Showing 18001 words to 21000 words out of 40319 words
wato
hospital d'inshi dan tun dare ake ta yimai waya'akan anason ganinshi ,shi burin shi bai wuce
yaga ya illata Khadija ba ,ita kuma Khadija tak'i fitowa saboda tsoron Humaid ,gajiya yayi da
zama duba 'agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunshi yayi ,k'arfe goma da rabi 10:30 bai fita
ba duk akan wanan shegiyar yarinyar?"yake tambayar kanshi tsaki yaja ya fice zuwa bedroom
d'inshi wanka yayi yana fitowa yaga har sha d'aya tayi 11:am zaro ido yayi ,kamar maijin kashi
,shiri yakeyi jikin gaggawa kamar mai tashi sama da sauri yayi waje gurin motar shi , ya tayar ya
mik'i hanya".
Tanajin fitarshi ta fito da gudu tayi d'akin shi ganin kayayyakin daya siyo tayi zaro ido tayi
tace"shiyasa ko ya nemi abubuwan dana d'ebo tabb aikuwa saina kwashe wa in an ma ,fara
jidowa tayi tana haki ta kwashe kayan abincin dukka harda su carton d'in maltina dana madara
dakuma k'wai duka ta kwashe tana dawowa taga wani kayan ganin jikin kwalin anrubuta
golden ai kawai ta loda takai d'aki a ranta ko tana cewa shikenan 'na huta da girki ko lemon
kwalba ma ya isheni, kitchen taje ta d'auko tukunya da wuk'a dakuma mangyad'a da kayan
miya tadawo d'aki tasa key .
Misalin k'arfe biyar na yamma yadawo a gajiye ya shige toilet ya watsa ruwa yana fitowa kwai
yaji yana sha'awar shan golden beer zuwa inda ya 'ajijiye kayan yayi ganin baiga komai ba
yasashi zaro ido ,cikin kunar 'rai yace "wato wanan tsinanniyar bacin zina har giya takesha?"
zama yayi a bakin gado yadinga girgiza k'afa yana bala'i arayuwa bayason a d'auki abinshi ba'a
tambayeshi ba ,cikin masifa yafice daga d'akin 'nasa yana zage zage kuma ya kudurta 'a ranshi
ko k'ofar zata 6alle yau saiya ci uban Ladidi ,yana zuwa yaji kamar kullum k'ofar a rufe take da
key dukan k'ofar yakeyi kamar mahaukaci amma tak'i bud'ewa itako tana tsoron karfa ya 6allah
k'ofar nan yazo yakusa kasheta dan yau kamar yasha ya bugu,shigewa cikin drower tayi tanata
zaro ido kasancewar akwai gurin sa sak'ata ta ciki kuma tanada zurfi ba lallai mutum ya bud'eta
da garaje ba....✍️✍️✍️.
Mom Islam ce
*LADIDIN K'AUYE*
Funny & love story.
*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*
*NA*
*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*
*MARUBUCIYAR:*
*ZAINABU ABU*
*AND NOW*
*LADIDIN K'AUYE*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Episode:* 27_28
_____Cikin k'arfi ya bigi k'ofar har saida ta bud'e tsayuwa yayi yana maida nunfashi kasancewar
k'ofar bata ra'go bace ,kutsa kai yayi cikin d'akin yana haki yana cewa inakike dan ubanki yau
saina karyaki ,dube dube yakeyi amma ina baiganta ba bud'e toilet yayi nanma bata nan rik'e
k'ugu yayi kamar mace yanason yaga ta inda zata bullo amma inna ko alamun ta baigani ba,
wata muguwar tsawa ya daka, Khadija dake cikin kaya saida ta firgita 'amma dayake tasan tayi
lefi ko k'ok'arin guduwa batayi ba , ficewa yayi da gudu yaje ya d'auko wani key a d'akinshi yazo
ya kulle k'ofar a tunaninshi ta fice yawo ne, yana fita ta fito.daga ma6oyar ta sai gumi take
sharewa ,zuwa gurin kwalayen data d'ibo tayi ganin golden beer dama tasa biyu a fridge ta
bud'e ko karantawa batayi ba ta hau sha jin zak'i zak'i yasata lumshe ido ,tanagama sha ta
wurgar da gwangwanin ."
Luuu tafara gani wata zabura tayi tafara maganganu tanacewa wai naga kamar duniyar tak'ara
haskene tabb naga ta kaina yaukuma gashi goma na dare amma basai ankunna fitillah ba
tafara layi tana surutai ,gyatsa tayi tace"sweet lemu kamar nasha zuma kai firig zonan kabud'e
in k'ara ,ganin dai fridge bashida niyar zuwa yasata mik'ewa tana layi ta bud'e zata d'auka
tafad'i k'asa tana cewa to wane mugunne kuma yake k'ok'arin ganin bayana?"can kuma tasa
dariya tace"ni wallahi nagaji da wannan duniyar kuzo ku kaini duniyar ku.
Jin alamun bud'e k'ofa yasata zubawa da gudu yana bud'e k'ofar yad'n matsa yana so ya
kamota aikuwa ta fice da gudu tayi kitchen tasa sak'ata lokacin tafara dawowa hayyacin ta ,baibi
takan d'akin 'nataba bare yaga 'abinda tasha hannu ya buga'a bango yanacewa kokuma 'ajanun
k'auye sun shafeta ne shiyasa take 6acewa?"can kuma ya mik'e yayi d'akinshi jin ana kiran
sallahr mgrib , bayan yayi alwala ne ya kulle gidan ta baya ya wuce masallaci ,Khadija najin
fitarshi taja jiki tana tafiya tana layi tayi d'aki ,ganin gwangwanin madara yasata bud'ewa ta
saida ta shanyeta tass tukun ta kuma kwanta 'a gurin bacci mai nauyi ya d'auketa ...
Jin wani sanyi mai kamada ruwan k'an k'ara ya tashe daga baccin da takeyi duka taji ko ta ina
tarasa waye mai dukan 'nata ihu takeyi 'iya k'arfinta 'amma innaa bbu halin tashi bud'e
idanuwanta dasukayi mata nauyi tayi ganin Humaid a tsaye kamar wani soja yasata cewa to
Allah ya isarmin mugu kawai buge bakin yayi ya cire bell d'in wandinshi yana dukanta ta ko ina
ganin babu mai ceton ta yasata juye juye tananeman abinda zata buga mai ,ganin babu komai
yasata dai daitar saitin wandonshi ta murd'e gabanshi ta zura da gudu wani wahallalen k'ara
yasa mai wuyar fassara wa yarasa maiyakeji ,jiyayi kanshi na juyawa rike da mararshi ya fad'i
k'asa sumamme, Khadija ko kitchen tanufa ta fere doya ta wanke ta dafata daganan ta soya da
mai tanayi tanacewa kafin ya tashi naci nak'oshi mugu kawai ,tana gamawa ta soya miyar k'wai
kasancewar akwai kayan miya batasha wuyaba seda taci ta k'oshi dak'yar take iya tafiya da
ruwan gora 'a hannunta ta k'arasa d'akin ,ganinshi kwance yarik'e gurinda ta murd'e kumfar
yawu na zuba 'a bakinshi yasata rugawa d'akinshi da gudu cikin tashin hankali wayarshi tagani
a kan gado duba number tahauyi ,ganin doctor Umar yasata danna kira ring d'aya ya d'auka 'a
zatonshi Humaid ne ,jin muryar mace yasashi cewa madam barka dai, cikin firgici Khadija tace
"Umar dan Allah kazo ka duba Humaid dan Allah kayi sauri ko motsi bayayi ,a tsorace Umar
yace " karki damu ganinan zuwa to tace"kawai domin hankalinta yafi na 6arawo tashi.
Ba'a d'au wasu mintuna ba saiga horn d'in motar doctor Umar yana zuwa ya nocking d'aga
murya tayi tace"shigo doctor ,da y'ar jakarshi a rataye ya k'araso yana haki'i tsabar kukan daya
ku6ce mata bata iya magana ba nunamai d'akin da Humaid yake kwance tayi , shigewa yayi da
sallama Doctor Umar ganin halinda Humaid yake ciki yasashi rik'e kai yana cewa innalilahi wa
innailahirraji'un ya Allah help me,idonshi cike da hawaye ya kinkimi Humaid kamar gawa yasa 'a
mota cewa Khadija ta kulle gidan ta biyoshi yayi to kawai ta iya cewa kasancewar gani takeyi
kamar Humaid ya mutu ne."
Rufawa doctor Umar baya tayi dole ta shige gidan gaba saboda 'an kwantar da Humaid a back
side ,tun doctor Umar na hanya yake waya akan a tanadar musu d'akin saboda Humaid babu
lafiya kuma yana buk'atar temakon gaggawa kasancewar hospital d'in akwai nisa saida sukayi
tayi maid'an 'nisa sannan suka iso a keken tura marar lafiya 'aka turashi direct d'akin da 'aka
tanadar musu suka tafi likitoci biyar ne akanshi amma kowa sai share gumi yakeyi ,itako Khadija
sai safa da marwa takeyi a harabar asibitin ,likitoci sun shafe wajen awa 1 hour suna bincike
akan suma samu nunfashin ya tsaya 'abin ya citura sai da suka kuma shafe mintuna talatin
sanan sukayi sa'a ceto rayuwar shi ,ba'amayi batun gurinda 'akayiwa illa ba tukun ganin ya
bud'e ido yasa likitocin cewa Alhamdulilh Allah mun gode maka ,jin ana hamdalah yasa Khadija
saurin k'arasowa tana kuka tana ganin Humaid ya bud'e ido takama dariya tana yiwa Allah
godiya.
Likitocin'ne sukace to yanzu saimu koma kan inda yaketa nunawa tun d'azu a kunyace Khadija
ta fice daga d'akin ganin ana k'ok'arin duba gurin bayan sunyi y'an bincike ne suka gano cewar
yasami matsala 'agurin kuma indai ba fita dashi k'asar waje akayi ba to kafin yayi sex da
matarshi zai iya kaiwa shekarar biyar kokuma k'asa da hakan kasancewar Nigeria basuda
cikkakun kayan aiki,kwanansu hud'u a hospital d'in Doctor Umar shike jigila 'akan kayan abinci
asibiti dai babu bataun biyan kud'in domin mai asibitinne a kwance babu lafiya.
Yaune aka sallamesu Khadija na tsoron gayawa momy halin da 'ake ciki saboda hukuncin dazai
biyo baya ,amma babu inda ta iya dole ta sanar dasu ,tanashirin d'aukar wayane Humaid yace
"karki kira su momy dan wallah natashi saina kusa karyaki ,Khadija ce taja baya ta murgud'a
mai baki tace a hakanne zaka karyani tabb wlh gara kayi a hankali karka famo gurin da
'akayima bandeji hhh, harararta yayi sanin bazai iya tashi ba yasata fad'ar hakan, rugawa tayi
da gudu ta d'auki wayar ta danna number momy ring biyu ta d'auka momy ce tace" my daughter
yakike lafiya tace"cankuma tace momy Humaid babu lafiya fa momy ce tace"maiya sameshi ?
Shiru tayi can kuma tace" fad'uwa yayi a toilet momy ce tace"to yaji ciwo ne?eh Khadija
tace"dan yanzuma 'a kawance yake kwananmu hud'u a asibiti shine yace"wai karna fad'a
muku,momy ce tace"to gamunan zuwa 'Allah yakawoku lafiya Khadija tace"daganan ta shige
bedroom d'inta ta kwaso kayan abincin datakai can tana cikin kwasowa ne hankalinta yakai kan
kwalin golden beer d'inda tasha tana karantawa tahau salati ,can kuma tayi gumm da bakinta
mayar da kwalin golden beer d'akin Humaid tayi ta tura 'a k'ark'ashin gado sauran kuma takai
kitchen ,wanka tashiga tayi kwaliya kamar maishirin fita anguwa ,shidai Humaid na parlor
magana ma ta isheshi ....✍️✍️✍️.
Mom Islam ce
*LADIDIN K'AUYE*
Funny & love story.
*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*
*NA*
*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*
*MARUBUCIYAR:*
*ZAINABU ABU*
*AND NOW*
*LADIDIN K'AUYE*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Episode:* 29_30
_____Momy ce ita da dady suketa sallama cikin sassanyar murya Humaid
yace"wa'alaikumussalam shifowa sukayi ,ganin Humaid ya mugun ramewa yasa momy
k'araswa kusada shi da sauri tace"my son maiya faru dakai naga ka koma haka ?"cewa yayi
momy babu komai kwai banida lafiya ne dady daya saki baki yace"to ai Khadija tace "mana
zamewa kayi ?" shiru yayi yana tunanin k'arya irinta Khadija cewa yayi eh hakane kasancewar
inya fad'a musu halinda suke ciki zai 'iya fuskantar matsala dukda ciwon dayake damunshi ,
Allah yabada lafiya sukace daganan saiga Khadija ta fito sake baki momy tayi ganin wata uwar
'rama da Khadija tayi amma taja bakinta tayi shiru ,rungume momy Khadija tayi tana murmushi
tace "momy na kinzo lafiya ?dady ne yace" to gani a gefe tunda 'an manta dani rufe fuska tayi
tace"dady afuwan kunzo lafiya cikin farinciki dady 'yace"lafiya yamai jikin ? dasauk'i tace
"cankuma ta shiga damuwa momy ce taga 'alamun fuskarta tace" lafiya Khadija??" fashewa da
kuka tayi shidai Humaid na gefe ido ne nashi ,tsagaita kukan tayi kana tace "momy matsala
Yaya Humaid yasamu momy ta bud'e baki tace" a ina?shiru tayi can kuma tace"kuma doctors
sunce sai an fitar dashi waje!!! jin wanan kalmar ta k'arshe ya girgiza su momy sukace to
matsala yasamu a brain d'inshi?a'a tace" tashi tayi taje ta d'auko file d'in asibitin mik'awa momy
tayi ,momy na kar6a ta mik'awa dady Humaid ko dariyace taso kufcemasa wai takasa fad'ar
abinda yasameshi hhh,dady na dubawa yace"innalilahi oh Allah momy ce tace"maiya faru ne
?dady daya had'a zufa ba kud'in fita k'asar wajenne damuwar shi ba larurar Humaid d'ince
damuwar shi ,dady ne yagawa momy komai dagan suka fara jinjina lamarin.
Dady ne yace ”Allah yakaimu gobe ,dady ne yakira waya airport saboda 'ayimusu tanadin jirgi ,
yayi sa'a zasu samu na k'arfe 4pm zasubi , dady ne yace ”maganar hospital d'in babu matsala
wuyarshi Allah ya kaiku lafiya ,Khadija ce tace ”dady nidai bazanje ba momy ce tamaida
dubanta ga Khadija tace ”to ko maiyasa bazaki ba Khadija? "shiru tayi ta sunkuyar dakai ,tana
wasada fingers d'inta ,momy ce tace ”aikuwa tafiya dake dole kece matarsa mukuma daga baya
zamu biyoku anjima zan sa driver yakawo miki waya saboda gaisawa ,to kawai tace” saboda
musu ba halinta bane mik'ewa sukayi suna yiwa Humaid Allah yak'ara lafiya 'amen kawai
yace”daganan suka fice ,mita tashiga yi tana cewa mutum bai damu dakaiba baidamu da
damuwarka ba baisan darajar kaba 'amma kaje kayimai jinya daga baya 'yazo ya
wulak'antaka,shidai Humaid na jinta bashida lokacin bata 'amsa kasancewar shi ta ciwon jikinshi
yakeyi ,wurgamai harara tayi daganan takuma cewa wallahi mukaje ka walak'antani saina k'ara
janyo wani jan aikin tunda mutum cin zali yayimai yawa ,zaro ido yayi kuma yana mamakin wai
yatsaya wanan shegiyar yarinyar tana gayamai maganganu baid'au mataki ba ,tunawa yayi sai
an temakamai zai 'iya tashi k'wafa yayi ya maida kai ya kwanta 'akan kujerar bud'e baki Khadija
tayi tace ”da dukana zakayi ahayye ni Dije wallahi kama sameni ne da lokacin da nake garinmu
ne tabb dakadinga yimin ladabi dan bana d'aukar 'raini, Humaid maganganun Khadija sun
6atamai rai sosai amma da yanada lafiya babu abinda zaihana ya hukuntata, amma 'akwai
lokaci ."
Komawa d'aki tayi tafara had'a kayanta dakuma 'abubuwan dazata buk'ata kitchen ta wuce ta
d'ebo naman kaza 'a fridge ta sa kayan k'amshi dasu atta ruhu ta tafasa naman yana dahuwa
ta d'auko turmi tafara dakawa da 'alamu dambun 'nama zatayi bayan tagama ne tahau suya
rana gama suya ta d'ibo dakkaken yaji ta zuba 'a roba takai jakar tafiya , d'akin Humaid ta nufa
tana duba kaya tana dariya gajerun wanduna ta d'ibar mai sunkai guda ishirin sai t sheet guda
goma ,nikwa nace to ina manyan kayan ?" golden beer d'inshi ta d'iba har guda biyar tasa 'a
jakarshi ,saikuma man shafawa dakuma takalmanshi tana gamawa ta fice ta nufi d'akinta .
Washe gari misalin k'arfe 9am saiga driver da abincin karyawa dakuma kwalin waya ,tana rawar
jiki suka gaisa mik'a mata sak'on yayi godiya tayimai tashige ciki da gudu ,ganin babu Humaid
yasata rik'e baki tace ”toshi harya sami sauk'i ne?"batada mai amsa mata tambayarta yasata yin
shiru ,tafara duba wayar spark 2 ce maikayau sosai bud'e abincin tayi ganin soyayyen dankali
dakuma wainar k'wai a gefe yasata kwashe k'wan tabar dankalin a dining, komawa d'aki tayi
tacigaba da shiri wnka tayi ta fifito da kayan data d'ibar musu komawa tayi hanyar d'akin
Humaid tana shiga ta hangoshi rik'e da waya 'a hannu da 'alamu charting yakeyi ,girgixa kai tayi
tafara cewa lallai to ai basai anje Indian ba tunda kaji sauk'i barin cewa su momy wai abarshi
,da mamaki yake kallonta dubanta yayi 'irin kallon kinrainani d'inan yace”wallah zan 6a66allaki
wucemin anan dan ke bata yimiki amfani shine zakimin mugunta ko muguwa kawai dariya tasa
tace”kai kadamu da iskanci nikam Allah ya sitiri buk'wai ,shiru yayi ganin raini zai shiga tsakani
,k'arawa gaba tayi tace ”daya d'auka ni yar iska ce ,hmm to ma wai da dayakecemin mazinaciya
menene amsar hakan?tana yiwa kanta tambayoyi can kuma tace ”ok natuna lokacin da Ammar
ya saceni shine yake zargin 'nice naje d'akinshi?rasa maibata 'amsa tayi hakan yasa takoma
d'akinta tana saka sim card a wayar ta memo ta d'auko wanda tayi seven number k'awayenta
dakuma ta momy saka numbobin tashiga yi tana murna."
Da misalin k'arfe 3:dai dai dady 'yakira Khadija kasancewar sund'au number tata tana d'agawa
dady yace”to inkun kammalah gamu nan a hanyar zuwa airport ku hanzarto angama komai tun
jiya to tace”gamunan zuwa dady ,zuwa d'akin Humaid tayi tace ”kafito gasu dady can a hanyar
airport mik'ewa yayi jiki babu k'wari yace ina kayana?cewa tayi gasunan a jaka bud'e gurin
kayan 'nashi yayi yakuma lodar 'rigada wando kamar yasan bata d'ibarmai ba ,cemata yayi bar
'rawar jiki dan kona sami lafiya 'aure zan k'ara ,Khadija ce tace ”a hakan da babu k'arfin jikin
kana tafiya kamar mace,zaro ido yayi yace"wlh zanci ubanki shigewa tayi tarabu dashi tasandai
koba komai ta gasamai magana.
Shigewa mota sukayi sun d'anyi tafiya sanan suka iso airport d'in samunsu momy sukayi a
zaune suna jiransu k'arasawa gurinsu sukayi suka durk'usa suna gaisuwa Humaid dak'yar ya
mik'e itako Khadija dariya takeyi k'asa k'asa jin lokacin tafiyarsu yayi yasa momy yimusu fatan
'nasara ta mik'awa Khadija wani babban jaka mai zurfi ,dady ne yace ”nayima transfer na kud'i
bakada matsalar su godiya yayiwa dady daganan suka shige jirgi ,hawaye Khadija tafara
shareware saboda tasan momy ma dauriya kwai takeyi ,jin tashin jirgin yasata rik'o Humaid ta
matseshi tsaki yaja yace ”dalla ni karki sakamin k'azamin jikinki banza kawai ko kulashi batayi
ba tacigaba da rik'eshi ,shikuwa bashida k'arfin kokawa yasa ya k'yaleta....✍️✍️✍️.
Mom Islam ce
*LADIDIN K'AUYE*
Funny & love story.
*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*
*NA*
*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*
*MARUBUCIYAR:*
*ZAINABU ABU*
*AND NOW*
*LADIDIN K'AUYE*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Episode:* 31_32
_____Suna sauka cikin ikon Allah saiga wani bature yazo yake cemusu ance yanuna musu
masaukin su Humaid saboda rashin yarda yace "saiya kira dady aikuwa yana kira dady
'yace”nine na turoshi dafatan kun sauka lafiya ?lafiya Lou Humaid yace”daganan suka shige
motar wanan bature ,itadai Khadija gajiyace ta