Showing 9001 words to 12000 words out of 36994 words

Chapter 4 - ASP Zahra Complete 1 by Asmau Bint Abubakar

da suke yi. A tsakiyar ɗakin wani haɗaɗɗen gilashi ɗauke da
kyawawan kifaye a saman shi cikin ruwa suna ta shawagi yayinda ƙasan gilashin ke ɗauke da
wasu kyawawan halittun ruwa da bazan iya tantance sunayensu ba.

Maganganun ke tashi a cikin falon saidai banga alamun ta inda nake jiyo maganar ba, muryar
namiji ne ke maganar inda yake cewa.
"A matsayin marainiya mai neman aiki domin tallafawa mahaifiyarki zakije gidan, sannan ki
tabbatar bata cikin gidan yayinda zakije neman aikin saboda kaucewa matsala."
Har zuwa wannan lokaci mai maganar bai bayyana ba illa wata matashiyar yarinya da tafito

daga wata kusurwa a cikin falon, kyakkyawa ce daidai gwargwado sannan fatarta ta kasance
kalar chocolate.
Kallo ɗaya mutum zaiyi mata ta gane tana cikin damuwa sosai sakamakon idanunta da sukayi
jazir saboda kukan da tasha.

Ƙofar dazata sadata da farfajiyar gidan ta buɗe tare da fita a falon, babban fili ne sosai dake
ɗauke da gine gine a wani gefe sannan shukoki kala daban daban da suka ƙawata wajen ciki
harda manyan bishoyin kwakwa wanda su sukafi yawa a wajen. Sai ƙananun shukoki da aka
tsarasu tamkar a ƙasar turai, a ƙasa kuwa wasu kyawawan duwatsu ne masu haske da sheƙi
waɗanda ke ƙara bayyana kyawu da tsarin farfajiyar wannan gida da ya kasance tamkar na
sarauta. Jefi-jefi mutane na shawagi a farfajiyar inda yawancinsu suka kasance mata sa'an
masu ƙananun shekaru.

Tafiya tayi sosai kafin ta iso wani keɓaɓɓen guri da ruwa ke gudana tsakanin waɗansu
matsakaitan duwatsu, wasu mata ne ke zaune su uku suna ɓare kwakwa. Ta farko keyin hanya
a jikin kwakwar, ta biyu kuma ke ƙarasa barewa yayinda ta ukun cikinsu ke ɗauraye jikin
kwakwar bayan a ɓare tare da jerasu cikin wani kyawawan kwando.
Zama matashiyar yarinyar tayi a gefe tare da jingina kanta a jikin wata ƙaramar bishiya.

Gabaɗaya suka maida hankalinsu kanta, kafin wacce ke wanke kwakwar tace.

"Meke faruwa ne Raliya, wani abinda ya miki ne.?"

Ɗago kanta tayi tare da maida kallonta garesu tace.

"Zanso ace wani abu ne ya shiga tsakanina dashi saidai babu abinda yamin illa aiki dazai turani
a gidan da waƴannan lu'u lu'un suke."

"Raliya wani lokacin kina saka mana shakku akanki, dukkan mu anan fata muke mubar cikin
wannan azzalumin gida ke a lokacin ne keki fatan kasancewa da mai gidan ki dinga aikata
haramtaccen abu dashi." Fadin ɗaya daga cikinsu bayan ta maida hankali kan ɓarar kwakwar
da takeyi bayan jin furucin Raliyan.
"A yanzu bana fatan barin wannan wajen saboda waƴanda nayi fatan ƙara kasance dasu basa
duniyar zan fiso na cigaba da kasance anan saboda ko bana nan ɗin zaiyi wuya na tserewa
*ALPHA* tunda na rigada nasan wasu sirrika nashi, bazai taɓa barina a raye ba tunani zaiyi
asirin shi zan tona." Faɗin Raliya
Ɗayar da tun fara maganar bata tofa ba tace.

"Ki dinga yiwa kanki kyakkyawan fata Raliya idan ba haka ba zuciyarki zata iya rikeɗewa ta
koma irin tasa na marasa imani."

"Hauwa kenan ai yanzu haka banajin akwai abinda zuciya da gangar jikina zasu kasayi indai
umarnin Alpha ne. Ku da iyayenku kawai ya rabaku ya kawoku nan amma nifa? Da hannayena
guda biyu yasa na kashe iyayena, zuciyata ta gama bushewa tun a waccan ranar. Zan iya raba
kowaye da jindaɗin sa kamar yadda akasa na raba kaina da nawa jindaɗin." Ta faɗa tana mai
maida kanta ga kishingiɗar da tayi a jikin bishiyar.

Babu wanda ya kuma tankawa a cikinsu domin dai sun saba da jin kwatankwacin wannan furuci
a bakin Raliyan tin bayan da tasamu kusanci da Alpha lokacin da tayi nasarar ganin yatsun
hannunshi, mutum ne shi mai matuƙar taka tsantsan kasancewar shi wanda jami'ai ke nema ido
rufe shiyasa baya taɓa bada damar a ga wani sashi na jikinshi koda kuwa farce ne. Idan kuwa
kayi nasarar ganin wani abu nashi to daga wannan lokaci zaka zama makusancin shi bayan an
shiga dakai wani ɗaki mai taken _Kusanci da Alpha_, wata ɗaya cur ake kwashewa ga duk
wanda ya samu nasarar shiga wannan ɗakin saidai mutum yakan fito ne a galabaice. Idan mai
tsawon kwana ne zaiyi dogowar jinya, idan yazo da ƙarar kwana kuma saidai a wuce da mutum
kabari. Babu wanda yasan abinda akeyiwa mutum a cikin wannan ɗakin domin hatta Raliya da
aka shigar da ita tace bazata iya tuna komai da ya faru ba.
Ko bayan mutum ya samu kusanci dashi bazai ƙara samun damar ganin wani sashi na jikinshi
ba saidai zai kasance yana kasa saɓa umarnin Alpha ɗin koda kuwa umartarka yayi da kashe
kanka.

*Abuja*

Cikin kwanciyar hankali da tsari ake gudanar da taron na ƙarawa juna sani a harkar aiki inda
Zarah tayi zarra kwarai wajen baiyana dabaru da koma salon aiki da kowani jami'i ya kamata
yayi amfani dasu, a cikin kwana huɗun da tayi a gari Abuja an samo nasarar zaƙolo manyan
masu laifi da aka daɗe ana nema, hakan yasa aka shirya karramata a ranar ƙarshe da za'a
kammala taron a matsayinta na jajirtacciyar ƴar Sanda da hukuma ke son irinta.

Kasancewarta mace kuma kyakkyawa yasa manyan masu muƙami a rundunar Ƴan Sanda ke
ƙoƙarin janta a jiki amma taƙi bada damar hakan, domin hatta ɗakin da aka kama mata a hotel
ɗin da aka sauki baƙi irinta wanda sukazo daga wani gari taƙi karɓa. Gidan wata abokiyar
karatunta na sakandire dake zaune da mijinta a cikin garin Abujan nan ta sauka.

*Bauchi*

A yau ne akayi addu'ar kwana bakwai na rayukan da aka rasa a farfajiyar gidan marigayi Alhaji
Abdul_Jalal, inda akayi saukar alqur'ani mai girma tare da yiwa mamatan addu'o'i.

Ƙarfe biyu jirginsu Ammi ya ɗaga zuwa Cairo ita da maigidanta da kuma Rahma da suka wuce
da ita domin cigaba da duba lafiyar saboda har zuwa wannan lokacin bata magana tun bayan
farfaɗowarta.

Daddy da Momi ma bayan sallar la'asar suka ɗauki hanyar tafiya Bauchi. Sai gidan ya ragw
daga Baaba sai Muhammad Jawwad da wata tsohuwa da Daddy ya samu domin tayasu zama
sannan jami'an tsaron da Mustapha ys ɗauki nauyin ajiye musu guda biyar.

Shima Muhammad Jawwad a washegarin ranar zai wuce Abuja ya ziyarci wani abokinshi dake
aiki acan, sa'an nan daga can ya wuce ƙasar England domin haɗo takardunshi tare da takardar
shaidar aiki da yakeyi acan saboda samun sauƙin cigaba da aikinshi a Nigeria.

Washegarin kuwa shima ya wuce garin Abuja, kasancewar su Daddy basuyi mishi batun Zarah
ba shiyasa baisan tana garin ba.
Ƙarfe 12:30nr ya isa garin Abujan inda abokin nashi yazo ta taryeshi a airport ɗin, daga nan kai
tsaye gidanshi suka nufa.
Bayan yaci abinci ya huta ne ya buƙaci su fita domin zaga gari.


Ta fito da nufin tafiya gurin da suke ƙaddamar da taron kiran wata abokiyar aikinta Toyin wacce
suka haɗu wajen taron ya shigo wayarta inda ta buƙaci ta biyo ta hotel ɗin da take domin su
wuce tare.
Agogon hannunta ta kalla taga akwai sauran mintuna 45 kafin a fara taron hakan yasa ta yanke
shawarar tsayawa a wani resturant da tagani domin siyan burger da ta tashi da marmarin ci a
yau.

Suna ƙoƙarin fitowa daga *Koise Delicies* ita kuma tana ƙoƙarin shiga waya kare a kunnenta,
karo sukayi da Abdallah wanda ke gaba yayinda Muhammad Jawwad ke bayan shi.

"Sannu dan Allah." shine abinda ta furta sannan ta cigaba da tafiya tana mai magana a waya
inda takw cewa.

"Jirani a reception na hotel ɗin bansan ɗakin ba."

Dogon tsaki Muhammad Jawwad ya saki bayan sun shiga mota kafin yace.

"Suna fakewa da aikin ƴan sanda suna abinda suka ga dama, yanzu menene abin burgewa ga
mace a aikin ƴan sanda kuma musulma.?"

Dariya Abdallah yayi sannan yace.

"Nikam naga abin burgewa sosai, ka dubi yadda tayi shiga cikin kamala ba kamar wasu matan
dake irin aikinta ba, sannan maganar hotel da kaji tanayi ƙila wani aikim zai kaita can kasan su
aikinsu babu inda bayakai mutum."

Baki kawai ya taɓe batare da ya kuma magana ba....

*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Daga Alƙalamin_✍🏻
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_🌸🌸

*Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin
sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin.
Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da
sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.* *Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin
al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi
lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.*

*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba.
Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin
kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin
banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga
group*.

*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da
izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
👩‍✈️
👩‍


Free Page

Alhamdulillahi taro yayi kyau an watse lafiya bayan kyaututtuka da aka rarrabawa jami'ai tare da
karrama wasu daga ciki inda Zarah ta kasance cikin waɗanda aka karrama.

Saida ta ƙara kwana biyu cikin garin Abuja sakamakon jirginsu Jiddah dazai sauka ta garin
bayan ya taso daga ƙasar Malasia.

*_Jiddah ƙawace ga Zarah tun zamanin ƙuruciya, tare sukayi makarantar firamari da sakandire
inda bayan sun kammala Jidda ta wuce jami'a yayinda itakuma Zarah ta wuce makarantar bada
horo na ƴan sanda. Duk wasu sirrika na Zarah Jidda tasansu kamar yadda yake a ɓangaren

Zarah itama._
_A shekarar data gabata ne Jiddah tayi aure inda mijin data aura ya kasance Barrister wanda
yake aiki a ƙasar Malasia wato Bar. Saleem, dakyar aka rarrashi Jiddah tabi Saleem ƙasar a
waccan lokacin bayan tayi iƙirarin ita bazata iya tafiya wata ƙasa batare da Zarah ba, shima dai
Saleem ɗin bawai yana ƙaunar aiki a wata ƙasa bane illa dai kawai yanason ƙarasa yarjejeniyar
aiki da sukayi da ƙasar. Tun bayan tafiyarsu kuma basuzo gida ba sai wannan karon da suka
tattaro gabaɗaya suka dawo ƙasarsu ta gado._"

Sallama tayi da ƙawarta ta tare da yimata godiya sannan ta wuce filin jirgi inda tanan zasubi
wani jirgin zuwa Bauchi.

Tana tsaye jirgin ya sauko daga sararin samaniya, bayan wadu mintuna kuma matafiya suka
fara fitowa ɗaya bayan ɗaya, sam bata kula ba sai ji tayi an rungumeta gam tamkar za'a tsaga
ta.

"Nayi kewarki sosai sahibaty.''
Jiddah wacce ita ke da alhakin rungumar ta faɗa cike da farin ciki, kana ta saketa tare da
ƙamewa ta sara mata kana tace.

"Na gaida ASP da kanta."

Murmushi kawai tayi tare da maida hankalinta ga Saleem dake cewa.

"Zan shigar dake ƙara fa Zarah, ganinki kawai yasa ta mance dani ma gabaɗaya."

Dariya sukayi duka sannan suka nufi gurin da aka tana da domin zaman ma tafiya.
Mintuna kaɗan jirgin dazai sadasu da garin Bauchi ya keta hazo.

*England*

Tsaki yaja a karo na ba adadi cike da takaici, tashinsa kenan daga bacci sannan kamar koda
yaushe yau ma mafarkinta ya ƙarayi wanda ya haddasa wajabcin wanka ya hau kanshi. Ya rasa
dalilin dayasa tun ranar daya ganta kullum dare sai yayi mafarkin yana wani abu da ita wanda
hakan ke silar dole idan ya tashi sai yayi wankan tsarki. Wannan shine dalilin dayasa yake jin wata muguwar tsanarta a cikin ranshi.

Miƙewa yayi tare da shiga banɗaki, bai jima sosai ba ya fito cikin shirinsa na farar riga da baƙin
wando.
Wayoyinshi ya ɗauka da niyar ficewa a ɗakin, saidai missed calls din Ammi daya gani a cikin
wayar ne yasa shi dakatawa tare da zama a gefen gadonshi yana ƙoƙarin kiranta.

Bugu biyu ta ɗauka tana mai sallama, amsawa yayi tare da gaisheta.

"Har yanzu banga wani alert ba fa Jawwad." Ammi ta faɗa.

Cikin son gane mai take nufi yace.

"Ammi wani irin alert kuma na mene ne."

"Zan saɓa maka fa, ka maidani sa'ar wasan kace. Ko ba dakai mukayi magana zaka turo kuɗi a
fara haɗa lefen ba.?" Ta ƙarasa magana cikin hassala.

Dafe kai yayi saboda tunawa da abinda take nufi, gaba ɗaya ya manta da batun aurenshi da
Daddy yace zai haɗa da ƴar marigayi wacce bai ma santa a fuska. Shi a tunanin shi girman kai
ne ya hanata zuwa ta gaidashi ko tabari su haɗu lokacin da yaje Nigeria, shiyasa yaji baya
ƙaunar yin auren duk da matsalar da yake fama da ita na ƙarfin sha'awa.
"Ayi haƙuri Ammi zan turo insha Allah." Ya faɗa cike da biyayya.

"Toh ina jira kada ka sake na ƙara kiranka akan wannan batun idan ba haka ba kuma ranka ɓaci
zaiyi." Ta faɗa gami da kashe wayar.

Dafe kai yayi cikin damuwa, shifa yana da ra'ayin irin matar da yakeson aura, amma gashi
yanzu Daddy ya ruguza mai duk wasu tsarin shi.

Miƙewa yayi jiki babu laka ya fita domin yana a farkon sabuwar wata da za'a yakeson komawa
gida gaba ɗaya, shi da ƙasar turawa kuma sai ziyara ko hutu ko kuma wani abu mai
mahimmanci.


.......................

A bakin gate su Zarah suka tarar da wasu mutane biyu da alama dai miji da mata ne sannan
marasa ƙarfi.
Ganin motar ne yasa su miƙewa daga durƙusun da suke a gefen gidan.

Tsayar da motar Saleem yayi kamar yadda Zarah ta buƙata, buɗe ƙofar baya ta fito ta nufi inda
suke tsaye.

Da sassafar matar ta ƙaraso tare da durƙusawa akan gwiwoyinta tace.

"Ranki ya daɗe ki taimake mu, kwana uku kenan muna zuwa gidan nan amma anƙi bamu
damar shiga. Hatta ofishinku ma an hanamu ganinki dan Allah ranki ya daɗe ki sauraremu."

Ɗagota Zarah tayi kana tace.

"Kada ki bani kunya ta hanyar durƙusawa a gabana domin neman wata alfarma, hakan zai sa
nayi tunanin ko baki ɗaukeni a matsayin ƴa ba. Ku tashi mu shiga daga ciki muyi magana a
nutse."

Ta ƙaramar ƙofa suka shige bayan su Saleem sun shige da motar tuni.

Falon saukar baƙi ta kaisu kana taje kicin da kanta ta kawo musu ruwa da lemo.

"Bismillah ga ruwa ku sha sai muyi maganar abinda ke tafe daku."
Fadin Zarah bayan ta aje tiren dake dauke da gorar ruwa da lemu a kan ƙaramin teburin dake
tsakiyar falon.

"Ranki ya daɗe ba zamu iya shan komai ba ahalin da muke ciki." Faɗin mijin

"Meke faruwa ne.?" Zarah ta faɗa tana mai zama a kujerar dake fuskantarsu.

"Ranki ya daɗe ƴar mu akayi wa fyaɗe, sannan mun tabbatar da wanda ya aikata laifin. Yaron
wani ɗan majalisa ne dake maƙobtaka damu amma bayan mun sami mahaifin yaron da batun
ya ƙaryata lamarin tare da faɗin zaiyi shari'a damu duk sanda muka nemi ɓata masa suna ko
ɗan shi. Yanzu haka yarinyar na gadon asibiti ana neman kuɗin aiki sannan bamu da halin
biya." Ya faɗa yana mai fashewa da kuka inda matar ke taya shi.

Sosai zuciyarta ta tsinke da lamarin musamman da taga manyan mutanen da suka haifeta a
shekaru suna zubar da hawaye.

"Amma meyasa baku kai ƙara ofishin ƴan sanda dake kusa ba.?" Zarah ta tambaya a raunane.

"Tun faruwa lamarin muka kai ƙara ofishin ƴan sanda dake kusa damu, saidai bayan sun gana
da mahaifin yaron suka fatattake mu tare da faɗin sharri mukeson ƙullawa ɗan sa. Wannan
dalilin yasa muka garzaya ofishinki bayan wani maƙocin ya bamu shawarar yin hakan, tun
kwanaki uku da suka wuce muke zirya a ofishin an hana mu shiga shine mai gadin wajen ya
bamu adireshin ki." Matar ke wannan bayanin.

Kai kawai ta jinjina tare faɗin.

"Ina zuwa." kana ta miƙe ta fita.


Bata daɗe ba ta shigo tare da Saleem da Jidda, zama sukayi tare da gaisa.

"Wannan shine Bar. Saleem tare da matarsa Dr. Jidda, za muje asibitin tare domin ganin halin
da yarinyar take ciki kafin shigar da ƙara a kotu." faɗin Zarah bayan tayi nuni da kujerar da
Saleem ke zaune shida Jidda.

Godiya su kayi sosai kana suka miƙe gaba ɗaya suka nufi waje.

Motar Zarah suka shiga duka inda Saleem ke tuƙin.

Mintuna kaɗan suka iso asibitin, kasancewar Zarah ƴar sanda shiyasa basu wani sha wuya ba
wajen isa ɗakin da yarinyar take.

Ita kaɗai ke kwance a gadon jikinta rufe da zani yayinda acan kusurwar dakin wata ke zaune
kan dadduma da alama dai itace mai jinyar.

Bayan sun mata ya jiki ne suka zazzauna inda Saleem ya ciro ƙaramar sound recorder tare da
jan kujera ya ƙarasa bakin gadon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0