Showing 36001 words to 36994 words out of 36994 words
Chapter 13 - ASP Zahra Complete 1 by Asmau Bint Abubakar
sosai baƙi duk sun tafi suna farin ciki tare da fatan alkhairi.
Nasiha sosai Momi da Ammi suka yi wa Zarah wanda ko da mahaifiyar ta ce iyakar abinda zata
iya faɗa mata kenan, ita kam in banda kuka babu abinda takeyi saboda tuno mahaifanta da tayi,
shikuwa Daddy da aka kai mishi Zarah domin yi mata faɗa kasawa yayi illa kawai yace.
"Fatimah yadda kikemin biyayya a matsayina na mahaifinki ina roƙon Allah ya baki masu yi miki
fiye da yadda zakimin, nasan ko ba'a faɗa miki ba zakiyi wa mijinki biyayya, Allah ya kareki
daga sharrin maƙiya kamar yadda kike ƙoƙarin ganin hakan a kaina, Allah ya dauwamar da farin
ciki a zuciya kamar yadda kike ƙoƙarin ganin hakan a kaina, Allah ya albarkaci rayuwarki ya
baki nasara akan duk abinda kika sa a gaba."
Mutanen dake falon ne suka amsa da Amin, daga haka kuma yabar falon ya shige ɗakinsa
domin kwallace ke neman sauko mishi.
Ita kam Baaba da aka kai mata Zarah miƙewa kawai tayi ta bar gurin tana kuka kamar ranta zai
fita wanda mutane da dama suka fara zargin akwai dalilin da yasa ake ta wannan koke-koken,
duk da cewa ansan wannan kukan ya zama kamar na al'ada amma wanda sukeyi ya wuce
ƙa'ida. A haka a sakata a mota aka wuce da ita gidanta dake Federal lowcost Gombe, duk
wannan budurin da akeyi Jidda bata ciki domin tun yamma Saleem yazo ya ɗauketa a gidan
bikin saboda irin kukan da takeyi.
Duk yadda Abdallah yaso amma M.J ya tubure akan babu wani wanda zaiyi mishi rakiyar ango,
dole suka rabo dashi ya wuce gidansa shi kaɗai.
Da haka dai biki ya watse sai fatan zaman lafiya ga amarya da ango.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Wayarsa dake ta faman ruri ne ya saka dole ya sake baturiyar suke manne da juna akan gado
ya miƙa hannu ya ɗauko wayar, ganin mai kiran ne yasa shi firgita tare da sauka a gadon yana
kara wayar a kunne.
"Barka dai yallaɓai."
"Don't dare to yallaɓai me, wato kaje ƙasar waje kana hutawa kabar komai yana lalacewa anan
ko, wannan shine amanar da zaka yi min eye? Saboda na wadata ka da kuɗi shiyasa kake duk
abinda kaga dama ko.?"
Cikin ina ina yace
"Ba haka bane yallaɓai ayi min afuwa."
Tsawa ya daka mai cikin fusata ya kuma yin magana yace.
"Afuwar me za'a maka, wato kai kaje ƙasar waje kana sha'aninka koh, ace ina tare da
commisioner of police gabaɗaya amma a kama Raliya kusan fiye da sati uku amma ankasa yin
komai akai."
"Innalillahi! Yallaɓai Alpha kace an kama Raliya."
"Bani da buƙatar maimatawa tunda kaji me nace."
"Amma garin yaya waya kamata."
"Wa kake tunani.?"
Ido C.P ya waro waje kamar wanda yaga wani mummunan abu mai firgitawa yace.
"Zarahh.???"
"Ka amsa tambayarka."
"Ohh shit! Dole zan dawo ƙasar gobe a fito da Raliya."
"A fito da Raliya fa kace! kasan ko a wani ofishin ƴan sanda Raliya takr zan iya zuwa na fiddata,
amma ba anan take ba bansan a ina yarinyar nan ta ɓoyeta ba. Kayi gaggawar kiranta ka bata
umarnin fito da ita a ko ina ta aje ta."
"Bari na kira ofishin su yanzu, Raliya bazata kuma kwana a hannunta ba"
Umma"Ina jiran sakamako mai kyau."
"Toh yallaɓai yanzu zan kira."
Cikin rawar jiki ya danna lambar mataimakin shi, ringing biyu ya ɗauka yana gaidashi, bai tsaya
amsawa ba ya fara magana.
"Ka kira office ɗin ASP Zarah ka bata umarnin sake yarinyar da ta kulle a cell, ka gayamata
wannan umarni na ne."
"Yallaɓai ai babu wata yarinya a ofishin nan wacce aka kulle."
"Ba tambayarka nakeyi ba umarni ne nake baka."
"Amma yallaɓai naga Zarah yanzu ba anan take aiki ba, kila bata zda masaniyar abinda ke
faruwa ko dai ba ita ɗin bace.?"
"Bata aiki kuma ??? ASP Fatimah Zarah Abduljalal nake nufi fa."
"Ehh yallaɓai ai ta nemi takardar transfer zuwa Bauchi saboda za'ayi aurenta, jiya ma muka
dawo daga ɗaurin auren."
"Damn it!! Wane ne ya aiwatar da hakan ba tare da sani na ba."
"Yallaɓai ta je Abuja ne daga can ta gama komai, wasu signing ne kawai da akeson kayi ni
nayisu a madadinka."
"Meyasa ba'a tuntuɓeni ba eyee??"
"Ranka ya daɗe kamar naga babu buƙatar hakan."
Tsaki ya ja gami da ya kashe wayar batare daya kuma magana ba, kanshi ya dafe cikin
taraddadin yadda zai kira Alpha ya gaya mai wannan labarin, gabanshi ne ya faɗi ganin kiranshi
na kuma shigowa, cikin fargabar mai zai faru ya ɗaga kiran.
"Ya ake ciki??" ya tambaya babu walwala.
"Ehmm dama.."
"Straight to the point, banason dogon zance."
"Yallaɓai wai anyi mata transfer zuwa garin Bauchi saboda zatayi aure acan, jiya ne aka ɗaura
auren nata a garin Bauchi."
Shiru yayi baiyi magana ba har hakan ya baiwa CP tsoro, sai can yace.
"Duk abinda kakeyi kabari a yau ɗin nan ka dawo ƙasar nan, sannan karka kuskura ka kirani
matuƙar ba shaidamin zakayi ka kuma Bauchi da aiki ba." daga haka ya yanke kiran.
Babu yadda commisioner yayi iya dole ya fara haɗa tarkacensa bayan ya sallami baturiyar da
suke tare, cikin lokaci ƙanƙanin lokaci ya gama shirin komawa ƙasarsa Nigeria....✍️✍️✍️
*Tammat bi Hamdulillahi!! Littafi na ɗaya ya ƙare anan, zamu shiga littafi na biyu da izinin Allah
kafin sallah. Nima zan ɗanje hutu na kwana biyu kafin mu ɗora.*
*Ina yinku sosai Zarah's fans, Mrs. Khaleel from VIP ina yinki sosai ina godiya da ƙaunarki a
gareni Allah ya bar xumunci a tsakanin mu. Sai kunjini a kashi na 2*í ¾íµ°
*By*
*Jasmine*í ¼í¼¸í ¼í¼¸