ka tafi Office ɗinka
kawai Uncle,ka yi latti wata rana naje." Ya ce, "amma ni ne nace ki tashi muje." Ta ce, "Ka bar shi mun
riga mun yi waya da ita." Ya zuba mata idanu sai ya ji ranshi yana zafi,wato ita wannan haushi ta ji kenan?
Ya ɗaure fuska. " Kina nufin cewa haushi ki ka ji?" Ta girgiza kai, ya ce to in ba kin ji haushi ba, menene na
cewa kin fasa? Kina nufin kada in amso mata magani? Ko don ba ke ba ce? Mamaki ya cika A'isha, ta
shiga kallonshi a tsorace, muryarta tana rawa ta ce ba fa nufina kenan ba, ya katse ta, "Ke da Allah yi min
shiru,ke in kina naki ciwon menene bana miki don kawai na amso mata magani za kiyi fushi? To ki fashe
duk wadda na aje sonta nake don ki ji ki sani." Ya juya ya fita.
Kanta ya ɗaure matuƙa,lafiyan Uncle kuwa? Itama ta miƙe ta shiga zirga-zirga a tsakar ɗakinta, ba ta taɓa
shiga cikin irin wannan halin ba, ba ta taɓa ganin Uncle ya faɗa irin haka koda ga wani ba bare ita. A
ƙarshe ta ba wa kanta laifin cewa ƙila ya ji haushi ne ba ta bi umurnin shi ba,in ya dawo zata ba shi
haƙuri. Ranar dai yini ta yi tana zubar da hawaye.
Shi ko yana fita ya shiga mota har zaya tada Jabir ya rugo da gudu ya ce, "Gani maigida, ya bashi makullin
ya matsa gefen direba, maimakon baya da ya saba zama. Ya ƙwantar da naganshi a kujera ya yi ajiyar
zuciya, ya lumshe idanu. Yana son tuno meke damunshi ne? Jabiru ma ya lura yau kam maigidan nashi
ranshi ya na ɓace ne. Ko a Office bai ba wa sakatariyar sa damar ta shigo masa da kowa ba, duk da jiran
da mutane suke mishi. Ya lumshe idanunshi yana karanta sunayan Allah,kusan minti talatin sannan ya
soma ganawa da mutane. Kaɗan-kaɗan zuciyarshi ta soma sanyi, ƙarfe biyu yana zaune a ƙayataccen
gidan cin abincin da nan ya kan ci abincin rana. Yana so ƙwarai ya sha zoɓon A'isha, ya ɗauki waya ya kira
ta lokacin tana zaune kan sallaya har lokacin tana zubar da hawaye gaya ma Allah take yi da sauri ta miƙe
ta ɗauki wayar, muryarta a dusashe ta ce, "Salamu alaikum." Ya amsa sai lokacin ya ke tunawa sun fa ɗan
samu matsala da safe, take kuma ya ji a ranshi tamkar bai mata adalci ba, ya amsa da
wa'alaikumus-salam , Beby zan samu zoɓon kuwa?" Ta ce, sai dai a dafa, ya ce to Uche za ya kawo min
ko?" Ta ce eh, ta miƙe ranta ya yi ɗan sanyi ta shiga kujuba-kujubar dafa zoɓo.
Cikin mintina ƙalilan ta gama, musamman da ya ke tana da ƙanƙara ta kira Uche da wayarta. Tabawa ƴar
rahoto tana kallon lokacin da Uche ya amshi ƙwando ya fita,ta shiga gurin Hadiza. "Antina wai menene
ake fita dashi cikin ƙwando kullum?" Hadiza ta taɓa baki,zoɓo ne wahalalliya kullum sai ta dafa shi an kai
ma maigidanmu." Tabawa ta ce, amma ya kamata a ɗauki mataki kan wannan zoɓon, Hadiza ta ce,ƙyale
ta tayi,ni dai ba zan iya wahala ba. Tabawa ta gyara zama ta riƙe ƙugunta tare da miƙa kai ta ƙanƙance
idanu, "Antyna an ce miki haka kawai Hajiya Lanti ta kawo ni aiki nan gidan? Ta cigaba to in baki sani ba
bari na sanar da ke, sai da na ɗauki alƙawarin tarwatsa gidan nan tare da karɓar miki ƴanci gurin
mijinki,ko kin san ni ce na kawo shawarar ace kina da ciki? Shin haka bai miki daɗi ba yanzun? Cikin
mamaki Hadiza ta matso daf da Tabawa ta ce ,"Da gaske ki ke yi?" Tabawa ta ja tsaki "An ce miki a banza
maza suke shakkar aurena? In da zaki ji tarihina tun ina ƴar ƙanƙanuwata sai kin sha mamaki, domin tun
ina ƴar shekara uku na kashe auren wata da Ubana kan daddawa, sannan na hana duk matar da ya auro
zama,to ki gaya min auran wa zan bari? Hadiza cikin jin daɗi take jinjina kai, sannan ta ce, "Tabawa nayi
farin cikin samun ki, to yanzun me ki kace a batun zoɓo?" Tabawa ta ce, "Yauwa kin san takan zoɓon nan
sai tafi ku ƙwarjini? Don haka ki bar batun zoɓon a hannuna kina nan za a gabza rigima takan tsinanne
kuma a daina yin shege,in kun bar ni da yarinyar nan ba sai an kai ta gaban malami ba,tsabar kissa ma ta
isheta, ita kuwa waccan tsohuwar guzumar biyu zamu haɗa mata." Hadiza cikin murna ta kai hannu suka
tafa da Tabawa, tare da cewa. "Haka ni ke son ki ƴar gari."
Misalin ƙarfe shida saura ya shigo, Tabawa ce kurum zaune a falo tana kallon T.V da sauri ta miƙe tana
mishi sannu Alhaji sannu da zuwa,ya ce yauwa ya nufi ɗakin jummy. Ta yi karaf ta ce "Ta fita Alhaji bata
nan." Ya dubi Tabawa,a ranshi baya son irin waɗannan mutanan, ya nufi ɗakin A'isha,tana zaune kan
kujera fuskarta na kallon T.V amma zahiri ba tasan me ake yi cikin aƙwatin ba, har yanzun in ta tuna
kalaman Uncle suna soya zuciyarta,sam bata ji murɗa ƙofar shi ba, kuma bata ji sallamar shi ba. Ya tsura
mata idanu ya ce "Beby." Ba ta ji ba,ya sake cewa "Beby." Da ɗan ƙarfi ya yi maganar, firgigit ta ce
"Na'am."
######
[12/18, 21:24] Ummi Tandamaí ½í¸‡: *í ½í³”í ½í³”í ½í³” Page 3*
Ta dubeshi ta zamo ƙasa tana mishi sannu da zuwa. A sanyaye ya amsa ta miƙe kamar yanda ta saba,ta
ɗauko mishi ruwa ta cika kofi ta miƙa mishi cike da girmamawa,ya amsa yana kallonta, ya zauna yana
sha,yasha kusan rabi kafin ya dube ta, Beby ba ki da lafiya ne? Ta dube shi hawayan da take ɓoyewa suka
sulalo, cikin rawar murya irin ta masu kuka ta ce "Uncle don Allah ka yi haƙuri." Ya matso ya ɗagata ya
rungume yana shafa kanta,ina tsokanarki ne fa Beby,ba wai faɗan gaske nake miki ba, daina kuka ya shiga
share mata hawaye,kusan minti biyar yana lallashinta sai da yaga tabbas ta haƙura sannan ta yarda kan
cewa yana mata wasa ne sannan ya fita.
Tabawa tana son sanin me yasa Alhaji ke daɗewa a ɗakin A'isha, duk in ya shiga ba ranar girkinta ba?
Kuma me yasa sauran ɗakunan baya daɗewa? Ɗakin Hadiza ya nufa wadda tuni Tabawa ta sanar da ita
dawowarshi, ta kuma bata shawarar cewa tunda ita ce dashi ta aje ciwo ta tashi ta yi shirin amsarshi, ta
kuma ce wannan garin maganin da na baki ki tabbatar cewa kin yi tsarki dashi." Ta juya da sauri zata fita
don kada ya isko ta ciki,ta juyo ta ca "Af,na manta ki tatsi kuɗi dai." Ta fice dai-dai lokacin da shi kuma ya
fito daga gurin A'isha kamar ya wuce sai kuma ya tuna ya bar ta babu lafiya,don haka sai ya shiga. Tana
cire kaya zata shiga wanka zaninta na ɗaure a ƙugu ta cire riga ta juya tana mishi sannu da zuwa,ya dubi
ƙirjinta ya kauda kai, ya ce kin samu sauƙi kenan? Ta yi fari tare da cewa sosai ma,ya ce mun gode Allah,
bari in shiga in ɗan watsa ruwa kafin a kira magriba.
Bayan sallar isha'i ya gama koman shi har yanzun zuciyarshi tana tana tausaya ma A'isha tana ƙara son
Aisha tana muradin yarinyar sosai, ya kasa sukuni saboda ɓata mata ran da ya yi gani yake har yanzun
tana can ranta ɓace, saboda bata iya fitina ba, ya ɗauki wayarshi ya kira ta ta ɗaga ya ce, "A'isha me ki ke
yi ne yanzun?" Ta ce, "Ina kan sallaya ne ina Istigfari yau duk ban samu zama ba sai yanzun." Ya ce, "Allah
sarki, Bebyn Uncle yau ya ɓata miki rai ko? Kiyi haƙuri..." Ta yi saurin katse shi da cewa,kar kace haka
Uncle,kada ka bani haƙuri,ba ka min laifi ba,kai babba ne ba na zaton zaka yi abinda zaya sa har ka bani
haƙuri,ta yi ƴar dariya,mun wuce gurin komai ya wuce, ya ce "shikenan Beby kiyi bacci tare da mafarki
mai daɗi" ta ce kaima haka.
Sha ɗaya da ƙwata Hadiza ta shigo ɗakin maigidan, lokacin yana zaune gaban laptop jikinshi sanye da
fararen kar ɗin kayan bacci, ya ji shigowar ta amma saboda bata yi mishi sallama ba sai yaƙi ɗago
kanshi,ta zo ta zuba yatsunta a kafaɗarshi, lokaci guda kuma ta sumbaci kumatunshi, har lokacin share ta
ya yi,ta manna ƙirjinta da bayanshi tsaf ya tsaya sannan ya ce wai Hadiza yaushe za ki koyi shiga wuri da
sallama ne? Ta sa hannu ta matsar da laptop ɗin,ta ƙwanta a cinyarshi ni da ɗakin mijina sai nayi
sallama? Ya ce ko ɗakinki zaki shiga ya dace kiyi sallama,tasoma yi mishi wasu salon nata da ta haddace
su, na jan hankali,kafin wani lokaci ta zurma shi sai da suka yi nisa ya ɗanɗani maganin ta lura kuma ya
soma zaucewa, sannan ta yakice shi ta ɓata rai, ya kasa ɗaurewa ya soma lallashinta ta ce ita shikenan
kullum sai dai ya ƙwanta da ita ba ya bata komai,ta gaji, ranshi ya ɓaci amma ba zaya iya haƙura da
abinda ya ɗanɗana ba, cikin zaƙuwa ya ce gaya min me ki ke so tunda ke ba zaman aure ki ke ba,babu
yanda za'ayi in amshi haƙƙina gare ki sai na biya? Ta ce zaka sai min mota? Ya ce a'a ki je abinki, ta ce to
in zaka bani dubu ɗari to in ba zaka ba ni ba shikenan. Ta kuma ƙwanta,don ta sani dole ne ya dawo mata
tunda shima ba baya ba, ballantana ya dangwalo wannan laƙanin nasu wanda suka yi wa laƙabi da sa
maigida hauka, yanda kuwa ta yi tunanin haka ne kasa jurewa ya yi sai da ya nemo ta tare da amincewa
zaya bata dubu ɗari, amma abinda ya ba shi mamaki irin daɗewar da ya yi har kusan Asubahi ya kasa
biyan buƙatar shi, sai da ƙyar, tun a nan ya soma zargin ta yi amfani da wani abu tunda yasan kan shi.
Hajiya Kari ta kalli Hajiya Jummai," ke matsalarki kenan, kullum in an ce miki ga wani malamin sai kina
gida ba su iya aiki ba,kin fi son na daji ko na ƙauye, alhalin irin ɓarnar da na gidan keyi,zaki sha mamaki"
Jummai ta ce to ai ni sai in zata na cikin gari imani ne dasu ba za suyi maka wani abin ba, Karima ta
ƙwashe da dariya sannan ta ce, "Bari in sanar da ke wani abu,kin ga wannan malamin da na ce muje
gurinsa? Bata jira amsa ba ta ci gaba "Tantirin malami ne,kin san mun ci karo da gwamnan garin nan a
gurin shi ranar da na je da daddare? Jummai ta ce, ke haba? Kari ta ce, wallahi ban ma gane shi ba shi
kaɗai ya zo a sace, malamin ke faɗa min." Jummai ta ce in ko haka ne muje domin duk wanda ki ka ga
ƴan siyasa suna zuwa gurinshi kin san ya yi ne. Karima ta ce haka ne, yanzun dai abinda nike so da ke in
mun je ya buga bai ga mutuwar kishiyoyinki ba, to sai ki ce mishi ya yi miki na wani abin abu ko ciwo ko
hauka,ko ki dinga haɗa su husuma da maigidan,ke kuma ki koma kiyi ta lallashin mijinki."
Jummai ta ce "ai ni na tsani in gansu ne a gidan,Kari ta ce in lokacin mutuwarsu bai yi ba ya za kiyi?
Jummai ta ce haka ne, tunda gashi nayi-nayi ɗin sun ƙi mutuwa, musamman wannan A'ishan duk nafi jin
haushin matsiyaciya, wallahi da za a bani bindiga ace in kashe wanda na fi ƙi ko? Wallahi Kari A'isha zan
kashe ita ce mutum ta farko da ta karya min ƙwarina, irin kuɗin da na narkar kan ta mutu yarinyar nan ko
ciwon kai bata yi ba, sai ma ɗaukaka da kullum take samu gurin miji, nasara ɗaya na san na samu kanta
shi ne cire cikin nan nata." Karima ta ce, "yanzun dai in mun je gaban Malam ki baje kolin matsalolin ki.
Jummai ta ce shikenan.
Misalin ƙarfe huɗu suka isa gidan Malam, Kari ce ta zaɓar musu wannan lokacin a cewarta ba'a cika
samun layi ba, mutum biyu suka samu. Ɗaya a ciki ɗaya na zaune kan ɗaya daga cikin kujerun da ya jera
a cikin zauran nashi,don zaman jiran shi. Suka dubi na zaunen suka ce da baƙi ne ko? Ta ce eh. Jummai ta
kuma kallon matar lallai wannan mutumin da gani mai yi ne, tunda ta ga irin waɗannan mata.
Tunanin ta ya tsinke lokacin da taga waɗanda suka fito daga cikin ɗakin Malamin suka kalli juna ita da
Karima kamar yanda suma waɗanda suka fito daga ɗakin Malamin suka kalli junansu, mai jira ta shige
gurin Malamin daidai lokacin da Hajiya Kari ta ce (cikin kissa irin ta matan bariki) a'a Hajiya Lanti duniya
ashe kema ki kan zo wurin Teacher? Lanti ta gyara zama cikin ƙarfin hali ta ce, a'a ai mu sai da su muke
iya kama gashin kuma ko'ina sai mu cinye mu bada siɗi." Karima ta ce,ana ki tunanin kenan, tunda dai jin
ta take tamkar ta dawo ta koma. Hadiza kuwa ita ma duk ta warware kallon kallo suke yi wa juna, Hajiya
Lanti ta kama hannun Hadiza suka tafi. tana cewa wa kada ki damu ni dama ai na daɗe da sanin Jummai
a wannan fagen sai dai ita da kanta ta sheda cewa ko gidan giya akwai babba,ta jima da sanin cewa ina
samanta.
Ita ko Jummai ta kalli Kari ta ce, "Anya zamu shiga gurin Malamin nan? Kari ta ce, shiga kai,in kinji shiga
ɗaya kenan." Ta ci gaba da cewa, "ke dai shawarata da ke ɗaya ita ce,ki saki kuɗi in har ki ka cire maƙo, to
har sirrin su sai mun ji a gurin shi." Jummai ta ce kuma zai faɗa? Kari ta ce, sosai ma,in kin ji faɗi ɗaya
kenan. Da zaki ji tawa ma tashin farko ki bashi kujerar Makka,kin san Allah da kin sha mamaki." Kafin ta
ce komai har ta ciki ta fito,dan haka Kari ta yi saurin jan hannun Jummai suka shiga.
Yana zaune kan wani farin ƙaton buzu, gabanshi wani ƙaton carbi ne da wata ƙasa cikin faranti ko ina in
ka kalla zaka ga kaya,ƙwalabe ne, litattafai ne da dai sauransu, suka zauna kan tabarma,ya ɗago ya zuba
masu idanu zuwa can ya ce "Hajiya sannunku da zuwa,a tare suka amsa sannan suka gaidashi, Kari ta fara
da cewa, " Na zata baka gane ni ba" ya yi ƴar dariya sannan ya ce me zai hana ni gane