Showing 33001 words to 36000 words out of 40319 words

Chapter 12 - Ladidin Kauye Hausa Book Compelet

15 Aug 2026

615

kyauta ,juyawa tayi gurin inna tace inna kinci na sha biyar ko ? eh inna tace tana
zaro ido to talatin kenan ungo murtala sauran kuma sai kubiya ,yaronne yafara kuka yana ihu
,shigowar malam Adamu yasa Sahura zamewa ba tare da kowa ya ankare ba ."

6angaren su Jalal kuwa soyayya suke zubawa wacce babu algus kowa bayason yaji 6acin ran
d'an uwansa shiri takeyi zatace hospital gaishe da Khadija da ake yimata k'arin ruwa Jalal ne
yace ”Honey inkin gama kizo mutafi ,shagwa6e fuska tayi tace ”anya babyn ma zaibari na fita
kuwa ,k'arasowa Jalal yai dai _dai saitin cikin nata da zaiyi wata hudu ya kasa kunenshi yana
dariya ,girgiza kai yayi yace ”to baby's sunce ko America zaki saikin dawo ,dukan wasa ta
kaimai tana cewa tabb barinzodai mu tafi dan naji ance jikinata yayi tsanani ."


Emergency room aka kwantar da ita saboda lokacin da ta yanke jiki ta fad'i Allah yasa da
mutane a gefe ,kwance take ansa mata oxygen wato abin nunfashi ,nunfashinta baya fita sosai
kowa ya cire rai da khadija momy kuwa sarkin kuka kullum cikinsa take tanacewa kukuma
jarabawarku kenan wayo rayuwa, Saudat ce tayi sallama ita da Jalal amsawa su momy sukayi
itada k'anwarta durk'usawa har kasa sukayi suka gaidasu momy dagan an ya ajiye food folks a
gefe yace "ya jikin Khadijan da sauki momy tace ”had'a baki sukayi gurin cewa Allah yabata
lafiya amen momy tace ”bayan Jalal ya zauna ne yace ”momy number ya Humaid bata shiga
yau 3 days kenan ina gwadawa amma a kashe ,momy ce ta share hawayen da suka zubo mata
tace ”shima dajin wanan lamarin da yafaru a gidannasu ya kwanta rashin lpy dan naji ance jikin
ya tsananta sosai ,Jalal ne ya tausayawa yayan nashi yace ” momy insha Allah jibi zantafi dubo
shi to Allah ya kaimu tace ”daganan shiru ya biyo baya."


Momy ce ta shiga room d'inda aka kwantar da Khadija samunta tayi ido a kakkafe tana kuka
momy tsabar firgici tayi gurin doctor tana kuka ,da sauri doctor Umar ya shigo yafara gawaje
gwaje ,cikin sa'a nunfashin ta ya dawo normal can tafara bud'e ido ruk'o hanunta momy tayi
tace ”alhamdulilh daughter Allah yakara miki lafiya ,Khadija babu bakin magana sai kalle kalle
takeyi..


Tabarmai nagani da mutane a k'ofar gidansu dady kowa kaganin fuskarsa bbu dad'i zaman
makoki akeyi dakuma adu'oi , dady ne keta kar6ar gaisuwa gurin jama'a suna yimasa ya karin
hakuri ,washe gari jikin Khadija yayi kyau sosai dan har tana cin abinci sosai ,sallama aka basu
suka wuce gida ,Khadija na ganin yan zaman makoki tafara tambayar waye ya rasu ,momy ce
ta tuno da sharud'an da doctor ya gaya mata akan ta kiyayen 6acin ranta kokuma shiga
damuwa ko gani ko jin fargaba ,momy ce tace ”suna hutawa ne kinsan wanan watan dolle sai
anyi meeting da ma'ai kata ta gamsu da baya nin momy shiyasa ma bata k'ara d'aga hankalinta
ba....



Kai nimafa mom Islam abin ya d'auremin kai 😢meya faru a gidansu Khadija ??waye ya rasu
??? tabb todai kubiyoni danjin inda muka dosa�.

Kwance take tana wani matsanancin kuka rabonta da abincin kirki tun da wanan abin ya faru
,tarasa ina zatasa kanta gashi Allah ya jarabeta da abubuwa duka biyu ,alwalah ta d'auro tazo
tafara nafilfili tana gayawa Allah damuwarta ,washe gari yaune akayi sadakar uku mutane sun
ragu sosai ba kamar daba ."
Kale ² takeyi a d'akin tarasa meyafaru bazata iya tunowa ba ihu tafarayi dan razana take koda
wane lokaci ,momy da tatashi akan darduma tayo d'akin da gudu ta sami Khadija nata juya kai
tana ihu ,wasu zafafan hawayene suka zubowa momy tayi waje da sauri ,driver ta k'walawa kira
cikin azama yazo ya drk'usa a gaban momy _momy ce tace ”maza ka fito da mota mu koma
hospital ,komawa tayi ta ruk'o Khadija tafito da ita hijab d'inta ta Sanya mata daganan sukayi
mota ,dak'ayar momy ta sata a mota suka wuce hospital, sunyi sa'ar ganin doctor ,inda yake
sanar musu cewar su dage da adu'a kuma akwai abinda take tunawa yake tsorata ta
magunguna ya kuma basu yace ”ku kulla sosai da ganin tasha magani."


Haka driver ya dawo dasu gida ,matane keta shigowa gidan momy suna yimata ya karin hakuri
,wanan su shigo wanan su fita dayake momyn ta mutane ce .



*KAUYE*
Sahura ce ta shigo gidan inna da gudu tana shewa ,had'e fuska inna tayi tace ”fitarmin a gida
nace kifice ko ,dariya Sahura tasa tace ” inna ya alelen ranan waya biya kud'in ¿"ubanki ne ya
biya kinji ,sahura ce ta zaro ido tace ” ubana fa sirikinki ne ,inna ce ta d'auko sanda tana shirin
buga mata wani yaro yai sallama yace ” Aslamu alaikum zakusi kai da kafar kaza ?" tsalle
Sahura ta doka tace ”kai yaro kawo nan shigowa yaron yayi ya nemi guri ya zauna ,Sahura ce
ta dubi inna tace ” hmm sai na tuna lokacin da mukaje gidansu Ladidi kullum sai naci kaza
,amma yauma Allah yasa inada ragowar kud'in da Humaidu ya bani d'ari biyu na siya ,dajin
haka inna ta washe hak'ora tana dariya tace ”yoo ai siyama zakiyi koda na d'ari ne Sahura ce ta
tambayi yaron nawa nawa ashirin ashirin yaron yace ”kasiyar uku hamsin ¿"eh kawo .


Kai ta d'iba guda biyu k'afa kuma d'aya duban inna tayi data zuba tagumi tace ”toke bazaki
d'auka bane ?inna ce tace ”to masu abin basuce in d'auka ba ni na isa ,dariya Sahura tasa tace
”laaa ina ki d'auki na hamsin ,inna na sid'ar hannu ta d'auka harda zubo romo ,yaron yana
zaune har suka gama ci Sahura tace ”ga hamsin d'inka kajira wanan tsohuwar ta baka kud'inta
inna na sud'e hannu tace ”kan uban ke kin biya naki hakafa kikayimin ranar sai malam ne ya
biya yana fad'a Sahura dake taunar k'ashi tace ” maganin mai kwad'ayi komai mutum saiyyaci
,inna ce ta kunto zaninta gudar d'ari biyar ce a jiki mik'a wa mai kai da k'afa tayi tace ”k'aromin
na hamsin ,dan ubanta ni zata rainawa hankali*LADIDIN KAUYE*

funny & love story



51_52
Yaro dai na ganin ikon Allah ya je ya samo canji ya kawowa Inna ,Sahura ce tace ”au kewai
inna kina gadarar zaki bani haushi ne aikin 6urr saidai inbaki haushi ta ja gyalena ta d'aura a
kwankwaso ta fizge kwanon da inna tasa a dad'o mata naman ta ruga da gudu ,kuka inna tasa
tana tsinewa Sahura tana cewa ,shegiya ga kashe d'ari danayi tashi d'aya gashi iya romo na
tsaya sud'a ta wafce kwanon ,shidai mai talla gaba yai yabar inna tanata surutunta."


_JOS_

da sallama ya shigo yana cewa momy yau akayi sadakar bkwai to Allah ya gafarta masa kuka
momy takeyi sbda inta tuno abinda yafaru amma aikin gama ya gama rayuwar batajin dad'in
yinta sbda Khadija har yanzu sai sauk'in Allah yanzu ciwon 'nata ya koma kamar na mai aljanu
in ciwon ya tashi to guduwa take burin yi dady abubuwa sunyi mai ywwa sosai duka dai familyn
gidan basuda wal wala ,kwance take tana bacci sai kuka takeyi kuma da k'arfi ,momy ce ta
shigo d'akin ta sameta tana bacci kuma tana kuka ,adu'oi tashiga yimata tana tofa mata
,yunk'urowa tayi tana gurnani zata hankad'e momy ,cin sallamar Jalal yasa momy k'wala masa
kira ,da sauri ya shigo yana cewa momy lafiya kuwa ¿inafa lafiya Jalal ?narasa yaza’ayi da
ciwon Khadija kullum abin baya lafawa kullum cikin fad'a muke gashi banda kunu batacin komai
y'an aikin gidan suntafi garinsu ,sai kuma tasa wani kuka mai ban tausayi ,hak'ik'a momy mace
ce wace batada zalunci batada mugunta kuma bata fifita wani akan wani ,Jalal shima abin
yafara damunshi kukan da momy keyi ya kuma tayarmai da hankali ,sukan sunga jarabawa
Allah yasa su cinyeta duka."

Washe gari antashi da wani sanyi mai shiga mai shiga jiki tunda gari ya waye khadija keta ihu
tana k'ok'arin fitowa wani girgiza d'akin yakeyi ga wasu k'ara dake baiyyana a cikin d'akin ihu
takeyi iya k'arfinta ,dady daya shigo yanzu yai d'akin da sauri ,ganin inda jikin khadija keta 6ari
yana makyar kyata yasashi cire hular kanshi adu'oi yaketa karanto mata amma sauki sai lokacin
da Allah ya nufa ,gefenta wasu abubuwa take gani masu ban tsoro sai nuni take yiwa dady ina
shikam bai gani ba ,ihu take kuma yi tana ruk'o hannunshi amma dady babu abinda yagani
yarasa wane ciwo ne ke damun khadija , adu oin da yai mata yasamu jikin ya lafa dan har bacci
ya d'auketa."


D'akin momy ya nufa zaune ya sameta kan sallahya tana azkar shigowar sa ne yasata shafa
adu'a tace ” barka da dawowa mijin kirki ,dady ne ya fitar da wata zazzafar iska daga bakinshi
ya d'aga hannu sama yana cewa Allah mun gode da jarabawar da kayi mana Allah ka kawo

mana mafita ba yawan arzik'inmu ba bakuma yawan ibadunmu ba Allah ka dubemu ,suka shafa
tare da cewa amen.


Wata girgiza sukaji mai firgitarwa momy zata tashi dan taga meke faruwa dady ya tsayar da ita
yana cewa kibari in lek'a ,momy na shirin kuka tace ”gaskiya sai dai muje tare ,hannun dady ta
rik'e tana kuka suka fita , duk wanan hayaniyar da girgizar duk a part d'in Khadija yake faruwa
hatta k'ofar ma girgiza takeyi kuma a bud'e take ,dady na shirin lek'awa momy ta rik'oshi tace
muje mu nemo malamai dan Allah ,hankalin dady a tashe damu warshi wane hali baiwar Allah
take ciki marainiya ,kutsa kai yayi momy na tsaye ya wuce ,kwance ya sameta d'akinta duk
ruwa mai had'e da jan abu mai kamada jini sai wasu surutai takeyi ,kafin dady yace ”bismillah
kawai aka d'aukeshi aka gwara da jikin bango ,ihu momy takeyi iya k'arfinta gadai khadija a
kwance shikuma dady ,kowaye yayi mai haka oho , mai gadi ne da driver sukayo cikin gidan a
tsorace ,momy babu magana sabda kuka yaci k'arfinta saidai nuni da hannu ,hango dady sukayi
a mak'ale a jikin bango shi bai sauka ba shikuma bai yi sama ba, wani hayaki ne ke fitowa
amma Khadija na kwance tana bacci ,driver ne yace ”anya babu shed'anu a lamarin kafin ya
rufe baki yaji an wankamai mari ,ganin basuga kowaba yasa mai gadin da driver da momy suka
arce da gudu , d'akinta momy ta koma ta d'auko wayarta ta kirawo Jalal ring d'aya ya d'aga
yana sallam momy ko amsawa batayi tace ”Jalal.ka kirawo mai ruqyya dan Allah dadynku tana
kuka to yace kashe wayar momy tayi tana adu ar datazo daga bakinta , bayan 30minutes sai
gashinan shida wani babban malami sun shigo ."



Gai sawa sukayi da momy daganan tayimai bayanin ciwon Khadija dakuma halin da dady yake
ciki ,ruwa ya buk'ata domin alwalah bayan ya idar da alwalar ne yace ”a nunamai d'akin ,momy
ce ta shige gaba itada Jalal shikuma malamin na baya da Qur'ani a hannunshi ,da hannu momy
tayimasa nuni da d'akin ,lek'awa yayi ya hango dady jingine a jikin bango shi baya k'asa
auxubillahi yace ” a lokacin da yake karanta suratul bak'ara ,jikin dady ne ke jijiga yana wani
gurnani tsananta adu'a malamin yayi , Allah cikin ikonsa saiga dady ya fad'o yana tangad'i
,malamin ne yace ”asamu yayi wanka kuma ya kwanta ,kan Khadija aka koma daketa bacci ko
motsi batayi adu'oli iri _iri malamin yayi amma har yanzu shiru ,d'akin sai fitarda wani hayak'i
takeyi mai ban tsoro."



Fitowa malamin yayi yana yarfe gumi yace ”zanje in dawo ,to su momy sukace daganan suka
rufo k'ofar khadija ,da fitar malamin gidan duka ya kaure da kururuwa mai firgitarwa daga momy
har Jalal sun kasa koda motsi ne ,dama dady bai tashiba tunda yai wanka ,jin girgizar tayi yawa
yasa momy shiga bathroom d'inta d'auko buta tana shirin zuba ruwan alwal wasu abubuwa
tagani na ban tsoro hakan yasata ficewa tana salati Jalal ne yace ”momy to yanxu ya za'ayi ¿ jin
momy tayi shiru yasashi kallon inda take kallo ,wata halitta ce mai abin tsoro da girman ta ya
zarce tsawon d'akin a sunkuye take tafiya ,idanuwan momy suk k'afe bataji bata gani ,kafin

wanan abin ya iso Jalal cikin tashin hankali ya cici6i momy yai da ita d'aki suna gudu halittar na
binsu Allah yabashi ikon rufe k'ofar ba tareda wanan halittar ta shiga ba."




Ruwa yadinga yayafawa momy amma shiru ,a karo na biyu ne ya bud'e ma dai _dai cin fridge
d'inta ya ciro ruwan sanyi yana yayyafa mata cikin sa'a ta mik'e tana salati, sallamar malam
sukaji babu wanda yai k'ok'arin tashi malamin yace ”yanaga babu kowa Jalal ne cikin d'aga
murya yace ” kaje d'akin mara lafiyar ,gamunan momy na ce babu lafiya ,shigewa d'akin
malamin yayi daganan yafara adu'oi yana tofa mata yanayi yana tofa mata wata atishawa tayi
mai k'arfi wacce tayi dai dai da tashin dady daga bacci ,momy take kira iya k'arfinta ,momy najin
muryar Khadija ta fice da sauri tana cewa yaushe rabon da daughter ta kirani, fara'a ce ta
baiyyana a fuskarta tashiga d'akin zaune ta sameta ,da shigar momy Khadija tace ” momy
maiya faru ne babu komai momy tace ”daganan malamin yace ”hajiya muje parlor inyi miki
bayani OK tace suka wuce Khadija tashi tayi ta shiga wanka ,ganin duniyar takeyi kamar
sabuwa.*LADIDIN KAUYE*




Page 53 & 54

Malamin ne yace ”dole sai kun kiyaye da shan maganinta to momy tace ”yabasu adu'oi da zasu
dingayi a gidan , momy ce tacewa "Khadija ta shirya suje airport itada Khalel , cikin sauri ta nufi
d'akinta dan yanzu burinta bai wuce taga mijinta ba , Jalal ne yashigo yana k'walawa khadija
kira , fitowa tayi cikin wata shiga mai d'aukar hankali , less ne pink a jikinta sai gyalenta fari
takalmi fari jaka pink and wait, wow kuzo kuga Khady , suka shige mota zuwa airport , mutane
ne keta saukowa , hango wani had'ad'en saurayi tayi mai kamada Humaid ,tunani tafara kodai
humaid ne ?" sanye yake da bak'ar rigar sanyi my adon flawoyi gashi yayi haske sai dai ya
rame sosai , da zuwanshi yayi hugging gimbiyarshi , shidai Jalal na gefe yana zaro ido ,
sunkuceta yayi ya rungumeta yana yimata rad'a a kunne wanda nima banji me suke cewa ba
,Jalal ne yace ”wato ni an manta dani ko ?"dariya Humaid yayi ya doki k'afad'arshi yace ”am
sorry kuna raina dukkan ku , mota suka shige ,Humaid da Khadija a Back side ,Jalal yana gaba
yana driving,da isarsu gida sukaci karo da anshirya walima gagaruma gurin ya kawatu da
flawoyi masu wuta suka shige ciki ."


funny & love story


55_56

Dady da momy suka zauna a kujerun da aka zagaye gurin suna adu'a Jalal ne yace ”bari a
yanka cake sai 'intafi gida ,momy ko dariya takeyi farinciki fall zuciyarta ,durk'usawa Humaid
yayi ya gaida dady yaje ya gaida momy ya dawo kusada Khadija ya zauna sunci sunsha dan
abinci ma daga hotel aka kawo ,misalin k'arfe biyar dady yacewa Humaid ya d'auki matarshi ya
wuce ,wanan karon dai Khadija batayi kuka ba, sai da sukayi sallahr isha'i sanan suka
d'unguma zuwa gidansu ,hira sukeyi jefi jefi ,da isar su gidan sabon mai gadin da dady 'ya sa
musu ya wangale gate d'in yana yimusu sannu da zuwa ,da shigarsu yai parking a ya fito yana
mai yiwa Allah godiya ,itama fitowa tayi suka nufi cikin gidan ,kowannensu d'auke da sallama a
bakinsu ,da shigarsu parlor suka yada zango Humaid ne ke dariya yana kallon Khadija yace
”baby kingaji ko farr tayi da idonta tace ”yaya mungaji dai cikin sigar tsokana yace ”to gafa
tsaraba na kawo miki dan nasan bakya bata kunya tasowa tayi tazo kusa dashi ta zauna wata
leda ce mai kyau ya ciro mata gasashiyar kaza ,murna takeyi tana godiya Humaid ne yace ”to
yanz mekuma kikeso ,rufe fuska tayi tace ”nakasa tashi d'auko ruwa zansha yana dariya ya
mik'e ya d'auko ruwan ,bayan ta cika cikinta ne humaid yace ”to muje muyi alwala yaukam
'zamuyi nafila a sa'a lol."

Hhh wata nafilar aka kumayi akayi adu'oi sosai daganan 'naga Humaid ya sunkuci Khadija yana
harara ta ,garin gudu har nakusa fad'uwa 'asbha tagari amarya da 'ango.



Bayan komai ya lafa ne na hango Khadija nata kuka tana cuno baki ,Humaid da fitowarshi daga
wanka kenan yace ”haba baby kiyi shiru mana ya marai raice murya kamar mai shirin kuka
,dariyace da kufce mata tace ”kazo ka d'agani 'inka gama tsokanata ,kaya yafara cire mata
sanan ya sunkuceta ya kaita bathroom cikin ruwan wankan daya tara mata wani ihu tasa kamar
wacce ake shirin cirewa rai can anjima ta lumshe ido sabda zafin ruwan ya ragu ,zubarda
wancan yayi yakuma tara wani ,dubanta yayi yace ”to fito inyimiki wanka ,kuka tafara tana yaya
dan Allah kaje ka fitomin da kayan dazansa please zanyi da kaina ,zai juya ya hangota ta
kwanta kamar wacce ta sami katifa cikin bahon wanka ,dawowa yayi ya fara yimata wankan
tana had'ashi da Allah yanayi bai fasa ba."


Nad'ota yayi cikin towel kamar baby hhh ashefa babyn ce ,kwantar da ita yayi a kan gado yafara
shafa mata mai , yana gamawa ya d'auko ta ya zaunar da ita gaban dressing mirror ,itadai ta
koma kamar photo ko magana batayi powder yafara shafa mata dagan an ya d'auko k'wali ya
sanya mata ya d'auko janbaki ya shafa mata hh gurin yin jagira ne yayimata kamar titi
fakaceciya dariya sukasa ,gogewa yai yace ”to ainayi mai wuyar ko kinga inda kikayi kyau kuwa
hmm kamar sarauniyar kyau , to zomuje kisa kaya ko baby ,kuka zata fara yace ”mai yafaru
kuma¿uhm uhm ni yaya bazan iya tafiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0