Showing 24001 words to 27000 words out of 36994 words

Chapter 9 - ASP Zahra Complete 1 by Asmau Bint Abubakar

a cikin mafarkinshi tun
bayan haɗuwarsu da ita a Abuja, take yaji wutar tsanarta ta ƙara ruruwa a zuciyarshi, tsaki yaja
mara sauti bayan ganin irin kallon da Alhaji Mati yake yiwa Zarah na tsantsar maitar buƙata,
tamkar zuciyarsa zata fito waje haka yake ji lokacin dayaga sun shige É—akin bayan an buÉ—e
mata ƙofar. Kwafa yayi shima yabi bayan Abdallah suka shige nasu ɗakin.

"Duk sanda nayi magana sai ka dinga ƙaryatani bayan sai na tabbar nake faɗa, gashi yau dai
ka tabbatarwa idanunka." cewar M.J

Kallonshi Abdallah yayi cikin rashin fahimta yace.
"Kai da waye kake magana haka."
"Ina tare da wani bayan kai ne anan.?" cike da jin haushin tambayar ya amsamai.
"Sorry ranka ya daÉ—e bangane akan me kake magana ba."
"Kwanakin baya ba tare da kai mukayi maganar wata Æ´ar sanda a Abuja."
"Oh wannan yarinyar da har yau nake fatan sake ganinta , gaskiya duk da bansanta sosai ba ta
burgeni matuƙa."
"Mtswww" M.J yaja tsaki tare da kuma faÉ—in
"Sai kayi kuma ai, itace wacce muka hauro tare suka shiga next room É—in nan."
Miƙewa Abdallah yayi daga kwancen da yake tare da cewa.
"M. J banason wasa fa wai da gaske kake police É—in nan ce muka hauro tare dasu."
"Dama ina wasa da irin wannan maganar ne."
"Allah ya kyauta" shine kawai abinda Abdallah ya faɗa tare da miƙewa ya shige toilet, bai jima
ba ya fito bayan yayi wanka. Shima M.J toilet É—in ya shiga yayi wanka ya fito, basu wani jima ba
suka fita domin isa inda zasuje.

A ɓangaren Zarah kuwa bayan shigarsu ɗakin, hannunta Alhaji Mati ya riƙo da nufin janyota
jikinsa ya rungumeta saidai kafin yayi hakan cikin dabara ta zame hannayenta tare da zama a
gefen gadon tana faÉ—in.
"Alhaji bazaka watsa ruwa ba tukun, kayi dogowar tafiya kayi wanka zaka fi jindaÉ—in aiwatar da
komai cikin nutsuwa."

"Tabbas wannan shawarace mai kyau, bari nayi wankan na fito, ko zaki taimakamin ne." ya
ƙarasa faɗa yana mai kashe mata ido.

"A'a shiga kafito dai, yanzu nayi wankan kafin na fito."

Bai ce komai ba ya cire babbar rigarsa tare da shigewa banÉ—akin, ganin shigarsa yasa tayi
saurin nufar inda akwatin kayansa yake, bata wani sha wuyar buÉ—ewa ba saboda ta rigada
tasan komai, kamar yadda suke zargi, kaya ne sosai a saman jakar saidai acan ƙasa rafar kuɗi
ne sosai sai hodar ibilis. "Zaku iya shigowa Bala zarginmu ya tabbata ku shigo cikin shiri." ta faÉ—a a hankali.
A buɗe ƙofar take dan haka jami'an suka shigo tare da yiwa ɗakin ƙawanya cikin shirin ko ta
kwana.

Zigir! haihuwar mahaifiya , haka ya fito daga banÉ—akin yana faÉ—in.
"Gaskiya baby ina...." maganarshi ce ta katse take tashin hankali yayiwa fuskarshi tambari,
juyawa yayi da nufin komawa cikin banɗakin saidai hakan bai yiwu ba sakamakon damƙarshi da
wani jami'i yayi, zagaye shi sukayi sa'an nan wani a cikinsu ya taimakamai da kayansa, shidai
ya kasa cewa komai illa rawar É—ari da yakeyi, ankwa aka É—aura mishi hannu tare da tisa
ƙeyarsa aka wuce dashi batare da an bashi damar magana ba duk da irin kallon da yakewa
Zarah na zargi tare dason yi mata maganan.
Bincike suka cigaba da gudanarwa tarw da sauran jami'ai biyu dake tare da ita, sun jima kafin
suka tattara zuwa ofishin nasu.

Sai da Abdallah ya tirsasa M.J kafin ya yadda suka tsaya a wani mall suka yiwa Zarah siyayyar
abubuwan da sukasan mace zata buƙata musamman mai shirin yin aure.
Cike da murna Baaba ta tarbesu bayan isarsu gidan, nan suka gaisa tare da hirar yaushe gamu
wanda yawanci tsokanace kawai take yimusu, sun daÉ—e suna hira kafin daga bisani Abdallah
yayi ƙarfin halin tambayar Zarah ganin har zuwa wannan lokacin batazo ba sai Raliya dake ta
hidima dasu.
"Zara'u dai sai shiriyar ubangiji, saida nace karta fita aikin nan yau saboda zuwanku amma tayi
biris dani wai akan idan kunzo akirata aiki zatayi mai mahimmanci a can ofishin nasu." cewar
Baaba cikin kwafa.

"Allah sarki dama tana aiki ne.?" Abdallah ya kuma tambaya.

"Ehh tana aiki kuma itama shugaba ce a wajen, ko bataje ba bazata samu matsala ba amma
dan naci saida ta tafi, bari na kirata ta dawo yanzu ungo dubamin numbarta anan zakaga
ansaka Zara'u." takarasa faɗa tana miƙa mishi ƙaramar wayarta.
Shidai M. J yanajinsu amma bai tanka ba, saidai ranshi yayi mugun ɓaci da lamarin wannan
yarinyar da akeson ya aura, wato an faɗa mata zaizo shine ta saka ƙafa ta fita.

Kiran wayar ake tayi amma bata É—agawa, hakan yasa M.J ya umurci su kuma falon Abba su
zauna, nan suka bar Baaba tana ta mitar Zarah taƙi ɗaga mata waya da gangan saboda bata
da gaskiya.

🥶🥶🥶🥶🥶🥶🥶🥶

A hankali ta kulle ƙofar tare da murɗa key ɗin jiki kana ta isa kan gadonta ta zauna tare da fiddo
da wata ƙaramar waya da ke ta kawo wuta alamun ana kiranta, karawa tayi a kunne tare da
faÉ—in
"Barka da safiya ranka ya daÉ—e."

"Baki da hankali ne Raliya, shin ban tsara miki yadda nakeson ki gabatar da komai ba, wato
saboda kinga bakya kusa dani kike tunanin zakiyi abinda kikaga dama ko? Toh wallahi duk wani
motsinki kinsan a tafin hannuna yake, saboda bakisan mahimmancin abinda ya kaiki ba har

zakiyi saken da za'a cire camera daga inda kika aji. Mtssww! Baki san darajar wannan abun da
muke nema koh, wallahi ki kiyayeni Raliya kiyi abinda nagaya miki cikin tsari, yanzu tayaya
zamu samu masaniyar inda abun yake bayan ancire cameras É—in, kiyi gaggawar nemowa kanki
mafita tun kafin raina ya kai ga ɓaci, Nonesense!." Batare da jiran abinda zatace ba ya kashe
wayar.

Kuka mai ciwo ne ya kwace mata, kifa kanta tayi akan pillow tare da fara rera kukan cike da
takaicin maganganun mutumin da take matuƙar so da ƙauna a gareta, a gefe guda kuma
takaicin cire cameras É—in ne ya dameta wanda ta tabbar wannan aikin Zarah, ta rasa gane
alƙiblarta, tamkar mai aljanun da suke faɗa mata sirrin mutum haka take, a ɗan zaman da
sukayi ne ta fahimci haka. Tabbas a da taso ta rangwanta mata kodan albarkacin Baaba, amma
a yanzu batajin ko iyayenta dake kabari ne zasu dawo rayuwa suce ta haƙura da satar Diamond
É—in nan ba zataji maganarsu, dole ta sake shiri domin tasan ta wannan hanyar ne kaÉ—ai zata iya
cimma burinta na rayuwa da Alpha a matsayin masoyi.
Miƙewa tayi tare da share hawayen da ya ɓata mata fuska ta nufi ƙofar fita daga ɗakin saboda
jin kiranta da Baaba keyi.

"Gani Baaba". Ta faÉ—a bayan ta iso falon.

"Yauwa Raliya kiramin direba na aikashi ya tahomin da Zara'u tunda naga batada da niyar
dawowa."

"A'a Baaba kinsan yanayin aikinsu fa, ki barta zata dawo yanzu idan yaje ma ba lallai su barshi
ya ganta ba."

"Shikenan amma tabbas zata gamu da fushina idan ta dawo, yanzu da ba Æ´an gida bane ai
kunyata mu zatayi kenan."

"Ayi haƙuri Baaba, kina buƙatar wani abu ne." Raliyan ta faɗa tana mai sunkuyar dakai ƙasa.

"A'a bakomai jeki kema ki huta kinyi aiki sosai."

"Nagode" ta faÉ—a tare da nufar É—akinta.


✈�✈�✈�✈�✈�✈�✈�✈�✈�✈�✈�
*SINGAPORE*

Daddy ne zaune da wani kyakkyawan matashin saurayi a wanj keɓaɓɓen lambu mai cike da
shukoki kaloli daban-daban, kallo É—aya zaka yiwa saurayin kaga tsantsar kama da sukeyi da
Zarah da kuma Rahama saidai ƙarin hasken fata da Zarah tafiso duka, hannun Daddyn na akan
kafaÉ—ar saurayin da idanuwanshi sukayi jazir saboda kukan daya sha, hankacif ya saka tare da
ƙara goge mishi idanunshi yana faɗin.

"Kayi haƙuri Son muma har yanzu haka mukeji a zuƙatan mu bayyanawa ne kawai bama yi,
amma kayi hakuri ka biyoni mu koma gida." cewar Daddy

"Daddy bazan iya zama a Nigeria ba alhalin babu waÉ—anda zan iya gani na samu farin ciki."

"Kada kace haka As-Siddiq zaman ka anan bashine zai iya dawo da waÉ—anda suka rasu ba,
idan kace baka da kowa toh mufa ko baka É—aukemu a matsayin iyaye bane dama, Æ´an uwanka
mata fa, bawai ina nufin bazan iya riƙesu bane tamkar ƴaƴan da na haifa amma suna buƙatarka
a kusa dasu a matsayinka na wanda zasu dinga gani tamkar É—an'uwana da ya rasu, kaine kaÉ—ai
zaka iya rarrashinsu musamman Zarah da ita bata kukan fili saina zuciya wanda yafi ƙuna, kayi
haƙuri ka shirya mukoma gida tare dan Allah ina neman wannan alfarmar."

"Daddy kai ubane a wajena baka da buƙatar neman alfarma a wajena, umarni kawai zaka bani
na aiwatar, insha Allahu zuwa ƙarshen shekara zan tattaro na dawo gida."

"Me zaka tsayayi anan har ƙarshen shekara? Bayan haka ma bikin ƴan uwanka za'ayi nan da
wata É—aya da sati biyu ka shirya kawai mu tafi tare."

Idanunshi da suka fara washewa ya waro wanda hakan yayi mishi kyau matuƙa, kafin yace.
"Wasu Æ´an uwan nawa kuma Daddy."

"Ehh Æ´an uwanka Zarah da Jawwad, insha Allah nan da wani lokaci za'a É—aura aurensu."

"Amma ita Zarah ce ta amince da auren Bro Jawwad ɗin? Ko dama suna soyayya ne ban taɓa
sani.? Amma yarinyar nan batada hankali duk ana maganar nan shine bata taɓa faɗamin ba
É—azu ma fa munyi waya da ita amma take cemin babu komai, yanzu ina ita ina miskilancin M.J
mut..." lura da yayi da wanda suke maganar ne ya sashi yin shiru batare da ya gama maganar
ba tare da sunkuyar da kanshi ƙasa cike da kunyar maganganun daya yiwa Daddyn.

"Kada kaji kunyata Son, ko nine a matsayinka tambayar da zanyi kenan yanzu tamkar uba kake
a garesu kanada damar yin bincike a duk wani lamari daya shafesu."

"Kayi haƙuri Daddy, zan shirya mu wuce tare."

"Toh nagode Son, Allah yayi albarka".

"Ameen" yace kana ya tsiyayi ruwan dake ajiye akan teburin wajen yasha, nan suka zauna suna
hira kafin daga bisani suka miƙe tare da barin wajen.

👩�✈�👩�✈�👩�✈�👩�✈�👩�✈�👩�✈�👩�✈�👩�✈�

Saida ta kammala duk wasu mahimman abubuwa da duka dace game da case É—in kafin ta nufi
gida cikin hanzari saboda jiran da ake mata .

Da sallama ta shiga falon, ganin Baaba a zaune ta sha kunu ne yasata faÉ—in
"Dan Allah ayimin afuwa Baabata aikine mai matuƙar mahimmanci ya tsayar dani."

"Zaki wuce kije ki samesu ko yaya."

"Haba ko wanka bazaki bari nayi ba, da kayan aikin zanje ne wai"

"Wallahi idan baki wuce ba zan saɓa miki, yo menene ai gwara suka ganki da kayan aikin su
san ba ƙarya na musu ba, ki wuce kafin raina ya ɓaci"
Babu yadda ta iya haka ta nufi ƙofar falon Abban saboda batason tayi abin da zai ɓata ran
Baaba tunda yanzu ita kaÉ—ai ta rage musu.

Abbdallah na kishingiÉ—e a doguwar kujera yayinda M.J ke zaune yana danna waya, sallamar da
akayine tasa ya miƙe daga kwancen yana amsawa shikuwa M.J. ko ɗago kanshi baiyi.

"Amaryar..." maganar Abdallah ce ta katse lokacin daya kalli Zarah lokaci É—aya kuma ya waro
ido, kallonta ya ƙarayi sosai tana sanye da abaya amma hakan bazai hana mutum ganin kayan
Ƴan sanda dake jikinta, dariyarshi ya ƙunshe tare da amsa gaisuwar da take mishi.

"Amaryarmu kin shanya mu har mun bushe."

"Ayi haƙuri dan Allah aiki ne ya tsayar dani shiyasa ." ta faɗa tana zama a kujera.

"Toh gaki ga angon dai domin yayi fushi kinga ko kallonki yaƙi."

Kallon shi tayi kana tace
"Barka da zuwa ayimin hakuri na barku kuna ta jira."
Kusan second goma dayin maganar kafin ya É—ago da nufin kallonta, ido ya waro sosai domin
tabbatar da abinda ya gani, miƙewa yayi tare da nufu inda take zaune yana tafa
hannayenshi......��


_Tammat Bi hamdulillah! Nan na kawo ƙarshen free pages, ga maison cigaba da karantawa sai
a tuntuɓeni. Nagode sosai da addu'o'in ku da soyayyarku a gareni, sakallahu khairan._

*By*
*Jasmine*🌸🌸
07048961623
*ASP ZARAH*

Tsayuwa yayi a gabanta na wasu sakonni kafin ya durƙusa a gabanta yace.

"Naji mamaki matuƙa sannan nayi farin ciki da wannan zaɓin na mahaifina, a ɓangare guda
kuma ina takaicin haÉ—ani aure da karuwa da za'ayi, sannan mace mai fuska biyu. Albishir da
shawara zan miki a yanzu.."

Maganar shi ta katse saboda dafashi da Abdallah yayi yana cewa

"Haba M.J wane irin magana kakeyi ne haka.?"

"Kayimin shiru Abdallah bana buƙatar jin komai daga gareka, ka zuba ido kawai."

Baice komai ba ya kuma ya zauna cike da takaicin abinda M.J din yakeyi.

Sunkuyawa ya kuma yi tare da dafa kujerar ta take kai da hannunshi biyu ta yadda suna iya jiyo
numfashin juna.

"Ina baki shawarar ki shirya tarban kowani ƙalubale da zaki fuskanta a zaman da zakiyi a cikin
gidana domin zai kasance tamkar maƙabartarki domin zakiso ki tsince kanki cikin kabarinki fiye
da gidana, sannan ina miki albishir cewa bazan dakatar dake daga aikin naki ba wanda kike
rufarufa dashi kina aikata saɓon Allah amma ki sani bazan lamunta ba ace kina aurena kina
yawon karuwanci. Banza, ballagaza, karuwa kawai mazinaciya."

Ba iya Zarah ba hatta Abdallah saida yaji zafin kalaman M.J akan Zarah, sunkuyar da kanshi
yayi cike da jin kunyarta amma uban gayyar ko a jikinshi illa ma zama da yayi ya ɗora ƙafa ɗaya
kan É—aya tare da tsiyaya ruwa a kofi yana sha.

Tun bayan rasuwar iyayenta bata sake tsintar kanta cikin baƙin ciki da ɓaci rai irin na yau ba,
zuciyarta takeji tamkar xata tsago ƙirjinta ta faɗo, a yau tanaji duk wanda zai kirata da kalmar
_Marainiya_ bazata ƙi amsawa ba, kamar ko da yaushe idan ranta ya ɓaci bata taɓa iya yin
kuka na hawaye saidai na zuciya.
Abdallah ne yayi ƙarfin halin magana ta hanyar faɗin

"Dan Allah Zarah kiyi haƙu...."

"Karka ƙarasa Abdallah mutane masu daraja ake baiwa haƙuri idan anyi musu ba daidai amma
ba marasa tarbiyya irinta ba, tashu mu tafi."

Bai kuma tankawa ba saboda tsananin ɓacin rai illa bayanshi da yabi bayan shi suka fice a
falon.

Tafi mintuna talatin a zaune ta kasa ko da motsawa, bakin ciki tamkar zai kashe ta, murmushin
yake tayi ƙoƙarin yi saboda muryar Baaba da taji a bakin ƙofar falon.

"Me kikeyi anan kuma Zara'u bayan sun tafi." cewar Baaba daga bakin ƙofar.

Miƙewa tayi cikin fara'ar da ta aro tace

"Tunanin masoyina nakeyi, inajin tamkar na kai kaina gidanshi mu cigaba da rayuwa."

Kaucewa tayi daga dukan da Baaba ta kawo mata tana dariya.

"Allahu ya shiryaki Zara'u, muje kici abinci nasan wunin yau duka bakisa komai a cikinki ba."

Nan suka fice a falon tana ta ƙoƙarin biyewa zolayar Baaba cikin dauriya gudun kada ta fahimci
wani abu, sai da É—an tsakuri abincin kafin ta barta ta wuce É—akinta.
Gaban hoton iyayenta ta isa tare da ɗauka ta rungume a ƙirjinta, sai a wannan lokacin kukan
yayi nasarar zuwa mata, batayi jayayya ba domin itama tanason yin kukan ko zai rage mata
raɗaɗin da takeji a zuciyarta, nan ta shiga rera shi mai taɓa zuciya. Ƙarar da wayarta keyi ne
yasa ta tsagaita da kukan tare da miƙa hannu ta ɗauki wayar , ganin mai kiran nata ne
murmushin da batasan dashi ba ya kwace mata, da sallama a bakinta ta kara wayar a kunne,
sai da ya amsa sallamar kafin ya fara jero mata tambayoyi.

"Meyasa kika amince da auren Bro Jawwad.? Dama kuna soyayya? Meya hanaki sanar dani
halin da ake ciki har kina shirin yin aure amma kin kasa sanar dani? Meke damunki ne?"

"Duk wannan tambayoyin Bro wacce kakeso nafara amsa maka ne.?" Ta faÉ—a cikin
marairaicewa

"Duka nakeso ki amsamin, haba mana little wannan zurfin cikin naki yayi yawa."

"Toh ya kakeso nayi Yaya, me kakeso nace maka."

"Gaskiya nakeso ki faɗamin tsakaninki da Allah, kada ki ɓoyemin komai dan girman Allah baki
da wanda ya fini a halin yanzu kinji."

Cikin sanyin jiki ta amsa mishi da "Toh".

"Kuna soyayya da M.J ne.''

Tambayar tazo mata wani irin amma ba yadda ta iya tunda tayi alƙawarin faɗar gaskiya duk da
bataso wani yasan halin da take ciki.

"A'a Yaya"

Numfashi yaja mai ƙarfi kafin yace.

"Ya akayi kuma kuke shirin yin aure?"

Shiru tayi batare da tayi magana ba.

"Ki amsamin banason nadawo nayi abinda bai kamata bane."

"Dear zakazo ne." cikin É—oki tayi tambayar.

"Ehh" ya faÉ—a a takaice sannan ta cigaba da cewa.
"Ki amsamin tambayata, kun haÉ—u da juna ne."

"Ehh basu daÉ—e da tafiya ba ma yazo Bauchi"

"Ya kukayi dashi."

"Yaya..."

"Shikenan tunda bakyason magana idan nazo zan nemi mafita da kaina ko da kuwa dakatar da
auren ne.''

''Haba Bro...."

Bai jira ta ƙarasa ba ya kashe wayar gabaɗaya, zama tayi ta dafe kanta da hannuwa biyu, lallai
ya kamata tasan yadda zatayi ta rarrashi É—an uwan nata akan maganar auren nan duk da itama
a yanzu tana dana sanin amincewa amma ƙaddara ta rigayi fata.

🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢

Babu wanda ke magana a cikinsu har suka isa masaukin nasu, sun daÉ—e a zaune kafin
Abdallah yace

"Yanzu M.J abinda kayi kana ganin ka kyauta kenan.?"

"Mene abin rashin kyautawa anan."

"Oh kai kana gani kayi daidai kenan, ya za'ayi kaje kana zagin baiwar Allah batare da ka
tabbatar da abinda kake zargi ba, ina faÉ—a maka aikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0