Showing 33001 words to 36000 words out of 36994 words
Chapter 12 - ASP Zahra Complete 1 by Asmau Bint Abubakar
ciki da mamakine suka turnuƙeshi lokaci guda.
"Ni kika É—aga hannu kika mara.?" Ya faÉ—a yana huci.
"Na mare ka kuma in gab da yi maka abinda yafi mari zafi matuƙar zaka taɓa mutuncin iyayena,
banza kaw..."
Bata ƙarasa ba itama ya wanke mata fuskarta da mari kafin ta kuma ankara ya ƙara wanke
mata ɗaya ɓarin da mari mai zafi, saidai ko kaɗan Zarah bataji zafin shi a fuska ba saboda zafin
zagin iyayenta da yayi yafi komai ƙuna a gareta.
"Kina karuwa har kin isa ki ɗaga wannan hannun naki mai cike da ƙazantar zina ki mare ni,
wallahi baki isa ba kuma ƙunci yanzu kika fara shiga cikinsa nonsense."
A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shigo duk da halin da yake cike bai hanashi yin sallama
ba, kai tsaye inda take a durƙushe ya nufa batare da yayi magana ba, hannu biyu yasa ya miƙar
ta ita tsaye tare da riƙe hannuwanta suka nufi ƙofar fita daga falon, ɗan tsayawa yayi sannan
yace "Dama sallama nazo yi muku, idan kun tafi Allah ya kiyaye hanya."
Yana gama faÉ—in haka ya ja hannunta suka fice a falon, daga Abdallah har M.J babu wanda ya
tanka, shikam Abdallah baƙin ciki yakeji na abinda abokin nasa ya aikata tare da dana sanin
wannan rakiya da yayi, a ɓangaren M.J kuwa babu wani abu da yakeji a ranshi face ɓacin ran
da Zarah ta sakamai ta hanyar marinshi. Miƙewa Abdallah yayi tare da ɗaukar kayan da Zarah ta ajiye mai ya fita batare daya kula M.J
É—in ba, bayanshi ya bi ganin bai kulashi ba suka fita tare, sun rigada sun sanar da direban dazai
kaisu airport ya shirya dan haka bayan motar suka shiga yajasu zuwa airport É—in.
Ko da suka isa basu yima juna magana ba har zuwa lokacin da suka shiga jirgi ya keta hazo
dasu.
Kuka take me matuƙar ban tausayi da sosa ran duk wani mai sauraro har suka isa ɗakinta, kan
gadon É—akin ta faÉ—a tana cigaba dayin kukan, shikuwa Sadiq nufar inda hoton mahaifansu dake
gefe yayi ya ɗauka tare da rungume hoton a ƙirjinshi, sai a lokacin kukan daya danne ya
hanashi fitowa yayi nasarar bayyana kanshi batare dayayi ƙoƙarin dakatarwa ba shima ya fara
kukan yana faÉ—in
"Meyasa zai rabamu daku, me muka mishi zai rabamu daku ya barmu cikin gararin rayuwa da
rashin gata, Abba! Mami kuna ganin yadda rayuwarmu ta tagayyara da bakwa tare damu, Abba
meyasa bakace mutuwar ta ɗaukeni ba ta barka ka kula da ƙannena, Abba inajin kamar na
gaza riƙe amanar ƴan'uwana da kullum kake daɗa jaddadamin, Mami kina gani koh? Ki tayani
roƙon Allah yayi gaggawar ɗaukan raina bazan iya jure ganin ƴan'uwa cikin halin baƙin ciki da
ƙunci ba alhalin ina raye. Kaicona dana kasa riƙe amanarka Abbana yau ga ƴar'uwata tana
zubda hawayen baƙin ciki dana maraici sannan ina kusa na kasa aikata komai, Ya Allah kayi
gaggawar É—aukan ra...."
Hannu aka saka tare da rufe mishi bakinshi, bashi da ƙarfin dazai iya hana hakan shiyasa ya
cigaba da rera kukan shima mai ban tausayi.
Zama Baaba tayi a gefen gadon ta É—ora hannun hagunta a bayan Zarah tana bubbugawa
alamun rarrashi hannunta na dama kuma na kan Sadiq tana shafawa a hankali.
Sun É—auki tsawon mintuna a haka batare da sun daina kukan ba, ganin haka yasa Baaba tace.
"Idan rai ya ɓaci ambaton Allah akeyi ba kuka ba."
"Baaba na gaji bazan iya jure wannan baƙin cikin ba, na gaji ta dalilinsu fa muka shiga wannan
halin amma abinda zasu saka mana dashi kenan, bazan iya jure wannan cin mutuncin da
akeyiwa iyayena ba zan maida musu da Diamonds É—insu ko zamu huta da wannan takaicin."
Zarah ta faɗa cikin fitar hayyaci, da sauri ta miƙe ta nufi gaban dressing mirro ɗinta tana watsi
da duk wasu abubuwa dake kai batare da ta kula da irin ɓarnar da takeyi ba. Sai da zuba komai
na kan wajan a ƙasa kafin da fara ƙoƙari tura dressing mirro ɗin gefe.
"Me kike ƙoƙarin aikata ne haka Fatimah?" Baaba ta faɗa a fusace.
"Bazan iya ba Baaba zan basu Diamonds ɗinsu kawai na huta." ta ƙarasa fada lokacin da tayi
nasarar tura dressing mirror É—in gefe, tsugunnawa tayi a gaban wani tiles a wajen, hannu takai
da nufin taɓawa sai dai kamar a danna mata remote ta dakata saboda jin kamar anayi mata
raÉ—a a kunne. "Raliya!!! Batula Raliya na waje." haka taji a kunnenta tamkar wani ke magana, da hanzari da
nufi ƙofar fita bata ko ganin gabanta saboda tsananin tashin hankali, da mugun ƙarfi ta buɗe
ƙofar.
Rasss! Rasss!! Rassss!!! Haka ƙirjin Raliya ya bada sauti wacce ke tsaye a jikin ƙofar riƙe da
sound recorder da kuma ƙaramar camera tana ɗauka duk wani abu dake faruwa ta ɗan ramin
ƙofar data buɗe kaɗan ganin mutanen ɗakin basa cikin hayyacinsu bare su lura da ita, tsananin
tashin hankali da firgici ne ya ziyarceta lokaci guda ta fara É—ika saboda zufar da tayiwa jikinta
ƙawanya lokaci ƙanƙani..
Wata irin shaƙa Zarah takai mata........��
í ½í¸±í ½í¸±í ½í¸±í ½í¸±í ½í¸±í ½í¸±í ½í¸±
*YANZU NE FA ZA'A FARA ASALIN LABARIN _ASP ZARAH_í ½í±©â€�✈ï¸� MATAR MUHAMMAD
JAWWAD KAWAR JIDDAH MATAR SALEEM. LOKACIN DA ZAMUGA �OYAYYEN SIRRIN
DAKE TATTARE DA JIDDAH YAYI FAí ¾í´”*
*SHIN ZARAH ZATA MAIDAWA DADDY DIAMONDS ÆŠINSA KO KUWA ZATA BARSHI A
WAJENTA HAR SAI ZUWA LOKACIN DA ZATA KAUDA ALPHA.???*
*ME ZAI FARU TSAKANIN ZARAH DA RALIYA NE A WANNAN FITO NA FITO DA
SUKAYI.???*
*WANI MATAKI DADDY ZAIYI NE IDAN YAJI LABARIN ABINDA ÆŠANSHI YAKE AIKATAWA GA
YARINYAR DATA SADAUKAR DA KOMAI NATA DOMIN KARE DUKIYARSA WACCE TA
DALILIN HAKANE TA RASA IYAYANTA SANNAN ƳAR'UWARTA TA FICE A
HAYYACINTA.???*
*AURAN MUHAMMAD JAWWAD DA FATIMAH ZARAH NA YIWUWA KUWA.???*
*SHIN ALPHA YANA SAMUN NASARAR MALLAKAR WAÆŠANNAN LU'U LU'U MASU
MATUƘAR DARAJA.???*
*YA BATUN RAHAMA A CAIRO. INA MUSTAPHA KUMA???.*
*SHIN TANA SAMUN NASARAR KAMA ALPHA KAMAR YADDA TASHA ALWASHI.???*
*MEZAI FARU NE IDAN M.J YA GANE IRIN SADAUKARWAR DA ZARAH TAYI AKAN
DUKIYAR MAHAIFINSHI.???*
*INA BATUN ALMAJIRAR DA ZARAH TA TA�A HAƊUWA DA ITA NE.???*
_DUK AMSOSHIN TAMBAYOYIN DAMA WASU NA TARE DA JASMINEí ¼í¼¸í ¼í¼¸ A CIKIN
LITTAFIN ASP ZARAHí ½í±©â€�✈ï¸�, YANZU AKA FARA_.
*BY*
*JASMINE*í ¼í¼¸í ¼í¼¸
*ASP ZARAH*
Wata irin shaƙa Zarah takai mata saidai cikin zafin nama ta kauce tare da hankaɗa Zarah ta faɗi
ƙasa sannan ta nufi hanyar matattakalar da zai sadata ƙasa, ganinta tayi a gabanta tamkar
wacce aka jefo kafin ta ankare taji saukar duka ta ko ina a jikinta ta yadda babu ta inda zata iya
kare kanta, dukanta takeyi sosai tamkar wacce ta kama ɓarawo a bayan kanta.
"Baki da hankali ne Zara'u me tayi miki kike dukanta? Ki sake ta tun kafin raina ya ɓaci." Baaba
kenan ke faÉ—i bayan ta fito taga abinda ke faruwa, shikuwa Sadiq yana gefe a tsaye bai tanka
ba domin yasan hakan nan Zarah baza ta yiwa Raliya wannan dukan ba idan ba wani
mumminan laifi ta kamata dashi ba. Saida taga ta daina motsi kafin ta sassauta duk kuwa da hargowar da Baaba keyi mata akan ta
rabu da ita, hannu ta saka ta fincike hijabin dake jikin Raliyan saidai ga mamakinta ba hijabi
É—aya bane a jikinta, saida ta cire hijabai uku kafin tayi tozali da jikinta kai tsaye hannu ta saka ta
juyata daga kwancen da take kamar gawa ta duba gefen wuyanta, kamar yadda tayi tsammani
kuwa zanen tatto ne a gefen wuyan nata, bishiyar kwakwa ne da sunan Alpha da aka ƙayata ta
hanyar zanen, É—aki ta shiga ta É—auko wayarta ta É—auki hoton gurin kana ta danna kiran waya
tana karawa a kunnenta.
"Kuzo da mota biyu gidan mu." shine kawai abinda ta faÉ—a kafin ta juya ga Baaba wacce ke
sharar kwalla tana sambatu.
Hannunta ta riƙo suka koma cikin ɗakin ta zaunar da ita a gefen gadon itama ta zauna tare da
karɓar ruwan da Yayanta ke miƙa mata tasha sannan ta maida kofin yaƙara tsiyayawa ta miƙa
ma Baaba itama.
"Shikenan kin ja mana zagi a gari Zara'u za'ace mun kasa riƙe waɗanda ke ƙarƙashin mu."
"Baaba tun ranar da kika gayamin kin É—auki yarinyar nan aiki na nunq miki banso ba, haka ne."
"Eh sai me dan bakiso ba ai ni inaso, shiyasa kike neman ki mata lahani tana marainiya."
"Wai ke waya gaya miki wannan yarinyar marainiya ce Baaba? Spy ce fa aka turo mana a
matsayin mai aiki."
"Mene ne haka.?"
"Ƴar leƙen asiri mana, Alpha ne fa ya turota.?
Wani zabura duka su biyun sukayi a tare suka kuma haÉ—a baki wajen faÉ—in
"Alpha.???"
"Kwarai kuwa."
"Kin tabbata little.?"
"Sosai na daÉ—e da tabbatar da haka banaso na kamata a bisa zargi ne shiyasa amma da ta
daÉ—e da zama a kurkuku, zo muje É—akinta ka gani."
Miƙewa sukayi duka suka nufi ɗakin Raliyan, sosai Baaba tasha mamakin abubuwan da Zarah
ta nuna musu a É—akin wanda babu ko tantama duk wanda yaga wannan yasan akwai abinda
ake ƙullawa.
"Tabbas ɗan adam na da wuyar fahimta, ki duba kiga yadda yarinyar nan ta ɓadda kama ta zo
min a maraice tana roƙon abata aiki ashe cutar mu tazo tayi, Allah ya toni asirinta. Allah sarki
Zara'u shiyasa sam baki yadda ko gurin zama ku haÉ—a ashe kinsan abinda kika gani, ni kuma
duk da haka ban fahimci komai ba."
"Gaba saiki kiyaye kisan waɗanda zaki dinga zaɓa kuyi mu'amala tare..." Ringing ɗin wayarta
ne ya hanata kai aya a zancen nata.
"Ehh ku shigo falo" haka kawai ta faÉ—a ta kashe wayar.
"Jami'ai sun iso muje."
"Ina za'a kaita ne little."
"Za'a cigaba da tsaronta har zuwa lokacin da za'a kama maigidan nasu a yanke musu hukunci."
"Kina ganin hakan bazai janyo wata matsalar ba."
"Babu abinda zai faru Yayana da izinin Allah."
"Toh Allah yasa."
"Amin " suka haÉ—a baki wajen faÉ—a ita da Baaba, sannan suka bar É—akin zuwa falo inda jami'an
suke.
"Ku tafi da ita Nura a fara kaita asibiti a duba lafiyarta daganan sai a wuce da ita station a rufe
ta, ban yarda ko waye yazo a fito da ita ba, sannan duk wanda yazo belinta indai ba jami'i bane
to a haÉ—a dashi a rufe, kuna jin abinda na faÉ—a koh."
"Zamu kiyaye ranki ya daÉ—e."
"Joy da Halima ku É—auketa ku kaita mota sai ku wuce."
Sara mata sukayi duka sannan sukayi kamar yadda tace suka fita a falon.
"Allah ya kyauta ya daÉ—a karemu daga kaidin wannan mutumin."
"Amin thumma Amin.'' cewarsu duka.
"Yauwa Baaba sai batun auren Little da M.J gaskiya za'a janye ba za'ayi wannan auren ba."
"Akan wani dalili za'a janye batun auren? Toh indai akan abinda Muhammadu yakeyi ne wannan
auran babu fashi sai anyi shi, watarana ko kuÉ—i aka bashi yayi wannan abun bazai iya ba."
"Amma fa kinajin irin alwashin da yake É—auka akanta muddin ta amince akayi auran."
"Naji tun ba yau ba nasan duk abubuwan da yake faÉ—a game da ita wanda nasan ba haka bane
amma inaso mu tura mishi aniyarsa ayi auran. Duk abubuwan da suke faruwa fa bai sani ba na
tabbata ranar dazai san wani abu a game da abinda takeyi zaiyi nadamar komai daya aikata a
gare ta, dan haka aure nan da sati biyu babu fashi."
"Shikenan Allah yasa haka shine mafi alkhari."
"Amin ai addu'ar daya kamata kayi kenan Allah ya zaɓa mata abinda yake shine alkhairi a
wannan auren."
"Uhmm! Little me kuka shirya game da events ne."
"Babu abinda zamuyi Yaya."
"Bai kamata ba gaskiya, ko sports daya ai zamuyi."
"Hakane fa Bro kuma kamar kasan mun daÉ—e bama yin sport wallahi."
"Eh nasan Sis Rahama zataso hakan sosai."
Murmushi kawai tayi mai kama dana ciwo domin duk sanda za'ayi maganar sports sai ta tuna
mahaifanta.
"Wani wasa kika zaɓa."
"Dear inajin volley ball zaifi tunda kaga harda mata a ciki."
"Hakane amma gidan Daddy akwai pitch ne."
"Ehh mana ai saboda mu yasa akayi sports garden tun waccen lokacin idan mukaje muna
playing dasu brother Adil da Nusaiba..." sai kuma hawaye shar ya biyo bayan maganarta ta.
"Bana sonki da yawan kukan nan fa little, addu'a kawai zamu cigaba dayi musu, ko kinaso ki
haifi yara a rasa gane wacece uwar idan kuna kuka dukanku."
Hannayenta ta saka ta rufe fuska tana faÉ—in.
"Kai Yaya."
"Ehh mana, tashi muje kitchen mu haÉ—a dinner kafin Daddy ya dawo."
"Ohh kasan na manta da Daddy na gidan nan, ina yaje ne."
"Ya fita yun É—azu zai haÉ—u da wani abokin kasuwancinsa."
"Nagode wa Allah da bayanan wannan abu ya faru."
"Muje kitchen É—in."
"Yaya akwai abinci fa."
"Ni dai muje muyi ko ma mene ne, da kwaɗayi na dawo ƙasar."
Hanyar kitchen ɗin suka nufa suna hira kamar wasu ƙawaye.
''Allah ya shirya ku."
"Amin" Zarah ta faɗa daga kitchen ɗin...��
*Ayimin uzuri da wannan pls banjin daÉ—i ne, ayi haÆ™uri.*í ½í±�í ½í±�í ½í±�í ½í±�
*Jasmine*í ¼í¼¸í ¼í¼¸
*ASP ZARAH*
_Duk abinda aka sama lokaci..._
Kamar yadda yau ta kasance saura kwanaki biyu kacal a É—aura auran Zarah da angonta M.J,
baƙi na nesa da na kusa duk sun hallara, inda Ammi da Momi suka dage wajen gyara Zarah
sosai tamkar wacce zata auri shugaban ƙasa. Babu wasu events da akayi sai sports day da
sukayi sai kuma walima da za'ayi bayan ɗaura aure. Suna zaune su uku a wani keɓaɓɓen guri a cikin garden ɗin gidan Daddy, Sadiq ne a tsakiya sai
Zarah da Rahama da suke a gefensa kowaccensu ta É—aura kanta a kafaÉ—arsa, kallo É—aya
zakayi musu duka ka tabbatar da cewa suna cikin damuwa sosai, idan ko mutum yasa da
mutuwar mahaifansu toh tabbas za'ace maraici ne ke damunsu. Sadiq ne yayi gyaran murya
yace.
"Sis kinji abinda ke shirin faruwa da little fa kuma Baaba ta hana a dakatar da bikin nan, ni
banaso taje tana shiga damuwa ne kinsanta da rauni."
Rahama wacce tun bayan abinda ya faru ta zama miskila ta wucin gadi, shiru tayi na mintoci
kafin tace.
"Dakatar da auren bashi ne mafita ba Yaya, mu bari muga idan anyi auren yana cutar da ita sai
mu nemi mafita."
"Bakomai amma indai ya cutar da ita sai na bi mata haƙƙinta ko da kuwa igiyar zumuncin dake
tsakanin mu zata tsinke."
"Haka ma bazata faru ba."
"Toh Allah yasa, little tashi kije Daddy na nemanki tun É—azu mantawa nayi ban gaya miki ba."
Cikin sanyin jiki Zarah ta miƙe tana faɗin
"Ku jira ni fa yanzu zan dawo."
"Mu ma yanzu zamu shigo gidan."
"Toh sai kunzo".
Kai tsaye falon Daddy ta nufa inda yake zaune shi kaÉ—ai da alama ita yake jira, gaishe shi tayi
sannan ta zauna a gefe, bansan me suka tattauna ba sai dai daga ƙarshe muryar Daddyn naji
yana ta godiya tare da samata albarka.
"Daddy ka daina bani kunya ta hanyar gode min, idan kana hakan sai naga kamar baka É—auke
ni a matsayin Æ´arka bane."
"Har abada zaki cigaba da kasancewa Æ´ata, amma kinsani cewa godiya wajibi ne ga wanda aka
kyautatawa, Allah ya miki albarka ya baki zaman lafiya a É—akin aurenki."
"Amin Daddy."
"Babu wani abu da kike buƙata ko."
"Babu komai."
"Tashi ki kuma cikin Æ´an uwa da iyayenki."
Cikin rashin kuzari ta miƙe tare da ficewa a falon, wata hanya ƙarama tabi sai gata ta ɓullo a
wani babban falo wanda aka wadata da kayan alatu na more rayuwa tamkar É—akin shugaban
ƙasa, Jidda kaɗai ta gani a falon tana duba wasu takardu, zama tayi a gefenta tace.
"Ya naga gidan yayi shiru haka."
"Ehh duk suna backyard wajen gyaran naman nan, saboda Momi tace kar a barwa Æ´an aiki aikin
zasu lalata shi."
"Ok nima daga falon Daddy nake."
Kallonta Jidda tayi na wasu sakanni kafin tace
"Ina fata komai ya zama steady."
"Ehh babu wata matsala yanzu."
"Wa kun haÉ—u da angon kuwa.?"
"Uhmm tun ranar daya bar Bauchi ba mu ƙara haɗuwa ba, Abdallah ne ke jigilar zuwa da kuma
kira."
"Sai kinyi haƙuri da lamarin angon nan naki idan ba haka ba zai ɓata mana shirin mu."
"Dole zan kula domin nima jikina yana bani cewa na kusa kama Alpha da hannuna."
"Nima inajin hakan, ya batun Raliya kuwa."
"Na saka an ɓoyeta a wani keɓaɓɓan guri sai ranar da burina ya cika zan fito da ita."
"Hakan yayi kyau, ya kukayi da oganki ne da kikaje neman transfer."
"Ohh Mr. C.P ai saida na tabbatar baya ƙasar kafin naje na processing komai, saidai kawai ya
dawo yaji labarin nayi aure a wani gari na barsu da garinsu."
Dariya Jidda tayi kafin tace
"Kin manta waye CP kenan zai iya miki makircin nasa."
Dariya dukayi duka tare da miƙewa suka fice a falon.
í ½í²«í ½í²«í ½í²«í ½í²«í ½í²«í ½í²«í ½í²«
A yau ne dai aka É—aura auren Muhammad Jawwad Sulaiman da Fatimah Zarah AbdulJalal sai
fatan samun zaman lafiya a tsakanin ma'auratan biyu duk da ba haka aka tsara ba.
Duk da ba'a shirya shagula ba amma mutane sunzo sosai harda waÉ—anda ma ba'a gayyata ba
duk sun nuna bajin ta, da yamma kuma akayi walimar mata a cikin gidan inda malamai sukayi
wa'azi sosai wanda duk akan zamantakewar aure ne.
An raba kyaututtuka