Showing 27001 words to 30000 words out of 36994 words
Chapter 10 - ASP Zahra Complete 1 by Asmau Bint Abubakar
ƴan sanda babu inda baya iya kai mutum
daga inda ya dace har inda bai dace ba, amma kaje kana cin zarafin yarinyar nan, baya ga
haka ma fa ƴar uwarka ce, why M.J?"
"Idan ka gama saika faɗamin, look Abdallah wannan rayuwata ce and yarinyar nan ni zan zauna
da ita ba wani ba, banason ka kuma yin magana akai babu ruwanka da lamarin dake tsakanina
da yarinyar nan."
"Kamar yadda kace zan fita a lamuranka da yarinyar nan amma inaso ka saka a ranka cewa
ranar da zakazo kana neman alfarmata na shiga lamuran bazan shiga ba."
"Bazan buƙace ka bama" yana gama faɗin haka ya shige bandaki, shikuwa Abdallah miƙewa
yayi yaje reception da nufin binciken tun yaushe Zarah suka kama ɗakin, saidai hirar da wasu
matasa sukeyi ta ɗauke mai hankali, nan ya zauna can gefe yana sauraron su, mata biyu ne da
namiji ɗaya. Ɗaya daga cikin matan ne tace.
"Wallahi bantaɓa jin ƴan sanda sun matuƙar burgeni kamar yau ba, kiga yadda yarinyar nan ta
kama munafikin mutumin nan cikin sauƙin da babu wanda zaiyi tunanin."
"Ai baku ga komai ba indai ASP Zarah ce, idan ta zaƙolo muku wani mai laifin sai mamaki ya
kusa kar ku, wanda kake tunanin bazai taɓa aika wani mummunan laifi ba idan kaji laifin shi sai
kayi ta mamakin yadda yake aikatasu." cewar saurayin.
Hirar Zarah suka cigaba dayi wanda yawanci yabonta ne sukeyi tare da jinjina ma yanayin
yadda take aiki da gaskiya da riƙon amana, gabansu Abdallah ya ƙarasa tare da baiwa saurayin
hannu suka gaisa sannan yace.....✍️
*By*
*Jasmine*í ¼í¼¸í ¼í¼¸
*ASP ZARAH*í ½í±©✈️
"Dan Allah naji kuna magana akan wata ƴar sanda shine nace bari nazo naji gaskiyar batun."
Dake saurayin irin masu surutun nan ne bai tsaya wani dogon nazari ba ya fara labarta mishi
abinda ya faru awanni uku da suka wuce, na yadda Zarah ta jagoranci jami'i sukayi basaja suka
kama mutumin da babu wanda zaiyi zaton mai laifi ne, ya daɗe yana zayyano mishi kyawawan
halinta tun daga kan shiga har fannin aiki, ganin saurayin bashi sa niyar dakatawa ne yasa
Abdallah miƙewa tare da ajiye musu rafar kuɗi akan teburin da suke zaune ya wuce sama.
Murmushi yayi mai cike da ma'anoni, tabbas bazai gayawa M.J wani abu da ya sani akan Zarah
ba, zai barshi har zuwa lokacin da zai gano da kanshi, a wannan lokacin zai taya Zarah
ramuwar abinda ya mata amma duk da haka yana fatan ya saduda da wuri kafin dare yamai
nisa.
Ko da ya kuma ɗakin bai nuna mishi wata alama dazai gane yana cikin wani yanayi akan
abinda ya faru ba, hirarsu suka cigaba dayi har zuwa lokacin da aka kira sallar magrib suka fito
masallacin dake farfajiyar hotel ɗin domin sauke farali.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Duk yadda taso taƙi saka abin a ranta ta kasa, kusan kwana tayi a zaune tana tunanin mafita
babu shawarar da zuciyarta bata raya mata ba daga mai kyau har wanda bai dace ba, daga
ƙarshe dai ta yanke shawarar ɗaukar lamarin a duk yadda yazo mata, zata karɓi tayin kowane
irin zama da yakeso suyi, damuwarta ɗaya ce kuma ya magance mata wato cigaba da aikinta,
bata da wani sauran abinda zata damu dashi matuƙar zai yarje mata cigaba da aiki.
Washe gari idonta yayi luhu-luhu saboda rashin baccin da bata samu ba ga kuma kuka da tayi
sosai, hakan ya haddasa mata ciwon kai mai tsanani har taji bazata iya fita gurin aiki ba, tana
kwance akan sallayar da tayi sallar asuba ta kasa miƙewa ta koma kan gadon.
Ganin har ƙarfe takwas Zarah bata sauko ba yasa Baaba miƙewa da kanta ta haura saman
domin duba lafiyarta, da sallama ta shigo saidai duhun dake ɗakin bai barta ta hangi komai ba,
lalubawa tayi har Allah ya bata sa'ar samun switch ɗin ta kunna haske ya gauraye ɗakin,
kalle-kalle ta farayi ganin bata ganta kan gadon ba har Allah yasa ta hangota acan kusurwar da
take sallah. Da hanzari ta ƙarasa inda take tare da tattaɓa jikinta ganinta a duƙunƙune.
"Subhanallahi Zara'u baki da lafiya shine baki faɗa ba tuntuni a kaiki asibiti, saiko zauna da ciwo
a jikinki haba sai kace ƙaramar yarinya."
Cike da juriya da ƙarfin hali tayi ƙoƙarin miƙewa zaune tare da jingina bayanta a jikin gado tace.
"Ba wani abu ke damuna ba fa Baaba, kawai ɗan ciwon kai ne daya haddasa min zazzaɓi
amma yanzu zanyi wanka nasha magani."
"A'a Zara'u ban yarda da wannan ba ki lallaɓa kiyi wankan sai a rakaki asibiti, ko kuma zaki jira
su Muhammadu suzo ne saisu kaiki naga kamar zaifi."
"Baaba nace miki karki damu ba wani abu bane fa zansha PCM yanxu zai sauka."
"Tunda haka kikace ai shikenan Allah ya baki lafiya, dama naga baki sauko bane nazo faɗamiki
cewa ɗazu Babanku ya kirani wai sun fasa bari sai wani sati saboda Sadiku ya matsa sai sun
dawo shine yau zasu biyo jirgin yamma su dawo."
Wanj irin zabura tayi kamar ba mai jinya ba tace.
"Da gaske Baaba.?"
"Mtsww! Iskancin banza, ni ina nan na ɗaga hankali na baki da lafiya ashe ƙarya kike yi tunda
har zaki iya wannan zaburar."
"A'a fa Baaba, kinsan daɗewar da nayi banga ɗanuwana ba dole nayi ɗoki yanzu da naji zai
dawo."
"Shikenan ai kiyi wanka kizo ki karya saiki sha maganin."
"Toh yanzu zan sauko."
"Karma ki sauko yanzu inkin so." Ta faɗa tana mai ficewa daga ɗakin.
Miƙewa tayi dakyar saboda sarawa da kanta keyi ta shige banɗaki, ruwa mai ɗumi ta tara ta
shiga ciki, ta daɗe a kwance cikin ruwan kafin ta canja shi ta tare wani kana ta ɗauki sponge ta
fara murzawa jikinta a hankali har ta gama ta ɗaureye jikinta kana ta fito a ruwan ta ɗaura towel
tare da ficewa a banɗakin. Zama tayi gaban dressing mirro tana ƙarewa kanta kallo ganin yadda damuwar dare ɗaya ke
neman ramar da ita, ya zama dole tayiwa kanta alƙawarin cire duk wani damuwa dake ranta
akan wannan auren ta maida hankalinta wajen binciken inda zata nemo _Alpha_ domin zuwa
yanzu tanajin wani irin kwarin gwiwa akan binciken da take a kanshi, tana iya gudanar da komai
batare da tsoro ko shakkar wani abu zai faru da ita, hakan na ƙara bata tabbacin cewa lallai ta
kusa tozarta Alpha a idon duniya. Abu ɗaya yanzu takeson sani shine haƙiƙanin inda yake
rayuwa, zata iya riskar kowani haɗari matuƙar zata gano inda yake, hanya ɗaya gareta yanzu,
hanya ɗaya tak! Wato Raliya. Ta hanyar Raliya ne kawai zata iya gano inda Alpha yake, dole
tasan yadda zatayi ta samu duk wasu bayanai a gurin Raliyar.
Tunanin damuwar Alpha da tayi ne ya mantar da ita badakalar auren dake gabanta, mayukanta
ta shafa tare da wadata duk wata gaɓa na jikinta da turare, gaban wardrobe taje ta tsaya tare
da kallon tulin kayanta dake ciki, idonta ne yakai kan kayan sports ɗinta dake can gefe a ninke,
zaro su tayi tare da ƙura musu ido tana tuna lokacin baya da kowace ranar lahadi sai sunyi
wasanni kala-kala da yayarta Rahama saboda haka ma Abba ya saka aka ƙawata musu wani
sashi na cikin garden dinsu da kayan wasanni, wasu lokutan ma hatta Abban yakan kasance
tare dasu domin shima yana matuƙar son wasan Table Tennis. Wasu marayun hawaye ne suka
zubu daga idonta, hannu tasa ta share tare da yiwa iyayen nata addu'ar samun Rahamar
ubangiji, kayan ta mayar ma'ajiyarsu kana ta ciro wata material kalar blue da golden, ɗinkin riga
da skirt ne wanda ya matuƙar karɓan jikinta.
Wayarta kawai ta ɗaukan sannan ta fice a ɗakin.
"Ya jikin dai" Baaba ta tambaya bayan saukowarta cikin falon.
"Da sauƙi." ta faɗa a hankali.
"Allah ya ƙara afuwa, ga kalaci akan dinning idan kin gama saiki sha magani."
"Toh" ta faɗa tare da miƙewa ta nufi dinning ɗin da Raliya ke gurin tana ƙara ƴan goge-goge,
kujera ta jamata ta zauna tare da cewa.
"Ina kwan Anty."
"Lafiya" ta amsa a taƙaice kana ta kuma cewa.
"Jeki kawai." ganin Raliyan na ƙoƙarin zuba mata abincin.
Tea kawai tasha sha sai dankali da ta ɗan tsakura, sannan ta miƙe ta koma cikin falon ta kwanta
a doguwar kujera, tana daga kwance take ƙarewa Raliya dake zirga-zirga kallo, tabbas akwai
abinda take ɓoyewa domin tun zuwanta gidan bata taɓa ganinta babu hijabi ba kullum cikin
saka hijabai take kowani irin aiki da takeyi ko yanayi da ake ciki. Toh mene ne Raliyan bataso a
gani??? Ta tambayi kanta, shiru tayu na wasu mintuna kafin ta saki wani murmushi mai sauti
wanda har saida ya jawo hankalin Raliyan dake moping, tabbas ta samu amsa. Lallai akwai tatto ɗin Alpha a wuyanta wanda batason a gani shiyasa ko da yaushe take cikin
hijabai.
Wayarta da tayi ringing ne ya katse mata tunanin da takeyi, da murmushi a fuskarta ta ɗaga tare
da karawa a kunnenta.
"Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida." Jidda ta faɗa daga ɗaya ɓangaren.
"Dama nasan idan bake ba babu mai kirana da sanyin safiyar nan."
"Saboda baki da aurene yasa kike ganin yanzu yayi safiya, toh yakike ya angon namu? Kun
gana dai koh?"
"Yanzu wace tambaya zan fara amsa miki maganaɗisu."
"Duka nake buƙatar sani."
"Alright to duka lafiya lau."
"Hmm to ya angon kun sasanta dai koh."
Shiru tayi batare da tace komai ba, hakan yasa Jidda cewa.
"Wato ɗan iskan maganganu yazo ya faɗa miki koh? Kuma shine kika zuba mishi ido batare da
kin ɗau mataki ba, wai ke wace irin mace ce habibaty."
Batayi mamakin jin abinda ya fito a bakin Jiddan ba domin idan da sabo ta saba da wannan
halin nata, sau da dama ko bata faɗa mata abu Jidda na iya fahimtar hakan a yanayinta, da fari
tayi tunanin ko Jidda nada aljanu akanta ne masu gayamata sai daga baya ta gano nature ɗinta
ne hakan da kuma tsantsar ƙaunar da takeyi mata shiyasa take iya karantar ko wani yanayi
nata, ƙwafa tayi kana tace.
"Toh madam mai gani har hanji ya kikeso nayi idan ba shirun ba."
"Wato abinda ya faru kenan dai, ke kuma saboda gaki mai biyayya kika zura ido kina kallonshi
yana gasa miki maganganu, toh wallahi ki kiyayeni tun kafin nakai maƙura na shiga lamarin da
bai shafeni ba."
"Kiyi hakuri Mama" Zarah ta faɗa cike da zolaya.
"Toh na haƙura ƴar nan, yanzu ya ake ciki wasu event zamu shirya ne naga alaman idan aka
biyewa ra'ayinki bazamu gwangwaje."
Dariya tayi sosai kana tace.
"Kinsan nifa ustaziya ce."
"Matar uztazu koh, shikenan ma bazan kuma yi miki magana ba zanjira Ammi su shigo next
week sai mu tsara komai da Sis Rahama."
Miƙewa tayi zaune daga kwancen da take tace
"Wace Ammi."
"Ammi nawa muke dasu dama.?"
"Wato saboda anjireni a cikin dangi yasa duk wanda zaizo kasar ba'a faɗamin koh".
"Ke kika sani nikam na tafi gurin habibi na."
Kafin ta kuma magana kashe wayar, miƙewa tayi da nufin zuwa ɗaki sai....✍️
*VIP ayimin haƙuri dan Allah jiya banji daɗi ba shiyasa banyi typing ɗin ba. Sorry dan Allah*í ½í±�
*ASP ZARAH*í ½í±©✈️
Shigowarsu ce ta dakatar da ita daga ƙoƙarin miƙewa da take domin zuwa ɗakinta, sallamar da
Abdallah keyi ta amsa ɗauke da murmushi a fuskarta.
Bakj M.J ya kyaɓe lokacin daya zauna a kujera tare da faɗin
"Mutum a fuska kamar na Allah saidai a baɗini ɓarnar da ake aikatawa ko kare bazai shinshina
ba, Allah dai ya shirya wanda ya mayar da kanshi kwarkwar."
"Ameen kuma gani kuturwar uwa zama dani dole." ta faɗa cike da basarwa kamar ba ita tayi
zancen ba.
"Amaryarmu ni dai yunwa nakeji ki rabu da wannan angon naki ki ceto rayuwata."
Taƙaitacciyar dariya tayi har kyawawan haƙoranta suka bayyana sannan dimple ɗinta ya lotsa,
ta gefen ido ya kalleta cikin rashin sanin dalilin dazai saka yaji haushin fara'ar da takeyi ma
Abdallah.
Kallo ya bita dashi lokacin data miƙe har ta shige kicin, tsaki ya kuma ja sannan ya kalli
Abdallah yace
"Akan wani dalili zaka dinga sake mata fuska haka.?"
Dariya yayi harda buga ƙafa kana yace.
"Ikon Allah! Tunda baza kayi mata fara'a ba ai saika bar masu yimata koh bawai ka dinga jin
haushin mu ba."
Bai kulashi ba sai miƙewa da yayi ya nufi ɗakin Baaba, shima miƙewa yayi tare da bin bayan shi
domin zuwa gaida Baabar.
Ganin basa cikin falon yasa ta shirya musu komai a dinning, ɗakinta ta kuma ta ɗau mayafi da
makullin mota ta fita domin zuwa kasuwa tayi cefanen abubuwan da zata buƙata na girkin tarbar
ɗan uwanta da kuma mahaifinta. Yayanta nason masa sosai shiyasa zata fita da kanta ta siyo
sauran abubuwan buƙata na miya da basu dashi. Tare suka fito falon da Baaba inda suka nufi dinning table yin breakfast.
"Bari na kirata ta zuba muku, Zara'u" cewar Baaba, Raliya ce ta taho da sauri ta iso gabansu
tare da cewa
"Hajiya Baaba bari na zuba musu, Anty Zarah ta fita."
"Ina taje kuma."
"Wallahi bata faɗamin ba amma kaman ba nisa tayi ba, naga batayi shiri ba."
"Ai shikenan zuba musu, amma zata fita shine bazata sanar da ni ba."
Ranshi ne yaji ya ɓaci saboda mummunan zaton da shaiɗan ke kitsima mishi na cewar gurin
wani ta tafi domin suyi lalata, baice komai ba ya cigaba da cin abincinsa batare da ya kula
Abdallah dake cewa.
"Ko dai anyi mata kiran gaggawa ne."
"Ina tunanin haka nima, kasan Zara'u da ƙulafucin aiki bataji bata gani idan aka kira ta wannan
aikin nasu duk wani abu da takeyi saita ajiye ta tafi."
"Yanayin aikin nasu kenan Baaba sunyi rantsuwar kare haƙƙin mutane."
"Toh Allah dai ya tsare."
"Ameen" Inji Abdallah
Ko da suka gama cin abincin falon suka dawo suka zauna, hira suka cigaba dayi da Baaba
wanda yawanci akan dawowar da su Daddy zasuyi ne.
"Gashi shigowar yamma zasuyi kuma mu yau mukeson tafiya saboda aiki."
"A'a ku tsaya mana dai ku gana duk da ma zaku haɗu acan amma ya kamata ace kun tsaya an
tarbesu da ku."
"Shikenan saidai muma muyi tafiyar jirgin kenan, bari na duba ko za'a samu jirgin dare."
"Mezai hana ku ƙara kwana?."
"Baaba nace miki fa akwai aiki."
"Ku zama na'ura saboda aiki idan kun so."
Dariya M.J yayi yace
"Duk rashin son magana da nakeyi sai kinsa ni."
"Yo me za'ayi da mutum miskili."
"Ba zaki gane bane ai Baaba, babu fa'ida ace mutum ya kasance mai yawan surutu."
"Shiyasa ma aka haɗa ka da wacce ta dace dakai gurin rashin son magana."
Bai kuma magana ba illa cigaba da danna wayar shi da yayi, itama Baaba miƙewa tayi ta nufi
kitchen.
í ½í²Ží ½í²Ží ½í²Ží ½í²Ží ½í²Ží ½í²Ží ½í²Ží ½í²Ží ½í²Ží ½í²Ž
"Raliya! Raliya!! Raliya!!! sau nawa na kiraki?" ya faɗa cikin fusata.
Cikin shessheƙar kuka ta amsa mai da "Sau uku ranka ya daɗe."
"Wai ke wace irin daƙiƙiyar yarinya ce da batasan abinda takeyi ba, duk tsawon lokacin nan da
kika ɗauka a cikin wannan gidan aikin me kikeyi da har yanzu kika kasa samo wani
gamsasshen bayani .?"
"Kayi haƙuri yallaɓai wallahi ina ƙoƙarin ganin na samu masaniyar inda lu'u lu'un suke."
"Kullum abinda kike faɗamin kenan, amma sai yaushe ne zaki kawo min wani bayani mai
amfani eye.?"
"Fashi da makami."
"Ke Raliya! Baki da hankali ne, kada ki kuskura ki fara aikata wannan mummunan kuskuren,
wannan hanyar ba mai billewa bace. Da mai amfani ce bazamu kai war haka batare da mun
mallaki wannan kadarar ba, ko zamu kuma aikata hakan ba nan kusa ba akwai sauran lokaci."
"Amma yallaɓai naji kamar batun aurenta akeyi."
A kishingiɗe yake amma jin wannan batun yasa shi miƙewa batare da yasani ba, cin hargagi
yake faɗin.
"Aure! Aure dai? Meyasa baki faɗan hakan tuntuni ba Raliya, sai zuwa yaushe ne ƙwaƙwalwarki
zata dinga yin abinda ya kamata ne."
"Kayi haƙur..."
"Hell with this fucking word Raliya! Hakurin me zanyi, abubuwa na shirin lalacemin kice wai nayi
hakuri."
"Amma yallaɓai naga wanda zata aura ɗan gida ne shiyasa banyi tunanin komai."
"Wanene wanda zata aura ɗin."
"M.J ne."
Wani murmushi yayi mai sauti kana yace.
"Woow! Komai ya kusa zuwar mana da sauƙi, kin tabbata shine wanda zata aura."
"Na tabbata ranka ya daɗe yanzu haka ma yana garin Bauchi yazo ganinta."
"Ki tsaya ki saurareni dakyau Raliya, wannan ne lokacin mu na samu ko rashi, a yanzu ne muke
da damar yin duk wani abu da muka daɗe muna shiryawa, inaso ki lura sosai da duk wani
motsinta daga yau, saboda inada tabbacin cewa nan bada jimawa ba za'a nemi sauyawa
diamonds ɗin nan wajen zama, ki sanar dani duk wasu bayanai da zaki samu, zan organising
team ɗin da zakuyi aiki tare da zarar angano inda suke kiyi ƙoƙarin samu mana bayanai kawai."
"Zan kula sosai yallaɓai."
"Ohk" kawai ya kuma faɗa tare da kashe wayar.
Shiru tayi bayan gama wayar tasu tana tunani, tabbas wannan ita kaɗaice damar da take da ita
domin ƙara samun kusanci da Alpha, ya zama dole yanzu ta shirya ɗamarar yin fito na fito da
Zarah akan Diamonds ɗin nan, ba damuwarta darajarsu ba ko kuɗin da za'a samu akansu,
babban abinda ya dameta shine ta wannan hanyar ne kaɗai Alpha zai dinga ganin ƙimarta har
ta samu nasarar cusa soyayyarta a cikin zuciyarsa, saboda sanin yadda yake da babban buri
akan Diamonds ɗin.
"Lokaci yayi