Showing 30001 words to 33000 words out of 40319 words

Chapter 11 - Ladidin Kauye Hausa Book Compelet

15 Aug 2026

611

yayyar kaza
ba ,haka yadinga bata 'a baki tana ci tana yanga suna gama ci yace ”taso muje muyi sallah dan
nuna godiya ga Allah ,a gajiye take amma batada za6i dole ta mik'e sukaje yin alwalah ,suna
idarwa ne yazo yaja musu sallah raka'a biyu sukayi yai sallama bayan sunyi adu'oi masu yawa ,
ya d'ora hannu a kanta yana yimata 'adu'a ,suna kammalawa ya mik'e ya nufi bedroom d'inshi
sleeping dress yaje ya sako ita kuma lokacin tsabar gajiya kwanciya tayi da kayan jikinta
,Humaid bai kulata ba yaja filo ya kwanta 'acan gefe ."

Washe gari bayan tayi sallah ta duba bataga Humaid ba ,jin alamun shigowarshi yasata
durk'usawa har k'asa tace ”barka da safiya yaya ,yww barka dai amaryar yaya ,da 'alamu baki
damu da yayan naki ba ko ¿sunkuyar da kai k'asa tayi tana wasa da fingers d'inta surarta yai
yace ”zomuje mu kwanta bacci nakeji please ya marai raice kamar yaro ,dariya yaso bata tace
”gaskiya not ni yanzu bazan kwanta ba buh wlh wanka zanyi tana magana kamar zatayi kuka
Humaid ne ya shige ya barta 'a gurin ,juyi yakeyi baccin ma yak'i d'aukarshi tunani ya fara ,ina
murna farinciki na ta dawo ashe akwai problems a gaba oh god Allah kadawo min da Khady kan
hanya ."

Breakfast ta had'a musu mai rai da lafiya chips ne na dankalin turawa sau wainar k'wai dakuma
tea mai kauri wanda yaji kayan kamshi ,dining room ta wuce dashi kasancewar ankuma gyara
gidan ,tana fitowa ta koma kitchen kayan data 6ata ta wanke ta rufo kitchen d'in ,tsintsiya ta
d'auko tafara share parlorn tanayi tana hutawa 'a haka ta gama mopping d'in tayi daganan ta
kuna turaren wuta ,wani sihirtaccen k'amshi ke tashi a gidan ,bedroom d'inta ta shige ta cire
kaya ta d'aura towel ta shiga wanka ,ta dad'e tana wanka da sabulun da momy ta bata mai
kamshi tana fitowa ta ciro kayanta , gaban dressing mirror ta zauna simple makeup tayi ammafa
ta had'u atamfar ta d'auko mai ratsin wait and black tayi d'auri mai kyau ,kin shiga bedroom d'in
Humaid tayi can kuma ta shige da sallama tana cewa yaya Humaid katashi breakfast is ready

ohk yace ”dagan ya mirgino yana yimata wani kallo cikin sigar wasa yace ”ke bakisan inda ake
tashin miji daga bacci bane ¿" am sorry tace "daganan ta fice, brush yaje yayi daganan yai
wanka ya shafa manshi man kamshi ya fito sanye da shadda pink sai d'aukar ido takeyi
,murmishi ya sakarwa Khadyja yace ”lovely mai yasa baki kirani nazo na tayaki ba ¿cikin sanyi
murya tace ”nagama ai ,janyo gwangwanin madara da ragowar kayan tea yayi saida ya k'ara
komai bacin wanda tasa dagan yace ”to bud'e baki naga 'alamun bakison cin abinci sosai ko
¿shiru tayi daganan tafara cin abincin ,kad'an taci tace ta k'oshi."


Kallonta Humaid yakeyi yarasa mai yasa yarinyar nan yanz bata sakewa dashi ,duk rashin
kunyarta da neman tsokana yanz duk sunyi sanyi ,tunani ya shigayi to aure babu hira ina labari
,duk inda naso naga ta fahimceni amma lamarin ya citura ,mik'ewa yai yace ”lovely biyoni ki
kar6i wani abu ,cikin sanyin murya tace ”ya Humaid banajin dad'i ynz kaina nayimin ciwo
,subhanallah to zomuje hospital a'a kabarshi inada maganin a d'aki please zani in kwanta ohk
yace ”yarasa mai yaiwa khady take wanan slow d'in ,kodai har yanzun bata sonshi ne kwai tabi
umarnin Momy da dady ne ,iska ya fesar mai zafi ya bugi bango yana dogon nazari itako tun
tuni ta shige part d'inta."



Kwance take tana kallon sama tana tunanin rayuwarta tada 'a cikin gidan hmm da yace ”baya
sona yanz kuma yace ”yana sona kai da 'ayar tambaya wlh but naji masoya na cewa in mutum
ya k'ika daga frko to karshe koyace yana sonka yai karya , haka ta dinga juyi a bed d'inta tarasa
maiyake damunta .

Washe gari ai yuka ta gabatar inda tasaba ko ina ta gyareshi gidan sai zuba k'amshi yakeyi ,yau
7 days da auransu ,nocking taji batayi azamar tashi ba saboda Humaid na nan ,ganin gimbiyar
bata tashiba yasashi mik'ewa ya bud'e k'ofar ,su inna Hauwa ya gani ita da wata yarinya zatakai
13yrs a duniya sanye take da rigar banba lasta rigada wando sai hijab da yaji jiki ,inna ce tace
”munsha hanya fa khadija najin muryar inna ta mik'e da gudu tana oyoyo ,Humaid ne ya kar6i
kayansu ya shige dashi d'akin bak'i yadawo suka gaisa ya fice sbda ana kiran sallah ,khadija ce
tace ”inna kunsha hanya ya su baba ,lafiya Lou inna tace ”tana kalle² khadija ce ta dubi wanan
yarinya tace ”inna naso in ganeta amma ta 6acemin ,yarinyar ce tace ”uhm ai wanan daular
haka dole bazaki ganeni ba to inkin manta nice sahura waro ido khadija tayi tana duban sahura
tace ”wai kece kika girma haka ? Sahura ce ta dubi khadija tace ”to ke kinga inda kika koma ne
walahi kamar matan turawannan da muke gani a shagon mai shayi na anguwarmu ,dariya
sukasa dukansu ,khadija ce ta shige kitchen sbda yimusu girkin lokacin 11am shinkafa jollof mai
kifi da carrot dakuma green bean's dataji alaiyahu lokaci k'alilan gidan ya kaure da kamshi sosai
,Sahura ce tayo kitchen d'in da sauri tana cewa kufa y'an gayu inzakuyi girki bakwa gayya
dariya khadija tasa tace ”to a wanan girkin menene abin wahala ?Sahura ce tace ”walhi ku kula
saboda ance yawan ciye _ciyen kayan dad'i nasa ka mance da lahira Khadija dai bata kulata ba
sai aikinta takeyi ,Sahura ce taga bread a saman fridge tsalle tayi ta d'auko ta yaga tace ”oh sai

natuna lokacin da kike cutar mutane ki gudu amma yanzu ana yimiki magana ma sai kinyi ra'ayi
,hmm kawai khadija tace ”sbda hankalinta na kan girkinta."



Khadija ce ta dubi sahura tace ”to muje muyi sallah sai muci abinci ko ?Sahura ce ta yago
bread tace ”tabb inma zaki zubo abinci ki zubo dan ni wata shegiyar yunwa nakeji yasin khadija
ce tace ”zan zuba miki naki nikam zanyi sallah , tunda khadija ta zubo abinci Sahura ke had'iyar
yawu tana lashe baki ,khadija ce ta mik'a mata tare da wani soyayyan nama a kai Sahura ce
tace ”ke bakida wayo nikam kawo naman injishi a hannuna kar azo ba'a sawa inna ba tace
saitaci ,khadija kam wucewa tayi tabarta a gurin tana tura nama cikin aljihun wando, bayan sun
kammalah cin abincin khadija ta kwashe takai kitchen saida ta wanke sanan ta fito ,inna ce ta
mik'o wa khadija wani k'ullin buhu tace ”lalle ne da barkono da kuma citta godiya khadija tayi
sosai daganan inna tace ”zasu wuce Sahura da ido yai ja tace ”nifa inna kitafi walahi bazan
koma k'auye ba kicewa babanmu sai yazo aurena ,dariya suka sa khadija ce tace ”to kizaune in
kikayi sati biyu ko uku saiki koma ,tsalle sahura ta doka ta cakumi khadija tana murna ,inna ce
tace ”to anta6a yanke hukunci babu mai gida khadija ce tace ai ya Humaid bashida matsala,
haka inna ta tafi tabar Sahura ."


Washe gari Sahura ce gaban TV tana kallo a MBC action wani film suke yi mai fad'a suna cikin
fadanne wani ya kaiwa dan uwansa naushi Sahura ce ta doka tsalle ta kaiwa khadija naushi har
tana neman k'ara mata ,a razane khadija ta dago tana kallon Sahura da hankalinta ya tafi ga TV
nuno gurin kuka 'akayi aifa ta zauna tadinga kuka harda gumi ,khadija ce ta tashi ta kashe TV n
sallamar humaid sukaji Sahura ce ta dubi humaid tace ”barka mijin ta jikin t b juyiwa yai yace
”to waye ta jikin t b ?kallon khadija data had'e rai tayi tace ”to ai naga yan gayu idan mijinsu ya
dawo fara'a sukeyi kekuwa kin wani had'e rai kamar dillaliya anzo cin bahi lolz ,wani mugun
kallo khadija ta jefeta dashi shikuma humaid na kallonta baice komai ba ya *LADIDIN KAUYE*


funny & love story

47_48

Ganin abin zuba sharar gidan ya cika mai zuwa kwashewa bai zoba yasata d'auka ta nufi wani
guri tafiya takeyi tana dube dube a uban kwandon zuba shara a kanta ,hango wani k'aton kare
tayi yana shirin dosota jikinshi duk gashi cikin tsoro tafara gudu aikuwa kare yadinga binta duk
inda ta shiga saiya bita gudu takeyi da kwandon shara a kanta ,tama manta layin dazata dosa
gashi gidajen duk kusan kala d'aya wani mutumi ta hango yana gyra parking din motarshi
k'arawa tayi da gudu tace ”dan Allah ka temakeni karya halakani ,mutumin ne ya kalli karen
yace ”mai tayi ma kake binta ?itako Sahura ganin yana neman raina mata hankali tace ”shi
mutumne dazaka tsaya tuhumarshi ko kaima mugune irin karen ,mutumin ne ya rike baki tana
salati cewa karen yayi duk inda tashiga kabita karka raga mata."

Aikuwa kare yafara bin Sahura gudu take ci babu mai temakon ta ,humaid ne tafe a cikin mota
hango ta yai tana gudu ashe harta zo anguwar takuma juyawa yanzukuma ta dawo duk bata
sani ba ,fitowa yai daga cikin motar yana cewa keee!!da k'arfi ziwa tayi ta cakumeshi tana ihu
,karen humaid yabawa hak'uri daganan yace ”to ga gidan nan amma ina zaki da kwandon shara
cewa tayi naje zubar muku da shara shine kare ya biyoni wata shu'umar dariya humaid yasa
yace to jeki gida maganin mai yawo kenan ,murgud'a mai baki tayi ta shige ciki , tana shiga
tafara cewa Ladidi ki fito yau nakusa mutuwa ,da sauri Khadija ta fito tana cemata na k'arshe
karki sake cemin ladidi ,to natuba dan kunga ku yan gayu ne shine kikeso kisa a maidani gida to
ta Allah ba takiba ta shige d'akin da yake mazaunin nata."



Washe gari salamar momy ce ta karad'e harabar gidan da gudu khadija ta fice tana oyoyo
momy a tare suka shigo parlor rik'e da hannun juna ,Sahura na zaune tana kallo tace ”hajiya
barka da zuwa momy ce tace ”yww daughter yar aiki kika samu ne ¿khadija ce tasa dariya tace
”tare sukazo da inna hauwa ,oh momy tace ”na tuna ai ta fad'a min amma bbu wani matsala kho
eh momy komai normal , nan momy ta jata zuwa bedroom d'inta tanata bugar cikinta 'akan ko
tana cikin wata damuwa ,juyin duniya khadija tak'i fad'awa momy komai,momy ce ta fiddo da
wani turare tace ”yau d'inan 'nakeso kiyi using dashi ,to Khadija tace ba tare data musa ba
,nasihoyi momy tayi mata akan ladabi dakuma hak'urin zaman aure,momy ce ta d'au jakarta
tana shirin tafiya narai _narai Khadija tayi da fuska zatayi kuka momy tace ”nazo kuma dan
inganki inji dad'i shine zakiyi kuka kull kiyi hak'uri zaman aure ba wasa ba ,raka momy tayi har
gurin motar da tazo sukayi sallama ,magrib nayi tayi wanka tasa riga da wando rigar dai _dai
cinya wandon kuma dai _dai gwuaiwar k'afarta ,turaren da momy ta bata ta fito dashi shafawa
tayi a fuska tana mai jin k'amshin yayi mata dad'i ,,jin sallamar Humaid yasata fitowa a kunyace
tace ”barka da dawowa yaya uhm barka yace yana k'are mata kallo ,wani lamari yakeji mai
wuyar fasarawa sabda inya kalli fuskarta ,cewa yai kaimin bag d'innan ciki ohk tace ”ta wuce
taje kaiwa ,tana shirin fitowa taga an kashe light d'in d'akin anbar kadan zaro ido tayi lokaci
guda kuma tsoro ya baiyana a fuskarta ,cikin zuciyar shi yana cewa da nace sai lokacin da kika
amince to yau na soke wlhi ,nufota yakeyi tana ja da baya ,a haka har tasamu tayi d'akinta da
gudu ,6acin rai ne ya dirarwa Humaid sabda yafara wani tunani daban akan Khadija yafara
zarginta sosai sabda had'in kan datak'i bashi tana nufin Allah bazai kamata da laifi ba
kenan?takoma kamar jahila wacce batayi karatun islama ba ,yau dai 6acin rai yasa Humaid
maganganu marasa kan gado juyi yakeyi yana tunanin anya wani bai rigashi ba hmm ."


Yaune Sahura zata koma gida sai kuka takeci kamar an aikota wai zatayi kewar burodi da shayi
ga kayan dad'i harda bubuga k'afa ,a haka suka had'a mata goma ta arziki akwati sabo Humaid
ya siya mata hardasu atamfofi driver akasa ya kaita.

Khadija batada wal walah kwata ²komai cikin sanyin jiki takeyi gashi ta koma very silent abin
haushi ma dariya tsada takeyi mata ,washe gari da safe kira ya shigo wa Humaid cewar wanan
doctorn yanason suyi wani aiki tare urgent yaje ya sanar dasu momy fatan alkairi sukayimai
sanan sukace to matarka fa ?"sosa kai Humaid yai yace ”tace batason yawo lolz tunkafin ka
tambaya hh,a tunanin su momy cikine da ita dan yau bikinsu 1 month kenan ,ficewa yai sunata
sanya mai albarka komawa gidansa yai yasami gimbiyar na goge TV k'arasawa yai ya
rungumeta yana cewa lovely munsami cigaba fa kitayani murna ,murmishinta tayi mai tsada
tace ”Allah ya tabbatar da alkairi ,wanan adu'ar tasa yaji dad'i sosai ,yace to kishirya muje tare
a'a tace ”a tak'aice shiru yai bai sake magana ba ,yanason cewa ki shiryamin kayana a jaka
yakasa ,hakadai ya shirya da sauri sauri ,Jalal ya kira akan yazo ya kaishi airport sai ya dawo
da motar ,yayi yayi Khadija ta rakashi koda airport d'inne amma ttak'i."



Haka tayimai Allah ya tsare ,yana tafiya ta fashe da wani matsanancin kuka ,ring d'in wayarta
taji mik'ewa tayi ta d'auko wayar ganin number babu suna yasata kallon number, dauka tayi
had'e da sallama dagacan 6angaren akace ya kike kwalli lpy Lou Khadija tace ”dan bata gane
mai maganar ba Fati ce kokin manta da mukayi school tare oh na tuna yakk hope kina lpy eh ya
amarci dariya Khadija tasa tace ”amarci nan sai wanda ya k'aru daganan sukayi sallama
,zaman shirunne ya isheta ta zari hijab ta shiga mak'otan su gidane tangameme kuma tsararre
da yafi nasu komai ma nocking takeyi amma shiru , can mai gadi ya bud'e yana kallon Khadija
yace ”daga ina ne ?cewa tayi ga gidnmu nan wanan na jikin nakun ,Allah sarki yace dagan an
yabata hanya ta shige ,da isaera k'ofar parlorn wata k'ofa ce ta glass tana haske kala kala
sallama tayi jitayi an amsa ,matar dai batasan Khadija ba amma dayake batada girman kai yasa
tace toshigo mana sister."



Shiga tayi matar da a shekaru zatayi 27 tace ”saidai ban ganeki ba wlhi tana murmishi ,Khadija
ce tace ”ga gidanmu nan jikin naku ,oh ko kece amryar da aka kawo kwanaki 8 months da suka
wuce ,jinjina maganar Khadija tayi tace ”wata takwas kina nufin Humaid yayi aure kenan ?matar
ce ta dubi Khadija tace ”oh su6utar baki please karki tada hankalinki ita wacan ba zaman aure
ya kawo ta ba ,kinga ni sunan na Rahma yarana biyu kin gansu nan a photo yarane kyawawa
masu kamada uwarsu sunsha kyau sosai Khadija ce ta dubi Rahma tace ”ni kuma sunana
Khadija danan hira ta 6arke kamar sun dad'e da sanin juna horn sukaji Rhma ce ta mik'e tana
lek'awa ta window ,oh kinga sweety ya dawo please ina zuwa , Khadija ce ta mik'e window da
Rahma ta lek'a nanta fara lek'awa wani kya kyawan magidanci ta gani fari sol kamar bature
,hango Rahma tayi ta bud'e masa mota ta kar6i jakar ta rataya ta kuma ruk'o masa hannu
shikuma ya rungumota suna tafiya suna dariya ,Khadija ce tace ”danasan iskancin da zan gani
kenan da banzo gidannan ba wlhi ni nazo domin d'ebe kewa amma naga abinda yafi k'arfina
nifa bazan iya k'arewa a yiwa namiji bauta ba hmm ,ita kad'ai taketa maganarta ,can kuma taji
gabanta na fad'uwa sosai ,yarinya tagani wacce zatayi shakara hud'u a duniya tace ”jeki cewa

momynki bakuwar ta tafi ,da gudu ta shige tana cewa momy bakuwa zata wuce ,OK kice
ganinan Rahma ce tace ”sweety zani yiwa bakuwata sai gobe ,janyota yai yace ”daga ina tazo
a mak'otanmu take ,Rahma ta fice tana dariya ,samun Khadija tayi a bakin get a tsaye ,Khadija
ce tace ”to aunty Rahma sai wani lokaci godiya Rahma tayi mata ,Khadija ta fice.shige
ciki....✍️.*LADIDIN KAUYE*



funny & love story



49_50


Jin fad'uwar gaban ya tsananta sosai yasata k'ara saurin tafiyar ta ,tana dosowa bakin get
abinda taganine yasata kurma uban ihu ta fad'i sumammiya .


Sahura ce zaune tana cin tuwo tana turo baki ,inna Hauwa ce tace ”nifa banasan kinibibi
garama abincin gidanmu naku da ko kafi zabo babu ,kuka Sahura ta fashe dashi tace ”ni walahi
sonakeyi in koma jos gurin Ladidi ,zaro ido inna tayi tace ”to ga hanya nan kitafi k'wad'ayayya
sunmayi namijin k'ok'ari da har kikayi musu sati biyu batare da sun koroki ba ,wani kallo tayiwa
inna harda murgud'a baki tace ”to dan kiji ma yasin ni bazanyi aure a nanba saboda talauci yayi
muku kanta ,salati inna keta jerowa ita ko sahura surutunta take jerowa ,jin salamar yaro yana
tallar alele hhh fans means allale ,tace ” kai d'an hanse kawo dan uwarka ,inna ce tace ”walhi ki
kiyayi zagi saikace baki zuwa islamiya ,mugud'a inna baki tayi hakan yabawa inna damar yin
shiru ,Sahura ce tace ”wa yaron biyar biyar ko¿" a'a yaron yace wake ya k'ara tsada goma
goma ne , cewa tayi to sako na wazobiya inna mik'omin kwanon kusa dake ,mik'o mata inna tayi
duban yaron tayi tace ”kasamin manja da yaji sosai ,bayan yasa ne tace ”inna bismillah kawo
kwanonki ,inna da bata wuce tayi ta mik'a kwano aka samata guda d'aya ,Sahura ce taga
yaronna kallonta cewa tayi d'an hanse zakaci alelen ne eh yace aikuwa tace to ci d'aya da rabi
ninikuma inci biyu inna ga wanan rabin ki kara ,inna na rawar jiki ta kar6i alale tanaci tana lashe
rroba."




Saida suka gama ci yaron yace ”Sahura bani kud'in ?" cewa tayi kai na nawa kaci ?" yace ”to ai
kece kika bani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0