Showing 18001 words to 21000 words out of 36994 words
Chapter 7 - ASP Zahra Complete 1 by Asmau Bint Abubakar
my lord ayimin haƙurin lattin da nayi
hakan ya faru ne a sanadin cunkoson ababen hawa da na samu a hanya." cewar Saleem
wanda shigowarsa kenan ya nufi gurin zaman lauyoyin.
"Bar. Saleem a kiyaye na gaba." cewar alƙalin.
Ba iya Alhaji Mai Riga bane ya shiga mamaki da ruɗun jin abinda ya fito daga bakin Saleem,
hatta Labaran saida ya ruɗe domin dai ko kafin a fara gabatar da zaman kotun na yau sun
tattauna da Zarah a matsayin shi na wanda zai tsayawa Fahima. Lallai ya tabbatar ta samu
labarin zaiyi tawaye shiyasa ta tanadi wani lauyan.
Zufa ce ta fara keto masa ta kowani sashi ba jikinshi, ɗagowa yayi jin alƙali ya buƙaci su
gabatar da shaidar su ta farko, sai dai me...............✍í ¼í¿¼
*BY*
*Jasmine*í ¼í¼¸í ¼í¼¸
07048961623.
*ASSALAMU ALAIKUM*
*Uwargida da amarya har yanzu fa ƙofa buɗe take, zaki iya samun damar kasancewa da ni
HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA a cikin zafafan darussan da nake gabatarwa a ASP
ZARAH SPECIAL FANS GROUP, domin samun dabarun zama da miji, ɓoyayyun sirrikan da
zakiyi amfani da su wajen mallake mijinki cikin sauƙi, tare da sahihan kayan gyara na
musamman sha yanzu magani yanzu. Kada ki bari ƴar uwarki ta labarta miki.*
*Cikin ikon Allah a ƙanƙanin lokaci group ɗin mu na farko ya cika kuma yanzu haka mun buɗe
wani sabon group ɗin ga masu buƙatar su shiga a baje wannan kolin dasu. Kada kumanta dai
zaku iya samun damar shiga wannan group ta hanyar tuntuɓar wannan number 07048961623.
Ina jiran zuwanku, ni ce dai takun da bani da tamka HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA*.
*ASP ZARAH*í ½í±©✈️
_Paid book_.
_Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300
kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP
idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki. Za'a turo kuɗi ta wannan asusun
0153109156 Union Bank, sannan a turo shaidar biya ta 07048961623.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Zarah ya gani ta kafe shi da idanunta masu rikitarwa, nan take ya ruɗe har saida yaji Gideon na
gabatar da tambayoyi ga Kabeer kafin ya maida hankali.
Mintuna talatin ana fafatawa tsakanin ɓangare biyun inda Saleem ke gabatar da zafafan
shaidun daya tada hankalin Alhaji Mai Riga da muƙarrabansa, domin hatta inda yake cewa
Zarah tabbas ɗan shi ya aikata laifin da ake zargin shi saida aka gabatar a gaban kotu. Nan fa
kotu ta rikice kowa na faɗin albarkacin bakinsa musamman ƴan adawan Alhaji Mai Riga.
Hutun rabin lokaci aka alkali ya bayar, gaba ɗaya jama'a aka fita waje.
Duk yadda Mai Riga yaso ganin alkalin a wannan lokacin abu ya gagara, hankalin shi ne yaji ya
tashi amma tunawa dayayi da irin maƙudan kuɗin da ya bawa alkalin sai ya ɗan samj nutsuwa
tare da tabbatarwa kanshi samun nasara.
A daidai wannan lokacin kuwa Baaba tana zaune a falo tana kallon wa'azi a sunna TV, ɗaya
daga cikin masu tsaron ne ya shigo tare da shaida mata cewa tana da baƙuwa, batare da
dogon tunani ba tace ya shigo da ita.
Jim kaɗan ya dawo tare da Raliya wacce ta ɓadda kama sosai tamkar ba ita ba, wasu tsofaffin
kayane a jikinta wanda a kowani lokaci zasu iya yagewa sai wata ƙaramar Ghana-Must-Go
itama ta tsofa sosai.
Da sallama ta ƙarasa cikin falon sannan ta zauna ƙasa nesa da inda Baaba take.
"Ki hau saman kujerar mana baiwar Allah." Inji Baaba.
"A'a nan ma yayi Hajiya, ina wuni." Faɗin Raliya.
"Lafiya lau sannu da zuwa, sai dai ban shaida fuskar taki ba kodai gurin Zara'u kika zo ne."
"A'a Hajiya dama nazo neman aiki ne."
"Wane irin aiki kuma daga ina kike.?"
"Ni marainiya ce a garin Tilden Fulani nake, iyayena sun mutu ne sanadiyyar gobara da ta cinye
gidan mu tun daga lokacin kuma na rasa masu taimakamin. Toh akwai wata Mata a can gurin
namu da take shigowa birni tana aiki shine ta bani shawarar na shigo na zaga gidan masu hali
na nemi aikin yi saboda nasamu abinda zan dinga rufawa kaina asiri dashi."
"Duniya ta lalace mutane basason taimako, ai shi maraya idan ka taimaka mi shi tamkar ka
zuba adashe ne da zaka kwashe ranar lahira. Kada ki damu insha Allahu za'a baki aiki koda na
goge-goge ne."
"Nagode Hajiya Allah ya saka da alkhairi."
"Amin babu komai ai hakkin maraya ne mukeson saukewa."Inji Baaba.
Sun ɗan jima suna taɓa hira kafin Baaba ta miƙe ta shige ɗaki bayan tabar Raliya a falo tana
kallo, da sanɗa tabi bayan Baaba dan ganin mai zatayi a ɗakin, ganin shigewarta banɗaki ne
yasa tayi saurin komawa falo tare da buɗe jakarta ta ciro wani abu kamar bead na kitson yara ta
nufi saman bene. Bata sha wuyar gane ɗakin Zarah ba saboda taswirar gidan da ta haddace a
kanta, ɗakin a buɗe yake dan haka tana shiga ta nufi gaban durowar kayan Zarah, wannan
abun ta ajiye acan saman durowar ta yadda babu wani mahaluƙin dazai iya cewa akwai wani
abu a gurin idan ba anfaɗa ba.
Komawa falon tayi cikin sanɗa tamkar ɓeran dayayi sata yana tsoron a kamashi.
A can kotu kuwa bayan mintuna talatin sun cika aka koma aka cigaba da fafatawa tsakanin
ɓangarorin guda biyu, domin dai da alama shari'ar ta kwana ɗaya ce.
Shiru ya ratsa cikin kotun bayan shuɗewar wasu mintuna, duk wannan abu dake faruwa Alhaji
Mai Riga lokaci zuwa lokaci yake ɗagowa ya kalli ɓangaren da Zarah take yana yi mata
murmushin ƙeta domin dai zuwa yanzu ya gama tabbatarwa kanshi cewa shi ɗin mai nasara ne
sannan baza a yankewa ɗansa hukunci ba. Ita kuwa Zarah zancen zuci take a duk lokacin daya kalletan sai tace.
"Shi dai mutum mara basira ko ina yake ana ganewa."
Alƙali ne ya fara magana kamar haka.
"Bayan sauraron shaidu da ɓangare biyu suka gabatar tare da hujjoji wanda suka gamsar da
kotu da kuma kundin tsarin shari'a na ƙasa, kotu ta yankewa Kabeer hukuncin zama a gidan
kaso na shekaru goma tare da aiki mai tsanani sa'an nan zai biya tarar miliyan biyar domin
nemawa Fahima lafiya, Alhaji Nuhu Mai Riga kotu ta kama shi da laifin yunƙurin baiwa ɗan
sanda cin hanci, dan haka kotu ta yanke mishi hukuncin zama gidan horo na wata biyar ko
kuma tarar miliyan ɗaya." yana gama faɗin haka ya buga gudumarsa wanda ke nuna alamar ya
gama aikin shi na wannan rana.
Kotu fa ta rikice inda Alhaji Mai Riga keta zage-zage tamkar mai taɓin hankali ana riƙeshi, nan
fa ƴan jam'iyun adawa da ƴan jaridu suka samu inda sukayi ta ɗaukan hotonan shi, wasu harda
yi mashi video.
Haka yana ji yana gani aka wuce da ɗanshi ɗaya tilo tamkar rai zuwa gidan kaso, take kuma ya
zube a ƙasa tare da sakin kuka mai tsanani.
"Jidda mu wuce gida kawai ki rabu da Saleem ɗinki da ƴan Jaridun nan." cewar Zarah bayan ta
janyo hannu Jidda zuwa wani keɓeɓɓen waje a bayan kotun.
"Mene ne haka wai Zarah ki barni mana a haskani a jarida tare da hubby na."
"Mtssww mu wuce Jidda banason dogon zance, jikina na bani wani yanayi da ban gamsu dashi
ba." ta faɗa tana tura Jiddan cikin motar ta, wuta ta baiwa motar bayan ta shiga itama, nan suka
bar farfajiyar kotun zuwa gida...... ✍í ¼í¿¼
*By*
*Jasmine*í ¼í¼¸
*ASP ZARAH*í ½í±©✈️
_Second to the last free pages._
_Paid book._
_Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300
kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP
idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki. Ku tuntuɓeni a 07048961623
domin biya._
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*M*. *W*. *A*.
Gudu takeyi tamkar zata tashi sama, yayinda Jidda ke mata ƙorafin karfa tayi sanadin tafiyarta
lahira bata shirya. Ko kulata batayi ba har suka iso bakin gate ɗin gidan, horn tayi aka buɗe
mata ta shigar da motar ciki, sai a lokacin ta samu nutsuwa amma duk da haka tanajin wani irin
yanayi a tattare da ita.
''Haka kawai kin rabo ni da mijina, toh wallahi garin ma zamu bar miki tunda mun gama yin
abinda ya tsaida mu." Inji Jidda.
"Ba iya garin nake so ku bari ba, dan Allah ku bar ƙasar ma baki ɗaya." Zarah ta faɗa cike da
tsokana lokacin da take fita a cikin motar.
Da gudu Jidda ta bita suka nufi hanyar babban falo tamkar wasu ƙananan yara.
"Allah ya shirye ku, wannan ai sai kusa nima na ruga da gudu, manya daku kuna wasan
guje-guje, ke Hauwa idan ita bata rigada ta gama girma ba ai ke kam kin girma saiki daina biye
mata." Faɗin Baaba wacce ke zaune a falo lokacin da suka shigo da gudu.
"Kai Baaba kin manta wai nafi Jidda shekaru ne.?" Inji Zarah.
"Yo idan kin fita shekaru ai yanzu kam ta fiki tunda a ɗakin mijinta take."
"Saboda kawai tayi auren.?"
"Ehh mana ai ko ƴar shekara 14 tayi aure yanzu dole za'a kirata da yayarki."
"Faɗa mata dai Baaba ko zata daina raina ni." Jidda kenan ta faɗi.
"Nima dai auren nan na kusa yinshi na huta." Ta faɗa tana zama a kujerar da Baaba take kai.
"Ahh lallai da bamu yi shawarar aurar dake ba gaba bamu san abinda zaki dinga furtawa a
gaban mu ba." Faɗin Baaba tana tafa hannayenta.
Bata kulata ba saima plate ɗin dake gaban Baaban data janyo wanda ke ɗauke da lafiyayyen
dambun shinkafa da yaji haɗi.
"Baaba yau kin tuna da gargajiya ne haka, shiyasa kika kasa jira mu dawo muyi girkin." Zarah ta
faɗa tana ɗebo dambun a cokali da nufin kaiwa baki.
"Allah sarki bama nina dafa ba, baƙuwa mukayi shine nace ta shiga kicin ta girka mana gudun
kada ku dawo a gajiye, kin ganshi nan yanzu aka gama shine na ɗebo naci."
Harta buɗe baki da nufin cin dambun da ta ɗebo, amma jin abinda Baaba ta faɗa yasata dawo
da cokalin tare da maidawa kan plate ɗin.
"Wacce baƙuwa kuma.?" Ta tambaya fuska a yamutse.
"Ƴar aiki na samu mana, tunda Iya Delu dai bamusan ranar dawowarta ba."
"Ƴar aiki kuma.?"
"Ehh ko banyi daidai bane uwata.?"
"A'a kawai nayi mamakin inda kika samo ƴar aikin ne bayan ba fita kikeyi ba."
"Nan tazo neman aikin, toh ganin muna buƙata yasa na ɗauketa, kuma naga tana da hankali da
nutsuwa shiyasa bayan haka kuma marainiya ce."
"Ana ɗaukan aiki batare da bincike bane Baaba.?"
Harara Baaba ta wurga mata kana tace.
"Nasan ki ai da shigen bin ƙwaƙƙwafi shiyasa ma na nemi wacce ta kawo ta birnin muka zanta,
bayan haka kuma ga lambar ta nan na karɓa idan kinason jin ƙarin bayani, mtsww."
"Me yayi zafi Baaba tunda ke zata dinga taimakawa, nikam ai bani da matsala tunda ba gidan
nake wuni ba."
"Yo ai nayi tunanin koh kulle ni zakayi tunda nayi abu batare da izinin ki ba."
Ita dai Jidda bata saka baki ba, tana zaune a kujera ta kurɓar fresh milk ɗin da ta ɗauko,
saboda surutunta ne ma yasa bata saka baki ba domin dai Baaba batasan a fara magana a bari
ta daɗi ba, shiyasa ta barta da Zarah sanin da tayi cewa Zarah bata da magana sosai, tasan
zancen bazai yi nisa ba za'a ƙarƙareshi.
"Kin ci dambun ne Baaba.?" Zarah ta tambaya fuska babu walwala.
"Na ɗebo kenan zanci ai kuka shigomin a birkice."
Batace komai ba ta ɗau plate ɗin dambun ta nufi hanyar kicin.
"Ina zaki kaimin abincin kuma.?''
"Yau ba dambu na tsara zamu ci a gidan nan ba, dan haka babu mai ci. Habibaty taso mu dafa
wani abu mai sauƙi kafin SaJid ɗin naki da baya jurar yunwa ya dawo." ta faɗa tana mai
shigewa corridor ɗin dazai sada ta da kitchen.
Jidda ma tashi tayi da sauri ta bita tun kafin Baaba tayi magana.
"Ki kiyayeni fa Zara'u wallahi zan saɓa miki, ki kawomim abincin nan tun kafin na iso gurin na
sameki." Faɗin Baaba dake ƙoƙarin tashi ta nufi kitchen ɗin.
"Kulle ƙofar nan SaJid karta zo ta dame mu."
"Toh ke wai meye dalilinki na hanata cin dambun ne, nima wallahi ya bani sha'awa so nake
naci."
"Kawai naji ban yarda da girkin bane, dan haka babu mai ci."
"Kamar ya baki yarda da girkin ba? tsabtar shi ko me.?"
"A'a bansan hanyoyin da aka bi aka sarrafa shi ba ne shiyasa, da ace ina gida ma babu wata
ƴar aiki da zamu ɗauka saidai mu jira har zuwa lokacin da Iya delu zata dawo."
"Ƙyanƙyami ne kawai irin naki amma kina ganin dambun nan ai kinsan an tsabtace shi, nikam
banga ƴar aiki da ake magana akanta ba ma."
"Ƙila tana ɗakin da Iya Delu ta zauna. Mu haɗa Jallof ɗin cous-cous kawai nima yunwar nakeji
sosai."
Cikin ƙanƙanin lokaci suka haɗa lafiyayyen cous-cous da yaji kayan haɗi da nama, sai lemun
citta da fruit salat da suka yi. A faranti suka jere komai, inda Jidda ta ɗauka domin zuwa ta jere
a dinning, ita kuwa Zarah fruit salad ta ɗeba a plate ta nufi cikin falon.
Baaba na nan zaune inda ta barta, saɓanin ɗazu da take ita kaɗai yanzu tare suke da wata da
bata ga fuskarta ba, remote ta ɗauka tare da canja tasha daga Sunnah TV zuwa TVC News
kana ta zauna a kujerar dake fuskantar Raliya dake zaune a ƙasa rakuɓe a jikin kujera.
"Ya zaki canja mana tasha muna kallon wa'azi zuwa tashar arna." Faɗin Baaba a hassale.
"Kiyu haƙuri Baaba ta ki daina wannan fushin da ni kinji, labarai kawai zan kalla na tashi."
Sai a wannan lokacin Raliya da tayi nisa a cikin tunani ta lura da shigowar Zarah, kallonta tayi ta
ƙasan ido, ai nan dake ta ɗauke kanta daga kanta saboda wani irin kwarjinin Zarah da ta hango.
Cikin dakiya da dauriya tace.
"Ina wuni ranki ya daɗe."
Kafeta da ido Zarah tayi tana son gano wani ɓoyayyen abu a tattare da ita.
Ita kuwa Raliya kai ta sunkuyar cikin ruɗu tare da tunanin ko Zarah ta gane ta ne.
"Banason haka fa Zara'u kin kafe baiwar Allah da ido tamkar mai laifi a bayan kanta."
"Marabar kaɗan ne." cewar Zarah a cikin ranta duk da batada wani tabbaci akan yanayin rashin
gaskiya da zuciyarta ke gayamata akan Raliyan.
"Lafiya." ta faɗa a taƙaice tana mai cigaba da cin fruit salad ɗin.
Sunanan a zaune a falon har lokacin da Saleem ya dawo, Baaba ce take tambayar Saleem ɗin
yadda shari'ar ta kasance, baki ya buɗe da nufin labarta mana amma saidai kallon da Zarah ta
mishi ne yasa shi cewa.
"Baaba munyi nasara." yafaɗa a takaice domin ya gane ma'anar kallon Zarah a gareshi, nufinta
karya faɗi yadda shari'ar ta kasance.
"Hubby kai muke jira tun ɗazu, mu ƙarasa dinning yunwa mukeji."
Su uku suka miƙe suka nufi dinning ɗin, Jidda ce tayi serving ɗinsu, nan suka fara cin abincin.
Kamar wacce aka tsikara haka ta miƙe da sauri ta nufi ɗakinta batare da ta amsa tambayar da
Jidda ke mata ba......
*ASP ZARAH*í ½í±©✈️
_Paid book._
_Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300
kacal na normal group, VIP kuma N500. A tuntuɓeni a 07048961623 domin biya._
*í ¼í¼�MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*í ½í³ší ½í¶Š️
*M*. *W*. *A*
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*Free Page*
Haka nan taji tamkar ana umartarta ta zuwa ɗakin, da sallama a bakinta ta shiga duk da tasan
babu kowa a cikin ɗakin, maida ƙofar tayi ta rufe kana ta jingina jikinta a jikin ƙofar tana mai
ƙarewa yanayin ɗakin, yana nan kamar yadda ta barshi. Gaban durowar kayanta ta isa tare da
tsayawa tana kallon gurin, tabbas wani ɓangare na umartarta da bincikar gurin saidai ɗaya
ɓangare na hanata ƙoƙarin haka. Ƙarar wayar ta ne ya fargar da ita, kallon fuskar wayar tayi
taga Ammi ce mai kiran, saida ta zauna a bakin gadon tukun kafin ta ɗaga wayar.
"Ammi na." ta faɗa a hankali..
"Na'am daughter ya kuke."
"Lafiya lau Ammi ya jikin Rahma."
"Alhamdulullahi jiki ya fara samuwa, yanzu tana iya yin magana wasu lokutan amma ba sosai
ba."
"Allah ya ƙara lafiya."
"Kin fara gyaran jiki kuwa Zarah." cewar Ammi
Cikin son gane mai take nufi Zarah tace.
"Wani irin gyara jiki kuma Ammi.?"
"Zan saɓa miki fa, kina nufin baki fara amfani da kayan da Momin ku ta turo miki ba." cewar
Ammin.
Dafe kai Zarah tayi, sam ta manta batun kayan da Momi ta aiko mata dasu.
Jin shiru ne