Showing 9001 words to 12000 words out of 38755 words

Chapter 4 - Mummunan Zato Book 3 Complete Halina Mashi

09 Jul 2025

2067

ta ce
gini kuma? Nafisa ta ce bai sanar da ke ba kenan? A'isha ta ce, yace min dai yana gyaran gida. Nafisa ta
ce, to ai gyaran kenan, Jummai ya fafaramma gini irin kuɗin da yake narkarwa a ginin sai kin gani yanzun
ya gama kayan da za'a zuba ma daga (Chaina) za'ayo Odar su, A'isha ta ce to Allah yasa alheri." Nafisa ta
ce,au! Ke bakiji haushi ba? Ta ce, to in naji ma Anty Nafisa ya ya zan yi? Tsaki Nafisa ta kuma ja,ke tafi can
ke dai son miji ya yi miki yawa,ba ki iya ganin laifin shi. A'isha ta yi ƴar dariyar takaici, sannan ta ce to in
ma naga laifinshi me ganin laifin za ya maganta min? Nafisa ta ce shi kenan mu dai mun ga laifin shi
gidaje nawa gareshi cikin Katsina da kewayenta? Ya maidata wani mana za'a tsaya ɓarnar dukiya,kin san
Allah, Alhajinmu da Hajiyarmu sun ji haushi, harkokin shi ma fa yaƙi ya maida hankali sai ka ce yau ya
soma gini. A'isha ta ce Allah ya ƙyauta kuyi haƙuri kada suyi fushi da shi,tamkar Nafisa ta shiga ta waya ta
doddoke A'isha don haushi, ta kula A'isha ba zata taɓa ganin laifinshi ba, don haka sai ta canza zancan da
cewa,ki je asibiti mana? A'isha ta ce nima tunani na kenan, sai kuma naga ni ba ciwo cikin ke min ba,
kuma ba wani guri ne ke min ciwo ba a jikina, sai naje na cewa Likita ina jin motsi? Nafisa ta ce kin ji irin
haukan naki ba? Ki je ki yiwa Likita bayani,in yaso ayi miki (Scanning) a ga me ke damunki,in bai ga komai
ba a koma Islamic." A'isha ta ce, shi kenan zan je, ki gaida min su Hajiyarmu."

Lamo ta ƙwanta tana tunanin me ya shiga kan Uncle ne? Don kawai yana yiwa Jummai gini sai ya share
ta? Zata ce kada ya yiwa Jummai gini ne? Ba tare da ta gansu ba? Haƙiƙa ranta fa ya ɓaci sai dai bata son
ta nuna ma ƴar uwarshi ne. Ta kira wayarshi abin al'ajabi ya ƙi ɗauka, har sau uku, sai ta tura mishi da
text cewa,in ta mishi laifi ne don Allah ya yafe mata, rashin sa ya saka ta cikin damuwa,don Allah yaushe
zai zo? Saƙon na isa sai kiranshi har tana murna ga zatonta sulhu zaya nema, sai kurum ya ce "ke kin fa
matsa min da yawa......

######
[12/19, 22:33] Ummi Tandama😇: *📔📔 Page 5*



Ban cika son mace mai jarabar tsiya ba, duka-duka yaushe ne ban zo ba na shekara ne? Kin dameni don
Allah daina kirana in na matsu zan neme ki da kaina." Kan A'isha ya yi matuƙar ɗaurewa,bakinta yana
rawa ta ce, "Yi haƙuri Uncle nima ba wai na ce kazo ba ne,na zaci na maka laifi ne shi yasa." Tsaki ya ja
kafin ya kashe wayar, wannan lamarin ya firgita A'isha sosai, baiwar Allah ranar sai dai bacci ɓarawo,
amma bata runtsa ba. Maƙotanta su kansu cikin ƙwanaki sun fuskanci tana da damuwa koda suka
tambaye ta sai ta ce musu bata jin daɗi ne. Anty Maimuna ma ta matsa mata dason sanin damuwarta,
amma A'isha sarkin zurfin ciki ta yi ƙememe ta ce zuwan jarabawa ne. Yanzun suna karatu ba dare ba
rana,Anty Maimuna ta ce to Allah ya taimaka.

Cikin haka ne A'isha ta samu ziyartar asibiti inda ta samu ganin Likitan mata. Bayan ta gama mishi bayani
ya tambaye ta ko tana da ciki ne? Ta shaida mishi ita kam bata da komai,don haka ya bukaci ta ƙwanta
kan gadonsu na likitoci don yi mata (Scanning). Bayan ya gama bai ce mata komai ba, sai da ya fitar da
sakamako ya dube ta, "kina da miji?" A'isha ta ce "Eh." Ya miƙa mata sakamakon, tana buɗewa idanunta
na sauka kan (EDD) ta maimaita kalmar a fili (EDD) kuma? Ta dubi Likitan ta ce,kana nufin ciki ne da Ni?
Ya ce wata baƙwai ta zaro idanu tare da ɗora hannunta kan mararta, sannan ta ce Likita ka kuwa duba
sosai? Ya yi ɗan murmushi,a katin ki naga cewa ke ɗalibarmu ce amma kin kasa gane kina ɗauke da
ciki,kina nufin ko kaɗan ba wata alama da ki ka gane kina ɗauke da ciki?" A'isha ta girgiza kai tare da
cewa, "Ina al'ada duk wata sannan wata bakwai ɗin da ka ke magana nayi ɓari lokacin wata uku."

Ya zuba mata ido, "Ya ya abin ya faru wancan lokacin? Ta bashi labarin a taƙaice, ya ce to wankin cikin da
baayi miki ba shi ne dalilin da ba a wanke ɗan ba, Allah ya sa zaya taka doron ƙasa, sai dai zaya iya
kasancewa watannin cikin ya koma baya. Yanzun dai cikinki wata bakwai da sati ɗaya.

Jugum A'isha ta yi tana tunanin wannan lamarin na Ubangiji,lallai wannan shine mafi girman abinda ya fi
bata mamaki,iyaka tsawon rayuwarta, sannan ta yi murna mara adadi kuma ta san wannan labarin in ta
bawa Uncle shi zai kawo karshen rashin jituwarsu, ko ta ce fushin da yake yi da ita, wanda bata san
silarshi ba. Ta jawo wayarta ta shiga neman shi da glo ɗin shi har sau biyu tana rurinta tana katsewa bai
ɗaga ba hakan (MTN) ɗin shi jikin ta ya yi sanyi, amma duk da haka ta daure ta kira (Seltel) ɗin shi daf da
zata katse ya ɗaga, gabanta na faɗuwa ta yi sallama,rai ɓace ya amsa sallamar, kafin ta yi magana ya ce
wai lafiya ne? Ta ce a'a dama ina son muyi magana ne. Ya katse ta da cewa,bani da lokaci, sannan ya yi
tsaki ya kuma kashe wayar. A'isha ta zabga uban tagumi nan take kanta ya shiga sarawa,kuka mai ƙarfi ne
ya ƙwace mata,ta yi shi har ta gaji babu mai lallashi. A'isha ta zama tamkar wata zararriya wa zata tunkara
da matsalarta? Zuciyarta ta ce mata Ubangijinki, ranar kuwa ƙwana ta yi kan sallaya tana kaiwa Allah
kukanta, zuwa safe ta ji ɗan dama kuma ta yanke hukuncin har ma cikinta batun cikin jikinta dama
Ubangiji shi ne ya ɓoye kayanshi, ko Nafisa ba zata faɗa mawa ba, haka ta ci gaba da rayuwarta cikin
makaranta.

Jummai kuwa ta samu yanda take so,da tace kaza za ya yi mata, gini kuwa an gama an kuma danƙara
kaya na iyayan kuɗi sannan ta shirya walimarta ta gani ta faɗa suka shige ita da Suby da Sofy Sai gefen
maigidan. Hakan ya yi matuƙar tunzura Hadiza nan ta tada bala'in cewa ba zata yarda ba, rigimar ta kai su
ga manya inda Alhajinmu ya ce tunda ya yi wa Jummai dole ne sauran matan ya yi musu, dole yasa aka
bige gefen Hadiza da nashi da na Jummai na da aka hau yiwa Hadiza nata amma A'isha dama ko ƙasa da
sama za su haɗe ba za ai mata wani gyara ba. Ya dai sa an ragi falon an bar mata ɗan ƙarami ya zuba
mata tsofaffin kujerun falon. Rashin kunyar da Hadizan ta mishi lokacin ya isa sakinta, sai dai ɓarin da tayi
ne yasa ya bar ta ko Allah zai sa ya kuma samun wani rabon daga gare ta, don shi ya yarda har ga Allah
ciki ne kuma ya amince cewa ɓarin ta yi irin kuɗin da ya kashe lokacin da suka zo da batun ɓarin suna da
yawa, sannan sun hana shi zuwa asibitin a cewar su ba sai ya je ba,daga ƙarshe ma da suka ga ya matsa
kan cewa zai je sai suka dawo da ita gida, Likitan da suka naɗa na ƙarya ya ci gaba da zuwa duba ta.


**** **** **** ****

A'isha tana matuƙar tausayawa kanta don zurfin cikinta ya hana ta sanar da wani bare a tausaya
mata,don haka ta shiga rama ta koma sirit sai nono sai ko cikinta wanda ya bayyana lokacin Anty
Maimuna ta yi ta yi da A'isha ta sanar da ita matsalarta, amma ta ƙi cewa kurum take karatu ne don bata
son tambaya ma ta rage zuwa gidan, cikin haka ne suka samu hutu na ƙwana goma jal, tamkar kada ta
tafi Katsina, amma ya zamar mata dole tunda bata da kuɗi duk sun ƙare komai nata ya yi ƙarƙaf, ta yi ta
kiran Uncle a waya don ta sanar da shi a zo a ɗauke ta, amma yaƙi ɗaga wayar. Abin ma ya daina bata
mamaki ya shiga bata tsoro,bata son kowa ya san halin da take ciki, don haka ta ƙi kiran kowa ta nufi
tasha.

Sun iso Katsina biyar saura,nan ma ta ɗauki shatar Taxi zuwa gida, har cikin harabar gidan ta ce ya shiga.
Maigadi na ganinta ya buɗe Gate ɗin gidan,tana fitowa Uncle ta gani tsaye jikin mota yana waya, Jabiru
yana riƙe da jakar Uncle ɗin ta Office da alama dawowarshi kenan daga Office ya bi motar da kallo don
ganin wanene ya shigo masa cikin gida da Taxi? Ranshi ya yi mugun ɓaci lokacin da suka yi arba da A'isha,
sai ya ji tamkar ya hau ta da duka,nan take ya ɗauke kanshi daga kallon gurin da take. Ganin haka bai
bata mamaki ba, domin nata zaton na ma zaya kore ta ne, ta ciro kuɗi ta bawa ɗan Taxi ta saɓa jakarta
tare da jan akwati, sai lokacin ta soma tambayar kanta wane gefe zata nufa, domin gaba ɗaya fasalin
gidan ya canza, tana kallonshi ya nufi sabon ginin wanda take zaton shi ne na Hajiya Jumman.

Ƙofarsu ta da ta nufa duk da ta kula nan ma akwai ƴan gyare-gyaren da aka yi,taja ƙofar a kulle take gam
don haka ta shiga ƙwanƙwasawa. Jim kaɗan ta ji muryar Tabawa tana tambayar wanene? A'isha ce ta
ce,nice Tabawa buɗe. Ganin A'isha sai ta hau sheƙa dariya,dama ke ce haka? Ta taɓa baki,ai yanzun
ƙofarki ta koma can, ta nuna gefen gareji, A'isha bata gane ba, amma yarda Tabawa ke tuntsire dariya shi
ne ya sa ta saɓa kayanta ta nufi gefen gareji. Sule mai bawa fulawa ruwa ya nufo ta da sauri yana yi mata
sannu ta amsa mishi, ya ɗauki akwatin tare da cewa ai Hajiya an samu ƴan gyare-gyare ne a gidan suna
isa ƙofar tana kulle ya ce bari in amso miki makullin gurin maigida, da gudu ya nufi sasan Jummai.

Ya samu maigidan nashi yana shirin shiga wanka in da Jummai ke ta faman riritashi tamkar ƙwai, ya yi
sallama Sofy ta zo menene? Ya ce maigida nake nema,taje ta sanar da shi. Jummai ta fito tace menene?
Wanka zai yi, ya ce ranki ya daɗe zan amshi makulli ne na gefen gareji, ta yi guntun murmushi sannan ta
juya. ya fito fuskarshi ɗaure hannunshi riƙe da makullan, gashi ka bata sakaryar yarinya kawai,Sale ya
amsa ya fita daidai sanda Alhajin ya ci gaba da cewa don iskanci sai ta kama shigowa motar haya Taxi har
cikin gidana? Jummai ta taɓa baki wannan tsageruwar yarinyar mara kunya mene ne ma ba zata yi ba,ya
katse ta da ɗaga hannu saurara min tsagerancin me Beby ta yi miki? Nan ta tuna da sharadin boka da ya
ce kada ta yarda ta kushe A'ishan a gabanshi, yin haka zaya ringa lalata aikin dole sai ta saka kissa cikin
lamarin. Aikin da kissa zai tafi ba da hassada ba, don haka sai ta wayance da cewa ba Suwaiba ka ke nufi
ba? Ya girgiza kai ni ban ce miki Suwaiba ba, kuma bana son in Ina ma wata faɗa a dinga sa min baki ta
dafashi muje kayi wanka mijina,ni kaina ban za ci kana nufin Bebynka ba, ina zaton Suwaiba ce shi yasa,ni
ko me A'isha zata min na tsageranci,yarinyar da magana ma bata dame ta ba,ai ita ce ta dawo? Lallai ina
mata Sannu da zuwa,tsaki yaja sannan ya nufi gurin wanka.

A'isha ta buɗe ƙofa ta shiga, tsayawa ta yi tana kallon ɗan tsuku kun falon, kujerun suna da ne cikin falon
sai ko T.V ta tura ƙofar ɗakinta ta shiga duk ko'ina ya yi ƙura,bata gaji ba ta tuɓe ta shiga gyaran ko'ina, da
falo ta soma har ga Allah ita waɗannan dakunan sun ishe ta, ina laifi mutum mai zaman kabari ya samu
ciki da falo a gidan duniya ai ya ishe shi rayuwa, ta goge komai sai abinda ke bata mamaki shi ne ba taga
kitchen ba. Me hakan ke nufi? Ita dai tasha alwashin ba zata taɓa mishi zancan ba,zata fito da kayan

girkin ta ko a ƙofar ɗaki ne ta saka risho, ta yo wanka bata shafa mai ba saboda zufa ta zumbula doguwar
riga ta zo falo ta zauna, yanzun matsalarta yinwa ta miƙe ta fita harabar gidan, duk mazan ƴan aikin sun
tafi gida sai Baba maigadi kurum. Ta isa gurin shi ta ce don Allah Baba duk su Sule sun tafi ne? Ya ce sun
tafi Hajiya kina son wani abu ne? Ta ce biredi nake so, da kayan tea, ya ce to bari a karɓo miki dama ɗari
biyar ɗin kenan ta miƙa mishi gashi duk yanda ya kama ka sai min,ta koma ciki. Can ta fito don tago ko ya
dawo dai-dai lokacin da aka soma kiran magriba. Ya miƙo mata saƙon daidai lokacin da Uncle ɗinta ya
fito,ya bi ledar da kallo ita dai ta amsa ta juya bayan ta ce ta gode.

Uncle ɗin nata ya bita da kallo tafiyarta irin ta masu ciki ya raya a ranshi ya isa gurin maigadi Baba ina ka
je ne? Ya ce Hajiya na siyoma kayan shayi. Kayan shayi? Eh, inji Baba maigadi. Uncle ya kaɗa kai ya nufi
masallaci. Ranshi ɓace,me yasa A'isha ke sha'awar wulaƙanta shi a idanun duniya ne? Ɗazun Taxi ta
shigo mishi da ita har cikin gida yanzun kuma kayan tea ƙulli-ƙulli kamar gidanshi, motocin shi nawa?
Sannan shaguna nawa ke gareshi cikin plaza, daban-daban? Ya yi ƙwafa.

Ita kam ta samu ta jona ruwa ya tafasa tasha tea ɗin ta ta ƙoshi, ta yi sallolinta, ta ƙwanta don ta huta.
Sai dai maimakon bacci sai ta soma karanta matsalolinta. Tuni ta nemi bacci ta rasa, don haka sai ta miƙe
ta soma da yin alwala, ta shiga kai kukanta ga Allah domin iyaka tunanin ta shi ne kurum zai yi mata
maganin dukkan wannan halin da ta shiga.

Uncle ɗin ta kuwa don takaici ya kasa cin duk kayan alatun da Hajiya Jummai ta shirya mishi, zuciyarshi
sai ƙara zafi take game da Beby. Jummai tasan komai,don tun lokacin da ta ji dawowar A'ishan sai ta zuba
rushi cikin kasko ta kara hantar nan mai cake da allurai, shi yasa zuciyar maigidan ƙara zafafa,kamar
yanda Malamin ya tsara mata, ta dube shi maigidana wai me ke damunka ne? Ya ce wallahi Jummai
A'isha ce ta bani haushi. Ta ce haba Alhaji me A'isha zata yi maka ka ji haushi, irin haka bayan ka sani
cewa yarinya ce? Ka dai same ta ne ka nuna mata baka son shiga motar haya tunda Allah ya hore maka,
ya dubeta, to bayan ma wannan ina fita sai naga wai ta aiki Baba maigadi siyan biredi da madaran ƙulli
dibi wannan cin zarafin? Hajiya Jummai ta ce,lallai bata ƙyauta ba, amma ka mata uzurin cewa daga
tafiya ta dawo,kai itama da rashin dabara take maimakon ta zo nan ta amshi abinci in tana jin yunwa ne?
Ya ce girman kan nata zai bar ta ne? Ya sake yin ƙwafa, zuciyar Jummai kar da murna, ta ce to kaje can
gurinta don yau ita ce da kai tunda tafiya ta dawo. Ya ce bar ta ba zan je ba. Ta haɗa fuska wallahi sai kaje
don bana son shiga haƙƙin wani, Allah ma ya sani. Ya ce kina korata ne? Ta ce a'a ni dai nafi son ko lahira
mijina ya tashi daga cikin maza masu adalci, ya ce haka ne zata ci albarkacin ki ne zan je amma ba don ita
ba, ta miƙe ta zo ta ƙwanta a bayan shi na gode mijina nasan kai nawa ne daga duniya har abada, tashi ka
je bari na bika da abincin,ya ce bar su kawai ya fita ta bishi da kallo fuskarta ɗauke da murmushin cin
nasara tasan in ya yi arba da ita wani sabon haushin nata zai ji kamar yanda Malam ya tsara mata.

Yana ta bugun ƙofa ba ta ji ba sai daga baya, da sauri ta sallame ta nufi ƙofar, ta buɗe lokacin ya cika
tamkar zai fashe "waton wani sabon salon wulaƙancin ne haka,da kimarshi da komai a ce yana bugun
ƙofa ƴan aikin gidanshi suna ji,ya dubeta a zafafe, watan kina jina ina ta faman bugun ƙofa ki ka min
banza ko? Cikin sanyin murya ta ce kayi haƙuri Uncle wallahi ban ji ba, ina sallah ne ta kau ce ya shige ya
kalli falon ko'ina ya taɓa baki sannan ya shiga bedroom ɗin zuciyarshi na zugi so kurum yake yaga abinda
zai yi faɗa a kanshi ta buɗe fridge da nufin ta bashi ruwa amma sai taga wayam ta manta ɗazunnan ta
gyara shi babu komai ciki, ta dube shi yi haƙuri Uncle,ba ni da ruwa cikin fridge, ya katse ta nace nazo
shan ruwa ne? Ta girgiza kai, ya zauna kan kujerar madubi ita kam gabanta ne ke ta faɗuwa, ta cire
hijabinta tana ninkewa, ya zuba mata idanu can ya ce "ke." da sauri ta dubeshi "mene ne a jikinki? Ta
kallo cikinta kunya take ji ta ce mishi ciki ne don haka sai ta sunkuyar da kai tana ɗan murmushi da ƙarfi
ya ce "dake fa nake magana?...



######
[12/20, 19:35] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 6*



Ta dube shi cikin in ina ta ce shi ne dama nake ta kiranka ina son nayi maka bayanin baka saurareni ba, ya
ce bayanin me? Ya ci gaba da magana cikin ɗaga sauti kada ki ce min kina da ciki, ta zaro idanu gabanta
na faɗuwa, ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0