Showing 33001 words to 36000 words out of 55173 words

Chapter 12 - Auren Bazata Book Compelet Zainab Yakasai Shukra

shiga daki ta taimaka mata ta dauraye bakinta ta hada mata
ruwan wanka ta shiga sannan ta dawo palour inda Ammii "


" Sanda Safeer ya dawo gidan sai dube dube yake yanason ganin Shukrah Amma bai ganta,
Kiran Miemie yayi da hannu ta dawo kusa dashi ta zauna "

" Shukrah fa? Ya tambaye ta kasa kasa "


" Nan miemie ta masa bayanin komai, aiko yayi saurin ture plate din gabansa ya shige dadin
Mamah "


" Tana kwance a kasa da alama fitowarta a wanka knn idonta a rufe kamar me bacci ya kara sa
kusa da ita ya zauna, Shafa fuskarta da yayi ne yasa ta bude idonta da sukayi ja alamar tana jin
jiki sosai "


" Mikewa tayi ta shige jikinsa don ba abinda take bukata a halin yanzu sai shi, Tana so taji
dumin jikinsa "

" Kara rungume ta yayi tsam kamar za a kwace masa ita yana shafa gashi kanta har zuwa
bayanta, yana mata rada a kunnenta "



" Kara shigewa jikinsa tayi tana lumshe ido, ita kadai tasan abinda takeji a jikinta (Nace wannan
ko sun manta a gidan Mamah suke) "


" kokarin kunce towel din jikinta yake aka bude kofa ya juyo da sauri yana kallon kofa, miemi ya
gani a tsaye ya watsa mata harara "

" ME ya shigo dake cikin dakin nn? Ya tambayeta rai a bace "


" Ammii ce tace in kira kaci abinci "

" Dalla fita k bani guri ya fada yana nuna mata kofa "


" Fita tayi da sauri dan tana tsoron bacin ransa "


" Wayarsa ya ciro yana snapping fuskan Shukra, Kafin kuma ya shiga kiran Aysher "


" Da Sallama tashigo cikin dakin Amma ganin a yanda suke yasata saurin juyawa "


" Dariya yayi sannan ya ce ta daukowa Shukra kaya tasa "


" Fita tayi bata wani dade ba ta dawo kanta a kasa ta mika masa kayan ta fice da sauri"


"Da kansa ya saka wa Shukra kayan kafin ya soma lallabata kan tazo suci abinci amma tace
bata san cin komai, da kyar ta yadda zata sha Tea "


" 4:15 pm Ammii tace itafa gida zata tafi, Safeer ne ya maidata gidan sannan ya dawo "


" Sai bayan Magrib Abbah ya dawo suka gaisa da Safeer ya kara masa murnar zama manager
a San Francisco "


" Shukra ma tazo suka gaisa da Abbah inda yayi ta samata albarka yana addu ar Allah ya
sauke ta lafiya ya bada nagari "



" Sai da sukayi Sallar isha sannan suka musu rakiya har mota suka tafi gidansu, Gidan tsaf
yake don Aysher da Miemie sun zo jiya sun gyara"


"Shukrah ce ta fara wanka tana fitowa ta kwanta sai baccin gajiya, Safeer ma da ya fito daga
wankan kwanciya kawae yayi ya musu addu a sai bacci............

SAFIYA TA GARI






SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞💞
[4/22, 7:37 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻





WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA


Dedicated to Miemie bie 💞


Wishes to show my appreciation to you Bilkisu galadanchi $Safiyya galadanchi for your luv, care
and advice giving to me, I wish you Success where ever you may go more power to your elbows
�

2⃣9⃣



"Washe gari Safeer beje ko ina ba a gida ya yini, Sai bayan la 'asar ne Haiydar yazo, Sosai
suka yi hira, Shukrah ta fito daga daki da gani a bacci ta tashi, Tana ganin Haiydar ta saki ranta
suka shiga gaisawa cikeda girma ma juna, Kallon Safeer tayi taga ita yake kallo "


" Ta bata rai tana harararsa' Zani gidan Ibtee tace tana turo baki "


" Maida kallon sa yayi kan wayarsa yace 'Bazaki ba' "


" Tafi minti biyu tsaye tana kallonsa kafin tasa kukan shagwaba harda bubbuga kafa a kasa
kamar karamar yarinya "

" Ganin ko kallonta yaki yi yasa ta zuwa gabansa ta Fisge wayar hannunsa

"Ni wallahi sai ka kula ni"

"Dariya Dukansu kusa sa ba kamar Safeer da yakeyi tsakani da Allah harda Sakkowa daga
kujera "


" Abin ya kara bata haushi dama yanzu abin haushi ba wuya yake mata ba, Ta kara fashe wa da
kuka tana kallon Haiydar wanda yake kokarin tsayar da dariyar sa "

" Harda kai ko? Nagode "

" yi hakuri Shukra, Ki rabu dashi kinji, yi tafiyar ki gidan Ibtee ki tawo min da Amal in zaki dawo,
Safeer ya fada kamar bashi ya gama mata dariya ba yanzu "


" Bazani ba ta fada tana hullar da wayarsa a kasa sannan ta wuce dakinta ta rufe kofa harda
key ta fada kan gado tana cigaba da kukanta "


" A parlour Haiydar ya kalli Safeer "wae kae meye hk ne zaka sa yarinya a gaba kana mata
dariya"


"Dariyar ya kuma yi kafin yace ae mu biyu mukayi mata dariyar naga "inji Safeer


" Amma ae taka tafi bata mata rai, wae meye ma abin dariya "


" Ni mamaki ta bani Duk fa yau bata kulani ba in nayi mata magana sai tamin Shiru ko kallo ban
isheta ba, shine ta bani dariya yanzu ae tazo tana wani bata rai wae zata gidan Ibtee "


" Murmushi me kyau Haiydar yayi sannan yace me kayi mata taki kula ka?

"wallahi ban mata komai ba rigima ce kawai irin tata "


" To Allah ya kyauta Haiydar ya ce tana kallon wayarsa da ta shiga vibrating, Sanda Haiydar ya

daga wayar shi kuma Safeer mikewa yayi ya shige Dakin Shukrah "


" Tana zaune tana charting a bakin gado ya karasa kusa da ita ya zauna sannan ya karbe wayar
Hannunta "



" ME zaki ci, Ya tambaye ta yana kallonta "


" Murya can ciki tace bakomai "


" kamo hannayenta yai duka biyun yana kallon cikinta daya dan turo kadan dan ita shukra dama
cikinta a shafe yake, "Haba Mana Shukrah Cute ya zaki ce ba zaki ci komai ba, ki daure ko tea
kisha"


"Ni bazan sha ba ta fada wane zatayi kuka "


" Ni Gidan Ibtee zani tayi min Tuwo "

" To Alhamdulillahi tunda zaki ci tuwon tashi na rakaki gidan Ibtee, Ya fada yana nikam da ita,
Hijab ya dauka a kan gado ya sa mata ya rike Hannunta suka fito parlour inda tayiwa Haiydar
sallama don ba da wuri zata dawo ba "


" Har bakin gate din su Ibtee yakai Shukra yace ze jira ta ta kawo masa Amal, Tana shiga
parlour taga Amal tana wasa ta dauketa takai masa sannan ta koma cikin gidan "


" sanda ta shiga gidan taga Ibtee tana leka bayan kujera, Shukra ta hade rai don batason yin
dariya "


" Lafiya Ibtee, Meye a gurin shukra tace tana lekawa itama "

" Ke banga Amal ba kuma fa wallahi yanzu na shiga daki na dawo kuma ban ganta ba Ibtee
tace hankali tashe "

" Shukrah ta gimtse dariyar ta ba tare da Ibtee ta gane ba tace to waye ya shigo gidan ya
dauketa? dama baki rufe parlour ba? "


" Inafa na rufe, keni zo mu fita Dalla ta fada sanda tasa Hijab dinta "


" Ai kuwa bamuga ta zama ba Shukrah tace sannan tana hannun Ibtee suka fito "


" Fitowarsu tayi dai dai da fitowar Haiydar da Safeer, Amal na hannun safeer ya bata wayarsa
tana wasa da ita "


" wata Nannauyar ajiyar zuciya Ibtee ta saki ta kalli Shukra, Shukrah ta tuntsire da Dariya harda
rike ciki "


" Ibtee takai mata duka 'bakida kirki Shukrah dama kinsan tana gidanki baki fadamin ba kikasa
na tashi hankalina"


"Har anan Shukrah dariya take taja hannun Ibtee ni zo muje kimin Tuwo shi nake so wallahi, "


Kin jawa kanki ae bazan yiba"


"Haba Ibtee Swthrt, matar abu turab, uwar gida sarautar mata daga ke ba kari, Maman Amal
Beauty, dan Allah kimin tuwon kinji Shukrah ta fada sanda suka shigo parlourn "


" To naji zanyi shknn Ibtee tace tana karasawa kitchen, ita kuma Shukrah tayi zaman ta a
parlour dan in ta shiga kitchen taji kamshin miyar baxata iya ciba "



" Sai ba adi salamu magrib sannan Shukrah ta koma cikin gidanta inda ta dauko Amal ta dawo
wa da ibtee ita ta koma ta samu Safeer zaune a palour yana Aiki a system dinsa "

" Ya Safeer zo muci tuwo ta fada tana ajiye flask din hannunta a kusa dashi, Ta wuce kitchen
dauko plate da spoons ta zuba musu, Ta mike ta bude fridge ta dauko musu lacasera ta ajiye
tana kallon Safeer "

" Sai da ya kammala abinda yake sannan ya switching off system din sannan ya sauko suka
soma cin abincin "



" Washe gari gurin 11:00 Safeer yace Shukra ta shirya yakai ta gidan Ammii daga nan su biya
su gaida Hajiyar Haiydar, Shukra harda dan tsalle ta shige toilet don yin wanka "

" Safeer ya juya ze fita kenan ya hango wayar Shukra dan dressing mirror, Da sauri ya karasa
ya dauka Kai tsaye contact dinta ya fara dubawa cikin sa 'a kuwa yaci karo da wata Number
anyi saving as MY NUMBER, Da sauri ya dauko wayarsa ya dau Number yasa yayi dialing,
Tana fara ringing yayi saurin Rejecting yayi mata Saving number sa as "HUSBY"
"Sannan yayi saving tata number as "WIFEY"


"Koda Shukrah ta fito da sauri ta shirya ta samu Ya Safeer a parlour suka kama hanyar gidan
Ammii"


"sanda suka isa Safeer ne ya dauko wa Shukrah tsarabar su Ammii suka shiga a tare cikin sa a
kuwa suka tarar da Daddy na gida "

" Safeer ya dade sosai yana hira da Daddy sannan Y musu sallama ya tafi "


" Misalin karfe hudu da rabi wayar Shukrah dake hannun Areef ta soma ringing, mika mata yayi
da sauri
"Baki sake take kallon number ita dai tasan ba ita tayi saving number nn ba, Tana ta mamaki
har kiran ya katse wani ya shigo, Sai anan ta dauka da Sallamar ta"
"Jin muryan Safeer yana Answer mata sallama yasata sauke ajiyar zuciya"


"ki fito mu tafi gidansu Haiydar"


"To kawai tace sannan ta shiga dakin Mamah tayi mata sallama ta fito ta samu Safeer a motar
sa suka tafi Gidansu Haiydar "


" Sosai Shukrah ta samu karba ta musamman a gurin Hajiyar su Haiydar, Don Hajiyar Haiydar

mace ce mai kirki da son mutane duk da kasan ce watar ta mai kudin gaske amma kudinta be
sa mata girman kai ba "


" Sai da sukayi sallar isha sannan suka koma gidansu inda Hajiya ta cika Shukrah da tsaraba,
sosai Shukrah ta shiga ran Hajiyar don har tana tambayar ta sanda zata sake zuwar Mata.........





SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[4/27, 1:53 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻




WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA





Dedicated to Miemie bie 😘






3⃣0⃣



Three Months later


"Shukra zaune a dakinta ta sa akwatuna a gaba tana duba wa zallar kayan Babe ne aciki, a
zuciyarta tana mamakin irin wannan soyayya da iyayen ta, iyayen Safeer kai harma da Hajiyar
Haiydar suke nuna wa babynta, takai one hour tana aikin kayan kafin ta ture kayan ta jingina a
jikin gado tana shafa cikin ta dan wata shida wanda ya yayi girma sosai sai kace dan wata tara,

Mamaki da tsoron girman cikin ya hana mata nutsuwa a yan kwanakin nan ga nauyi kamar me "



" Tana cikin haka Safeer ya shigo cikin dakin yana Waya da alama da friend dinsa suke wayar,
Sai da ya gama ya juyo yana karawa Shukrah kallo wadda gaba daya ma hankakinta baya
wajensa, janyota yayi jikinsa yana shafa kanta "

" Shukrah meye matsalar??

"Tsoro nakeji ya Safeer ta bashi Answer kamar zatayi kuka "

" Dago kanta yayi yana mata kallon mamaki kafin yace tsoron me?


"Wannan cikin mana yayi girma da yawa kamar wadda zata haifi guda goma "


" To Shukrah ae lafiya ce, kuma ma ko guda goma kika haifa ai ba matsala bane indai Allah ya
baki lafiya ko "



" Kuka kawae tasaka masa wae ita BAZATA haifi guda goma ba "



" Safeer dae yana mamakin Shukrah yanzu ba dama ayi magana sai tasa kuka, ayi mata wasa
ta dauka da zafi, lallashinta yashiga yi yana cewa insha Allah daya zata haifa mai kama dashi
tunda batason goma "


" o o ni me kama dani zan haifa tace tana turo baki "


" To naji Allah ya sauke ki lafiya shike nan "


" A a "

" Sai me kuma "

" Sai da ta dauke kai kafin tace ni gidan Ammii zaka kaini "

" Kema dae kya ji kunya Shukrah jiya fa har 10:00pm kina gidan Ammii kuma yau ma wae sa rai
kike na kaiki "


" Kukan ta ta cigaba wannan karon har tana hadawa da kaimai duka "


" Ganin Abin Shukrah ba me kare bane yasa Safeer saurin ture ta a jikinsa ya mike ya fice, ita
ko Kukan ta take tsakani da Allah a haka dae bacci ya kwashe ta a gurin "



" Sai bayan sallah magrib sannan Safeer ya dawo gidan Shukra na zaune a parlour tana cin
gireba, suna hada ido ta daure rai ta maida kallon ta jikin TV"


"Yammata na, yanzu kina kallona na shigo cikin gidanki amma ba sannu da zuwa ba komai "


" Ban iya ba tace ba tare da ta kalleshi ba "

" Baki iya gaisuwa ba Shukrah ya fada sanda ya karaso kusa da ita yana binta da kallon
mamaki "

" To kaima baka iya dubiya ba ta fada tana murguda masa baki "


" iye Shukrah ya Safeer din kike yiwa haka? Yayi maganar irin abin ya bashi mamakin nan "


" komai ba tace ba sai ma juya masa baya datayi tana cin gireba hankali kwance "


" Ya dade a tsaye yana mata kallon mamaki kafin ya girgiza kansa ya wuce dakinsa a ransa
yana cewa

"Shukrah dae ta zama a lallaba"



"Shukrah na nan zaune har 9:00tayi, wayarta ce tayi ringing tayi saurin dauka kamar me jira DR

WAHEEDA ta gani jikin screen din sai da tayi murmushi kafin tayi picking, tayi mata Sallama ta
answer "


" Bayan yan gaishe gaishe ne, waheeda tace Shukrah bakida kirki wallahi ace kin samu cikin
har 6 Months amma baki fada min ba "


" Shukrah wadda kunya ta rufe tayi murmushi batada abinda za tace shiyasa tayi shiru "


" Kinyi Shiru Shukrah ko bakya jina ne? Waheeda ta tambaya "

" Da kyar Shukrah ta ce mata kiyi hakuri ae nayi tunanin ya fada miki "


" Inafa ya fada min, Ae zan gamu dashi ne kedai Allah ya sauke ki lafiya, Badai wata matsalar
ko?


"Ba matsala wlh "


" Daga haka dae Shukrah yi sallama Shukrah dae har anan bata dena jin kunya ba, Don sosai
take jin nauyin DR Waheeda hakan nema ya hanata sanar mata tun farko "






" To kamar yadda Safeer Yayi wa Shukrah alkawarin zasu sake zuwa San Francisco haka kuwa
akayi don yau Safeer Bayan ya tashi daga office Golden season travelling agency ya nufa kai
tsaye yayi musu visa shida Shukrah da Miemie "



" Sanda ya shigo gida tarar wa yayi Shukrah tayi baki wasu yan uwansu sune na katsina suka
zo, Tsayawa yayi suka gaisa sannan ya wuce, Shukrah kamar bazata tashi ba tayi zamanta ta
cigaba da hirar ta sai da wata Auntyn ta Aunty Nabeehart ta harare ta
" Kin tashi kin bi mijin ki ko sai na kwada miki mari tukun na"

"Turo baki Shukrah tayi ta tashi tana cewa Aunty fa banida lpy sannan ta shige dakin Safeer "


" Sanda ta shiga ta samu har ya shige wanka saboda haka sai kawae ta fito mai da kaya tayi
kwanciyar ta kana game a wayar sa "


" Sanda ya fito gaban dressing mirror ya nufa ya dauko cream ya dawo kusada Shukrah ya
zauna, Tana ganin haka tayi saurin minimizing game din ta ajiye wayar ta mike, sai da ta karbi
cream din hannunsa sannan ta kalleshi ta fara magana kasa kasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0