Showing 48001 words to 51000 words out of 76927 words

Chapter 17 - Auren Hadi Book Compelet Samira Haruna

22 Jun 2026

1119

nunata da hannu yace
"ke kuma wannan shiga haka bak'a k'irin kamar wata 'yar wuta."

Turo baki tayi duk da baya gani sannan tace "yaya Salman ka dubi lokaci fa ya wuce, wallahi
nayi retard."

Lokaci ya duba ya k'ara zaro ido yana fad'in "kai kai kai, lallai kam, to wuce muje ina fatan dai
kin karya?"

"Ni ban karya ba, kawai idan naje naci wani abu."

Wucewa sukayi bayan ta rufe d'akin, tunda suka kama hanya tayi shiru tana kallon gari, Salman
ne ya kalleta yace "ina fatan dai ba zaki cire nik'ab d'innan ba idan kinje can?"

"Haba yaya Salman dole zan cire mana dan nasha iska, lokacin zafi ne gashi yanzu ba'a ruwa
sosai."

Hararanta yayi yace "bana so, karki bud'e fuskarki kowa ya gani."

"Amma yaya Salman akwai takura fa, kai baka san nik'ab ba wallahi tana hana mutum
kyakyawan shed'a."

Kallonta yayi irin ba wasanan yace "wallahi idan naji labarin kin cireta, to daga ranar bake ba
k'ara komawa makaranta."

Cikin shagwab'a tace "to yayana idan zan ci abinci kuma fa?"

"To na yarda ki d'aga idan zaki ci abinci, amma da kin ida ki mayar."

Hararan gefen ido ta watsa masa a ranta tace "sai kace wani sona yake da yake takura min
haka"

Kallonshi tayi tace "wai yaya Salman ta yaya ka sama min gurbin karatu anan ne cikin sauri
haka?"

Ba tare daya kalleta ba yace "to miye na wahala a ciki, dama anan kike karatu kuma sun baki
gurbi in da zaki ci gaba, kawai baki zo da wuri bane har anyi karatun wata biyu babu ke."

Cikin tsoro Ummi tace "to yanzu idan suka tambayeni ya zance masu?"

"Na gama da wannan ma, dan na fad'a masu kinyi aure kuma yanzu ba kida lafiya."

Wani kallo ta masa tace "to me kace masu yake damuna?"

Wani kallon raini ya mata yace "na fad'a masu kina fama da laulayi ne."

A firgice ta kalleshi tace "laulayi, na ciki ko na me?"

"Ke wanne kika sani?"

Kallon gabanta tayi tace "na san na ciki."

Shima ba tare daya kalleta ba yace "to shi nake nufi."

Wani lallausan murmushi tayi tare da dafe cikin tace "wai ciki, Ummi da ciki, babbar magana."

Kallonta yayi yace "kina sonshi kenan?"

"Ina so sosai, Allah ya nuna min na samu nima."

Kallon ba kida hankali ya mata yace "keda ko hanyar daya bi baki bi ba, kuma a hakan kike
neman shi."

Bata kalleshi ba tace "to miye a ciki? ai abun rabone kura ta haifi akuya."

Kallonta yayi yace "lallai kam, amma ki sani wanna kura za tasha dukan tsiya idan ta haifi
akuya."

"Lallai kam, watak'ila kuma ba zata sha ba." fad'ar haka yayi daidai da zuwansu ecole d'in,
bud'a k'ofar tayi zata fita tace "sai anjima."

"Idan kun tashi ki kira ni." ya fad'a yana kallonta, har zata fita ta tsaya tare da tara masa hannu

tace "kud'in abinci na."

Hannu yasa aljihu ya fito da kud'i yana tambayar ta "nawa zan baki?kin san ni ba d'a gareni ba
bare na san nawa ake bayarwa, kuma ma ke har wani kud'i za'a baki da girmanki."

"To ina girman yake? har yanzu fa ban wuce jaririya ba."

Kallonta yayi sosai yace "a hakan, uwar wasu kakar wasu?"

Cikin shagwab'a tace "nifa yarinya ce, har yanzu a wanke nake babu datti."

"Allah ya shirya min ke 'yan matana, ni fad'a min nawa zan baki."

Dariya tayi tace "ameen yaya Salman, kawai ka kimanta sai ka bani."

Kafin su ankara suka ji k'arar k'araurawa (sonner) lokacin shiga aji yayi.

Cikin hanzari tace "kawai ka lissafa nawa ake baka da kana kamar ni."

"Ni ai ina kamar ki kud'in makaranta ma ni na biyawa kaina."

Cike da k'aguwa Ummi tace "to kawai ka ban 1000f ta isheni."

Dubawa yayi sai dai babu wacce ta buk'ata, dan haka ya bata 5000f tana karb'a ta fita tana
fad'in "zan aje maka canjinka, sai kazo."

Kallonta yayi sai gudu take har ta shige ciki, kai ya girgiza yaja motar yana fad'in "kaji gudun da
take kamar yarinya, ba zata yi hankali ba wannan har saina saita ta."

Yaji dad'i sosai ganin yanda kayan suka mata d'as da ita, gashi duk sun rufe jikinta sai idanunta
kawai da hannayenta ne a waje, dan takalman data saka ma k'afa ciki ne maras tudu(valerine)
bak'ak'e.




```SAM```�
11/03/2019 à 17:51 - Mamar Latif💃: 💑AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_


*HASBUNALLAH WANI'IMAL WAKIL*

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_��

*Page*


8⃣1⃣_8⃣2⃣


Su Jawahir sunyi farin ciki sosai ganin Ummi a makaranta ba zato ba tsammani, haka suka
kasance tare har lokacin tashi yayi Ummi ta kira Salman yazo ya d'auketa.

Sosai su Jawahir suka birge Ummi ganinsu da tayi kowace da d'an k'aramin cikinta tana turawa,
babban abinda yafi shiga ranta shine, ganin yanda suka canja lokaci d'aya duk sun canja
abincin cinsu, abinda waccen take ci yanzu bata ko san k'amshinsa, haka abinda wata bata ci a
da yanzu kuma tana cinshi sosai, wannan canjin ya birge Ummi sosai.
```ALLAH YA KAWO MAI ALBARKA```

Suna shiga gida ta cire nik'ab da hijab da jakarta ta yab'a akan kujerar falo ita kuma tayi ciki,
Salman kam ruwa ya d'auko a fridge ya zauna yana sha, ya jima zauna yana jiran ta fito ta fad'a
mashi abinda zata ci dan ya siyo mata amma shiru, mik'ewa yayi ya nufi d'akin, k'ofar kawai ya
bud'a ba tare daya shiga ba.
Da k'yar ya had'e wasu yawu da suka tarar masa sannan ya kau da kansa gefe yana satar
kallonta yana tambayarta "amm, dama na zone naji abinda zaki ci na siyo maki?"

Ummi dake ci gaba da shafa manta d'aure da d'an k'aramin towel d'in da ko cinya bai k'arasa
rufe mata ba, sannan duk ta barbaza manyan kitsonta a bayanta ya kwanta, cike da karsashi
tace masa,

"A'a yaya Salman ina zuwa yanzu saina dafa mana abinda zamu ci, saurin da nake kenan
dama."

Cikin satar kallonta yace "kefa yanzu kika dawo kina buk'atar hutu, kawai ki fad'amin me zaki
ci."

Juyowa tayi ta nufi wadrob ta bud'a tana duba kayan da zata d'auka tana fad'in "a'a yaya
Salman zan dafa da kaina, a cikin kwana shida na karatu, kwana hud'u duk zan dinga tasowa
k'arfe 13:30 , kaga idan nace zaka dinga siyomin abinci ai ban kyauta ba, dan haka ka barshi
yanzu zan fito na d'ora mana yafi ace munyi latin cin abinci amma ba siyowa ba, kuma ma naga
ai daga ni sai kaine a gidan."

Murmushi yayi tare da kallonta yace "sai kin fito."

Sai lokacin ta kalleshi taga yanata wani sunkuye kai, a hankali ta tako tazo gabanshi ta tsaya,
hannunshi ta kama kamar yaro ta d'ora a gefen fuskarta tace "kace Allah ya min albarka, kamar
yanda Abba yake min."

Duburburcewa yayi ya rasa me zai fad'a, gaba d'aya ya rasa network d'inshi take idonshi suka
sauya suka fara canja launi, Ummi kam tsoro ne ya rufeta dan haka taja da baya tana fad'in "ina
zuwa yanzu."

Kamar zai tashi sama haka ya fita daga d'akin ya shiga nashi, gado ya fad'a ruf da ciki yana taro
abinda k'wak'walwarshi ta gane mashi hakan yasa kuma ciwonshi ya k'ara tunzura yana dad'a
gaba.

Maganinshi ya d'auko ya b'alla yasha tare da mai sa bacci yasha, lokaci k'alilan bacci yayi gaba
dashi ba dan ciwon ya bari ba.


Ummi na fitowa cuisine ta shiga ta fara had'a abincin rana mai sauk'in sarafawa, 14:40 ta
kammala d'akin Salman ta shiga ta tashe shi daga bacci, yana fitowa tare suka ci abinci suna
idawa ta d'auke kwanukan ta mayar cuisine ta wanke ta goge duk inda ta b'ata.

Tana fitowa Salman ta gani da jakar makarantar ta ya fiddo litattafanta yana dubawa, k'arasowa
tayi tana kallonshi ta zauna, kallonta yayi yace "kin gane darasin da aka maki yau?"

Gyara zama tayi tace " taya zan gane da zuwa d'aya, dole ina buk'atar na samu mai koyamin
idan na dawo gida."

Cike da raha Salman yace "to in hakane ki dinga biyana duk
wata saina dinga koya maki."

Matsowa tayi kusa dashi tace "da gaske yaya Salman? to ka fad'i nawa kake so na baka?"

Cike da fara'a yace " ki fad'a da kanki me zaki iya bayarwa duk wata."

"Duk wata?" ta tambayeshi, kai ya d'aga mata alamar Eh, dan haka tace "ok, to ka koyamin, ni
kuma duk wata zan biyaka ta hanyar haifa maka kyakyawan yaro ko yarinya masu kama da
kai."

Salman bai san lokacin daya fashe da dariya ba yana fad'in "yara dai, duk wata? ba kida dama
Abu."

Turo baki tayi gaba cike da shagwab'a tace "Eh mana, miye a ciki?"

Da k'yar ya tsagaita da dariyar yana kallonta yace "to amma me yasa sai masu kama dani, me
yasa ba kya san ki haifi masu kama dake?"

K'asa tayi da kanta tace "to ai ka fini kyau ne shi yasa."

Ya mutsa fuska yayi yace "Ummi waya fad'a maki ba kya da kyau?"

Kallon idonshi tayi tace "kasha fad'amin haka sau da dama, har wani lokaci ma ka kan
kwatantani da mage ko aljana."

K'asa yayi da kanshi dan bai tab'a tunanin abin yana cikin ranta ba har yanzu, kallonta yayi yace
"Abu karki damu da wannan, kawai ina fad'a ne amma ba wai yana nufin ke mummuna bace,
kina da abinda ba kowa keda shi ba."

Hararan wasa ta masa tace "hmm, kamar me kenan?"

Kallonta yayi sosai kafin yace "kamar idonki masu abin al'ajabi, wanda basa kalluwa ga ragon
namiji bare kuma mace, sannan kina da dinple wanda yake k'ara maki kyau idan kina dariya ko
murmushi ke har ma da kuka idan kina yi."

Wai dad'i kashe Ummi, yau Salman d'inta ne ke yabanta haka, farin ciki ne ya k'umeta yasa tayi
fari da ido cikin kissa tace "hmm, to ni dai naji muyi karatun."


*A kwana a tashi* lokaci na tafiya al'amura na faruwa da dama daga rayuwar Salman da Ummi,
tun lokacin Salman kema Ummi lesson ba dare ba rana in dai har yana gida, shak'uwa sosai ta
k'ara shiga tsakaninsu a wani b'angaren kuma suna k'ara zurfafa soyayyar da sukewa junansu.

*Sati uku* da fara karatunta Salman ya sake tafiya Cotonou, da k'yar ya iya kwana goma a cikin
sati biyun daya d'iba zaiyi, dan kuwa babu abinda yake daya wuce tunanin Ummi da kewarta.

Haka ma a wajen Ummi, dan kuwa ko abinci ta daina ci sosai dan yanzu ta saba da cin abinci
tare da Salman, kafin ya tafi saida ya d'auko Islam tare da Momy (autar su Salman) ya kawosu
dan su tayata bacci, hakanne yake rage mata damuwa da tunani da kuma k'arfafa gwiwar da
Salman yake mata akan karatu duk lokacin da sukayi waya.
Tunda safe Salman ya kan kirata yaji ya suka tashi, kasancewar yana da jadawalin lokacin
karatunta (emploi du temps) yasa tana fitowa daga aji kiran Salman zai shigo wayarta, da dare
haka zasu sha hira abinsu har dama karatu yana k'ara kwatanta mata a waya.

*Ranar* da Salman ya dawo, ya dawo da k'udirin sauke hakk'in dake kanshi, yayi niyyar
kusantar Ummi ta hanyar data dace bawai ko ta halin yaya ba.

Rashin sa'a a ranar daya zo, a ranar bak'on Ummi yazo (period), bayan wannan kuma gashi
suna shirin shiga satin jarabawa, hakan yasa Ummi ta zama busy sosai bata da lokacin komai
har lokacin kanta, hak'uri kawai Salman yayi amma ba dan haka yaso ba.


*Litinin* Ummi suka shiga zana jarabawa, kwana uku sukayi kuma a kwana ukun nan Ummi ko
abinci bata san ci sai Salman ya matsa mata lamba sannan, hasali ma ba ita ke dafa abincin ba
siyowa Salman keyi, ririta ta kawai yake dan shirin shi shine suna gama jarabawa tofa shima
dole ya shiga hq dan tashi jarabawar.

*A kullum d'an Adam na nashi ne, Allah ma yana nashi, mutum baya da ikon tsarawa kansa
rayuwa sai yanda Allah ya tsara masa* su Ummi na fitowa daga aji aka fara ruwa kamar da
bakin k'warya, zuwan Salman dan ya d'auketa yasa Ummi fitowa daga mafakarta ta k'arasa in
da yake, ruwa sun jik'ata sosai hakan yasa tana shiga mota ta cire hijab d'inta da jakarta, suna
zuwa gida ma haka suka tsaya suna kallon juna ganin yanda ruwan ke sauka da k'arfi.

Cike da shagwab'a Ummi tace "to yaya Salman kaine namiji kuma mai hakk'in kula dani, dan
haka ka rufeni saimu shige ciki."


Hararanta Salman yayi yace "ahan, kenan yau kin tuna haka ko?"

Turo baki tayi gaba tace "to ni dai wallahi idan na shiga ruwan nan zan iya mura, dama gashi na
riga dana jik'e."

"To shikenan, ki shirya zan fita yanzu kema saiki fito."

Fita yayi ya zagaya ma zauninta ya kamo hannayenta ta fito, rumgumota yayi a jikinshi ya
matseta a hankali ya d'agata ya d'ora k'afafunta akan nashi sannan ya d'auko hijab d'inta ya
masu runfa dashi, a hankali ya fara takawa saboda tana bisa k'afafunshi ne kamar ya d'auketa
ne, idon Ummi na kan k'irjin Salman data d'ora hannayenta ta kasa had'a ido da shi, shi kam
fuskarta kawai yake kallo tare da k'ara matse kunkuminta da duka hannayenshi biyu.

Suna shiga falo ta zame jikinta daga nashi, sai dai duk da haka saida suka jik'e da ruwa take
jikin Ummi ya fara rawar d'ari, kallonta Salman yayi lokacin da yake cire takalmanshi k'afa ciki,
saida ya gama cirewa ya d'ago yana b'alle ma b'allan rigarshi yace,

"Ya dai malama?"

Bud'ar baki tayi zatayi magana ji kake "hatshimmm." ta b'arzo wata atshiwa, ja baya Salman
yayi yana fad'in "kai, haba ke kuwa atshiwa ba sanarwa kawai saiki fyace ni."

Wata maganar taje tayi amma ina sai wata atshiwar tare da fitowar majina a hancinta, ajiyar
zuciya Salman ya sauke cike da tausayawa ya matso kusa da ita yana kallon fuskarta,
kallabinta ya cire ya jefar a kujera haka ma ribom (chouchou) d'inta take gashinta marar kitso ya
zube a bayanta wanda ya jik'e da ruwa sai k'amshin man kai yake *(BLACK QUEEN
{COCONUT OIL} )*.

A hankali ya had'ata da k'irjinshi ya zura hannayenshi a bayanta ya zuge zif d'in rigarta, tana
kallonshi har ya rabata da rigarta yayi saura bras d'inta fara, sunkuyawa yayi yana shirin zame
wandonta daga jikinta tayi saurin ja da baya tana fad'in "a'a ya isa haka....atshimm." ta k'arasa
maganar tana k'ara atshaweshi.
Tissue ya ciro a aljihunshi ya matso kusanta yasa ya goge mata majina har da cewa "fyato"
kallonshi tayi sai dai ba tayi magana saboda ya rufe mata hanci da tissue, bud'e mata ido yayi
ya sake cewa "fyato"

Tsaf Ummi ta fyato ya goge mata, juyawa tayi ta bud'e d'akinta ta shige tana ci gaba da
atshiwar, shi kam binta yayi da kallo kafin shi ma ya nufi nashi d'akin.


Zuwa dare Ummi ta galabaita sosai dan mura bata mata da dad'i dama in dai ta damk'eta
abinka ga jar fata duk ta fita hayyacinta ta sukurkurce, tun doguwar rigar data saka dawowarta
har yanzu ita ce a jikinta, kanta duk ya yamutse saboda kwanci da take hancinta har yayi ja
saboda goge majina, idonta banda ruwa ba abinda sukeyi ko magana bata ji sosai dan
kunnuwanta sun d'ume, haka gaba d'aya mak'oshinta ciwo yake ga bala'in ciwon kai, duk ta
rikita Salman da kukan shagwab'ar da take bata tab'a tunanin zai damu haka ba, amma data ga
ya nuna damuwa a fili saita k'ara narkewa tana zuba shagwab'arta.

Zaune suke a falo duk Ummi ta dunk'ule a cikin k'aton bargon da Salman ya d'auko mata a
d'akinshi wai ita zazzab'i, Salman ne ya fito daga cuisine hannunshi rik'e da cup na tea, yana
zuwa ya zauna kusa da ita yana fad'in " yawwa Abun Alhaji to karb'i kisha wannan, Insha Allah
zaki ji sauk'i kinji."
Ganin bata amsa ba yasa ya kalleta, idonsu ne suka had'e dana juna ganin idonta suna neman
kawo ruwa yasa hannunshi ya shafe mata idon yana fad'in "miye kuma?"

Leb'en k'asa ta turo gaba kamar mai shirin fashewa da kuka tana fad'in "tsoro nake ji yaya
Salman."

Kallon mamaki ya mata yace "tsoron me kuma? keda kina tare da ni miye zai baki tsoro a

duniyar nan."

Wani shu'umin kallo ta masa tace "da gaske yaya Salman? to amma ai bana da tabbacin zaka
zauna tare dani har k'arshen rayuwata."

Wani kallo ya mata da yasa tayi k'asa da kanta kafin yace "Ummi, me yasa kike tunanin haka?"

Kai ta girgiza tana fad'in "ba komai."

"To in dai hakane karki sake wannan tunanin, ni ina tare dake kuma zan zauna dake har abada,
sannan babu abinda zan bari ya cutar dake matuk'ar ina raye, saboda ni yayanki ne mai alhakin
kula dake."

Dad'i ne ya kama Ummi yasa ta fad'a a k'irjinshi tana murmushi tare da fad'in "oh, mon ice
cream."

Lek'a fuskarta yayi yana fad'in "aw, da ice cream zaki had'a yayanki?"

Dariya tayi tare da tusa kanta cikin k'irjinshi tace "to ai saboda irin son da nake masa ne yasa."

"Kenan son da kike min ma baya dayawa?"

Da sauri ta d'ago daga k'irjinshi za tayi magana, suna had'a ido ya mata kwarjini dan haka tayi
shiru ta koma k'irjinshi tana fad'in "kawai ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0