Showing 15001 words to 18000 words out of 36994 words
Chapter 6 - ASP Zahra Complete 1 by Asmau Bint Abubakar
Hannunta ta riƙe kana suka haura sama inda suka shige ɗakin Zarah wanda yake farko a jerin
ɗakunan dake saman.
Tsalle Jidda tayi ta faɗa kan gado tare da yin juyi sannan ta fuskanci Zarah dake ƙoƙorin rage
kayan jikinta.
"Ɗazu Baaba ke tsegunta min wani zance."
"Wani zance kenan."
"Zancen auren ki da Muhammad Jawwad mana."
"Uhmm."
"Meyasa ba zaki amince ba Zarah, babu wani fa da zaki aura ya riƙe ki da daraja kamar shi.
Idan ma aikin ki kike tunani ai shi ɗan uwanki ne dole zai barki ki cigaba aikin ki batare da
tsauwalawa ba, nikam bana tunanin akwai aibu a cikin wannan haɗin."
"Kema kinsan dai Daddy uba ne a gare ni ko da ace Abba na yana raye shi mai zaɓa min miji
ne, bazan iya cewa a'a ba kawai dai zaɓin Allah nake nema a cikin al'amura na."
"Toh Allah ya shige mana gaba baki ɗaya ya kuma zaɓa mana abinda yake mafi alkairi."
"Ameen" Zarah ta faɗa tana mai shigewa banɗaki.
Duk wasu bincike daya kamata a gudanar sun gama haɗa shi, zuwa yanzu mai laifin ya daɗe
da kasancewa a bayan kanta a kulle sai jiran ranar shiga kotu duk da yaƙi amsa laifin nashi.
Har zuwa yanzu kuma Zarah bataje office ba tun bayan ranar sa takaiwa C. P rahoton
abubuwan da suka faru.
Yau dai ta shirya domin zuwa ofishin nata bayan tayi sallama da jama'ar gidan.
Kyawawan motoci guda uku ta gani a harabar ofishin nasu wanda ya tabbatar mata da sunyi
baƙin manyan mutane.
Tun kafin ta ƙarasa ta hango Alhaji Mai Riga zaune a inda suka tanada domin zaman baƙi.
Bata ko kalle inda yake ba lokacin da ta ƙaraso kusan shi saima shigewa ofishin ta da Sergent
Bala ya buɗe mata ƙofar.
Saida ta zauna kafin Sergent din yace.
"Ranki ya daɗe wannan mutumin shine wanda yake ta ziryar son ganinki a kwana biyun nan,
yau ma tun ƙarfe bakwai yazo saboda na faɗa mai zaki zo office yau."
Kai ta gyaɗa sannan tace.
"Ka shigo dashi."
Fita yayi bada jimawa ba kuma ya ƙara shigowa inda a bayan shi Alhaji Mai Riga ne da wasu
body guards dinsa da suka sha baƙaƙen kaya guda biyu.
Kujerar da Sergent Bala ya nuna mai ya zauna.
Shikuwa Bala sara mata yayi tare da ficewa a office ɗin.
"Alhaji a tunani na kaine wanda keson zantawa dani." Faɗin Zarah
Washe baki yayi tare da faɗin.
"Ehh nine ranki ya daɗe."
"Toh tsayuwar me waɗannan keyi anan."
Umarni ya basu da su fita waje, nan suka nufi ƙofar fita bayan daya ys ajiye wata brief case a
kan teburin........ ✍í ¼í¿¼
*ASP ZARAH*í ½í±©✈️
_Daga Alƙalamin_✍í ¼í¿»
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_í ¼í¼¸
*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba.
Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin
kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin
banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga
group*.
*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da
izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
í ½í±©✈️
í ½í±©✈️
í ½í±©✈️
í ½í±©✈️
í ½í±©✈️
.. "Na kwana biyu ina zuwa nan ranki ya daɗe bana samun ki." cewar Alhaji Mai Riga.
"Ayya." ta faɗa a hankali.
Zama ya gyara sannan yace.
"Dama nazo ne akan maganar case ɗin yaron waje na da aka ce ke kike riƙe dashi, duk da
naga wannan case ɗin na ƙananun jami'ai ne ba manya irin ku ba."
"Akwai kundin tsarin daya ce babban jami'i kar ya karɓi case ne.?"
"Ba haka nake nufi ba ranki ya daɗe, nazo ne kawai muyi magana akan case ɗin ne."
"Ka samo mana wata shaidar ne.?"
"Ba shaida ba dai ranki shi daɗe, kawai inason ayi wani abu akai ne."
"Bangane wani abu ba."
"Ehhm nace dama ko za'a bar maganar shiga kotun a sasanta a gida kawai."
"Bai aikata abinda ake zarginsa dashi bane.?"
"Ranki ya daɗe kinsan halin yara basa tunani kafin su aikata wani abin."
"Tambaya ce kawai nayi bai aikata bane."
"Ehh toh gaskiya yace min ya aikata amma...''
Hannu ta ɗaga mai alamun batason jin sauran zancen sannan tace.
"Toh Alhaji ya aikata ya kakeson ayi kenan."
"Yauwa nace a sasanta kawai anan inyaso sai abiya kuɗin da mahaifan yarinyar suka kashe
akan nema mata lafiya."
"Baka gudun ya kuma aikatawa."
"Toh kinsan halin yaran zamani su komai sukayi gani suke daidai ne."
"Yanzu kana nufin a janye ƙarar kenan.?"
"Ehh haka nakeso ranki ya daɗe, ni ɗan siyasa ne hakan zai iya jawomin cece kuce a tsakanin
jam'iyun adawa. Yanzu ga wannan." Ya ƙarasa faɗa yana mai buɗe jakar da body guard ɗin ya
ajiye, kuɗi ne maƙil a cikin jakar rafar dubu ɗaɗɗaya an jere su.
Murmushi tayi har saida dimple ɗinta ya lotsa sosai kana ta sa hannu ta taɓa kuɗi tare da ɗaga
rafa ɗaya ta jujjuya sannan ta aje.
Cikin ƙwarin gwiwa alamun nasara Alhaji Mai Riga yace.
"Shiyasa ban turo kowa ba nace bari nazo da kaina ayi maganar zamu fi fahimtar juna."
Gyaɗa kai tayi kana tace.
"Zan iya tambayan ka idan babu damuwa."
"Bakomai ranki ya daɗe yi tambayarki."
"Kana da ƴa mace.?"
"A'a babu yarona ɗaya ne dai wannan da muke magana akan shi."
"Ohk to kana da Yaya ko Ƙanwa mace."
"Gaskiya babu dake dukkan mu maza ne iyayen mu suka haifa. Amma lafiya kike min irin
tambayar nan ranki ya daɗe."
"Ban kai ga ƙarasa tambayata ba idan na gama zan amsa taka tambayar. mahaifiyar yaron nan
yakake jinta a ranka a matsayinta na waccw nake tunanin tun auren ƙuruciya shine har yanzu."
"Gaskiya bazan iya misalta miki yadda nake jinta a raina ba, wannan dalilin ne ma yasa har
yanzu banyi mata kishiya ba."
"Masha Allah, yanzu Alhaji misali wani ya shiga gidanka yayi wa matar ka fyaɗe sannan da
akayi bincike aka gano mai laifin, wani irin mataki zaka ɗauka.?"
"Wallahi da hannu na zan kashe shi, idan ban samu damuwar haka ba kuma zan tsaya da
dukiya da ƙarfina har sai naga an yanke mishi mummunan hukunci akan laifin daya aikata min."
Dariya Zarah tayi sosai sannan lokaci ɗaya ta gimtse kana ta jawo jakar kuɗin gabanta ta zuge
zip ɗin kamar yadda yake tare da tura jakar gaban Alhaji Mai Riga kana tace.
"Kamar yadda kakejin zaka tsaya da ƙarfi kuma da dukiyarka ni idan akayi qa matarka fyaɗe,
toh ni inajin fiye da hakan wajen ganin na tsayawa kowace mace da aka ketawa haddi domin
abi mata haƙƙinta. Wannan kuɗin da ka kawo bazai taɓa canzamin ra'ayi domin na saba riƙe
fiye da irinsu, cin hanci koh? Toh kasani cewa bakayi kuɗin da zaka iya bawa Zarah cin hanci
ba, wannan kuɗin ko albashin ma'aikatana na wata ɗaya bazai iya biya ba. Shin kasan girman
laifin da ka aikata na baiwa ƴar sanda cin hanci.? Tabbas zan baka mamaki kuma dole a
yankewa yaron ka hukunci daidai laifin daya aikata. Banason na ƙara jin ko da kalma ɗaya ce ta
fito daga bakin ka idan kuma ba haka ba, hmm kulle ka ba wani abu mai girma bane a wajena
sannan babu wani jami'in dayasa isa ya saka ni buɗeka idan nayi hakan. Dan haka kaɗau
tarkacen kuɗinka ka ficemin daga office." taƙarasa faɗi tana mai buga teburin, wanda hakan ya
ƙara ɗarsa tsoro a zuciyar Alhaji Mai Riga domin dai dama ƙarfin hali kawai yakeyi yake iya
mata magana amma ba ƙaramin kwarjini take masa ba.
Batare da tanka ba kamar yadda tace yaɗau jakar tare da ficewa daga office ɗin yana mai
banko ƙofar da ƙarfi.
Murmushi Zarah tayi sannan tace.
"Mai Riga kenan, ba shirin wasa nayi a kanka ba duk wani motsin ka yanzu a tafin hannu na
yake.".
Kiran wayar daya shigo ne yasa ta saka hannu ta jawo wayar daga inda take, numbar Daddy da
tagani ne yasa bata ɗaga ba har saida ta yanke sannan ta maida kiran.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaikumus salam daughter barka da safiya."
"Daddy ina kwana."
"Lafiya lau kun tashi lafiya koh.?"
"Lafiya kalau Daddy ya Momi."
"Gata nan lafiya lau, yasu Baaban dai da mutanen turai."
"Duk suna lafiya Daddy."
"Kin fita aiki ne yau.?"
"Ehh ina office."
"A'a toh bari na bari ki koma gida kar na katse miki aiki, dama nayi tunanin kina gida ne shiyasa
na kira muyi magana."
"Bakomai Daddy ba aiki nakeyi ba dama, zamu iya magana babu damuwa."
"Toh Masha Allah, nace ko Baaba ta isar miki da saƙo na.?"
"Ehh Daddy ta gayamin kuma na amince."
"A'a Zarah idan kina da wani ki faɗa kar na tauye miki."
"Babu kowa Daddy."
"Toh nagode kwarai Allah yayi albarka."
"Ameen Daddy."
"Sai anjima ki gaishe da su Baaban."
"Zasuji insha Allah."
Nan suka yi sallama ta aje wayar a gefenta tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi.
"Oh ni Fatimaj Zarah, aure da mijin da bansan shi ba."
Sai kuma tayi murmushi ita kaɗai tare da kaɗa kai.
.........
Shi kuwa Alhaji Mai Riga bayan fitarsa daga office ɗin Zarah cike da takaicin rashi haɗin kai da
bata bashi ba, kai tsaye gidan alƙalin kotun da aka shigar da ƙarar ya nufa.
Bai wani sha wahala ba aka shigar dashi cikin gidan, bayan sun gaisa da alƙalin ne yake faɗa
mishi abinda ke tafe dashi nason kar a yankewa yaronshi hukunci tare da korar ƙarar gabaɗaya.
Toh ƙasar tamu dai ta ɓaci kowa son kuɗi kawai, babu ɓata lokaci alƙalin ya amince gani irin
maƙuda kuɗin da aka aje a gabansa.
Sallama sukayi zuciyar Alhaji Mai Riga fal da farin ciki.
*By*
*Jasmine*í ¼í¼¸
*ASP ZARAH*í ½í±©✈️
_Paid book_.
_Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300
kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP
idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki._Za'a turo kuɗi ta wannan asusun
0153109156 Union Bank, sannan a turo shaidar biya ta 07048961623._
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Page 9*
*ALPHA VILLA*í ½í±½
Kamar koda yaushe ba'a taɓa ganin daga inda yake magana saidai a jiyo sautin muryar sa.
"Raliya ki kula sosai banaso a samu wata matsala, yanzu idan kuka bar nan za'a kaiki filin jirgi
inda daga can zaki wuce Gombe, kiyi amfani da adireshin dana baki ki isa zuwa gidan kamar
yadda na tsara miki, ki tafiyar da komai cikin tsari kada ki bari a gano ki. Gobe da safe ne zaki
isa zuwa gidan bayan ta fita zuwa gurin aiki. Kin fahimce ni."
"Na fahimta Oga zanyj komai yadda kace." Raliya dake rakuɓe a gefen ɗaya daga cikin kujerun
ɗakin ta faɗa kanta a sunkuye.
"Banason rawar kai Raliya, samo masaniyar inda lu'u lu'un yake shine kawai aikinki, ban baki
damar kiyi yunƙurin sacewa ba wannan aikin ba naki bane. Ina ƙara jaddada mi ki."
"Ba za'a samu matsala ba Oga."
"Ki tashi kije ki gama kintsawa ƙarfe biyar za ku wuce."
"Toh na barka lafiya yallaɓai." ta faɗa tana mai miƙewa daga durƙushen da ta ke sa'an nan ta
nufi ƙofar da zata fidda ta daga cikin falon.
........................................
Haka Alhaji Mai Riga yayi ta zagawa yana siye bakin waɗanda ke da masaniya akan case ɗin
hatta lauyan bogi da Zarah ta ɗauka saida ya bashi maƙudan kuɗi akan ranar da za'a shiga kotu
yayi tawaye yace shi lauya ne mai kare wanda ake zargi.
Yau ta kama ranar lahadi inda gobe ranar litinin za'a shiga kotu, dukkan su suna zaune a falo
suna hira jefi- jefi wanda akasarin hirar tsakanin Jidda ne da Baaba domin Saleem da Jidda
suna gaban na'ura mai kwakwalwa suna gudanar da aiki.
Baaba ce ta kalli gefen da su Zarah suke kana tace.
"Zara'u ince dai mahaifin naku ya faɗa miki matsayar da ya yanke game da bikin ku."
Kallonta Zarah tayi batare da ta tanka ba ta maida hankali kan abinda ta keyi, Jidda ce ta maida
hankalinta wurin Baaba tace.
"Wace matsaya kuma Baaba tunda ta rigada ta amince.?"
"Ai uban nasu yace nan da watanni biyu za'ayi bikin, shima Muhammadun ya kusa dawowa
gida domin fara hidimar bikin." inji Baaba
"Lallai kice mu ma mu fara shiri kenan Baaba mun kusa zama amare." Jidda ta faɗa cike da
zolaya.
"Sosai ma kuwa." Faɗin Baaba.
"Amma Yaya Sadiq zai dawo bikin koh.?"
"Ehh naji Sulaimanu na cewa sun gama karatun zaije da kanshi ya taho dashi, kinsan tunda yaji
labarin rasuwar nan shima yake ta noƙe noƙen son cigaba da zama a cikin turawa."
"Gaskiya kam ya dawo bikin ƙanwa babu babban Yaya ai ba zaiyi armashi ba."
"A toh su daɗi su keji ganin kansu a tsakiyar arna suna shawagi."
"Kai Baaba bafa duka bane arna akwai musulmai sosai."
"Duk jirgi ɗaya ya kwaso ku ai."
"Baaba watarana dai zamu kaiki ƙasar turawan nan kiji yadda akeji idan ana can."
"Allah ya tsareni ni Faɗimatu, bana fatan gani ko a mafarki na. Zara'u wani irin aiki ne kuke yi
haka da baza ki bari kizo kiyi karin kumallo ba, ina fa lura dake kwana biyun nan sam bakyason
cin abinci, shiyasa kike ta ƙarewa kamar kazar mayu." Ta ƙarashe maganar hankalinta na kan
Zarah.
"Baaba ko kece kika tsinci kanki halin da take ciki baza ki samu nutsuwa ba sai kin kai ga ci."
Faɗin Jidda
"Yoo wani hali ne take ciki banda na sama kanta damuwa sai an daina cin hanci a ƙasar nan,
waɗanda suka fita ma sun gwada sun ƙyale."
"A'a fa Baaba case ɗin fyaɗe ne a hannunta kuma gobe za'a shiga kotu, shiyasa take ƙoƙarin
tara duk wasu hujjoji gudun kada aka dasu, gashi dama iyayen yarinyar ba masu hali bane."
Salati Baaba ta shiga dokawa harda ƴar guntuwar kwalla kafin tace.
"Ashe har yanzu ana wannan rashin imanin a ƙasar nan, shikenan dai shi talaka bazai taɓa
hutawa ba. Yanzu mene ne ribar yiwa mace fyaɗe, kawai saboda tsantar zalunci da son
rugujewa mutum rayuwa. Insha Allahu duk asirin su saiya tuno an hukunta su, shiyasa nake son
aikin Zara'u saboda gaskiyar ta. Nayi ma Muhammadu magana ma dole zai barta ta cigaba da
aikinta saboda rashin ta zai iya saka al'umma cikin wani hali."
"Baaba ƙasar tamu yanzu ai sai dak kawai mu cigaba da addu'ar samun gyara, amma kullum
lamura ƙara taɓarɓarewa suke yi."
"Kullum cikin addu'a muke kuma bazamu taɓa gajiya wa ba."
Nan suka cigaba da tattaunawa akan matsalolin dake addabar ƙasar ta mu har zuwa lokacin da
su Saleem suka gama aikin suka dawo cikin falon aka cigaba da hirar da su.
Washe gari da wuri Zarah ta bar gidan bayan tayi sallama da su Jidda da zasu haɗu acan
kotun.
Kotun ta cika maƙil saboda ba shari'a ɗaya ake gudanarwa ba, baya ga haka kuma abokan
hamayyar Alhaji Mai Riga su ma sunzo dan ganin yadda zata kasance.
Shari'a biyu aka gudanar kafin azo kan case ɗin Fahima.
Kamar kowace shari'a, lauyoyin sun hallara a inda aka tanadar musu domin zama. Nan aka
umarci su gabatar da kansu.
"Suna na Bar. Labaran Ahmad tare da abokin aiki na Bar. Gideon Wangson mu ne masu kare
wanda ake tuhuma." Faɗin ɗaya daga cikin lauyoyi biyu dake zaune a inda aka tanadar musu.
"Shin Bar. Labaran bakai bane lauyan masu ƙara." Faɗin Alƙalin.
"Bani bane my lord." Inji Labaran.
Jinjina kai kawai alƙalin yayi kana yace.
"Ina lauyan masu ƙara."
Shiru babu amsa.
Alhaji Mai Riga ne ya kalli inda Zarah take tare da yin wani shu'umin murmushi mai cike da
ma'anoni, ita ma murmushin ta maida masa mai alamar bakasan me kake yi ba. Kafin ya gama
mamakin murmushin daya gani a fuskar ta ya jiyo sautin magana.
"Suna na Barrister Saleem Sa'ad ni ne lauyan masu ƙara,