Showing 15001 words to 18000 words out of 38755 words
Chapter 6 - Mummunan Zato Book 3 Complete Halina Mashi
kuwa ta yi ta maza ta daure bata ce
mishi komai ba har sai da ya yi wanda ya zauna cin abinci, ita kuma tana kusa da shi tana zuba kissa da
salo,can ta ce waini Alhaji daga masallaci ina ka nufa? Ya dubeta, gidan su Alhajinmu naje. Suna lafiya? Ya
ce lafiyarsu lau, suna gaida ku." Ta yi shiru don tana son sanin ta ina zata fara batun A'isha? Can sai ta kira
Uche wanda yanzun ta ɗauke shi zuwa sasanta, ta ce shirya breakfast ka kai wa A'isha ko? Uche ya ce to
zaya tafi sai Alhaji Saddiƙ ya ce bata nan,da sauri ta sha mur sai ka ce gaske,bata nan ina ta je Alhaji kada
dai ka ce min ka saki yarinyar nan? Ya dubeta dama na ce miki zan saketa ne? Cikin sanyin jiki ta girgiza
kai alamar a'a, ya ce to ƙyamin wannan tambayar, kiyi harkar gabanki wannan ba matsalarki ba ce,ta
karkata kai Allah ya baka haƙuri ni kaina bazan so ka rabu da ita ba,dama ganin yanda ranka ya ɓaci ne.
Ya miƙe tsaye ya nufi ɗakinshi ba tare da ya ce mata ƙala ba.
Lamarin fa ya dagule wa Jummai lissafi,in maigidan ya yi kamar zaya juyu son rai sai kuma ya murɗe, tana
fa so ta san shin ina aka ƙwana ne batun cikinnan? Dole ta je gurin Malam yau saboda ya yi mata bayani
filla-filla, Lallai kam zata ga boni in har su Hajiyarmu suka ji batun ciki.
Ɗakin A'isha yana daf da na Hajiyarmu,tuni tasa aka gyare shi A'isha tana ciki a ƙwance tunanin rayuwa
kawai take yi, ashe akwai wani lokaci da zai zo Uncle ɗin ta ya juya mata baya? Musamman irin wannan
lokacin da ya kamata ace ya jata a jiki,ya so ta ya riritata, amma ba komai ta sani jarabta ce ta Ubangiji
yana jaraba bayinsa ta kowace hanya, ta yarda itama yana jarabata ne don ya gwada imaninta, Uncle
kuwa tana ta ƙara ba shi uzuri ba ta so ta tsane shi.
Yau ƙwananta uku a gidan tana cin gyaɗa dafaffiya da ta ce tana so Hajiyarmu tasa aka dafa mata, Nafisa
ta shigo da sallama tare da ƴar tsokana tana cewa mai ciki Uhum ga ni nan tafe, A'isha ta yi murmushi ta
ce Anty Nafisa ce yanzun? Ta zauna tare da ɗiban gyadar tana cewa tun ɗazun na zo ina gurin Hajiyarmu
ne, A'isha ta ce ina yini? Suka gaisa ta ce Yaya Bebynmu? A'isha ta yi ɗan murmushi ta juya zancan da
cewa yau fa sauran sati ɗaya mu koma makaranta, Nafisa ta ce har an gama yajin aikin? A'isha ta dubeta
da sauri ba yajin aiki mukayi ba. Nafisa ta ce to tabbas ni naji da kunnena makarantarku suna barazanar
tafiya yajin aiki,in har ba a biya musu buƙatunsu ba. A'isha ta ja tsaki, Allah yasa kada a tafi. Nafisa ta ce
amin, Brother ya zo kuwa?
A'isha ta yi guntun murmushi, ina ganin abubuwa sun mishi yawa ne shi yasa, Nafisa ta kalleta cike da
tausayawa,ke dai A'isha ba ƙya son laifinsa ne, amma in yana gari kullum sai ya zo gidan nan, yanzun dan
kina nan ne shi yasa ya daina zuwa. A'isha ta ce to ni me zan ce? Nafisa ta ce, Allah duk da ke ma shiyasa
yake miki wannan abin,ni duk son da nake maka wallahi in ka taka ni zan nuna maka kuskuran yin hakan.
A'isha ta ce to Anty Nafisa kin san ko na mishi wani laifi ne? Ai da baya min haka, sai in ga tamkar nayi
butulci in har na manta irin rainon da Uncle ya yi min a baya. Nafisa har da tagumi tana kallonta, kafin ta
ce A'isha ke kam ban ma san irin ki ba,ko son shi ne ya yi miki yawa? Oho, A'isha ta yi guntun murmushi,
sannan ta ce ke ba ki son Uncle Bello? Nafisa ta ce so kai amma fa bashi zai hana in ya min wulaƙanci in
kasa ramawa ba.
A'isha ta tsura ma ƙasa idanu,son kawai take ta tuno ta ya ya zata iya yin sa'insa da Uncle ɗinta? Ko rama
wulaƙancin da ya yi mata? Nata ganin yana mata hukunci ne sakamakon wani laifi da tayi mishi,
damuwarta ɗaya shine ya sanar da ita wannan laifin ko zancan ciki ta mishi uzurin rashin sani ta kalli
Nafisa tare da girgiza kai ni kam Uncle yana da wata irin ƙima a idona,ba zan iya ɓata mishi rai matsawar
ina sane ba, kuma ko yanzun nasan duk yanda aka yi ina da laifin da nayi mishi mai girma,tsaki Nafisa ta
ja sannan ta fita daga ɗakin,yarinyar ba zata gane cewa maza ba'a musu haka ba.
Daren ranar Alhaji Saddiƙ ya zo da daddare falo ya samu iyayan nashi cikin girmamawa ya zauna ya gaida
su, Alhajinmu ya fi sakar mishi fuska,shima ɗin ba kamar yanda ya saba ba, ita ko Hajiyarmu da ƙyar ta
amsa kalma ɗaya daga cikin jerin gaisuwar da ya jero mata,nan ya shiga kame-kamen cewa ya yi tafiya ne
shine dalilin rashin zuwanshi, sannan in ya nemi Alhajinmu a waya bata shiga,sai Alhajinmu ya canza
maganar da cewa ɗazun kaga baƙi a Office ɗinka? Ya ce ,eh sun zo mun kammala da su, zuwa satin sama
zamu tura musu da kuɗi in mun ga kayan nasu. Alhajinmu ya ce, shikenan,ya yi ɗan jim sannan ya ce,
A'isha na ciki? Hajiyarmu yi tayi tamkar bata ji shi ba,isowar Uwani kenan ta dire mishi ruwa ta ce eh tana
ciki,ya miƙe ya shiga, daidai lokacin da A'ishan ke kan sallaya hannuwanta a sama idanunta suna zubda
hawaye,tana cewa ya Allah kai ne mahaliccina da kai na dogara, kai ne kaɗai zaka sama min mafita cikin
lamarin nan nawa da mijina. Ya Allah daidaitamu cikin gaggawa, Allah ka shafe wannan matsalar
tamu,nan ta shiga kiran Ubangiji cikin sunayen shi keɓatattu,yana tsaye yana kallonta har ta shafa sam
bata san da mutum ba, ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya shiga cikin ɗakin,ta bishi da kallo har ya zauna ta
miƙe ta nufi ƙofa,ya danne wani abu da ke taso mishi ya ce ina zaki? Ta ce zan kawo maka ruwa ne, ya
girgiza kai yanzun nasha a falon su Hajiyarmu, ta dawo ta zauna kan sallaya sannan ta ce ina yini? Ya
amsa cikin cijewa domin lokacin wani irin haushinta zai ce ko tsana ma? Bai san ya ya zai kira abin ba, duk
da ƙoƙarin dannewar da yake yi fuskarshi ta canza, ya daure ya ce ya ya jikin? Ta ce Alhamdulillah, ta sake
duban fuskarshi gabanta ya faɗi saboda ganin irin yanda ya ɗaure, duk da haka ta daure ta ce, "Don Allah
Uncle kayi haƙuri,bisa ga laifin da nayi maka,koda dai ban san laifin ba,ya miƙe tare da juya mata baya,ba
abinda ya kawo ni yanzun ba kenan nazo ne na duba ki sannan ki min lissafin abinda ki ke buƙata ke da
Bebyn."
Ta tsura ma bayanshi idanu bata gajiya da yaba mishi cikin kowace Irin shiga, muryarta a sarƙe ta ce sai
dai ka tambayi su Anty Nafisa, ya juyo duk abinda suka zaɓa miki ya yi? Ta ce eh, sai dai batun komawata
makaranta, ya kuma dubanta yaushe ki ka dawo? Ta ce, Uncle mu ba ayi mana hutu, ya juya baya domin
in yana kallonta sai yaji ranshi ya fi ɓaci,ya ce makarantar ku sun tafi yajin aiki,ko dama ba a tafi ba bazan
bari ki haihu can ba." Ya nufi waje ni na wuce hope ba wata matsala? Ta ce babu,ka sauka lafiya, har ya
kai bakin ƙofa ta ce, "Na manta Uncle." Ya tsaya ba tare da ya juyo ba, ta ce wayata da kayana. To, kurum
ya ce ya wuce, don ya ƙosa ya bar ɗakin, haka kurum yake jin tamkar ya make ta,yana barin ɗakin sai ya ji
shi sakayau, ga mamakinshi da ya fito sai yaga mahaifan nashi sun canza mishi, da alama shigarshi gurin
A'isha ya yi musu daɗi,nan ya nufi gidanshi.
Haka A'isha ta ci gaba da zama gidan surukanta gata na duniya tana ganin shi matsalarta ɗaya ce, Uncle
ɗin ta wanda har yanzun yake nuna mata tsana da tsangwamma. Lura da ya yi cewa su Hajiyarmu ba su
da matsala in dai suka ganshi ya zo da gurin A'isha shiyasa shi kuma kullum zai zo da safe in ya taso Office
ma ya sake biyowa,duk kuwa da kasancewar dole yake ganinta,na ta gefen kuwa ta kan ji daɗin hakan
duk da ba wata magana mai daɗi ko kulawa yake mata ba, sai dai ta lura yana matuƙar ƙaunar cikin in
tayi la'akari da yanda ya narko ma Anty Nafisa kuɗi wai su je suyi siyayya, sai ga Anty Nafisa niƙi-niƙi,wai
ta zo suje siyan kaya,da taƙi zuwa sai da Hajiyarmu ta ce ta kimtsa su tafi dama Likita ya ce ta ringa motsa
jiki,ko a can idanu ta zuba Anty Nafisa ta ringa jidar kaya tamkar hauka, kuma bayan sun dawo washegari
sai ga Nafisa da wasu shirgin kayan wai na Bebynta ne ta fara siya kafin ta yi ɓari, A'isha ta ce Anty Nafisa
maimakon ki ajiye su tunda dai zaki samu wani, Nafisa ta ce don zan samu wani sai naƙi yiwa ɗan bros
ɗina hidima? A'isha in baki sani ba yaron da Brother zaya haifa, shi ne gaba da duk wasu ƴaƴa da zamu
haifa,koda gurin mahaifanmu, ballantana mu. A'isha ta yi ɗan murmushi ita kanta tasan hakan da Nafisa
ta faɗa gaskiya ne.
Ga su Jummai kuwa gata nan zaune gaban Malam tana sanar da shi damuwarta, ta ce Malam da farko fa
har ya ce cikin ba nashi ba ne, amma yanzun ya dawo ya amshi cikin, kuma sai faman zumuɗi yake yi kan
cikin nifa na fi so inga an yi waje da cikin. Malam ya na jin ta kuma yana zuba aikinsa, ya dubeta kafin duk
wannan aikin ina cikon kuɗina? Ta jawo jaka tana cewa, matsalarka kenan, kuɗi,ya ce kina zaton zan
zauna ne in ta aikata saɓo a banza? Ba duniyar bayan dama na san a lahira sai dai in ana bada haya mu
kama? Hajiya Jummai ta ce,ni dai gashi nan ya ya batun aikina yanzun? Ya ce sauƙi ne, amma in kin
tafiyar dashi yanda na baki, cikin ɓarin jiki ta ce zan tafiyar malam,kai in ka faɗi abu matsawar an yishi
babu mishkila aikin zaya tafi daidai, yanzun ka faɗa min duk dokar da ka ke so in kuma in cika aiki, ya
dubeta ta na farko dai cikin nan sai an haife shi, sai dai in an haife shin asan yanda za'ayi da shi, sannan
kamar yanda na taɓa gaya miki duk wadda ta soma haihuwa a gidan ita ce matar da zata zama uwar
ƴaƴanshi, sai dai in za kiyi ƙoƙari in ta haihu ki kawo mana mahaifarta." Hajiya Jummai ta shiga share
zufa, zuwa can ta ce tabɗijan aiki, Malam ya ce ba wani aiki ba haihuwar asibiti ba ne? Da zaran kin samu
masu amsar haihuwar kin jona su da ɗan wani abun zasu ɗauko miki, ta ce to in kuma gida ta haihu fa?
Ya ce ya ya kike yi kamar ba mace ba? Bana jin tunda sheɗan ya sara muku za'a samu wanda yafi ku iya
makirci,ke cikin irin taki kissar ba zaki iya ɗauko mahaifar ba? Ta yi jim sannan ta ce zan ƙwatanta sai dai
baka sanar da ni me za'ayi da mahaifar ba,don na fi zage dantse.
#######
[12/21, 08:48] Ummi Tandamaí ½í¸‡: *í ½í³”í ½í³”í ½í³” Page 8*
Ya ajiye allon dake hannunshi in har ki ka samu nasarar kawo min mahaifarta kin haye,don ina mai
tabbatar miki ke kanki sai kin haihu, ita kuwa zamu ruɓar mata da gabanta yanda ma mijin ba zai je kusa
da ita ba, sannan zamu maida ita juya har tsawon rayuwarta ba zata kuma haihuwa ba. Cike da farin ciki
mai tsanani Hajiya Jummai ta ce ni ko ko tawane hali zan nemo mahaifarta zan dai haihu ka ce ko? Ya ce
cire shakka, ta ce aikinka ba shakku a ciki, gafarta malam sai dai in ba a dire maka kuɗi ba, ya ce ashe kin
gane kuɗin aikinki dubu ɗari da saba'in za ki bada in kin kawo mahaifa sannan zaki ba da kuɗin, ta ce
aikin ma ya yi sauƙi na gode zan ƙoƙarta,kun ji matan da suka ɓata suka bar Allah da Manzo (S.A.W) Allah
ka shirye mu.
Hadiza ma halin da ta ke ciki kenan, ya ya za'ayi taga bayan A'isha,ga ƙaryar ciki da ƙaryar ɓari,ga kuma
amsar kuɗi hannun miji kafin ya yi auratayya da ita, duk sun haɗu sun firgita shi, shi da kanshi Alhaji
Saddiƙ ɗin in ya zauna sai ya yi ta tunanin yanda aka yi yanzun baya gane kanshi, kuma yana da yawan
addu'a ga ƙyautata ibada, haka nan mahaifanshi biyu suna tsaye kanshi da addu'a.
Wata tsurfa da Jummai ta ɗauka shi ne kullum zata zo gidan su Hajiyarmu dama-dama take da A'isha tare
da nuna kulawarta ga A'ishan,tun A'isha tana ɗari-ɗari da ita har ta saki ranta. Su Nafisa ne dai ma suke
cewa A'isha tayi hankali da Jummai,in Hajiyarmu ta ji sai tayi musu faɗa tare da cewa wato zunubi ne
koda ya kasance gaskiya ne, A'isha kam ta ɗauki nasihar surukar tata kan cewa kada ta saka batun su
Nafisa cikin ranta, ta zama mai zama da kowa cikin zuciya ɗaya. Wannan ne ma yasa har hira sukan yi da
Jumman, tunda dama ba su taɓa faɗan sa'insa ba, ita dai in taga Jumman ne sai gabanta ya ringa
faɗuwa,sai ga Jummai an je kasuwa an jido kayan beby na mahaukatan kuɗi an zo ana nuna ma
maigidan, shi ko baki ya taɓa dan duk wanda za ya ƙyautatawa A'isha shi ka baya birge shi, duk da wasu
lokutan yana ji cikin zuciyarshi cewa ba ya ƙyautata mata da ya so ya yi nazari kan abinda ya ke mata sai
ya ji tamkar ana raɗa mishi a cikin kunnanshi ce wa ita taja duk abinda kai mata,in ya tambayi kanshi
cewa da tayi ma ka me? Sai yaji zuciyarshi ta soma zafi ranshi ya shiga tafasa saboda kisisinar Jummai har
faɗa suke yi da Alhajin kan A'isha, wata ranar juma'a ya shigo ganin su Hajiyarmu bayan sallar juma'a
kamar dai yanda ya saba yi kowace ranar juma'a cikin ɗakin Hajiyarmu ya samu Jummai rashe-reshe tana
shan farfesu,ya shiga yana cewa ƴar gidan Hajiya wai me take baki ne, kullum kina nan? Cikin murmushi
ta ce ina zuwa taya A'isha rainon ɗanmu,ka dai san yanda na matsu mu ga Bebynmu.
Hajiyarmu tana kan sallaya duk da ta idar da sallar tuntuni tana ta addu'o'i,ya gaishe ta cikin girmamawa,
ya sani Jummai zata yi ta jan shi da hira ne shiko ba za ya sake ba gaban Hajiyarmu, don haka sai ya miƙe.
Ya samu A'isha zaune kan sallaya duk ƙafafunta sun kumbura, cikin ya yi ƙato ita kuma ga ta duk ta
sirance ta ƙare yana son ya tausaya mata, amma ya kasa maimakon haka ma sai haushin ta. Ya juya mata
baya kamar ko yaushe wannan ɗabi'a tana mugun baƙanta ran A'isha,ya ya Uncle zaya dinga juya mata
baya? Nata ganin tamkar rahamar Allah ta juya baya daga gare ta ne, muryarshi ta katse ta kina bin
dokokin Likitan kuwa? Cikin rawar murya irin ta me kuka ta ce eh,ya ce wai ke baki da wani aiki sai na
kuka? Salon wani ya ji ya ce ina cutar da ke ko? Ta share hawaye sannan ta ce Uncle ina kukan baƙin ciki
ne tare da yin tir ga rayuwata,na aikata laifin da mijina ya kasa yafe min, duk da ban san laifin ba. Ya
juyo,na ce kin min laifi? Ya sake kauda kai daga gare ni baki min komai ba. Ta miƙe ta zo bayanshi sannan
ta durƙusa gwiwowinta ƙasa, Uncle don son da Ubangiji yake yiwa Manzonsa ka taimake ni ka sanar dani
laifin da na yi maka, kada ka barni cikin duhu, nasan laifin mai girma ne domin idanunka ba sa son
kallona,haka zalika kafi son juya bayanka daga gare ni, ta kama ƙafafunshi "Uncle don girman
mahaliccinmu ka yafe min." Ji ya yi tamkar ta zuba mishi wuta a daidai inda ta riƙe, cikin wata
matsananciyar tsawa ya ce "Sakar min ƙafa,kina hauka ne? Jummai ta shigo da sauri tana faɗin,
"Lafiya,me ya faru?" Domin tsawar da ya daka ilahirin wanda ke kusa ya ji, itama A'isha cikin masifar
tsoro ta sakar mishi ƙafar,don makirci Jummai sai ta ɗaure fuska tare da ɓata rai ta soma cewa, "haba
Alhaji, gaskiya abinda ka ke yi ya wuce min sherin,me yarinyar nan ta yi maka da ka ke mata wannan
tsawar? Duk lokacin da nazo gidannan cikin damuwa nake ganin yarinyar nan kuma na san kai ne zaka
sakata cikin wannan halin. Ya dubi Jumman,ita kin san abinda ta yi min ne? Ta ce ban sani ba amma ai
komai na duniya ɗan haƙuri ne ko? A'isha ta iso gurin Hajiya Jummai cikin matuƙar son ta san laifin da ta
yi mishi,ta ce Hajiya don Allah ki tambaye shi me na mishi? Hajiya Jummai ta dubeshi, Alhaji ka sanar da
yarinyar nan laifinta domin gaskiya kana cutar da ita." Ya dube su ya yi shiru kamar yana son tunowa, can
ya ce to wai ni na ce ne ta min laifi? Ni batayi min komai ba, duk abin da suke yi Hajiyarmu tana kallonsu
sai lokacinne ta yi magana cewa, kurum ta yi A'isha taho muje. A'isha kam ta bi Hajiyarmu zuwa ɗakinta,
Hajiya Jummai ta ce to ka gani ga shi ma har Hajiyarmu tana fushi da kai, ranta ya ɓaci bata son yanda ka
ke yiwa yarinyar, tsaki kawai yaja sannan ya fita.
Koda Jummai ta shigo ɗakin Hajiyarmu nata zaton za ta samu suna tattauna batun Alhajin, amma sai ta
samu Hajiyarmu tana waya, A'isha kuwa tana duba littafin Hisnul Muslim,