Showing 12001 words to 15000 words out of 36994 words
Chapter 5 - ASP Zahra Complete 1 by Asmau Bint Abubakar
yace.
"Baiwar Allah da farko dai ina ƙara jajanta miki akan wannan lamari da ya afku dake sannan
inason sanin ko ke wacece.?"
"Da farko dai ni suna na Fahima ina zaune ne tare da iyayena a anguwar bakin kura dake nan
jihar Bauchi. Sannan mahaifina mai ƙaramin ƙarfi ne." magana take a hankali alamum dai tana
jin jiki.
"Meya jawo afkuwar wannan lamarin a gareki."
"Ina aikine a gidan wani É—n majalisa dake nan anguwar mu wato Alhaji Nura Mai Riga. Tun
lokacin da nafara aiki a gidan É—an sa Kabeer ke yawan shigemin tare da nuna alamun yanaso
muyi sabo sosai saidai ban bada damar hakan ba. To a ranar larabar data gabata ne bayan na
kai masa abincinsa na rana kamar yadda na saba kowani lokaci bayan na gama girki ina kai
masa nashi bangarensa. Bayan na ajiye abincin ne ya miƙomin kofin dake hannunshi wanda ke
É—auke da lemu ya umarceni da na shanye, naso nayi jayayya saidai yace idan ban sha ba bazai
barni na tafi ba shiyasa na karɓa na shanye tare da miƙewa da nufin tafiya sai ya kuma cewa na
share mai falon shi yayi ƙura. Tunda nafara sharar nakejin bacci na fizgata kafin nagama kuma
bansan inda kaina yake ba sai farkawa nayj na ganni akan gadonshi ya ketamin haddi..." Ta
ƙarasa faɗa tana mai fashewa da wani marayan kuka wanda ke nuni da ciwon abin da takeji.
Kashe recorder ɗin Saleem yayi kana ya miƙe ya fita yana musu alama da ido.
Zarah da Jidda ma miƙewa sukayi kana Zarah tace.
"Insha Allahu za'a bi miki haƙƙinki sannan kafin mu tafi za'a sa hannu a shigar dake aikin da
za'a miki na matsalar yoyon fitsari da kika samu."
Godiya suka ƙara yi musu sosai.
Sanna su Jiddan suka bar É—akin.
Saida suka biya kuÉ—in aikin da za'ayi wa Fahima sannan suka bar cikin asibitin.
A hanyarsh da zuwa gida ne Jidda dake gaban motar ta waiwayo ta kalli Zarah data jingina
kanta a jikin kujerar bayan motar tace.
"Zarah kina ganin ba muyi ganganci ba wajen shiga cikin wannan case É—in daya shafi Alhaji
Nura Mai Riga.?"
"Banason halinki na saurin karaya Jidda, kada ki manta Allah yana tare da msi mai gaskiya." Ta
faÉ—a tana mai É—agowa daga jinginawar da tayi jikin kujerar.
"Waye ne Alhaji Nura Mai Riga.?" Saleem ya tambaya hankalinshi na kan hanya.
*ASP ZARAH*í ½í±©â€�✈ï¸�
_Daga AlÆ™alamin_âœ�í ¼í¿»
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_í ¼í¼¸í ¼í¼¸
*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba.
Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuÉ—i N300 kacal domin karantashi cikin
kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing É—in littafi dan Allah kada ki biya kuÉ—in
banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga
group*.
*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da
izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
í ½í±©â€�✈ï¸�
í ½í±©â€�✈ï¸�
í ½í±©â€�✈ï¸�
í ½í±©â€�✈ï¸�
í ½í±©â€�✈ï¸�
... Jidda ce ta gyara zama tare da fara magana.
"Wani sanannen É—an siyasa a ciki da wajen Bauchi, anyi mishi shaidar rashin arziki da
wulaƙanci gami da cin zarafin na ƙasa dashi, baya ragama kowa kasancewar yana da muƙami
ga dukiya kuma daya tara, shiyasa yake taka kowa ya zauna lafiya daga shi har É—an nashi. Ana
faÉ—in cewa zai iyayin komai akan yaronshi ko da kuwa kisa ne. Shiyasa nake tsoron kar wani
abu ya haÉ—a su da Zarah saboda baza'a haifar da É—a mai ido ba."
Kai Saleem ya girgiza kana yace.
"Gaki a haka kamar Jaruma amma zuciyarki fal take da tsoro, ni a gani na wannan ba wani abu
bane da za'a tsorata har ayi shakkun yin shari'a dashi. Insha Allah zamu zauna anan har sai
munga an kwatar ma yarinyar nan hakkinta. Kuma ni zan zame mata lauya."
"A zahiri bakai bane zaka zame mata lauyan amma a baÉ—ini kai ne." Zarah ta faÉ—a idonta a
lumshe kamar ba ita tayi maganar ba.
ÆŠan juyuwa Saleen yayi yana son fahimtar abinda take nufi.
"Wani lauyan zamu nema yanzu a matsayin wanda zai kareta, saboda zai iya siye duk wani
lauya da zamu É—auka da kuÉ—i. Bayan mun gama yarda muna da lauya sai ranar da za'a shiga
kotu mu rasa mafita. Shiyasa a yanzu dole mu É—au wani lauyan na ganin ido, amma a baÉ—ini
zamu cigaba da gudanar da bincike tare da haÉ—a shaidun da zamu gabatar a kotu." Cewar
Zarah
Sosai suka ƙara mamakin fasahar ta wajen yin tunani abinda masu laifi zasu aikata.
"Sam banyi tunanin haka ba da farko, kuma tabbas nasan Alhaji Mai Riga zai aikata haka."
FaÉ—in Jidda tana mai haÉ—e hannayenta alamun jinjina ga Jidda.
Haka suka cigaba da tafiya suna hira jefi-jefi har suka ƙaraso gidan.
ÆŠakinta ta wuce kai tsaye tare da shigewa banÉ—aki, wanka tayi sannan ta fito É—aure da towel a
jikinta. Zama tayi da nufin yin shafa amma ta kasa illa kwakwalwarta dake tariyo mata irin
matsalolin da take dasu a gabanta, riƙe kanta tayi da hannu biyu bayan ta kifashi a jikin mirro
É—in. Saitin zuciyarta ta kuma dafewa da hannu É—aya tanajin yadda take bugawa da sauri, tabbas
tasan watarana matsalolin ƙasar nan zata haddasa mata bugawar zuciya saboda yadda ta ɗau
matsalolin tamkar yadda take É—aukan duk wani abu da ya shafeta ko danginta.
Miƙewa take shirin yi ta nufin saka kaya batare data shafa man ba, turo ƙofar da akayi ne
yasata dakatawa tare da maida kallonta ga Baaba dake shigowa bakinta É—auke da sallama.
Amsa wa tayi tare da faÉ—in.
"Wannan tsohuwa me zakiyi min a É—aki ne haka daya saki haurowa sama, dan wannan zuwan
naki kam akwai abinda ta kawoki tunda nasan ba haurowa sama kikeyi ba."
"Yo idan ba wani abu ba mai zanzo nayi a bene nikam salon watarana na faÉ—i a garin sauka."
Baaba ta faÉ—a tana mai zama a gefen gadon Zarah.
Sai da suka gama barkwancin jika da kaka sannan Baaba tayi gyaran murya tace.
"Zara'u."
ÆŠagowa tayi ta kalleta, gani yanayin fuskarta ne yasa tagane magana ce mai mahimmanci
zasuyi.
"Na'am Baaba."
"Kin sani Zara'u kin kai mun zalin daya kamata ace kema kinyi aure kamar Æ´ar uwarki Jidda,
aure shine darajar duk wata ƴa mace koda kuwa tana da tarin dukiya, kyau, muƙami ko nasaba.
Ba mu da yawan zuri'a Zara'u kune muke fatan ku hayayyafa ku sama mana masu yi mana
addu'a damu daku gaba É—aya koda bama a raye, shekarunki na haihuwa fa yanzu 23 yakamata
ace kinyi aure kin sama kanki daraja musamman a irin yanayin aikin da kikeyi da ake tunanin
duk wata mace da takeyin shi bata da kamun kai. Dan Allah ki siya mana mutunci da kanki kar
a fara maganar a gari ana cewa mun barki sakaka."
Shiru Zarah tayi batare da tayi magana ba, Baaba ce ta kuma cewa.
"Munyi magana da babanku Sulaiman yace nagaya miki ki turo mishi wanda kika tsayar domin
manya su shiga maganar."
"Baaba bawai auren ne banaso ba, akwai burika na da nakeson cikawa wanda nasan va kowani
namiji dazan aura bane zai bani damar cikasu, shiyasa ma bana saka auren cikin lissafina a
yanzu amma idan lokaci yayi zanyi insha Allahu." Ta faÉ—a alamun maganar Baaba bata wani
dame ta ba.
"Toh akwai wani wanda kuka sasanta ne ko kuma kukeson ku sasanta tsakaninku dashi.?"
"Dan Allah Baaba ki barni ni babu wani da nakeso ko muke soyayya, aikina shine a gabana
yanzu." Cewar Zarah da ta miƙe ta nufi gaban durowar kayanta.
"Nima ai ina fatan ki kasance tare da aikinki kodan kawo ƙarshen waɗanda azzaluman
mutanen, amma ki dawo ki zauna muyi magana domin bankai ga faÉ—in sakon da aka aikoni na
isar ba."
"Waye kuma ya aikoki.?"
"Toh da farko dai mai saƙon yace bazai zo da kanshi bane gudun kada kiji nauyin shi kiyi abinda
bashi ranki ke so ba, alfarma ce yake nema a gurin ki nason haÉ—a zuri'a dake, ma'ana dai yana
neman alfarmar ki akan yanason ya haÉ—aki da É—ansa ku raya sunnar manzo S. A. W a
ƙarƙashin inuwa ɗaya. Kuma yana fatan ace wani bai riga shi ba sannan yace a barki kiyi
shawara kafin ki bada amsa."
Wani kallo Zarah ta mata kafin tace.
"Waye da wannan doguwar wasiƙa kuma Baaba."
Miƙewa tayi kana tace.
"Doddon ku mana Sulaimanu yace yana neman alfarmar ki amince da auren É—an sa
Muhammad Jawwad."
Dariya sosai Zarah tayi jin yadda Baaba ta kira Daddy wai Doddo kana ta tsagaita ganin har
Baaba takai kusa da ƙofa, ƙarasa wa tayi inda take sannan tace.
"Ban fahimce ki sosai ba Baaba."
"Ke dai ba kurma bace sannan kuma ke ba mahaukaciya bace bare nace bakya fahimta, abinda
dai kikaji shi nake nufi idan kuma kina tantama ne to ki ɗau waya ki kirashi ya miki ƙarin bayani."
ta faÉ—a tana mai ficewa a É—akin.
Ta daÉ—e tsaye a inda Baaba ta barta tana sakawa da kuncewa akan maganganun Baaban,
lokaci É—aya kuma ta watsar da zance daga tunaninta sannan ta nufi durowar ta É—auko wata
doguwar rigar atamfa super ta zura. Mai kawai ta shafa a leɓanta kana ta zura takalmi ta fice
zuwa falo inda tasan Jidda na jiranta.
A zaune ta same su ita da Saleem sun tasa laptop a gaba da alama abu suke gani a ciki mai
mahimmanci.
Jidda ce ta É—ago ta kalleta tace.
"Madam ASP tun ɗazu muke jiranki anan munkawo ƙara.''
Kyaɓe baki tayi kana ta gaishe da Saleem sannan ta kalli Jidda ta kuma cewa.
"Ace mutum shi kullum cikin zolaya kamar mara damuwa."
"Wace damuwa ne dani nikam, ga mijina a gefe ai sai farin ciki ko da yaushe." Jidda ta fada.
Bata kulata ba sakamakon abinda Saleem yake nuna mata a cikin laptop É—in, shiru sukayi gaba
É—aya suna mai maida hankalinsu kan laptop É—in.
"Na rigada na gama bincike kuma na tabbatar shi ne mai laifin shaidune kawai suka rage mana,
sannan nayi magana da babban likitan asibitin da yarinyar take akan Jidda zataje ta gudanar da
duk wasu bincike da rahoton likita da za'a buƙata a kotu, yanzu binciken ya rage na ɓangarenki
daga nan kuma a shigar da ƙara kotu." Cewar Saleem
"Abun zaizo da sauƙi ai, nima yanzu nake so na fita na gudanar da wasu bincike na saboda
gobe nakeson a shigar da ƙara kotu." Faɗin Zarah.
"Yanzu baiyi yamma ba Zarah.?" Cewar Jidda.
KaÉ—a kai tayi kana tace.
"Inason zuwa ofishin ƴan sanda da suka fara kai ƙara ne domin haɗuwa da Inspector ɗin wajen,
na samu labarin yafi zama a office a irin wannan lokaci."
"Ki tsare shi ya faÉ—a miki gaskiya fa Zarah kuma ya gayamiki nawa a bashi ya danne gaskiya."
Jidda ta faÉ—a cike da takaicin abinda aka aikatawa Fahima.
Dariya Zarah tayi sannan ta maida kallonta ga Saleem tace.
"Gaskiya Sa.Jid ina tunanin kwanan nan zan shigar da matar ka aikin Æ´an sanda ita ma, naga
alama ta fini zaƙewa akan aikin nan."
"A'a ki rufamin asiri, ai aikin Æ´an sanda sai irinkj jajirtattu bana su Jidda bane." FaÉ—in Saleem
cike da zolaya.
Dariya suka yi duka kafin Zarah ta miƙe ta koma ɗakinta inda ta ɗauko mayafi da jaga, sallama
ta musu sa'an nan ta fice domin zuwa inda ta faÉ—a musu.
A hankali take driving har ta iso bakin ofishin, kallon gurin tayi wanda ke tsabtace sosai sai Æ´an
sanda da mutane dake shawagi É—aÉ—É—aya.
Kasancewae gilashin motar mai duhu ne yasa jami'an basu gane wacce ke ciki ba har saida ta
fito, nan tsirarun da suke farfajiyar wajen suka ƙaraso gabanta da hanzari suka sara mata.
Kai kawai ta jinjina sannan ta fara tafiya a hankali inda suke take mata baya har zuwa ofishin
Inspector É—in.
Miƙewa yayi da sauri daga kishingiɗen da yake tare da miƙewa...... *MANAZARTA WRITTERS
ASSOCIATION*í ½í³ší ½í¶Šï¸�
*M*. *W*. *A*
_Putting smile on our readers face_
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
___________________________________
*ASP ZARAH*í ½í±©â€�✈ï¸�
_Daga AlÆ™alamin_âœ�í ¼í¿»
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_í ¼í¼¸í ¼í¼¸
*Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin
sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin.
Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da
sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.* *Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin
al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi
lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.*
*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba.
Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuÉ—i N300 kacal domin karantashi cikin
kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing É—in littafi dan Allah kada ki biya kuÉ—in
banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga
group*.
*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da
izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
í ½í±©â€�✈ï¸�
í ½í±©â€�✈ï¸�
í ½í±©â€�✈ï¸�
í ½í±©â€�✈ï¸�
í ½í±©â€�✈ï¸�
_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_
*Free Page 7*
... "Barka da zuwa ranki ya daÉ—e." ya faÉ—a cike da ladabi.
Zama tayi akan É—aya daga cikin kujerun office É—in sannan ta umarce shi ya zauna shi ma.
"Ina son sanin gaskiyar binciken da kayi game da case É—in fyaÉ—e da aka kawo maka kwanaki
biyar da suka wuce." Zarah ta faÉ—a tana mai zuba mishi idanu.
Daburcewa yayi alamun rashin gaskiya, take kuma zufa ta keto mishi duk da iskar fanka dake
kaÉ—awa a ofishin. Kana yace.
"Dama ranki ya daɗe ƙazafi ne ake yiwa yaron amma bai aikata laifin ba."
Bata ce komai ba ta ciro wata paper daga cikin jakarta ta miƙa mai tana mai cewa.
"Ka cire mana hular mu da belt É—in mu, sauran kayan kuma idan kaje gida ka aiko mana dasu.
Sannan duk wani abu daya kasance mallakin hukumar mu ka dawo mana dashi, karɓi wannan
takardar korarka daga hukumar mu ta Æ´an sanda ne."
Durƙosawa yayi akan gwiwan shi tare da faɗin.
"Ki rufamin asiri ranki ya daÉ—e wallahi zan faÉ—i gaskiya, wannan aikin dashi nake ci da iyali na
da mahaifiyata idan kika rabank dashi bansan ya zanyi ba. Sharrin shaiɗan ne yasa ni karɓa
kuÉ—in toshiyar bakin daya bani."
Shiru tayi batare da tace komai ba, hakan ya bashi damar cigaba da magana inda yace.
"Bayan an kawo case É—in ni da kaina naje har gidansu wanda ake zargin, bayan mun zauna da
mahaifinsa ne yake gayamin cewatabbas É—an sa ya aikata abinda ake zarginsa dashi amma
yana so a kori case É—in inda ya bani kyautar kuÉ—i naira dubu É—ari uku, dalilin dayasa na kori
case ɗin kenan. Dan Allah ranki ya daɗe ayimin afuwa bazan ƙara ba, nayi alƙawari."
Tsaye ta miƙe kana ta mayar da takardar cikin jakarta sannan tace.
"Ka shirya zama shaida a kotu."
"Nagode ranki ya daÉ—e insha Allah zan kasance mai faÉ—ar gaskiya."
Nan ya rakota har bakin motarta yana mai ƙara yimata godiya.
Gida ta wuce kai tsaye tana mai tuƙi cikin nutsuwa.
"Har kin dawo." cewar Jidda dake tsaye a dinning tana shirya kulolin abinci bayan Zarah ta
shigo cikin falon.
"Ehh sannu da aiki fa Madam."
Hararar wasa ta aika mata sannan tace.
"Yauwa ASP."
Tsayawa tayi a bakin bene da zai sadata da É—akinta jin maganar Jidda dake cewa.
"Jirani mu haura tare."