Showing 1 words to 3000 words out of 36994 words

Chapter 1 - ASP Zahra Complete 1 by Asmau Bint Abubakar

 *MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION*📚🖊️
*M*. *W*. *A*
_Putting smile on our readers faces._
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
___________________________________

*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Daga Alƙalamin_✍🏻
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_🌸🌸

*Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin
sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin.
Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da
sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.* *Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin
al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi
lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.*

*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba.
Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin
kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin
banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga
group*.

*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da
izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Free PAGE 1*

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".
Shine abinda matashiyar yarinya wacce ke sanye da kayan ƴan sanda take maimaitawa, alamu
sun nuna cewa suma tayi aka watsa mata ruwa ta farfaɗo duba da yadda take a kwance a ƙasa
idanu a rufe ga fuskarta data jiƙe da ruwan da aka watsa mata. Jin ana ƙoƙarin ɗagata a ƙasan
ne yasata buɗe ido domin ganin mai taɓatan, Ammi ce wacce take matsayin ƙanwa ga

mahaifinta.

Kallon fuskar Ammin tayi wacce ta kumbura tayi jazir saboda kukan da tasha domin hatta
idanunta sun koma can ciki ba'a ganinsu sosai saboda kumburin da fatar idon nata tayi.

"Zarah kuka ba shine mafita ba a yanzu, kizo kiyi sallama dasu domin a samu damar kaisu
makwancinsu da wuri." Ammin ta faɗa cikin dasasshiyar muryarta.

Buɗe baki tayi domin magana amma kukan data kasayi tun farko ya riga maganartata fitowa,
take kuwa ta fara rera kukan mai taɓa zuciyar duk wani mai sauraro.
Hannunta Ammi ta kama ta ɗagota tare da nufar inda gawarwakin mutane takwas dake sanye
da suturarsu ta ƙarshe a cikin makara, koda ta iso da ita wajen sake hannunta tayi tare dayin
baya domin kukane yakeson ƙara kece mata.

Cikin rawar hannu ta fara yaye mayafen daya lulluɓewa gawarwakin fuska tundaga kan gawa ta
farko.
"Mahaifina, Mahaifiyata, Kakannina uku, ƴan biyun ƙannena sannan ƙaramar ƙanwata.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." ta ƙara fashewa da wani sabon kukan mai taɓa zuciya, lokaci
ɗaya kuma ta tsagaita tare da gyara rufuwar mayafan sannan ta ɗaga hannu sama ta fara
addu'a.
"Ya rabbi, Ya rabbi, Ya rabbi. Ya Hayyu ya Qayyum ya Allah ina gode maka a cikin kowani
yanayi dana tsinci kaina. Ya Allah kaine shaidata ban shiga aikin ƴan sanda ba saidan na
taimaka gurin gyara ƙasata, Ya Allah kasani ina tsare duk wasu dokokinka bana saɓawa da
gangan saidai a rashin sani. Ya ubangijina nasan ka fini son waɗannan bayi naka shiyasa ka
karɓesu daga aron daka bamu, na karɓi wannan jarabawa hannu biyu sannan ina ƙara gode
maka.
Ya Allah ga bayinka nan zasu iso gabanka Ya Allah kayi musu gafara ka yafemusu zunubansu
wanda sukasan sun aikata dama wanda basu sani ba, Allah kayi musu rahama, Ya Allah ka
tsare daga duk wata fitina dake cikin kabari Allah ka karɓi shahadarsu. Ya Allah kabasu wani
ɓangare a cikin Aljannarka. Ya rabbi baka aikata zalunci sannan baka barin masu aikawa, Ya Allah na kawo ƙarar duk wani
wanda yake da hannu a cikin mutuwar bayinka muminai."

Hatta mazan dake farfajiyar wajen saida suka zubda hawaye tare da jinjina jarumtar Zarah.
Batare da ɓata lokaci ba aka sallaci gawarwakin sannan aka tafi sadasu da gidajensu na
gaskiya.

_Kafin faruwar wannan al'amarin_.


Tsantsar abota da aminci ne a tsakanin Malam Usmanu da Malam Adamu wanda ya rikiɗe ya
kuma ƴan'uwantaka hakan ya samo asaline tun daga iyayensu da sukayi zaman aminci tare,

hakan kuma ya ƙarayin sanadin da yaransu suka taso cikin shaƙuwa da son juna tamkar iyayen
nasu sakamakon gidajensu dake maƙotaka da juna.
Asalinsu mutanen garin Deba ne a jihar Gombe kuma a nan suke da zama da iyalansu, da
sana'arsu ta noma suke rufawa kansu da iyalansu asiri.
Malam Usmanu yanada mata ɗaya Faɗimatu da ɗansu Abdul_Jalal wanda shi kaɗai suka haifa.
Yayinda Malam Usmanu keda yara biyu Sulaiman da Rumaisa sannan matarsa Aishatu.
Yaran sun taso cikin so da kulawar iyayensu, tare sukeyin komai tun yarinta har zuwa
girmansu.

Sulaiman shine babba cikinsu wanda a yanzu haka yake zaune a cikin garin gombe tare da
yaransa biyu Muhammad Jawwad da Nusaiba dakuma matarsa Safiyat wacce yaran ke kira da
Momi. Inda ya kasance ɗan kasuwane a fannin ma'adanai.
Sannan Abduljalal dake zaune a garin bauchi da nashi iyalan inda yake aiki a babban asibitin
tarayya dake jihar bauchi. Yanada matarshi ɗaya mai suna Zainab (Mami) sai yaransa uku
Abubakar Sadiq, Rahma, sai Fatimah Zarah.

Rumaisa kuwa(Ammi) a ƙasar Cairo take zaune da mijinta wanda ya kasance ɗan kasuwa da
ƴan biyun ta Muhammad Adil da Muhammad Shahid.

Duk da kasancewar ba guri ɗaya suke rayuwa ba, sukan ware lokuta domin zuwa ziyartar
iyayensu a garin Deba. Hakan yasa yaran sukayi sabo da juna sosai in banda Muhammad
Jawwad da tun bayan kammala karatunshi na firamari aka kaishi England domin ya cigaba da
karatunshi a can. Haka wannan familyn suke kasancewa koda yaushe cikin so da ƙaunar juna.

Mafarkin Zarah nason zama ƴar sanda ya fara tun lokuta da dama da take ganin ana zaluntar
talakawa sannan ƴan sanda suƙi ɗaukan mataki, hakan yasa tasha alwashin zama ƴar sanda.
Daƙyar iyayenta suka aminci da wannan buƙatarta ta domin saida ta kaita ga kwanciya a asibiti
tamkar bazata rayu ba, ganin haka ne yasa suka amince tare da kafa mata sharuɗɗan kare
mutuncinta dana danginta.

Wani al'amari daya faru a rayuwarta wanda ta kasa mantawa shine.

_Garin Bauchi_
12:30nr

Gosulo ne sosai akan titin wanda ya kasance ana yawan samun cunkuson ababen hawa duk
ranar juma'a saboda tare wasu hanyoyi da akeyi sakamakon sallar juma'a da ake gabatarwa.
Cikin waɗanda gosulon ya tsayar harda direban daya ɗauko Zarah daga makaranta.
Saidai gabaɗaya hankalin Zarah dake cikin motar ya koma ga wata tsohuwar almajirah dake
gefen hanya zaune da roba tana bara, sosai ta bata tausayi ganin babu wasu masu bata
sadaka dayawa. Jakar makarantarta ta duba saidai naira ɗari biyu ne aciki..

"Baba Sule akwai kuɗi a hannunka ne". Ta tambayi direbansu dake jan motar.

"Ehh baza'a rasa ba".

"Zasu kai nawa ne."

"Inajin zasu kai dubu biyar ko sufi haka". Ya faɗa sanda yake ƙoƙarin ƙirga kuɗin daya zaro a
aljihunshi.


Karɓa tayi tare da fita a motar ta nufi inda matar ke zaune.

"Sannu Baba ya zaki zauna a rana ki koma inuwa mana". Cewar Zarah lokacin data ƙaraso
gurin.

"Ƴar nan idan kayi nesa da jama'a wasu bazasu zo inda kake su taimaka ba dole sai mutum
yazo inda suke."

"Allah sarki to baki da mai taimaka miki ne.? "

"Da inada mai taimakamin ba zaki ganni ni ɗaya ba ƴata."

"Sunana Fatimah Zarah ne, ga wannan sadaka ce babu yawa." ta miƙa mata kuɗin.

"Allah ya saka da alkhairi Batula, Allah ya albarkaci rayuwarki ya kareki daga sharrin maƙiya.
Allah ya bani ikon taimaka miki watarana kamar yadda kika taimakamin."
Cike da jindaɗi Zarah ke amsa addu'o'in kasancewarta mutum mai son taga babba nayi mata
addu'a.

"Bari naje direba na jirana zan dinga tsayawa wani lokaci mu dinga gaisawa."

"Toh nagode Allah ya albarkaci rayuwarki." Almajirar ta faɗa a fili amma cikin zuciyarta cewa
take "Bazaki ƙara ganina ba yau ɗinma na fito ne da niyyar taimakon mai taimako ne, kuma
gashi kinyi sa'ar kasancewa wacce zan taimakawa.

Tun daga wannan lokacin sai ya kasance duk dare Zarah zatayi mafarkin wannan almajira
sannan kullum zancen da take maimaita mata a cikin mafarkin shine. _Zaki haɗu da ƙalubale da
dama a rayuwarki, ki zama mai hakuri da juriya tare da fauwalawa Allah lamuranki a duk lokacin
da kika tsinci kanki cikin tsanani, sannan ki zama mai gaskiya a dukkan lamuranki. Kada kiyi
zalunci kuma ki bari wasu su aikata, ki jajirce wajen bada gudumawar da za'a kauda zalunci a
cikin al'umma._

Da farko abin baya damunta amma bayan tayi satikai tana neman wannan almajira a inda ta

ganta sai abin yafara tsorata ta musamman da mutanen wajen ke faɗin basusan wata almajira
ba, hatta Baba Sule data karɓi kuɗi a hannunshi wancan ranar yace bai san ina taje ba bayan ta
fita a wannan rana. Lamarin na matuƙar damunta saidai ta kasa tunkarar kowa da lamarin.

A wata ranar lahadi ne tayi mafarkin ƙarshe da almajirar wacce bata kuma zuwa mata ba saidai
maganganun data gayamata a wannan rana sun tsorata ta.
_Ni ba mutum bace ALJANA CE! kuma lokaci yayi dazan koma nahiyarmu, BATULA nayi miki
alƙawari bazan ƙara zuwa miki a mafarki ko a zahiri ba amma kamar yadda na alƙawaranta zan
taimaka miki idan lokacin taimakon yayi. Kada ki manta da nasihata a gareki domin zata
taimaka miki sosai._ Tundaga wannan lokaci bata ƙara mafarkinta ba wanda ya gaskata mata cewa aljana ta
taimakawa.

Lokacin data fara aikin ƴan sanda sai ya kasance ta jajirce sosai wajen ganin ta ƙwaci duk wani
haƙƙin talaka da ake dannewa, hakan ya jawo mata farin jini tare da ƙarin matsayi akai-akai har
zuwa yanzu da take matsayin ASP.

Alhaji Sulaiman, wato ɗan'uwan mahaifin Zarah nada tarin dukiya sosai da baisan adadinta ba.
Babba kuma sanannen kamfaninshi shine _M.J JEWELS_. Kamfanin ya samu sunan ne daga
Muhammad Jawwad wato ɗan shi na fari.
Ana sarrafa duk wasu nau'ika na kayan ƙaleƙale a wannan kamfani kama daga kan ƴan
kunnaye, sarƙa, awarwaro, zobuna, agogo da sauransu wanda ake sarrafasu daga ma'adanai
daban daban danginsu zinari, azurfa, lu'u lu'u da dai sauransu.
A shekarar data gabata ne yasamu nasarar mallakar lu'u lu'u wanda ya siya a hannun turawa
da darajarshi takai dallar amurka miliyan talatin, an sakashi a wani akwatin tsaro na musamman
wanda babu wani abu dazai iya fasashi koda guduma ne da bindiga dole sai mabuɗin shi
wanda yake tamkar flash na jikin laptop. Kasancewar sai yayi shekaru da dama a ajiye kafin a
iya sarrafashi yasa ya ɗaukeshi daga gidanshi inda yake da farko aka maida kamfaninshi
saboda hare-haren ƴan fashi. Inda aka ajiyeshi a wani ɗakin sirri dake kamfaninshi, amma duk
da hakan ba'a daina barazanar satar shi ba.
Ganin hakan ne yasa shida ɗan'uwan shi Alhaji Abdul_Jalal suka yanke shawarar maida shi
gidansa dake bauchi bayan an damƙa tsaronshi a hannun Zarah.

Hatta iyayen basuda masaniyar a inda lu'u lu'un da akwatin tsaronsa suke tun bayan da aka
damƙa mata ajiyarshi.

*ALPHA*👽

Alpha wani taƙadirin ɗan ta'adda ne dayayi ƙaurin suna a Nigeria dama maƙotanta, ya shahara
sosai wajen sace-sace da fashi gami da kisan kai. Saidai abinda yake matuƙar damun al'umma
shine babu wanda ya sanshi bare inda yake zaune domin yanada yara da dama masu yimasa
aiki saidai hatta wasu daga cikin masu yimai aiki basu sanshi ba. A duk lokacin da suka yi wani gagarumin laifi suna barin tambarinsu wanda yake sunan ALPHA

ne haɗi da zanen bishiyar kwakwaí ¼í¿�️, ta hakane ake ganewa idan sun aikata laifi saidai har
yanzu ƴan sanda sun kasa kama koda ɗaya ne daga cikin masu yimasa aiki sakamakon
manyan gwamnati da suke tare dashi.

Tun bayan daya samu labarin wannan lu'u lu'u daga bakin wani yaronshi na sirri wanda yake
aiki a _M.J JEWELS_. Yasha alwashin sace shi saidai matakan tsaron dake jikin akwatin ne ya
hanashi samun damar satarshi amma yana kan shiri wajen ganin ya mallaki wannan kadara
tare da ɗaiɗaita kamfanin _M.J JEWELS_.
Bayan ya samu labarin inda aka maida lu'u lu'un sai yafara kiran Alhaji Abdul_Jalal tare da
yimasa barazanar kashe wani nasa muddin bai sanya Zarah ta damƙa mishi akwatin da lu'u
lu'un ke ciki ba, ganin bai samu nasara ba sai ya maida akalar barazanar shi ga Zarah ganin ita
mace ce saidai yayi mamakin taurin kai irin nata domin akoda yaushe idan ya kira musayar
maganganu marasa daɗi ne yake wakana a tsakaninsu duk da barazanar dayake mata na rasa
wani daga cikin danginta.
Dalilin dayasa ya yanke shawarar taɓa wani a cikin danginta ko zata saduda.
_____________________________

Ciwon ciki mai tsanani ne yake damun Rahma wanda yayi sanadin harta kwanta a gadon
asibiti, satinta biyu aka sallamota bayan jikinta yayi sauƙi sosai.
Kasancewar lokaci ne na hutu yasa Ammi dake ƙasar Cairo ta yanke shawarar zuwa duba jikin
Rahman tare da samarin ƴan biyunta, a garin Gombe jirginsu ya sauka hakan yasa dole suka
ƙarasa garin Deba domin kwana washegari sai su wuce Bauchi.
Bayan gaishe-gaishe da hirar yaushe gamo ne suma tsoffin suka yanke shawarar ayi tafiyar
dasu domin suma dai basuje dubata ba tunda tayi rashin lafiyar, nan suka yanke cewa zasuyi
sammako gabaɗaya suje domin a ranar tsoffin sukeson suje su dawo saidai tafiyar bazata yiwu
da Baba Faɗimatu ba sakamakon ciwon ƙafa da take fama dashi.
Da daddare Momi matar Alhaji Sulaiman ta kira Ammi tayi mata ban gajiya inda ta roƙeta akan
tabar tata tafiyar sai jibi domin su tafi tare saboda gobe zataje ganin likitan ido akan matsalar
ido da take fama dashi. Nan Ammi ta yanke shawarar barin tafiyar sai jibi kamar yadda ta
buƙata wanda hakan zai bata daman zama da Baba Faɗimatu da za'a bari a gida ita kaɗai a
ranar.

Washegari kuwa kamar yadda suka tsara ƙarfe takwas suka ɗauki hanyar zuwa gari Bauchi
bayan sun tsaya a cikin garin Gombe sun ɗauki Nusaiba a gidan Alhaji Sulaiman wacce itama
za'ayi tafiyar tare da ita, Shahid ne ke tuƙa motar Adil na gefenshi yayinda Malam Usmanu,
Malam Adamu, Baba Aisha da Nusaiba ke baya. A haka suke tafiya lokaci zuwa lokaci suna
ɗan taɓa hira.

Safiyar yau bayan Zarah tayi shirinta na tafiya aiki kamar koda yaushe akan kayan aikinta ta
ɗaura Abaya sannan tayi rolling da mayafinta, fara ce kuma kyakkawa ce ajin ƙarshe daga
kyawun fuska har na jiki, tana da tsayi amma ba sosai ba. Kyakkyawar fuskarta na ɗauke da

dara-daran idanu wanda suke cike da gashin gira dana ido, dogon kuma matsakacin hanci ta da
kuma ƙaramin bakinta suke ƙara bayyana kyawun da take tattare dashi.

Kai tsaye falon Abbansu ta nufa, a zaune ta same su shida Maminsu alamun magana suke mai
mahimmanci, bayan ta gaishesu ne ta sanar dasu zata wuce gurin aiki. Abban ne ya dakatar da
ita daga shirin miƙewa da take sa'an nan yace "Zarah inaso na ƙara jaddada miki cewa duk
rintsi kada ki maidawa Daddyn ku Sulaiman ajiyarshi kowani hali kika tsinci kanki ciki matuƙar
bashi ya buƙaci ajiyarsa ba."

"Toh Abbah insha Allahu zanyi yadda kace." Ta faɗa cike da ladabi

"Allah ya muku albarka gabaɗayan ku ya ƙara haɗe kanku ko bayan bama nan."

"Ameen Abbah."

Daganan ta miƙe ta musu sallama tare da barin falon hakan takejin wani irin yanayi a tare da
ita.

Bayan fitarta ne Alhaji Abdul_Jalal ya kalli matarshi yace" Ina tsoron abinda taƙadirin nan zai
aikata ga yarinyar."

"Babu abinda zai sameta da yardar Allah."

"Ameen dai amma wannan mutumi abun tsorone."
Haka suka cigaba da tattaunawa game da lamarin Alpha ɗin har zuwa wani lokaci.

Ƙarfe sha biyu a cikin Gombe tayi musu kai tsaye suka nufi Gwallaga Inda anan gidansu Zarah
yake.
Cike da farin cikin ganin juna aka tarɓesu sannan aka cika musu gaba da abubuwan motsa
baki. Hira aka cigaba dayi har zuwa lokacin sallar azahar Inda mazan suka wuce masallaci
matan ma suka miƙe domin gabatar da tasu.
Bayan anyi sallah ne kuma aka zauna cin abincin gargajiyar da Mami ta shirya, cike da
barkwancin da kakannin keyiwa jikokin nasu.

Haka suka kasance cikin farin ciki har zuwa lokacin da sukayi haramar tafiya.

Baba Lado mai gadi na zaune akan wani benci dake jikin gate yaji anyi horn, koda ya leƙa bai
gane na cikin motar ba sai ya tsaya batare daya buɗe gate ɗin ba, wani ne ya fito daga cikin
motar sanye da manyan kaya ya iso jikin ƙofar inda Baba Lado ke tsaye.

"Baba dan Allah me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0