Showing 30001 words to 33000 words out of 55173 words
Chapter 11 - Auren Bazata Book Compelet Zainab Yakasai Shukra
Shukra har tayi mata tayin Aiki
cikin Asibitin, Shukra ta mata bayani kan cewa ita bakuwa ce a San Fancisco Aiki ne ya kawo
mijinta, Sun dan taba hira kadan Sukayi Exchanging phone number daga nn sukayi Sallama
Suka bar Asibitin "
" Koda Suka bar Asibitin ba gida Suka wuce ba Saida suka ce Bitch suka yi kalle kallensu
sannan suka dawo gida da niyyar gobe zasuje San Fancisco state zoological garden "
" Koda Suka dawo Gidan Sallar isha kawae sukayi kasan cewar sunyi Magrib nan cikin Asibiti,
Kwanciya Shukra tayi bacci me dadi ya dauketa, Shi kuma Safeer sai da Suka dade da Ahmad
a Parlour suna magana kan Company kafin sukayi sallama kowa ya shige dakinsu "
" Bayan Safeer yayi shirin bacci ne ya kwanta kusa da Shukra yana ta binta da kallo kamar me
Shirin gano wani abu a tare da ita, Kawai gani yayi ta kara haske tayi wani kyau, Idan har
idonsa be masa karya ba ze iya cewa Shukra tayi kiba, To ko weather garin ta karbeta ne "
" Matsawa yayi sosai ya Rungumeta a jikinsa yana shafa ta sai yaji jikinta yayi santsi kamar jikin
jariri, Ransa yana basa wani abu sai kawai ya share, Yana addu 'ar Allah yasa hasashensa ya
zama gaskiya A haka dae bacci ya kwashe shi "
" Washe gari gurin sha daya bayan sun gama breakfast ne suka shirya sai Zoological Garden,
Sosai gurin yayi wa Shukra kyau dan ko kusa bazaka hadasu da na Kano ba don iya shi ta taba
zuwa "
" Riko Hannun Safeer Shukra tayi lokacin da Zuwa zo Gurin lion, Yana ganin su ya fara ihu
yana tsalle kamar yana son fito, Shukra ta kankame Safeer a jikinta ta fasa masa kuka jikinta
har wani rawa yake ta tsorata iya tsorata har bata iya jin abinda Safeer din ke ce mata "
" Sun dau Tsawon lokaci a haka Safeer sai shafa bayanta yake yana bata hakuri a Ransa kuma
yana tunanin wannan irin tsoro na Shukra "
" Shukrah ce ta fara dagowa daga jikin Safeer ta kalle shi tana goge hawayen fuskarta
"Ya Safeer mu tafi gida Zazzabi nakeji"
"Sannu Shukra bari su Ahmad su Dawo sun dan za gaya can ne ya fada yana jan hannunta
suka zauna "
" Riko shi tayi sosai don har yanzu a tsorace take Shima ganin hakan yasa shi Kwantar da ita
kan kirjinsa yana buga bayanta a hankali, A haka su Ahmad suka dawo suka samesu inda
Safeer yayi musu bayanin komai, Nan dae suka koma gida"
"Shukrah ce ta fara shiga gidan ta kwanta nan palour ta rufe idonta, A tare suka shigo
dukkansu, Ahmad da Azeeza suka shige dakinsu Safeer kuma ya dauki Shukra cak ya kai daki
ya kwantar "
" Sai wajen 3:20pm Shukra ta farka duk jikinta ba dadi ga Zazzabi ta rasa inda zatasa kanta taji
dadi kawae sai tasaka kuka, Safeer yana toilet yajiyo kukan Shukra ya fito da Saurin sa ya
hawo kan gadon inda take "
" Shukrah tayi Saurin fadawa jikinsa ya kankameshi kamar zata shiga cikin sa, Nan yaji jikinta
yayi zafi sosai abin ya bashi tsoro, Yayi Saurin kwantar da ita ya fice daga dakin "
" Azeeza kadai ya samu a Parlour yayi mata bayanin komai, Nan ta mike da sauri takira Ahmad
suka je inda Shukra, Azeeza jin yadda jikin Shukra yayi zafi yasa ta fashe da kuka, abinda ya
daga hankalin Safeer "
" Da Hanzari Ahmad ya dauko car key dinsa Safeer ya dauko Shukra bayan Azeeza ta sa mata
Hijab Suka wuce Asibiti "
" Suna zuwa Aka karbe ta, Bayan test test da akayi Doctor tayi musu babban Albishir cewa
Shukra nada ciki har na wata Biyu "
" Zo kuga murna gun Safeer kai bama shi kadai ba harda Azeeza da Ahmad tunda su basu taba
haihuwa kuma sun dau Safeer da Shukrah tamkar yan uwansu wannan ne yasasu jin kamar su
za ayi wa haihuwar "
" Sai ba adi salatul Magrib sannan suka baro hospital kuma Alhamdulillahi jikin Shukra yayi
sauki sai dai rashin kwarin jiki kawai "
" Sosai Shukra ke samu gata gun Ahmad, Safeer da Azeeza, Don Azeeza ta hana tayin komai
cikin gidan har ruwan wanka ita ke hada mata da kanta "
" Kayan baby kuwa abin ba a cewa komai don kullum Ahmad ya fita sai ya siyo su hakama
Safeer don ya zama dan gari "
" Safeer ne ya kira Aysher ya gaya mata Ankoyi sa a ranar Ammii da Areef sun zowa Mamah
ziyara, Nan Aysher ta fada musu maganar cikin Shukra, zo kuga murna gun Ammii da Mamah
bakin su yaki rufuwa su a dole murnar samun babban jika suke a take Ammii takira Daddy ta
fada masa kusan ma Daddy duk ya fisu don cewa yayi inyagama abinda yake a Dubai zai wuce
san Fancisco ya gansu "
" Mamah ta kira Shukra tayi mata murna tayi mata addu 'ar samun lafiya, Ita dai Shukrah kunya
kamar ta nutse, sai bayan sunyi sallama da Mamah ta juyo kan safeer tana dukansa da hannu
biyu tana mai kukan shagwaba "
" Shine kaje ka fada wa su Mamah inada ciki ko? Yanzu da wani ido kake so na kallesu "
" Rike hannayenta yayi ya janyota Jikinsa ya Matse ta har sai da ta saki yar kara sannan ya
sassauta rikon "
" Shukrah Ai ko ban fadawa mutane ba zasu gani ae in mun koma "
" Ni bazan koma ba sai na haihu, Ta fada cike da shagwaba "
" Ae baki isa ba nanda 2 weeks zamu tafi don next week za a gama Aikin company kuma office
suna nema na "
" Ni bazan tafi ba sai dae kaje ka barni a nan "
" Bazan barki ba Shukrah "
" Nan dae Shukrah ta cigaba da kukanta na shagwaba wae ita bazata je aga cikin taba sai dae
a ganta da baby "
" Shiko Safeer shiru yayi yana jinta don yasan inya biye mata rigima zatayi tayi masa don ita
cikin nata da tabara, Rigima da shagwaba yazo mata, Ahaka dae bacci ya dauketa ya sauke ta
daga jikinsa ya mata addu a shima yayi ya Rungumeta sai bacci...........
SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE í ½í²ž
[4/22, 9:13 AM] í ¼í¾€Shukra yar gatan miemieí ¼í¾€: í ½í±®í ¼í¿»AUREN BAZATA í ½í±®í ¼í¿»
WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA
Dedicated to Miemie bie í ½í¸˜
2⃣7⃣
"Misalin karfe daya da rabi Shukra ce da Azeeza a kitchen da Alama Lunch suke hadawa,
Azeeza na daga gefe tana dafa white spaghetti Shukra kuma tanayin Beef Goulash "
" Wayan Shukra ne ya shiga ringing ta ajiye spoon din Hannunta ta nufi wayar, Ibteesam ce me
kiran shiyasa Shukra tayi saurin picking tana mata sallama
"Shukra Fadamin da bakin ki dan Allah inji Ibteesam da murnar ta"
"ME zan fada miki Shukra ta tambaya "
" Ki fada min SIRRIN BOYE (sabon Novel dina bayan AUREN BAZATA insha Allah) inji Ibtee
tana dariya "
" Dariyar itama Shukra tayi don ta gane me take nufi "
" Wata nawa ne?
"Wata Biyu ne "
" kice Amal ta kusa samun kanwa inji Ibtee "
" Ta kusa kam "
" Daga nn dae suka cigaba da Hirar su ta kawaye har sai da Shukra taji Beef Goulash dinta na
neman kamawa sannan tayiwa Ibtee sallama ta koma kan girkin ta "
" kamar yadda Daddy yayi Alkawarin zuwa San Francisco ganin Shukrah Haka kuwa akayi
ranar wata friday ya kira safeer ya fada Masa gobe ze biyo jirgi yazo ya gansu, Shukrah kamar
ta zuba ruwa a kasa tasha don Farin ciki "
" Ranar da Daddy zezo Abinci kala kala Shukrah da Azeeza sukayi, Karfe Uku saura jirgin su
Daddy yayi landing a San Francisco, Inda ya kira Safeer a waya Sukaje Shida Ahmad suka
tawo Da Daddy "
" Rungume Daddy Shukrah tayi don Murna kafin taja Hannunsa ta Zaunar da shi kan One sitter
ita kuma ta zauna a gaban sa tana masa labari sai dariya suke "
" Azeeza ce ta kawo wa Daddy Abinci da Drinks sannan Suka gaisa Nan Safeer da Ahmad ma
Suka zo suka kara Gaisawa da Daddy kafin suka tafi suka barshi yaci Abinci "
" Koda Ahmad da Safeer suka fita Hotel room suka kamawa Daddy sannan suka je sukayi
masa Siyayya me yawa suka kai Room din sannan suka dawo gida "
" Sanda Suka tafi Mosque ne suka yiwa Daddy bayanin Komai kuma yaji Dadi, Da suka idar
Suka kai Daddy Hotel din Sannan suka dawo gida "
" Safeer da Shukra zaune a dakin su Ga abinci a gaban su
"Shukrah yanzu bazaki ci abinci ba, kin taba ganin inda akayi haka? Bafa ke kadai bace ba "
" Ni bazan ci wannan abin ba ta fada tana nuna masa plate din gabansu kamar zatayi kuka "
" To naji me zaki ci "
" Dan wake ta fada tana kwanta wa a jikinsa "
" í ½í¸³Dan wake kuma Shukra? Haba da Allah yanzu a ina zan samu dan wake a nn, Kuma naga
da ae bakya cin Dan waken "
" Toni yanzu shi nake so ta fada tana fashe da kuka kamar an mata wani abun "
" Rungume ta yayi tsam yana lallashi amma taki jinsa sai kara volume din kukan ma tayi "
" Yi hakuri Shukra dan Allah ki fada min wani abun amma banda wanda bazan samu a nn ba "
" To naji na canja Dan - Malele zanci "
" Safeer kamar zeyi kuka yake ji, Tabarar Shukrah ta soma damunshi, "ynx fisabilillahi Shukrah
a ina zan samu wani Dan -Malele a nn"
"Toni shi zanci "
" Shiru yayi mata be kara cewa komai ba ya janyo plate din ya fara cin abincin sa "
" Shukrah ganin ya kyaleta ya sata fasa masa kuka sosai har tana bubbuga kirjinsa, Rike
hannayenta yayi da nasa guda daya yana cigaba da cin abincin sa har anan bece mata komai "
" Shiru tayi ta kara lafewa a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya har bacci ya dauketa "
" Sai da ta gama cin abincin sannan ya kwantar da Shukrah a kan gado sannan ya dauki plate
din yakai kitchen ya dawo ya kwanta a kusa da Shukrah bayan ya musu addu 'a, Da tunanin
rigimar Shukra bacci ya dauke shi "
" Cikin dare yunwa ta damu Shukrah ta mike ta fara bubbuga Pillow' n safeer, Bude idonsa yayi
ya sauke su kan Shukrah da tayi kalar tausayi tana kallonsa "
" Ya akayi? Ya tambayeta da muryan bacci "
" yunwa nakeji ta fada tana jan hannunsa "
" Mikewa yayi ya fita, kitchen ya je ya hada mata Tea sannan ya dawo ya samu ta shiga Toilet "
" Tana fitowa ta nufi inda yake da sauri ta karfi cup din hannunsa bata damu da zafin da tea din
yake da ba ta kafa kai ta fara sha, Bata ajiye ba sai da ta shanye tsat, Ta zauna bakin gado ta
rufe idonta tana maida numfashi, Wani tausayin ta yaji yana shigarsa sosai "
" wani zafi Shukrah taji tana ji sai gumi take, Ganin da yayi tana gumi ne yasashi shiga toilet ya
hada mata ruwan wanka, Ya dawo ya daga ta ya cire mata rigar jikanta ya dauketa cak sai
toilet, Da kansa yayi mata wanka sannan ya dauko ta ya dawo da Ita ya kwantar kan gado
shima ya kwanta sai bacci "
" Sai da Daddy yayi 1week a San Francisco, sosai yayi wa baby siyayya shima sannan Y soma
shirin komawa Nigeria, Shukrah yar Rigima wae sai ta bishi,jin safeer be ce mata komai ba
yasata yin shiru da maganar "
" Ranar da Daddy ze koma dukansu ne suka rakashi Airport sai da su kaga tashin su sannan
suka koma gida suma "
" Yau ake taro bude Company 'n Ahmad, Sosai manyan mutane suka halarci taron kasan
cewar Ahmad shahararre kuma fitacce a San Francisco state, Bayan gaishe gaishe, ciye ciye
Ahmad ya gabatar da Safeer a matsayin Manager' nsa, sosai abun ya bawa Safeer mamaki don
be taba tunani ba kuma koda wasa Ahmad be fada masa ba, "
" Se bayan da aka kammala taron ne Safeer ya samu kebewa da Ahmad inda yayi masa
godiyar wannan alherin da yayi masa "
" Nan Ahmad ya nuna masa ba komai ae duk daya ne, Saf
[4/22, 11:55 AM] í ¼í¾€Shukra yar gatan miemieí ¼í¾€: í ½í±®í ¼í¿»AUREN BAZATA í ½í±®í ¼í¿»
WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA
Dedicated to Miemie bie í ½í¸˜
2⃣8⃣
"Safeer ya kira Mamah ya fada mata irin Alherin da Ahmad ya masa, Nan Mamah ta bukaci
Safeer ya hada ta da Ahmad din, Ya bashi wayar kuwa inda Mamah tayi masa godiya sosai
sannan tayi masa Addu 'a, Sosai Ahmad din yaji dadin yadda Mamah tayi masa "
" Yau saura kwana Biyar su Shukrah su koma Nigeria, Sosai Ahmad da Azeeza suke musu
tsaraba wanda yawanci kayan Babe ne, Azeeza ce ma tayi wa Aysher da Miemie tsaraba, inda
Ahmad yayi wa Mamah da Ammii tsaraba shi kuma "
" Ana gobe zasu koma cikin gidan ba wanda yayi bacci suna tunanin rabuwa (sabo turken
wawa), Jirgin bakwai da rabi zasu bi hakan yasa koda su safeer suka dawo daga mosque
wanka ya shiga bayan ya fito ne itama Shukrah tayi "
" 6:40am dukansu suka fito suka shiga mota Sai Airport, Cikin mota Shukra da Azeeza sai kuka
suke sun rungume junansu, Suma su Safeer kawae dauriya suke irinta mazaje amma suna jin
ba dadi a ransu wannan ne dalilin da yasa basu hana su kukan ba ma "
" 7:30 aka fara kiran sunansu, safeer da kyar ya janye Shukra a jikin Azeeza bayan ya mata
alkawari zasu sake dawo wa kafin ta haihu tunda shine manager 'n company' n Ahmad so akwai
bukatar zuwansa San Francisco akai akai "
" Sai da Su kaga tashin su sannan Ahmad yaja Azeeza mota wadda har anan kukan take (Sabo
da dadi rabuwa ba dadi) "
" A Nigeria Miemie da Aysher ne a kitchen suna ta girki kala kala, Dama Mamah ta nemi
alfarmar Ammii kan tazo gidanta su tari su Shukrah gaba daya "
" Ammii bata watsa kasa a idon Mamah don tun 9:00am sukazo ita da Areef "
" To cikin jirgi Shukra sai kukanta take Safeer na Aikin lallashi, Da kyar ya samu tayi bacci
sannan hankalinsa ya kwanta "
" 2:00pm Jirgin su yayi landing a Airport na Malam Aminu kano, Suna fita Safeer ya kira Haiydar
ya fada masa sun karaso sannan suka koma gefe suna jiran zuwan Haiydar din "
" Bayan kamar minti ashirin sai ga Haiydar ya zo ya fito ya tayasu zuba kayan su a booth ya
jasu sai Farm Centre "
" Miemie najin tsayawar mota ta fito da gudu dai dai sanda Shukrah ke fito da ga motar Haiydar,
Miemie tayi tsalle ta Rungume shukra cike da murnar Ganinta, ita ma Shukra da murnar ta ta
rungume miemie suka shige gidan gaba daya "
" Shukrah na ganin Ammii ta fada kanta ta rungume hade da sakar mata kukan shagwaba "
" Baki Ammii ta saki tana kallon Shukrah da mamaki
"Kukan na meye to Shukrah"
"Na dadi ne Mamah ta bawa Ammii Answer "
" Sai Anan Safeer da Haiydar Suka shigo gidan Nan fa aka shiga gaishe gaishe kowa fuskar sa
dauke da fara 'a, Bayan an gama ne Aysher ta shiga kawo musu drinks "
" Ruwa kawai Safeer yasha suka tafi Mosque shida Haiydar, To itama Shukrah Sallah tayi
sannan tazo tace Miemie ta bata abinci taci don ita cikin nn harda wani mugun ci yasa mata "
" Coconut rice da Egg sauce Miemie ta zuba mata sai mixed fruit ta ajiye mata a gaban ta, "
" Ae Shukrah na kai Spoon din baki taji zuciyar ta ba tashi ta yarda Spoon din da sauri tana
kokarin mikewa, Amma kafin ta mike tuni ta fara Amai a inda take "
" A tare dukansu suka nufeta Aysher ta rike ta tana mata sannu jikinta sai rawa yake
"Aysher ki dauke wannan abincin banason ganinsa Shukra ta fada a wahale"
"Sai da Aysher ta dauke abincin takai kitchen sannan ta dawo ta fara gyara gurin "
" Mamah ko rike Shukrah tayi suka