Showing 42001 words to 45000 words out of 55173 words

Chapter 15 - Auren Bazata Book Compelet Zainab Yakasai Shukra

kasa zaune ya kasa tsaye sai kewaye yake ya rasa inda zaisa kansa, duk da Air
condition din dake gurin amma gumi sai zuba yake a jikinsa kafafunsa sai rawa suke jiyake
kamar ya cire ciwon ya dawo kansa, *Azeeza* da *Ahmad* sai kokarin bashi baki suke amma
sam yaki jinsu, ya zauna ma yaki zama *Shukrah* kam sai ihun ta take tana kiran *Ammii,
Mamah, Aysher, Miemie kai har meela ma sai da Shukrah ta kira, yana cikin wannan halin daya
daga cikin Doctors din da suka karbi *Shukrah* ya fito Sukayi Saurin mikewa suka nufeshi,
*Safeer* bakinsa sai rawa yake ya kasa ma yimasa magana, doctor ne ya dafa kafadar *Safeer*
yana bashi baki kafin ya miki masa wani paper wa yayi signing ayiwa *Shukrah* C. S "

" Duk jarumta irin ta *Safeer* besan sanda ya fashe da kuka ba, da kyar ya karbi pen a hannun
Doctor din ya dora kan paper, maganar da Wata Nurse ta fito tana yiwa doctor be kan yazo
*Shukrah* ta haihu ta samu baby Boy ne yasa *Safeer* wulli da pen & paper hannunsa ya bi
bayan Doctor cikin dakin, nan *Azeeza* da *Ahmad* ma suka rufa musu baya sai dakin,
Sanda suka shiga dakin har Nurse ta dauki Babyn ta fice dashi"

" *safeer* ya kara da gudu da niyyar rungume *Shukrah* Amma sai yayi Saurin dakatar da
kansa don ganin tayi wani mugun nushin sai ga baby Girl ta fito, Zaro ido sukayi cike da
mamaki da kuma farin ciki, *Safeer* ya rungume *Shukrah* tsam a jikinsa yasa kukan farinciki,
besan da bakin da zeyiwa *Shukrah* godiya ba don ta bashi farin cikin sa Twins, *Shukrah* tayi
karfin hali tasa hannunta tana goge wa *safeer* hawayen idonsa, Don tafi kowa sanin irin son
da *safeer* yakewa yara, Doctor ne yayi gyaran murya *Safeer* yayi Saurin daga *Shukrah*
yana goge hawayen daya gangaro masa "


" Nan dae Nurses su 2 suka shigo da babies *Safeer* yayi Saurin karasawa ya karbi Baby girl
din shikuma *Ahmad* ya karbi boy din, anan kuma Nurse ta shiga da *Shukrah* toilet don ta
gyara jikinta "


" Nan safeer ya shiga snapping babies yayi marking duk contact nasa na WhatsApp yayi musu
sending, nan fa aka fara kiransa ana masa murna, Aysher ma ta kirasa sanda yace takai wa
*Mamah* wayar kin karba tayi, tadai ce Allah ya raya *Twins* "


" washe gari akayi discharging nasu, Abokan aikin su *Ahmad* sai zuwa suke, kayan Babies
kuwa kamar zasuyi magana don yawa, sai zuwa dare sannan *safeer* ya samu damar kebewa
da *Shukrah* ya zuba mata ido tana rike da Baby girl dinta, tsawon minti Arba 'in suna hk, Har
sai da *Shukrah* ta gaji da da kallon nasa tayi magana"

"Your look is so intense, it makes me nervous, what do you want? *Shukrah* ta tambayi
*Safeer* sanda ta dauke kanta "



" *safeer* ma dauke kansa yayi sannan yace ALL what i want is your love, can you do me a
favour and give me that much? I promise to live with you for ever, Indeed you are a blessing,
kinbani farin ciki a rayuwa ta, i have never expected dis, being a Daddy of twins at this very tym"


"Why not? I will give you my luv for the joy you brought into my life, for understanding my needs,
for allowing me to be part of you at the same time for turning back to the face of all my mistakes
*Shukrah* tace harda dan hawayenta "


" Rungume *Shukrah* , *safeer* yayi itada Babies dinsu ya musu selfie.......






SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[5/11, 9:17 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN* *BAZATA*
👮🏻




*WRITTEN* *BY* *ZAINAB* *YAKASAI*
*SHUKRAH*





Dedicated to *MIEMIEBEE*

3⃣6⃣



" *SAFEER* ya kurawa twins dinsa ido fuskarsa dauke da murmushi, yanaji a ransa yanzu
bashida wata matsala tunda Allah ya masa babbar kyauta wadda ba kowa yake waba, a fili
yace 'Alhamdulillahi'

" *SHUKRAH* ta juyo ta kalleshi ya mata murmushi yace
'Baki tambayeni wani suna nayi wa yara khudubah (Huduba) dashi ba'

" tayi murmushi sannan tace abinda nake taso in tambaya kenan wallahi, wani suna aka sa
musu?

"Murmushi Ya fadada sannan ya dauki Baby boy dinsa ya rungume yace
'Saboda karamci, da mutunci, da Alfarma da kuma babbar kyauta da *ALHAJI* *SARAKEE*
Yamin yasa nayiwa dana huduba da suna *AMEENULLAH* Alkunyar sa kuma shine *LABEEB*
Inaso a ringa kiransa haka don suna ne me kyau sosai, Ya ajiye shi gefe sannan ya dauki Baby
girl din, itadai *SHUKRAH* sakin baki tayi bawae batayi sammanin haka ba, a a kawae dae
abin yazo mata a *BAZATA* ne, Ta zame daga kan bed din ta durkusa akan kafafunta zatayi
magana *SAFEER* Shima ya zame yayi Saurin sa hannunsa daya ya rufe mata baki sannan
yace, ita kuma nasa mata sunan Mamana wato Khadeeja za a dinga kiranta da suna
*LABEEBA* "

" Hawayen farin ciki ne yazubo mata tayi Saurin goge wa tana murmushi tana kara jin son
*SAFEER* Na ratsa jinin jikinta don ya mata komai a rayuwa yayi wa *DADDY* '
*NTA*Takwara, tasa hannu ta zame nasa hannun sannan tace
' Hakika banida bakin yimaka godiya don kayiwa mahaifi na abinda ba a taba yimasa, yayi
Saurin dakatar da ita ta hanyar cewa
'Nima Yamin abinda ba a taba min ba a rayuwa ta inajinsa kamar *ABBANA* , banajin a kawae
abinda zan masa nabiya sa abinda yamin saboda hk karki ce zaki min godiya kinji "

" Wayarsa ce ta fara ringing yayi Saurin mikewa ya dauko akan bed *MAMAH* Yagani ajikin
screen din yayi Saurin dagawa yamata sallama "

" Idan kai bazaka dawo ba to ka kawo min *SHUKRAH* kaji ko bakaji ba tace rai a bace "

" Dakyar ya iya bude baki yace *MAMAH* naji kuma insha Allah cikin satin nan zamu dawo "

" Gobe nake so ku dawo na fada maka... Tana gama fadar haka ta kashe wayarta "

" *SAFEER* YA juyo ya kalleta yace *MAMAH* Tace gobe take so mukoma so ynx zan fita
nayi mana Booking flight, Da sauri *SHUKRAH* tace to don itama zaman garin ya isheta

musamman ma ynx data haihu tana bukatar ganinta kusada *AMMI*' *NTA*
, tare suka fito *AZEEZA* Kadai ce a a parlour don *AHMAD* Bayanan, *SHUKRAH* ta mika
mata babyn hannunta sannan ta karbi na hannun *SAFEER* , "

" shiko yana fita ya nemi commercial car yace driver ya kaishi ' *AL* *HARAMAIN* *TRAVEL*
*AND* *TOURS* *LIMITED* , be dauki wani lokaciba ya gama komai, sai da ya shiga wani
shopping complex yayi shopping sosai sannan ya wuce gidan, Sanda ya isa ana kiraye~kirayen
sallar magrib nan yayi alwalla suka fice mosque tare da *AHMAD*, sai da su kayi sallah isha
sannan suka kamo hanyar gida, a hanyar dawowar sune *SAFEER* Yakewa *AHMAD*
Bayanin tafiyar su gobe, sosai *AHMAD* Yanuna rashin jin dadin tafiyar su koba komai sun
saba, kuma yana jin tausayin *Azeeza* sosai don tasa *LABEEB*& *LABEEBA* Sosai
azuciyarta, besan yadda zasuyi goben ba, Saurin goge Hawayen dasuka taru a idon sa yayi dai
dai sanda suke shigowa parlourn gidan, a tare *Ahmad* & *Safeer* sukaci abinci don tuni su
*SHUKRAH* sukaci nasu "

" Sanda suka gama cin abincin sukayi sallama, lokacin da *Safeer* yashiga dakin tararwa yayi
*SHUKRAH* na hada musu trolley yakarasa kan bed ya dauko *LABEEBA* Yamata kiss a kanta
yace Babyna ki tashi ga *PAPA* YA dawo, Baby kice you are welcome *Papa*"

" *SHUKRAH*tasa dariya tace kai *ya* *safeer* karfa son baby yamaka illa, yarinyar da kwanan
ta 3 kawae a duniya kake expecting tayi welcoming naka "

" Hade rai *safeer* yayi yana hararar ta toke ina ruwan ki, Ni banason irin hk ehe, Dariyar ta
cigaba da yi har sai da ta k'ularda Safeer yaja tsaki sannan ya kwantarda *Labeeba* ya musu
addu a sannan ya kwanta"


"Sanda *SHUKRAH* ta gama hada trolley toilet ta shige tayi wanka, koda ta fito kitchen ta wuce
tahada tea tasha sannan ta dawo dakin tasaka wata doguwar sleeping dress ta kwanta a bayan
*Safeer* "


" Ya Safeer kayi hakuri dani naga kamar kayi fushi, Shiru yayi mata alhalin yana jinta, nan ta
cigaba da masa magiya amma yaki kulawa, zuwa can dabara ta fado mata tasa harshen ta a
fuskarsa tafara yawo dashi, nan *safeer* ya juyo ya rungume ta....



*washe* *gari*

"Dukansu a airport, *Azeeza* rungume da *labeeba* tanata kuka kamar shi aka aikota, ita
tunaninta daya yadda zatayi rayuwa bau tare da Shukrah ba gakuma twins da tasa su a
zuciyarta,j *Ahmad* ganin kukan *Azeeza* bame karewabane yasashi mata alkawarin kaita

Nigeria before or after naming ceremony, saida sukaga tashin jirginsu sannan suka koma gida


~~~~~~~~~~~~~~~

*HAIYDAR* zaune gaban Hajiyarsa da alama fada take masa
"Haiydar wai kai yaushe zaka nutsu kayi Aure ne, akan idonka Safeer yayi Aure gashi har
matar ta haihu amma kai kaki kafitarda matar ko"

"Ba hk bane Hajiya yarinyar da nakeso yanzu tayi junior waec dinta, so jira nake tayi grads sai a
fara maganar auren "

" Kana hauka ne Haiydar, nace hauka kake Haiydar, ajinka zan cigaba da zama da kai har
nanda shekara 3 to inma bacci kake ka farka, Nabaka two weeks kakawo min mata ko in zabo
maka da kaina hajiya ta fada rai bace daga hk tafice ta barshi yana tunanin wae shi za a
samowa mata yarasa me zai kira wannan auren da Hajiya take shirin yimasa (Niko nace
*AUREN* *BAZATA* Xatayi maka), Ringing din dawayarsa yake ne yasa shi daukan car key
dinsa ya fice daga gidan, tafiyar minti talatin ce ta kai shi Airport, nan ya kwashe su sai gidan
Mamah, A hanya ne yake fadawa Safeer Hajiya zatamai AUREN BAZATA, me Safeer zeyi inba
dariya ba. . . Dakyar ya tsayar da dariyar sa yace karka damu Haiydar *AUREN* *BAZATA*
*ALHERI* *NE*. . .





*SHUKRAH* *YAR* *GATAN* *MIEMIEBEE*💞
[5/12, 1:48 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN* *BAZATA*👮🏻




WRITTEN BY
*ZAINAB* *YAKASAI*
*SHUKRAH*


Dedicated to *MIEMIEBEE*




3⃣7⃣

"Sanda suka karasa gidan Mamah cike suka shame shi da mutane as if to say ranar sunan ne,
*MIEMIE* Tazo da gudu ta rungume *SHUKRAH* tana murna da ganinta nan dae aka fara
gaishe gaishe, daga nan *Safeer* ya fadawa *Mamah* ze tafi gidan su *Haiydar*don nan
akwai hayaniya sosai, To kawae yace sannan suka fice "
" Saida *SHUKRAH*tayi wanka taci abinci Sannan ta kira *Amminta*, *Ammii* naganin kiran
amma taki picking don ita dama me alkunya ce, Text *SHUKRAH* ta mata tace sun sauka
lafiya, Bayan kusan awa daya ta mata reply tace sannun ku to"


*MIEMIE* sai nan nan takeda twins taki yarda kowa ya dauke su, wae 'ya' yanta ne


Washe gari *Ibteesam* tazo ta kawo wa babies kaya masu yawa, Hajiyar Haiydar ma tazo nan
take yiwa Mamah bayani cewa tabawa Haiydar two weeks ya kawo mata kuma taga kamar be
dau maganar T serious ba amma dae ta shirya bashi mamaki, don dama akwai wata yar
yayarta *Zafeera* zatayi wa yayar tata magana sai a hadasu don zafeera yarinya ce mai
hankali da nutsuwa sosai, dama tun farko tayi wa Haiydar sha awarta amma da taga kamar
zafeera bata gabansa yasa takyale amma tunda dae yanzu yaki kawo matar toko zata hadasu,
sosai Mamah ta goyawa Hajiya baya acewarta ae Haiydar ya girma, kuma ma ae shirme me zai
sashi cewa wae sai ya jira Miemie, nan dae suka gama magana Hajiya tayiwa Mamah alkawarin
duk me ake ciki zata fada mata, Sanda zata tafi ta ajiye wa twins Rapper na 100 sannan ta fice,
Mamah ta bita tana mata godiya "

" Duk wannan shirin da hajiya takeyi Haiydar be Sani ba don shi tunda tamishi magana bata
kuma yimasa ba, saboda hk yace ko dama wasa take masa shiyasa ma yasake ya cigaba da
harkokinsa"



"Gobe ne suna amma har yau *Ammii* taki zuwa taga su *labeeb* ,, *Mamah* ta kirata yafi a
Kirga amma kullum cewa take gata nan da taga abin bame karewa bane yasa takashe wayarta,
Gidan *Ammii* ya cika da yan uwa da abokan arziki amma ba *SHUKRAH* koda sukayi wa
*Ammii* maganar sunason akawo ta gidan ayi sunan anan cewa tayi ita ba ruwanta haka
sukayi ta surutansu suka gaji"



"Da yamma Alh Sarakee ya duro Nigeria don dama ya dade a Senegal bayanan ma akayi
haihuwar amma *SHUKRAH* ta mishi albishir din *Safeer* ya mishi takwara, Sanda ya iso ana
kiran sallar la asar saboda haka saida ya tsaya yayi sallah sannan ya karaso gida, *Ammii* ta

mishi girki kala kala amma saboda zumudin ganin *Labeeb*& *labeeba* Yasa koda yayi wanka
be tsaya cin abinci ba ya dauki babbar trolley daya shigo da ita ya fice, Sanda yake tada mota
*Ammii* ta same shi
"Yanzu Daddy fisabilillah gidan mutane xakaje ba kara ba alkunya, koni fa har yau banje ba"

"Daddy dariya yayi sannan yace to Ammii ni na hanaki zuwa ne? Akwai bukatar naga grand
child's dina shiyasa kikaga ma nadawo don bayau zan dawo ba ka ida sai next week zan dawo
amma na tattara komai na ajiye nazo sannan kice zaki hanamin zuwa ganin su, yana kaiwa nan
yayi reversed ya fice daga gidan, jiki ba kwari Ammii ta koma cikin gidan azuciyarta tana
mamakin Daddy don gaba daya yariga ya saba da turawa komai nasa irin nasu yake "

" Cikin Sa a Daddy ya samu Safeer da abbah a guest room da alama suna tattatuna abu me
mahimmanci ne, Da fara 'a Abbah ya tare shi yayi da Safeer ya durkusa har kasa ya gaida shi
cikeda ladabi "

" Ashe kuma an samu karuwa? *DADDY* Yace yana maida kallon sa gun *ABBAH*

"wallahi kam an samu Alh. *sarakee* D Hajiya *Khadija* Abban yace fuskarsa dauke da murna,
Allah dae ya raya mana su bisa tafarkin addinin musulunci "

" Hada baki sukayi dukansu wajen cewa Ameen "gyaran murya Daddy yayi sannan yace
Madallah Nagode da Girmamawa ko kuma ince da bani wani matsayi da kayi safeer, hakika kai
abin alfahari ne kuma ka can can chi yabo Allah ya maka albarka, Sakamon alkhairin dakamin
ka sama yaronka sunana nayi alkawarin daukan nauyin duk wani abu da za'a ci ko sha na kuma
dau nauyin gurin da za'a zauna kai hatta ragunan sunanma na hutar da kai insha Allah daga
nan zuwa dare za a kawo "

" Abbah yayi Saurin kallon shi yace haba Alhaji ae baza ' ayi haka ba, hidimar tayi yawa ae yau
fa ka dawo kasar ma gaba daya, ka barshi wallahi zamuyi komai insha Allah "

" Murrmushin manya Daddy yayi yace bafa ku kuka Sani ba haka kuma badan bazaku iyaba
yasa zanyi A a kawae dae tukwucin Alheri ne, so karku damu kudai kawai kuyi fatan ayi taro
lafiya a tashi lafiya "



Godiya dukansu suka mai kafin safeer yace bari yaje yasa akawo Twins, to Daddy yace
sannan suka cigaba da hirar su da Abbah"

"Sanda safeer ya shiga cikin gidan A parlour ya tararda *AYSHER*, *SHUKRAH* & *MIEMIE*,
Shukrah na Rike da Labeeba yayinda miemie ta rike labeeb, hararar miemie yayi sannan yace
waye ya baki ixinin daukar min yaro salon kiyar dashi ko, ke daman ba nutsuwa gareki ba, Hade
rai Miemie tayi ta ajiye labeeb da karfi kan kujera har sai da yaron ya fasa kuka, Safeer ya zo da

gudu zai rike ta tayi dakin Mamah da gudu ya bita, Aysher ce tayi Saurin daga labeeb tana jijjiga
shi "

" Jikin Hajiyar Haiydar ta fada, Hajiya Kinga ya Safeer yanamin gori akan 'ya' yansa ko, kuma
don na ajiye masa shine zai dakeni, tana kaiwa nan ta fashe da kuka kamar wadda ya daka, Shi
safeer ma mamaki ne ya hana masa cewa komai shi a duniya be taba ganin yarinya irin miemie
ba, Mamah tace ae sai ka fita tunda burinka ya cika kasata kuka kaji dadi, Miemie ta fakin idon
Mamah tamasa gwalo tace cikeda shagwaba Mamah yaushe zaki haifar mana twins muma
adena min gori "


" dariya sukayi dukansu sannan safeer ya fice yasa Aysher Da Shukrah su kaiwa Daddy twins"




WASHE GARI


Tun asuba mutane suka fara cika gidan duk da cewa a tourist camp za ayi taron sunan amma
kafin7:00 gida ba matsaka tsinke, ba ayi girki a gida ba kasancewar an riga anyi order a can
tourist camp din snacks kuma anyi order a me. Biggs, Drink ko Wata Aminiyar Mamah ce Hajiya
Maryam Anas ce tadau nauyi "

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

12:00pm na isa tourist camp gurin ya cika sosai da yan uwa da abokan arziki, Bayan bude

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0