Showing 18001 words to 21000 words out of 55173 words

Chapter 7 - Auren Bazata Book Compelet Zainab Yakasai Shukra

ta fada tana kara rusa kuka wane shi aka aiko ta"


"Da daddare Mamah cewa tai ita zata Zauna da miemie, Ammii ta tafi gida tana ganin kirki irin

na Maman Safeer "


" Washe gari da safe Aysher ta kawo abinci sannan ta wuce School "



9:00am Safeer da Haiydar suka shigo duba Shukra, Gaisawa sukayi da Haiydar sannan ya fita
dama Mamah da Miemie sun tafi gida don yin wanka saboda haka dakin ya rage daga Safeer
sai Shukra"


"Shiru ne ya ratsa dakin ba wanda ya cewa dan uwansa ci kanka, gajiya Shukra tayi da kallon
da Safeer ke mata ta mike ta shige toilet abinta "




" Shima Safeer mikewa yayi yaje ya samu Haiydar a waje suka fice daga Asibitin ma gaba daya
"




" Ammii ta riga Mamah zuwa saboda haka ta samu damar yiwa Shukra tatas "



" Sosai Shukra take kuka tanajin inama zata iya cewa Ammii
"Ni na shirya basa kaina shine be nemeni ba"
Amma bazata iya ba, Hakan ya sata ci gaba da kukanta kamar an aiko ta tanajin inama mutuwa
tazo ta dauketa a wannan lokacin ta huta da bakin cikin da take ciki a yanzu "


" Wasa - wasa sai da Shukra tayi one week a Asibiti sannan akayi discharging dinta, Mamah ce
ta dage sai ta tafi da Shukra gidanta saboda tana kallon yadda Ammii takewa shukra kamar ba
ita ta haifeta ba "



" Haka dai suka tattara suka koma gidan Mamah, sosai Shukra take samun kulawa gurin
Mamah da Aysher, Miemie ma ba a barta a baya ba don Sosai take damun Shukra da surutun
ta kuma itama Shukran tana jin dadin zama dasu, mutanen kirki yadda suke mata ko safeer

basayiwa haka "



" Sosai mutanen Mamah da Ammii suke zuwa duba Shukra, Abokin Safeer ma sunzo, Haiydar
ko dama kullum sai yazo kodan yaga sahibarsa (Miemie) "



" Kawayen Miemie duk sunzo dan gida - gida tarinka zuwa tana fada musu azo a duba Auntyn
ta batada lafiya, in ba kazo ba kuwa zuwa take ta tawo da kai "


" Sati biyu Shukra tayi a gidan Mamah sannan ta koma gidan Ammii kasancewar next week
zata koma gidan Safeer "




" Sosai Safeer ya gyara gidansa har furniture's din Shukra sai da ya changer mata, gida dai ya
hadu iya haduwa dan da mukaje nida Miemie cewa nayi bazan tawo ba(lols)


"Ammii ta dage sosai take gyara yarta dan ta fahimci ba abinda ya taba shiga tsakanin su da
safeer "


" Yau saura kwana 3 Shukra ta koma ji take gaba daya batasan komawa tunanin taya zata
soma zama da kishiya "



" Yau ta kama wednesday kuma tun 7:00pm Safeer yazo tafiya da Shukra kasancewar yau zata
koma, Kuka take baji ba gani ko a mota bata kalleshi ba sai kukanta ta take har suka karasa
gidan............

SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[4/8, 10:52 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻






WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA






Just to fulfilled a promise as you win the game, Am so grateful that you are following my novel
😘
Dedicated to miss softie



1⃣8⃣



"Cike da fargaba Shukra ta fito daga motar Safeer, Bakinta dauke da addu 'a ta nufi cikin gidan "



" Baki ta saki tana kallon yadda gidan ya changer yayi mata kyau wlh sai taji zuciyarta tayi sanyi
kamar bawani abu dake damunta, Amma data tuna wae su biyu ne cikin gidan sai taji wani
bakin ciki ya mamaye zuciyarta "


" Dakin ta tashige nanma sai da tasha mamaki don ya hadu iya haduwa, sai takejin inama ita
kadai ce a gidan da tayi amfani da damarta ta faranta ran mijin ta yadda ya faranta mata "



" Wanka shukra tayi tayi sallah'r isha ta kwanta zuciyar ta cikeda tunane - "tunane tana so ta fito

palour tayi kallo dan sam batajin bacci amma kuma tana fargaban haduwa fa Amarya haka dai
bacci barawo ya kwashe ta a gurin"




"Asubar fari Shukra ta farka, mikewa tayi bayan tayi Addu 'ar tashi daga bacci ta nufi toilet tayi
alwala tazo tayi nafila ta
Zauna tana addu' a kasancewar ba a tada sallah a masallaci ba "


" Koda ta idar da sallah zama tayi tana lazimi tanaso ta fita ta gyara gidan ta daura breakfast
amma tana tsoron ganin wata a cikin gidan ta "


" 10:14am tayi shahada ta fito daga dakin ta fitowar ta yayi dai dai da fitowar safeer daga
dakinsa, har kasa ta durkusa tana gaidashi tana kuma kokarin mayarda kukan dake son subuce
mata "


" Kin tashi lafiya Shukra "

" Lafiya kalau "

" Ya karfin jikin "
Alhamdulillahi na samu sauki ae"


"To masha Allah "

" Har ta wuce sai kuma ta dawo Ya Safeer ina Amaryar?

"Za tazo ku gaisa ae karki damu "

" Durkushewa tayi a gurin tana kuka mai tsuma zuciya "

" Ganin hk safeer yayi saurin zuwa ya daga ta ya rungume ta tsam a jikansa,

"Yi hakuri Shukra nasan ni Mai lefi ne a gurinki, A sanadiyya ta kika kamu da ciwon hawan jini "


" Kiyi hakuri nayi hakan ne dan na gwadaki naga ko kina sona ko bakya sona, Ashe dai kina
sona "

" Amma ba maganar Aure "


" Batasan sanda ta saki ihu ba ta kara kankameshi a jikin ta "

" Ya Safeer dan Allah ka kara gayamin bakayi aure ba, kacemin wasa kake min "



" Shukra wasa nake miki banyi wani Aure ba wallahi "


" Sakinsa tayi taja hannunsa suka zauna akan kujera "

" Ya Safeer bikin wa akayi to "

" Bikin Abokinmu ne Tareeq, a office dinmu yake"

"To invitation cards din fa da kaka kawo min zuwa kayi akayi maka su?

"A a na Tareeq dinne fa na kawo miki, baki ganiba "

" Sai a nan ta tuno hakan ta ta fara dariya kafin tace, Ae kana ajiye wa ka fita na tashi na jefa
bayan gado "


" Dariya safeer yake hadda rike ciki yace
"Har na tuno Shukra a gadon Asibiti tana cewa


"Ya safeer dan Allah ka rufa min asiri kamar yadda Allah ya rufa maka karka min kishiya "


" Dukan wasa ta fara kai masa yana dariya yana karewa, Ae ko ta sakar masa kukan shagwaba
'ni wlh ka dena bana so' "

" Janyota yayi zuwa jikansa yana lallashinta "


" Yi hakuri Shukra cute, dena kuka kinji yan mata na, Safeer naki ne ke kadai Shukra "

" Na miki Alkawari baki kulawa, Namiki Alkawari bazan miki kishiya ba, A gurina mazaunin
mace "HUDU" kike


"Kara lafewa tayi ajikinsa kafin tafara magana "



" Lokacin da akayi auren nn bada son raina akayi shiba, shiyasa na dinga horaka ta hanyar rufe
maka kofa "


" A hankali na gane AUREN BAZATA ALHERI NE"



"Ina kara rokonka da ka yafemin lefina a gareka "


" Baki min lefi ba shukra we only mis understood each other and now we burry da hatchet "


" Haka dai sukayita ga yawa juna su sirrin zukatan su (☹yan duniya ashe suna son junansu
gulma ta hana su bayyanawa) "



" Haka suka yini a gidan basuje ko ina ba suna ta hira kamar dama can suna shiri "



" Safeer sai wani farin ciki yake yau fa shi ango ne "


" Da daddare safeer ya je ya siyo musu kajin amarchi, ya dawo ya samu shukra tana jiran shi "


" Bude mata hannayensa yayi bayan ya ajiye ledar daya shigo da ita, Aiko da saurinta taje ta
fada jikinsa suka rungume junansu suna masu jin kaunar junansu"



"AS YOU START YOUR NEW LIFE TODAY I WISH YOU ALLAH 'S BLESSING, MAY GOD

BLESS YOU WITH BEAUTIFUL CHILDS, MAY GOD PROTECT YOU FROM EVERY EVIL
DEED"

SHUKRA & SAFEER 👌🏻
















SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[4/9, 5:54 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻





WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA






Dedicated to miemie bie 😘



1⃣9⃣

"Jan Shukra Safeer yayi Ya zaunar da ita a tsakiyar palour sannan ya wuce kitchen ya dauko
plate, fork, and knife ya dawo ya ajiye a gaban ta, sannan ya dauko ledar daya shigo da ita ya
juye musu kajin"



"Knife yasa ya yanka sannan ya dauka da fork ya kai bakin shukra"


"Cike da jin kunya ta kawar da kanta gefe guda, sannan tasa wani fork din ta dauka ta fara ci "

" Karki ce min kunya na kike ji Shukra "


" Komai bata ce ba sai ma sunkuyar da kanta da tayi, dan duk batajin dadin yadda ya kafe ta da
ido"


"Shiru sukayi suka ci gaba da cin abincin su zuciyoyin su cike da nishadi, duk daga idon da
shukra zatayi sai sun hada 👀hakan yasata mikewa kawae"


"Karki ce min kin koshi "

" Eh na koshi ta fada tana turo baki gaba "

" Tab ai biki isaba kefa Amarya ce"

"Amarya ko Uwargida 3 month wasa ne "

" Koma dai menene dawo ki kara "Ya fada yana kokarin kawar da waccan maganar"


"Seriously am satisfied ta fada tana bin hanyar dakin ta "


" Shima mikewa yayi ya kai plate din kitchen sannan ya shige dakinsa donyin wanka "


" Fito wa shukra tayi daga wanka ta karasa jikin wardrobe dinta ta fito da sabon sleeping dress
ta saka, sannan ta dawo jikin dressing mirror ta shafe jikin ta da lotion ta fesa turare sannan ta
hau gado donyin bacci "

" Shima da ya fito jallabiya yasa coffee colour ya shafa cream sannan ya feshe jikansa da turare
"


" Zama yayi a gefen bed ya dauko system dinsa ya daura kan bedside drower ya fara aikin sa,
construction na company yakeyi, wani balarabe ne ya basa kwangilar company 'n kuma nn
bada dadewa ba ze tafi don ayi komai akan idonsa "


" Sai 12:00pm safeer ya kammala construction din nan, kashe system din yayi ya mai data cikin
jaka sannan ya mike ya kashe globe din dakinsa ya fice"



"Dakin Shukra ya nufa da sallama ya shiga sai dai ba answer kasancewar Shukran baccinta
yayi nisa "


" Globe din dakin daya kunnan ne ya farkar da Shukra tamike tana salati "


" Karasowa yayi ya hau kan bed din sannan ta jawo ta jikin sa "


" Nokewa ta shiga yi dan ita tsoro take ji, fahimtar hakan ne yasashi fara mata magana "

" A a Shukra cute kwantar da hankalin ki ba abinda zan miki kawai dai bazan iya kwana ni daya
a dakina bane shine nazo tayaki kwana "


" Jitayi kamar ta daura hannu aka tasa ihu, tana son Safeer tana kuma so ta faranta masa,
tanajin zata iya jure duk wani radadi indai hakan ze se sashi farin ciki "


" ME yasa Bazai karbi hakkinsa ba a wuce gurin kawai? Sai taji tana data sanin nokewar da
tayi, ita kuma anata ganin ae jan ajine tunda mace dai da jan aji aka santa "


" Ji take inama zata iya cewa ya safeer a shirye nake "Amma BAZATA iyaba"

"Haka dai suka kwanta rungume da juna zuciyar ta na mata zafi, Amma tasan komai lokaci ne
in lokacin yazo ko bataso sai anyi "



" Da Asuba Safeer ne ya fara bude ido kasancewar dama sama - sama yayi bacci yau, A
hankali ya zare Shukra a jikinsa ya kwantar da ita sannan ya shige toilet don yin alwala "

" Ko da ya fito bata farka ba saboda haka ya karasa kan bed domin tashin ta "


" Hannunta na dama ya kama yasa a bakin sa yana tsotsa a hankali, sun kai kusan 2 mints a
haka kafin Shukra ta fara bude idonta a kansa "


" Yana ganin ta bude ido ya mikar da ita zaune yana karanto mata addu 'ar tashi daga baccin "


" Bin addu' ar tashiga yi har suka kammala sannan ta mike ta yi hanyar toilet din "

" Yi sauri Shukra kiyo alwalar kizo muyi jam 'i

"To tace sannan ta shige toilet zuciyarta cike da farin cikin kulawar da Safeer ya soma bata "



" Koda ta fito tarar wa tayi ya fito mata da hijab ya kuma shimfida musu abin sallah "



" Karasawa tayi ta dauki hijab din ta hau abin sallah shi kuma ya soma ikama "


" Koda Su kazo Sujjadar karshe Safeer ya dade yana musu addu 'ar samun kwanciyar hankali
da zaman lafiya a sabuwar rayuwar su"




"Bayan sunyi addu' a ne Shukra ta mike zata fita "

" Kamo Hannunta yayi ya jawota ta fada jikinsa ya rungume ta hade da dora kansa akan nata "

" Ina zaki kuma? Ya tamvaye ta murya can ciki "



" Duk sai taji ya kashe mata jiki da kyar ta iya cewa ' breakfast zan hada mana "



" No ki bari sai zuwa 10:00am in mun tashi a bacci kyayi kinji ya fada yana shafa smooth cheek
nata "

" Office dinfa ta tambaye shi a kasalance "


" Bazani ba kin manta ni Ango ne "



" Nan ta fara kokarin tashi daga jikinsa, yasake mai data ya kwantar "

" Ina zakije ne wai? Ko toilet zaki "ya rada mata a kunne"


"ji tayi wani abu na yawo a jikanta jin hucin bakinsa a kunnenta "

" Bacci zanyi ta bashi Answer da kyar "


" To kiyi kwanciyarki zansa kiyi bacci kinji "


" Komai bata ceba sai kara lafewa datayi a jikinsa hade da lumshe ido "


" Bayan ta ya shiga bubbugawa a hankali kamar yana son yasa baby bacci, A hankali baccin ya
kwasheta "


" Saukar numfashinta daya fara ji a hankali ne ya tabbatar masa tayi bacci, Don haka ya je ya
kwantar da ita a tsakiyar bed din shima ya kwanta ya rungume ta sai bacci "

" sai gurin 11:00 suka farka Shukra tayi hanyar kitchen shi kuma ya nufi dakinsa "


" Breakfast me rai da lafiya ta hada musu sannan tayi wanka, Tayi shirin ta cikin wasu English
wears riga pink, skirt blue tayi parking gashinta da pink ribbon dama shukra bata son kitso a
rayuwar ta "


" Pink din hijab tasa karami tasa blue slippers ta fito palour a gurguje, Suna hada ido ya sakar
mata murmushi, murmushin itama ta sakar mai sannan ta wuce dinning ta kwaso breakfast din
ta kawo palour...........







SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[4/10, 5:48 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻






WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA








Dedicated to Miemie bie 💞



2⃣0⃣

"Cikin plate daya ta zuba musu abincin, haka ma tea a cup daya ta hada musu, Haka sukaci
Abincin Safeer ba bawa Shukra Labarin Haiydar da Miemie sai dariya take kyalkyalawa abinta,
shiru yayi yana kallon yadda take dariyar bilhakki Sai yaga ta masa kyau, ita ko jin shirun yayi
yawa yasa ta dena dariyar tana kallon shi "

" Meye kake kallo na "Ta fada tana murguda masa baki"


"Shi abinma dariya ya basa kamar wata karamar yarinya har da murguda baki "


" Shiru sukayi dukansu har suka kammala cin Abincin, sannan Shukra ta kwashe kayan ta kaisu
Kitchen ta fara wanke wa "


" Jin shirun da Safeer yayi ne yasashi bin Shukra kitchen, Tana jikin sink tana wanke wanke
abinta, Ya karaso yana tattare hannun rigarsa "


" Kawo in taya ki "


" Jiyowa tayi tana kallonsa "ka tayani me?

" Wanke wanke ya bata answer yana kokarin karban sponge din hannunta "


" A a kabarshi wallahi "


" Bakya so namiki jika -jika ko shiyasa bazaki bani bako "



" A a ba haka bane hutar da kai nayi wanke wanke ae sai mata "


" To ae ni ko a gida ran duty'n Aysher nike mata wanke wanke da shara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0