Showing 3001 words to 6000 words out of 55173 words

Chapter 2 - Auren Bazata Book Compelet Zainab Yakasai Shukra

( Niko nace luv
ne).

To Daurin auren ya samu halartar manya manyan mutane daga ko ina a fadin Nigeria wanda
yawanchinsu abokan Abba da daddy ne
"An daura AUREN akan sadaki naira dubu dari.
Haka dai daurin aure ya watse kowa na farin ciki ana kuma ta sa albarka.
To kamar yadda daddy yace shukra BAZATA tare ba hk kuwa akayi bata tare dinba tunda ynx
ma final exam dinta xata fara ta kammala university.
To shukra fa sun fara exams gadan gadan wanda ynx ma sun kusa gamawa shikuma safeer
ya cigaba da zuwa Aikin sa kamar da.


Shukra ta kammala exams dinta kuma ansa ranar tare war ta nanda sati uku.

"Duka banga rorin biyu shirye shiryen su suke tunda xa ayi mothers night kafin akai amarya
dakinta.

" yau ta kama saturday wanda yaune xa ayi mothers night shukra taci kwalliya kamar ba gobe
"Fancy Makeover" itace ta mata kwalliya kuma tayi shirinta cikin wani material me tsadar gaske
kalar peach tasa head orange (hmmmm abin dai ba a cewa komai readers zanso kuga shukra
yau din nn ba karya) takalmi da jaka duka orange tasaka.....

"Daga nn dai aka dunguma zuwa" Shukra event centre "inda ann ne za ayi mothers night din.

To anchi ansha Alhamdulillahi guri ya kayatu daga nn ne aka kwashi shoki sannan aka rufe
taro da addu a aka dauki amarya aka wuce da ita gidan ta dake nn Nassarawa G R
A.................................









SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[3/27, 9:52 AM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻


WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA

Beauty, intelligent, respecting peoples are what makes you swthrt #MIEMIE BIE i Dedicated
this page to you.



0⃣5⃣


ASALIN SU

Alhj AL 'ameen sarakee haifaffen garin adamawa yola ne yayi karatun primary & secondry dinsa
a garin Adamawa wanda daga nn yayi exam jinsa wato Jamb ya kuma samu point me kyau
Ya nemi admission a usman danfodio university sokoto wanda cikin yardar Allah ya samu ya
fara karanta 'Geology'.
To bayan ya kammala karatun sa ne be dade ba yasamu Aiki a wani company a garin kano
inda ya tattaro gaba daya ya dawo kano da xama


"Alhj sarakee ya hadu da matar sa fateema ne (Mahaifiyar shukra) a saudiyya inda yaje aikin
hajji
" itama fateema gabaki daya yan gidan su suka je Aikin hajjin kasancewar mahaifinta me

Arzikin gaske shine senator na kano central a wnn lokacin
"To kasan cewar A lokacin Aikin hajji suka hadu yasa basu wani fahimci junansu ba sundai
yi exchanging numbers na niyyar in sun dawo gida sarakee zaije ya sameta.

" to bayanda suka dawo gida ne Alhj sarakee yaje gidansu fateema kuma ta hada shi da
iyayenta..
Baban fateema ya yaba da hnklin sarakee kwarai shiyasa ma bayan dayayi bincike a kanshi
sosai ya nemeshi ya kuma shaida masa ya turo iyayensa.

" Iyayen Alhj sarakee sun zo sun kuma yi duk abinda ya kamata akasa ranar biki wanda ba a
wani dau lokaci ba aka daura auren aka kuma kai fateema gidanta dake unguwar 'Farm center'.

To zaman fateema da sarakee xama ne abin sha awa domin akwai girmamawa da mutunta
juna.

'Haka zaman su ya cigaba har na tsawon shekara biyar wanda a wnn shekara biyar din
fateema ko bari bata taba yiba balle haihuwa abinda yayi matukar daga mata hnkl kenan
"A bangaren sarakee kuwa sam abin be dameshi ba shine ma kullum yake kwantar mata da
hankali yana cewa haihuwa ta Allah ce Kuma lokaci ne beyiba in yayi xa ta haihu
" To da wannan kalami na sarakee fateema tayi amfani wajen kwantar da hankalin ta.
Ana cikin haka ne fateema ta sami ciki, zo kaga murna wajen sarakee da fateema kai har ma
da iyayansu wanda daman suma rashin haihuwar ya damesu shiru dai kawae sukayi.

"Ciki dai yana samun kulawa yadda ya kamata
Haka suka cigaba da kulawa da cikunsu har watan haihuwa yayi wanda Alhj sarakee takanas
ya tafi 'Egypt' danyin siyayyar kayan baby

" To ana gobe fateema xata haihu sarakee ya dawo wanda washe gari da asuba fateema ta
tashi da ciwon mara da ciwon baya wanda sarakee be bata lokaci ba ya dauki fateema sai
asibiti.

" Cikin lokacin da be wuce awa daya ba fateema ta haifo kyakykyawar yarta me kama da Alhj
sarakee sak daga nn akayi discharging dinsu kasan cewar fateema da babyn lafiya kalau suke.

" Ranar suna yarinya tachi suna 'ZAINAB' wato mahaifiyar Alhj sarakee hakan nema yasa
suke kiranta da suna 'SHUKRA'



" Sai da shukra ta kai shekara 7 sannan fateema ta kara samun wani cikin. To wnn cikin ma
anyi farin ciki da samun shi kasancewar sun cire rai ma da kara samun wani cikin.

," Haka dai take ta rainoncikin har lokacin haihuwar yaxo inda ta haifi yaron ta namiji.
"shikuma sunan mahaifin fateema yaci wato Mukhtar suke kiransa da 'AREEF.


" Tundaga kuma wannan lokacin har zuwa ynx fateema bata kara haihuwa ba.
"Haka yaran suka taso cikin soyayya da kuma kulawar iyaye sosai yaran suke da tarbiyya
ga girma ma manya ga kuma kunya da tsoron Allah.






CIGABAN LABARI

" TO koda safeer ya taso daga office gidan mahaifin shi ya wuce kai tsaye inda iyayen nashi
suka hadu suna mai nasiha kan ya kula da matar sa domin amana ce a gurin.
" Godiya safeer yayi musu sannan kuma ya kama hanyar gidansa xuciyar sa cike da sake
sake tunani kawae yake wace irin tarba shukra xatayi masa?
" zata karbi kaddara ne ta zauna dashi a hk ko kuma BAZATA karba ba?
"To da wnn tunanin ne safeer ya karasa gurin wani suya spot ya siyi kaji da kuma fresh milk
xe kaiwa amaryar sa...........

" Bayan yagama da suya spot kai tsaye gidansa dake nassarawa G R A ya nufa koda ya isa
yayi worn a gate, gate man ne Y taso da fara arsa ya bude mishi yana gaida shi da fara arsa.
" To safeer dinma da fara arsa yake answer wa kafin ya wuce gurin da aka tanada don
parking yayi parking motarsa sannan ya nufi cikin gidan kai tsaye..........................





SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[3/29, 4:33 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻



WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA


I don't care weather people will like it or not, ☹if they like it "cool ' if not it left for them (Hmmmm

such is lyp). I only know that i luv u #MIEMIE BIE
Dedicated to you 👆🏻




0⃣6⃣



Ko da SAFEER ya shiga cikin gidan kai tsaye dinning area ya huce ya ajiye kayanda ya shigo
dasu sannan ya shige dakinsa.
"kayan jikin sa ya rage ya fada bathroom don yin wanka.



" A bangaren shukra kuwa yan kawo amarya na fita ta mike ta rufe kofar ta sannan ta koma
tayi wanka tasa sleeping dress nata ta kwanta.

"Bayan kamar 30 mints da shigar SAFEER toilet ya fito daure da towel a waist nasa da kuma
wani a hannun sa yana goge kansa dashi.
" kai tsaye gaban dressing mirror sa ya wuce ya shafe jikinsa da lotion sannan yasa turare ya
wuce kan gabon sa dan sa kaya wanda already dama ya fito dasu.

Bayan da ya gama shirya ne ya fito ya nufi dinning area ya dauko ledar da yashigo da ita
sannan ya wuce dakin shukra.

"Yana karasawa ya murda handle din kofar amma ga mamakinsa sai yaji kofar a rufe gam.

Cikin bacci shukra taji ana taba handle tsaki kawae taja tana hararar kofar kamar yana
kallonta.
" A zuciyar ta take cewa munafiki da ajinka xan bar kofar a bude ne" mtwsssssss ta dada jan
tsaki sannan ta juya baya ta cigaba da baccin ta.



"Shiko SAFEER juyawa yayi ya nufi dakinsa jin kofar shukra a rufe.



" Washe gari misalin karfe 12:00 na Rana ko wannen su na dakin sa.
"knocking din da ake a kofar falo ne yasa SAFEER fitowa ya karasa ya bude kofar.

"kokarin tureshi take yi xata shiga ciki da basket a hannunta
" ke bakida hankali ne wae kike ture mutane ya fada a tsawace yana binta da mugun kallo......
Wallahi ki kiyaye miemie inba hk ba hmmmm ya fada yana wuce wa cikin falo.

"Dan nazo gidan ka shine kake min hk ta fada tana tura baki gaba kamar xatayi kuka.
" Ammiki din ya fada yana hararar ta (shi sam be so wannan yarinyar tazo ba don surutun ta
yafi aikinta yawa).

"Wae ke me kika zo mn gida da sassafe.

" Baki ta saka tana kallon shi da mamaki 'ynx ne safiya ya SAFEER?...


"To ynx ma ba wannan ba ina Aunty na.

Tana ciki ya fada a takaice.
"Au ita bata rashi ba 🤔 ikon Allah koda yake ae da gajiya gwara ta huta.
" Gajiyar me ya fada yana mikewa wane zai daketa.

"Tana ganin haka ta mike gajiyar biki fa nake nufi.
God save you ya fada yana koma kan kujera.
" To ynx yaya haka xan tafi ban ganta ba.
"Ehhh yace yana nuna mata kofa 'fita Dalla kinzo kin Sani a gaba da surutu
Fita tayi tana waigensa tana zuwa bakin kofa ta labe shikuma ganin ta fita yasashi komawa
daki tunda bashi da abinda xeyi.

" Aiko miemie na ganin ya shige daki tashigo cikin gidan da saurinta tana waige- waige.
Kai tsaye dakin shukra ta huce aiko sai ta ganta tsaye jikin dressing mirror tana makeup.

" Aunty shukra ta fada tana yi mata murmushi.


"Murmushi itama shukra take mata haka kawai taji tana son yarinyar.
" ya sunanki ta fada tana kamo hannunta.
Sunana miemie.
"Miemie ya gida ya mamah?
" lafiya kalau muke.
Aunty wae me yasa yaya ya hanani inzo gurinki ta tambaye ta tana karewa dakin kallo.

"Bakomai miemie inaji saboda sanda ya fita ina bacci shiyasa yayi tunanin ban tashiba (Tayi
mata karya).

Ok na dauka sbd yaga kin gajine bayaso in tashe ki.

" Gajiyar me miemie? Ni ban gaji ba ae.
Uhmm kawae tace tana hayewa gadon.

" Dariya shukra tayi ta koma ta cigaba da makeup dinta.

"A takaice dai miemie a gidan ta yini sunata hira da shukra kamar dama sun saba da juna.
" Sanda miemie xata tafi sai da shukra ta cika katuwar leda da kayan makeup ta bata.
Godiya sosai tayi mata sannan SAFEER ya dauketa suka tafi.



" Yau ma da safeer ya dawo dakin shukra ya wuce amma yasame shi a rufe juyawa kawai
yayi ya koma dakinsa kasan cewar a gajiye ya dawo (shi dama ba wani abu xe mata ba kawai
dai zai duba lafiyar tane kamar yadda mahaifinsa yace amana ce a gurin sa).




" Yau sati biyu da bikin safeer & shukra amma cikin sati biyun nn safeer be taba sa shukra a
idonsa ba.


Dawowar sa daga masallaci knn amma ga mamakinsa sai yaga kofar shukra a bude ae
kuwa sai Y xarce dakin.

" Shigarsa yy dai dai da fitowar shukra daga toilet daure da towel dinda be karasa rufe mata
cinya ba..
Kallon kallo suka shiga yi kafin shukra ta bude baki ta fara zaggaga mishi masifa.





SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[3/29, 5:00 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻


WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA

Dedicated to miemie bie �



0⃣7⃣




Wnn wani irin hauka ne xaka shigo dakin Mutum ba excuse ta fada tana hararar sa..

Hauka ya nanata kalmar a zuciyar sa

"Allah ya baki hakuri ya fada yana juyawa zai fita.
" Yana zuwa bakin kofar ya rufe da key sannan ya xare key din ya sa a aljihun wandonsa.
"Takowa yayi gabanta fuskar sa a daure ba alamar dariya.

" Iya tsorata shukra ta tsorata nn ta shiga yin baya - baya shi kuma yana binta.

"Hannu yasa ya jawota yana kokarin kunce towel din jikin ta" Bari ba miki cikin mahaukachi
yanda ko waje kika fita kika ga mahaukachi vazakiyi masa goriba tunda kina dashi.

"Kuka tashiga yi tana turashi yayinda take rike towel dinta da dayan hannun, Amma dake
karfin ba daya ba sai da ya kunce towel din sannan ya turata zuwa gadon shima ya hau.

" Ganin batada wata mafita yasata fara rokonsa 'Dan Allah ya safeer ka bari wlh tsoro nakeji,
na tuba bazan sake ba.


" Gani kawai shukra tayi safeer ya mike ya nufi kofar fita sannan yasa key ya bude ya fece.
(shi dama beyi niyar mata komai ba kawae dae barazana ya mata).


" Tun daga wannan rana shukra take masifar tsoron safeer bakuma ta sakachin kin rufe kofar
ta.


" Yau ta kama monday kuma yau safeer zai koma aiki sbd hk ya tashi da wuri ya gama shirin
sa na zuwa office ya fito palour rike da briefcase dinsa. Ko dinning be kalla ba tunda yasan
shukra ba zatayi masa girki ba.

" Yasa kai xe fice kawae tasha gabansa hade rai yayi yana kallon ta shi sam be ma kula da ita
a palour'n ba,

," ya safeer dan Allah xan bika ka kaini gida
To jeki dauko hijabi mu tafi..

Ihu murna tasa ta shige daki da gudu



SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[3/31, 2:28 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻




WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA


Wishes to congratulates you as you finished your novel that always makes people happy,
because it composed a lots of lessons.
May God bless your entire life #MIEMIE BIE
Dedicated to you 👆🏻



0⃣8⃣


"koda shukra tashiga cikin dakin bata wani dade ba kasan cewar dama a shirye take mayafi
kawae ta dauko ta fito ta samu safeer zaune cikin motarsa yana jiranta.

"Bude motar tayi ta shiga bata cemasa ba shima bece mata ba haka suka kama hanyar gidan
su shukra kowa na sake sakensa cikin ranka.


"cikin lokacin da be wuce 40 mints ba suka karasa gidan su shukra, kasancewar safeer nada
aiki sosai a office yasa ko da shukra ta fita be bita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0