Showing 21001 words to 24000 words out of 40319 words

Chapter 8 - Ladidin Kauye Hausa Book Compelet

15 Aug 2026

613

buwaye ta dan burin ta bai wuce taganta tana
hutawa ba ,wani katafaren hotel suka sauka Khadija ce tazaro ido tace"nifa tsoron jajayen fata
nakeyi wallahi kar azo angama cinikinmu, Humaid ne ya gimtse dariyar sa shikuwa wanan
Bature babu abinda baijiba wanada Khadija tafad'a kasancewar yana mu a mula musulmai
sosai amma shi Christen ne saboda baya sallah ,door bell baturen ya danna k'ofar ta bud'e da
kanta zaro ido Khadija tayi tace”to Allah gamu gareka tana tafiya tana sambatu shikuwa Humaid
ko kallonta baiyi ba ,direct wani rantsatsen step naga sun hau d'aki mai number goma suka
shiga ,Humaid ganin ba'ayi maganar komai ga shuwagabanin hotel d'inba yasashi cewa to
sukuma masu hotel d'in anbiya sune?eh baturen yace”tun jiya dadynku yayi komai ,godiya
Humaid yayimai mutumin 'ne yace”sunanan Joseph barin baka number ta musayar lamba
sukayi daganan Joseph yace”suyi wanka su huta za'a kawo musu abinci .


Tana shiga d'akin Humaid ma yashigo tunda tashigo take kallon d'akin kyau tsari gakuma
nerorin da 'aka kashemai tabb tace ”lallai wasu basusan zafin kud'i ba ,Humaid da gajiya ta
tarumai yace”to sannu 'uwarsu zaki 'iya fita ki sanar musu ,ko kallon inda yake batayi ba tashige
bathroom wanka tafarayi kasancewar akwai sabon sabulun wanka da sabbin brush da man
goge baki saida tayi wanka sanan ta d'auro alwalah tafito ganin har bacci yafara d'aukar
Humaid yasata kurma uban ihu tace”wayoo nashiga uku ,a firgice Humaid ya farka yana salati
ganin Khadija tayi shuru yasashi cewa komai aka had'a da jaki saiyyaci kara ,zaro ido tayi
tace”waye jakin nikake kira da jaki, murmushin takaici tayi tace ”d'an adam mai mance hallacci
babu komai kasan ba'acin bashina ,mamakinta yakeyi dahar take gayamai maganganu san
ranta saboda taganshi a kwance bazai 'iya 'aikin k'arfi ba yasa takeyimai wulak'anci ,dariya
yasa lokaci d'aya kuma yace”yaro baisan wutaba saiya taka."

K'yaleshi tayi tafara sallah tana idarwa ta dubo al qur'anin data taho dashi tafara rera karatu ,
idon Humaid a lumshe kamar mai bacci ya bud'e ido yana saurarrar karatun Khadija jiyakeyi
kamar karta dena ,bayan takammala karatunne ta mik'e tayi gurin kayansu bud'e jakarta tayi ta
dubo atamfa rigada skirt mai adon flowers green zatasa kayan ta tuna 'aifa Humaid na d'akin
juyawa tayi tace ”malam zaka iya juyawa saboda zansa kaya karkuma 'a kalleni ehe, juyowa
Humaid yayi yace”wanan banzan jikin'naki mezan kallah jikinda kowa yagama ganinsa ,tanajin
takaicin wanan kalmar amma 'akwai lokacin ramako, d'ibar kayan tayi takoma bathroom ta
sanya sanan tazo tana shafa mai kasancewar garin da zafi kuma dukda sanyin AC mutum
gumi yakeyi ,kwaliyarta tayi a nitse sanan wuce dining table d'inda 'aka kawomusu abinci ganin
cimar kamar ba irin tata ba yasa ta had'e fuska tana rik'e ciki ,hango wayar tafida gidanka tayi
ganin 'number su a calendar yasata d'auka cewa tayi nifa bazan iyacin wanan jagwal gwalon ba
'akawomin tuwo kokuma indomie mutumin da baigane maitake cewa ba yace ” give me one
minute please am coming zaro ido tayi tace ”tabb 'banza shima turancin bai gama bakinsa bba."


Humaid daketa dariya yana k'arawa yace”LADIDIN KAUYE y'an mata had'e rai tayi tace”wallahi
kabari dan banhuce na d'azu ba, shiru yayi dan yasan komaiye ma zata rina 'aikatawa ,nocking
aka farayi Humaid ne ya lala6a ya mik'e saikuma ya tsaya yace ”saikije kiyimai bayani,Khadija
ce tace”bagane nawa turancin zaiyi ba dan 'naga shima koyo yakeyi yanzu hakama brain d'ina
tafi tashi ,wucewa kawai Humaid yayi ya bud'e k'ofar mutumin 'ne d'auke da farantin abinci
bud'ewa yayi yaga indomie ne aciki godiya yayiwa mutumin daganan yasauka k'asa da tiren
abincin samun guri yayi yafara loda indomie saida ya cinye duka sanan ya tashi yabar plet d'in
agurin yakoma sama.



Samunta yayi ta rafka uban tagumi tana kuka ko kallon gunda take baiyi ba bare tasanma
yaganta taji dad'in 'narkewa bathroom ya wuce yayi alwala yazo ya gabatar da sallah tunda yayi
sallama yaketa jero adu'a 'akan Allah yabashi lafiya ,itadai Khadija tarasa meke yimata dad'i a
duniya kasancewar bata ragawa ciki ko kad'an mik'ewa tayi taduba maid'an dama dama tafara
tuturawa badan yayi mata ba tana gamaci ta d'auki waya takirawo momy cikin farinciki momy
tace” daughter dafatan kuna lafiya dai ko?eh muna lafiya Lou "amma momy 'yaushe
zakuzo?momy tana murmushi tace”gobe ne insha Allah muna zuwa zamu wuce hospital amma
zaku rigamu wucewa,to kawai tace shikuwa Humaid dama can magana ba damunshi tayiba,
daganan sukayi sallama da momy.


Dare nayi basuci wani abinci mai nauyi ba ,Humaid na k'ok'arin hayewa gadon tarigashi
,hak'ura yayi ya koma k'asa ya shinfid'a bargo ya kwanta .



Washe gari bayan sunyi sallahr ashba babu wanda ya koma shirin tafiya 'asibiti sukeyi bayan

Humaid ya fito daga wanka yaduba jakarda Khadija, ta lodamai kaya 'acikin ganin gajerun
wanduna yasashi salati yace”wato kinmaidani d'an iska kenan ko ?cigaba tayi da kwaliyarta
daganan ta mik'e tana cewa to inka shirya nizan wuce ,Humaid ne yace”kin dad'e baki wuce ba
banza kawai jibeta 'ahaka kamar saliha ,shiru tayi saboda batason wanan kalmomin da yake
jifanta dashi amma burinta lokacin yazo .


Yana gama shirin ya fice ko magana baiyi mataba jitayi yana kiran Joseph a waya dagudu ta fito
tana tsaki ,ganin Humaid yashige mota yasata bud'ewa tashige da sauri wani katafaren hospital
suka nufa suna sauka koshi Humaid ' d'in saida ya jinjina kyau irinna asibitin suna zuwa 'aka
tarbesu office suka wuce domin ganin babban likitan suna shiga sukaci karo da wani mutumin
farine dogo yanada jiki amma ba sosai ba yanada bak'in gashi dakuma gashin baki wanda
yafito da tsananin kyawunshi ,kallon Humaid yakeyi kallon a ina nata6a ganinka Humaid ne
yace ”aslamu alaikum mutuminne ya mik'awa Humaid hannu cankuma mutumin yace”naso
nasanka koba kaine Humaid Abdullahi ba ?gingina kai Humaid yayi yace ”nine nima kamar
nata6a ganinka 'a lokacin da zamu bud'e hospital d'inmu ,tunani mutumin yayi cankuma yace”ai
dadynka abokina ne sosai kuma yayimin bayanin komai toya jikinnaka dasauk'i Humaid yace
”daganan yafara yimai tambayoyi."


Doctor d'inne yakai dubanshi ga Khadija yace” wanan iyalinka ce? a'a Humaid yace”.
K'anwata ce OK doctor yace ” please zaki iya bamu guri akwai wata magana danakeso muyi
maganar ta doki Khadija to kwai tace tafice daga office d'in ,tasami guri ta zauna tana zuba
uban tagumi ✍️✍️✍️.






Mom Islam ce



*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*

*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 33_34




_____Zuciyarta na k'una tarasa maike yimata dad'i amma babu komai ,doctor ne yakai
dubanshi ga Humaid yace” yakamata kasani akwai aikin dazamuyi maka kuma yana buk'atar
nutsuwarka gaskiya ko kanada mata saidai tayi hak'uri har na tsawo one month kasancewar
aikin 'na buk'atar kulawa ,cikin farinciki Humaid yace” doctor ashe zan warke daganan suka fito
doctor yanunamai d'akin dazai shiga ,batare da yayiwa Khadija magana ba yashige d'akin yana
murmushi 'itako Khadija dataga batada muhimmanci yasata komawa masaukin su zama tayi
tadinga rusa kuka kamar wace akayiwa mutuwa ,had'a kayanta tashiga yi tana surutai da alamu
ranta ya 6aci sosai ATM d'inshi ta d'auka ta d'auki jakarta tayi waje ,rasa ina zatayi tayi zuciyarta
ce take cemata ki koma Nigeria kawai ,hakan ko akayi ta d'auki shawarar zuciyar ta ,mutumin
dake jigila dasu wato Joseph shi ta kirawo a waya tacemai dan Allah yazo ya kaita airport
,cemata yayi aisu alhaji suna hanya mezatai a Nigeria ,cikin zak'uwa tace ” fils na maganin
Humaid aka manta kuma dole saidasu za'ayimai aikin , cemata yayi to bari yakirawo y'an airport
d'in yaji ko jirgin 'Nigeria ya tashi, to tacemai dan burinta taganta 'a k'asarta yana kira yacemata
nanda 30 minutes sasu tashi ,cikin hanzari taje ta tarkato kayaanta tafito ta kullo d'akin ,barin
keys d'in tayi a hotel d'in suka wuce filin jirgi 'itada Joseph ,lokacin da suka isa 'ana kiran Nigeria
dagudu tashige kasancewar yanzu harkar Bank akeyi tabiya kud'in komai .

Duba lokaci tayi a ’agogon dake d'aure a hannunta k'arfe 10:23am jin jirgin zai tashi yasata yin
adu'a can kuma taji hawaye tafara cewa kuyi hak'uri momy ba'asan raina nadawo ba 'amma
babu inda na iya saboda bak'incikin da Humaid ke k'unsamin bayan wasu mintuna ta jirgi ya
sauka murna dakuma danasani fall cikin Khadija saboda tana ganin kamar batayiwa su momy
adalci ba ,tana sauka tacire sim card d'inta tasai wani wanan kuma tasa 'a jakarta direct gidansu
ta wuce wato gidan Humaid ganin mai gadi nanan yasata farinciki nocking tayi had'e da sallama
cikin gaggawa mai gadin ya bud'e mata yana cewa hajiya sannunku da dawowa ywwa
tace”tashige ciki mai gadin mamaki yafara to ina Humaid d'in??tabb 'bashida mai bashi amsa
yasa shi yin shiru, da k'atuwar jaka tafito saboda ta d'ibo kayan abinci su katan d'in indomie
dakuma su Maggi star da mangyad'a duka ta loda 'a jakar ,mai gadi naganinta da d'irmemiyar
jaka yasashi zaro ido amma babu batun magana ,ficewa tayi batare datace ga inada zataje ba ,
bank taje taciro kud'i masu ywwa daganan ta dawo gida ,maida jakar tayi tana haki .



*ACAN INDIA*?


Tunda momy suka sauka take gwada number Khadija shiru a kashe ,dady ne yakira Joseph
yace”yakaisu hotel d'in da Khadija suka kama d'aki acan ,Joseph da jikinshi yafara sanyi
yacewa su dady wanan madam d'in yau tatafi Nigeria, what!!! Dady 'yace”cikin kid'ima ya 'akayi
hakan tafaru maikuma yafaru momy da batada wuyar kuka tace”wallahi Humaid ne sanadi
dama ba sonta yakeyi ba shine ko rayuwarta ta salwanta bashida matsala ko tana kuka tana
magana ,dady ne yace” Joseph muwuce hospital d'in kawai ,mota suka shige suka nufi asibitin
da isarsu sunyi sa'a wanan doctorn yanan office d'inshi suka wuce bayan sun gaisa ne sukace
ya mara lafiyar yake dasauk'i doctor yabasu amma tare da shada musu d'azu akayi aikin kuma
'akwai alamun nasara masha Allah sukace yanzu ina yake?doctor ne yace” yana room 3 ,
amma naga bank'ara ganin sister nashi dasukazo d'azu ba ,lokacinne momy tace”matarshi ce
doctor ne yace”amma shine yacemin ba iyalinshi ba ,dadyne ya mik'e suka fito dasu momy
dakuma doctor room d'in aka nuna musu suka shige."





Ganinshi kwance yana bacci yasa dady dka mai tsawa yace ”ina kakai Khadija?? "arazane ya
tashi yace”dady 'yaushe kuka iso ?babu wanda ya kulashi dan haka yayi shiru ,can kuma
yace”ai takoma hotel ,dady dayaga Humaid nason raina masa hankali yace ”hotel d'in ubanka
!!!...

Momy ce tace ”nidai yanzu damuwata number Khadija kuma gashi a kashe kiran number Jalal
sukayi yana gurin aiki yace”bai gantaba rasa yazasuyi sukayi saboda halin marainiyar Allah, ...




Haka sukayi kwana uku a daddafe duk a tunaninsu Khadija tana gidanta ,a kwana na biyar ne
aka sallame su kasancewar Humaid yaji sauk'i sosai gobe zasu dawo Nigeria tunda suka koma
hotel d'in Humaid yashiga damuwa dan yasan indai ba'aga Khadija ba to shima ya 6ata dan
wallahi saisu momy suncimai mutunci fiyeda tunani, washe sukayi shrin zuwa Nigeria ,jirgin safe
sukabi .


*NIGERIA*
Sun sauka lafiya daga saukarsu gidan Humaid suka wuce maigadi ne yace”hajiya fa jiya tabar
gidannan saboda naga ta loda kaya 'a wata k'atuwar jaka tashiga motar ta ko magana batayiba
ta shige ,momy ce tazaro ido tace”yanzu fargabar da Khadija take jefamu yayi kenan ?" Dady
cikin k'unar 'rai yace”kai kuzo muwuce duk inda zataje taje zamatadawo da k'afarta momy na
kuka tana kiran sunan Khadija gashi wayarta bata shiga ,Humaid kam yakasa magana dan
yasan kad'an suke jira sufara balbaleshi da masifa 'a motar Humaid suka wuce can anguwarsu
momy suna sauka Jalal na shigowa yana ganinsu yace”ina Khadija fa momy ce tashige ciki da
'alamu kukanne zai ku6ce mata shikuwa dady cewa yayi ta 6ata ,Jalal daya tsaya kamar gunki
yarasa takamai man amsa yace ”to nikam yaya Humaid ina Khadija? "wani mugun kallo Humaid
yayiwa Jalal daganan yashige ciki.





Damuwa iya damuwa sun shiga sosai amma shi Humaid bai damu sosai ba kasancewar ba
damuwarshi bace ,dady dayaga abin babba ne dan yau da dawowarsu kwana uku yacewa su
momy su shirya suje k'auye ko tana can ,momy batayi wata kwaliya sosai ba ta fito suka wuce
itada dady ...


Da isarsu malam Adamu yafara yimusu lale marhabun shigewa gidan sukayi suka sami 'inna
tana zaune tayi k'wad'on rama ,zubo musu tayi aka kawo musu ruwa mai sanyi na randar k'asa
,malam Adamu ne yace”ina zuwa can anjima saigashi yadawo da k'waryar fura da nono
dakuma ludaya ,zuzubawa su momy akayi bayan sunci sun k'oshi sukace dama 'abinda
yakawomu shine mund'auka Khadija tazo nanne?"inna dake cin rama tace”walhi rabona da ita
tunda 'akayi bikinsu nikam mukuma bamu k'ara wai wayarku ba malam Adamu ne yace”to yar

marainiyar Allah ina tashiga momy ce tace”har wayarta sun gwada amma 'a kashe ,shirin
komawa sukayi dady 'yabawa malam Adamu dubu hamsin sukayi gaba,godiya su inna suka
dinga jerowa suka yimusu rakiya,har zuwa gurinda sukayi parking d'in motarsu.



Dady 'yana tuk'i yana tunani anya ba wani abin Humaid yayiwa Khadija ba dan sunsan halinta
batada son zuciya ,momy ma 'a tata zuciyar tunani takeyi kodai Humaid ya cusa mata wani
mugun abunne yasata guduwa ,har suka bar garin babu maiyiwa wani magana,da isarsu jos
suka wuce gidan TV da gidan redio domin bada sanarwa ko 6ata tayi ...✍️✍️✍️.



Mom Islam ce

*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 35_36




_____Daganan sukayi gida jiki babu k'wari kowa ya sauka 6atan Khadija yazame musu tamakar
mutuwa tayi ,dady ne yakira Humaid a waya yake cemai maza _maza yazo yanason ganinshi
,gaban Humaid na fad'uwa ya shigo gidan bayan yayi parking d'in motarshi ne ya shiga parlor
ganin babu kowa yasashi wucewa d'akin dady ,samun dady 'yayi a kishingid'e kamar mai bacci,
da sallama ya shiga yanemi guri ya zauna zaice ina wuni dady, _dady 'yace”bana buk'atar
gaisuwar ka saboda yanzu batada 'amfani kuma wallahi kaje ka nemomin Khadija duk inda
tashiga kokuwa kayi danasani a rayuwarka ,gumi ne yafar a keto mai tako ina yace”dady nimafa
wallahi...wani azabbaben mari dayaji saida ya mik'e yana shirin bigewa da bango ,ficewa yayi
daga gidan yana gunguni ,shima Humaid d'in gidan TV da gidan redio ya nufa yabada cigiya
daganan yakoma gida yana 'adu'oi akan Allah ya baiyyana ta yafita daga masifar da iyayenshi
suka kirari ,yaukam hankalinshi ya tashi sosai ganin fushin dady ba k'aramin tsorata yayi ba .


Washe gari ko gigin zuwa gidansu baiyi ba kasancewar bayason jin kalmomin da zasu
hargitsamai k'wak'walwa , gashi yau saura sati d'aya ciwon jikinshi ta warke ,kuma yanada burin
yin aure domin 6arje sabon shafi ,amma baisan wazai tunkara da maganar ba tunda wanan
muguwar ta gudu ai ta jazamai fitina ,kwata_kwata bashida kwanciyar hankali kamar shine
marar gata 'a duniya 'amma yasan mafita k'auye ya nufa gidansu malam Adamu yana shiga
yasamesu suna ,zaune shida inna bayan ya gaishesu ne yake yimusu jajen 6atan Khadija
,malam Adamu ne yace”yau kimanin sati uku kenan Allah yasa tana raye ,amen yace ”can
kuma yace”dan Allah baba inaneman wata 'alfarma ne ,babane ya maida hankalinsa ga Humaid
yace” inajinka yaron kirki maiya faru ?"sunkuyar da kai Humaid yayi yace” baba sonakeyi nayi
aure kafin Allah ya baiyyana Khadija muci gaba dayi mata 'adu'a."




Jinjina kai malam Adamu yayi saboda lamarin babu dad'i wato shi ta 'aure ma yakeyi ,cankuma
yace” karka damu yarona yaushe iyayen ita yarinyar sukace ka turo ?"cikin rawar jiki Humaid
yace” ranar juma'a ne ,malam Adamu ne yayi lissafi yace” saura kwana hud'u kenan to insha
Allah zanzo kuma kafin inzo zankira mahaifinnaka muyi magana ta waya ,inna ko sai jinjina kai
takeyi tana tuno Khadija, godiya Humaid yayi tsabar farinciki bandir d'in y'an dubu ya 'ajiye
masa yana komawa mota ,yakira budurwar tashi saida sukayi hira sosai sanan sukayi sallama ,
ya mik'i hanya tafiya yakeyi cikin farinciki da nishad'i saboda yakusa zama 'ango hhhh...

Tunda yakoma gida ya kirawo masu decorection d'in gida gyra 'aka yiwa gidan kasancewar
yarinyar y'ar manya ce shiyasa yakeson shima 'asan d'an manya ne ,part d'inta na can gefe
gaban d'akin Khadija kayan Khadija kuma 'yadawo dasu k'asa 'amarya takoma sama ,kwana
uku da magana ,dama Humaid ko k'ok'arin dosar gidan baiyi ba ,momy dajin zancen auran
Humaid batace uffan ba haka shima dady 'yace” babu hannunshi ,malam adamu ne sukaje
gidan surukan shida Humaid shikuma Humaid ya wuce gurin budurwar sa mai suna khairat
,hira sukeyi cikin so da k'auna dama irinta ya dad'e yana nema wato mai budadd'en ido
,ruk'omai hannu tayi tace”zomuje zagayeshi tadingayi da girma dakuma shuke shuken gidan
suna rik'e da hannun juna....


Malam Adamu na fitowa ya koma can gidansu dady baisami dady a d'akinshiba yasa ya danna
number Humaid, yana d'agawa malam Adamu yace” to kazo anyanke magana ,cikin azama
Humaid yabaro gidan yayo gidan su ,samun malam Adamu dayayi shi kad'ai yaji dad'i sosai
,malam adamu ne yace” sun yake dukiyar aure nabada cikin kud'in da kabani d'azu to ansa biki
sati uku masu zuwa ,godiya Humaid yaketa yimai daganan malam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0