Showing 39001 words to 42000 words out of 76927 words

Chapter 14 - Auren Hadi Book Compelet Samira Haruna

22 Jun 2026

1107

kake ban sani ba, ashe duk cika bakin nan na banza ne, tirr" ta fad'a tare da kau
da kanta, ci gaba tayi da cewa,

"In dai haka kake to baka dace da girman kai ba, banyi tunanin haka daga gareka ba, kuma ka
sani wallahi koda ina cikin tsarki ba zan tab'a baka kaina ba, domin kuwa kana min kallon
k'ask'anci, na san zaman mu ba zai d'ore ba dan haka zan ci gaba da ajiyar budurci na dan na
kaishi in da ya dace."
Tana fad'a ta shiga toilet ta barshi nan, yanda kanshi ke sarawa ga jikinshi rawa kawai yake a
daddafe ya kai d'akinshi ya d'auki maganinshi saida ya had'iyi maganin sannan ya shiga toilet
ya kifa kanshi a pampo ya sha ruwa.

Fitowa yayi daga d'akin saboda har yanzu Islam bacci take, kai tsaye motar shi ya shiga ya
kifa kansa a stiyari ido rufe, kalaman Ummi ne kawai ke dawo masa wai " wallahi koda ina cikin
tsarki ba zan tab'a baka kaina ba."

Kuma wai "zan kai budurci na a in da ya dace"

"Waye ya dace kenan daya wuce ni mijinta?" babu amsar tambaya.


Ya jima sosai a haka kafin ya bud'a idonshi cikin muryar tausayi yace "Allah ka kare ni daga
aikata ba daidai ba"

Wasu zafafan hawaye ne suka zubo a kumatunshi, gogewa yayi tare da tayar da mota ya fita.

Yana saman hanya ya kira Khamis ya tambaye shi yana ina, cewa yayi "ina gida amma yanzu
zan fita, zanje gida wajen su Mama"

Cikin dakusashiyar muryarshi yace "ok jira ni ina zuwa yanzu."

"To sai ka zo" ya fad'a a takaice.

Yana zuwa Khamis ya fito suka wuce, a hanya ne Salman ne ya kalli Khamis yace "Khamis dan
Allah ka taimaka min, ka sanar dasu Abba ina neman auren Nuseiba wallahi bada wasa nake
ba."

Cike da kosawa Khamis yace "Salman na fad'a maka ka daina sani cikin maganar nan, idan fa
ka fad'a babu wanda zai hana ka auren Nuseiba amma ka tsaya ni kana takura min."

Cikin damuwa Salman yace "me yasa ba zaka gane ba Khamis? ina cikin wani hali kuma ina
buk'atar taimako wallahi bana so na ci gaba da zama da yarinyar nan a gidan nan mu kad'ai, in
ba haka ba ban san mi zai biyo baya ba."

"Khamis yau saura kad'an na aikata abun kunya, saura kad'an na jawa kaina raini, saura kad'an

na aikata abinda zai dameni a gaba, saura k'iris na kusance ta."

Cikin raini Khamis yace "wai raini, kai a ganinka wannan ne raini?"

"To bari kaji, wallahi ko yanzu in kayi wasa to ina baka tabbacin cewa abinda ya faru a baya
shine zai sake faruwa a yanzu, dan tabbas sai kaga likita."

"Cousin, kayi abinda ya dace da kai kafin ka jefa rayuwarka cikin matsala, kana da mata dan
haka banga dalilin da zaisa ka bari ciwo ya illata ka ba."

"Malam ka sauke girman kai da izza ka kwashi albarkatun dake tattare da mace, Ummi yarinya
ce sosai idan aka had'ata da kai, zaka iya tafiyar da ita yanda ranka yake so domin kuwa k'wace
goriba a hannun kuturu abune mai sauk'i."

Girgiza kai yayi yana kallon gabanshi yace "baka san wacece wannan yarinyar ba shiyasa, ka
san ma mi tace min?"

"A'a" kallonshi yayi yace "tace ba zata bani kanta ba saboda ban dace ba"

"Hahahaha, to ai gaskiya ta fad'a saboda yanda kake cin magani haka wacece zata yarda ta
baka kanta? ai su mata saida rarrashi da lallami sannan idan kayi sa'a su baka ka lasa."

Cike da mamaki yace "bayan rarrashin ma sai kayi sa'a?"

Dariya Khamis yayi yace "sosai kuwa, tunda kayan marmarin suna gurin su."

Kai ya girgiza yace "wannan k'ask'anci ai yayi yawa, bayan ma jikina da zata gani saina tsaya
ina lallab'ata bayan matata ce sadaki na biya, kuma a haka ace wai sai nayi sa'a haba."

Kallonshi Khamis yayi yace "kai ma ai jikinta zaka gani, ko kuwa?"

Tabe baki yayi bai sake magana ba har suka kai gidan, da sallama suka shiga sun samu su
Mama duka a tsakar gida suna 'yan aikace aikace, gaisawa su kayi kafin suka zauna.

Mama ce ta fara kiran "Rumana, Rumana" daga cikin d'aki ta amsa da "iye"

"Ke ki kawo ruwa"

"To" ta fad'a a takaice, Salman kam takaici kawai yake wai ace mahaifiyar ki ta kira ki kice mata
iye babu ladabi babu girmamawa, wannan shine dalilin da yasa baya san shiga harkarta ma.

Haka ta fito gantsar gantsar ta aje masu ruwa da wata doguwar rigarta ko d'an kwali babu a
kanta, ko kallon ruwan Salman baiyi ba dan yanda yaga kanta a cunkushe yaji zuciyarshi ma

na tashi, "ina kwana".

Ta fad'a tare da juyawa zata koma d'aki, cikin fad'a Salman yace "ke ina d'an kwalinki kike yawo
haka?"

Cikin jin kunya tace "yana d'aki"

"Oho shine kike yawo haka? to in kika sake bari mu kayi ido biyu dake haka wallahi saina k'ona
gashin nan"

Rumana kam dad'i ne ya kasheta dan wannan tsananin na yaya Salman shine yasa take
sonshi, dan a tunaninta idan ta aureshi zata rik'eshi gam tsananin shi kuma zaisa ya d'auke
kanshi daga wasu matan.

Tana shiga d'aki ya kalli Maman Nuseiba yace "Mama ina Nuseiba ne ko bata nan?"

Cewar Mama "tana d'aki kam kuma na san tana jinka, shiru dai tayi"

Shiru yayi har Khamis ya gama abinda ya kawoshi suka tashi zasu wuce, saida suka kai k'ofar
gida Nuseiba ta fito tana fad'in "ina kwana yaya Salman?"

Juyowa yayi yana kallonta yace "ashe kina ciki kika yi banza dani?"

Wani fari tayi da ido mai kashe zuciya tace "lah yaya Salman ba haka bane, kawai dai ina so mu
gaisa ne ba'a cikin mutane ba"

Shagala yayi da kallon bakinta daya sha pink d'in ja leb'e (in ji uncle d'i na), hira suka fara
tab'awa suna dariya Khamis kam ya gama k'ulewa ganin yanda take wani fari da ido na kissa,
haushi ne ya kamashi yace "kaga malam dan Allah wuce mu tafi, ke kuma wuce gida"

Saida ta harare shi ta k'asan ido tare da ji a ranta cewa yana mata bak'in ciki ne, ciki ta shiga su
kuma suka wuce.


Tunawa da Salman yayi yaune ranar komawar Ummi asibiti yasa ya dawo gida suka shirya tare
da Islam suka kama hanyar asibiti, suna zuwa suka nufi d'akin da zai sada su da wajen likitar
data duba Ummi ranar.

Layin da suka gani yasa su tsayawa suna k'ara kallon mutanen dake wurin, Salman mota ya
koma kafin layin ya rage, mutane na shiga kuma suna fitowa dan danan haka yasa layin ya
ragu sosai, mutane uku suka rage su Ummi su shiga Salman na ganin an kusa kawowa garesu
ya fito daga mota ya zo.

Suna haka wani kyakyawa kuma matashin likita ya fito daga wani d'aki kusa dasu, yana ganin
Ummi ya washe baki tare da fad'in "lah mutuniyar kece kika dawo? a to bari na kai sak'on nan
na dawo na rik'e ki dan na san yauma ba zaki tsaya ba."

Murmushi kawai ta masa shi kuma ya wuce d'aya d'akin, Salman kam kamar a tab'a shi ya
fashe saboda cika, an d'an d'auki lokaci kafin Ummi ta mik'e zata shiga, cikin fushi Salman ya
fizgo hijabinta yana fad'in "waye waccen?"

Saida ta kalleshi sama da k'asa tace "ban gane waye waccen ba?kai baga ko waye ba ko baka
iya fahimtar kayan aikin mutane?"

"Kamar zai bigeta kuma dai ya tsaya tare da fad'in "ina tambayar ki kina tambayata, ki fad'a min
miye tsakanin ki dashi?"

Ummi kam tuna Nuseiba tayi da irin haushi da k'uncin data shiga saboda su, dan haka tace
masa "ayya ai ya taimaka min ne ranar da muka zo nan shi ya rik'e ni aka min d'inki da allura."

"Ya rik'e ki" wucewa tayi ta barshi nan, bin bayanta yayi Islam kam na zaune daga waje da
k'yar Ummi ta mik'a k'afarta dan a cire mata zaren da aka mata d'inki, saida Salman ya matse
ta ya tutsa kanta a cikin k'irjinshi sannan aka fara d'ebe mata.


Ana gamawa Ummi ta d'ago kanta fuskarta duk ta jik'e da hawaye da majina, Salman kam duk
rigarshi ta jik'e sai kuma ta bashi tausayi haka aka gama masu suka kama hanyar gida.

Daidai *Maradi Store* yayi parking, Islam ya kalla dake baya yace "Islam muje ko."

Fita tayi shi kuma ya kalli Ummi yace "ki jira anan muna zuwa yanzu" har zai fita Ummi tace "ni
kad'ai zan zauna, me yasa ba zamu je tare ba?"

A dak'ile yace "banga anfanin zuwanki ba, idan kuma kina da sak'o ki kawo na siyo maki?"

Ba tare data kalleshi ba tace "ina da amma dole sai in ni naje da kaina."

Bud'a murfin motar yayi yace "sai kiyi ta zama anan to"


Ta jima zaune kafin suka fito daga ciki, ledar hannunshi ya mik'a mata tana karb'a ta bud'e farin
ciki ne ya bayyana a fuskarta ganinta kayan k'walam da mak'ulashe, bata tsaya b'ata lokaci ba
ta d'auki wata chocolat ta fara sha, jefi jefi Salman ya kan kalleta yana mamakin yanda ta kasa
masa godiya, amma Islam ma dake k'arama ta masa tun kafin su fito, ya san ba daga tarbiya
bace kawai dai tsarinta ne haka, haka har suka isa gida.

Ko abincin rana Ummi bata ci ba saboda ciye ciye da tayi, da yamma ma kam suna zaune
farfajiyar gida ita da Islam Jawahir ta shigo a hargitse, Ummi ce tace "ke kuma lafiya haka, daga
ina kike kamar an koro ki?"

Saida ta zauna ta cire nik'ab da hijab tace "kedai bari wallahi, hadari ne a gari shiyasa nayi
saurin k'arasowa karya riske ni a hanya"

Sai lokacin Ummi ta kalli sama tace "hadari fa, kinga muna nan sai a tashi duniya bamu sani
ba."

Dariya Jawahir tayi tace "idan aka kawo gareku ai zaku sani" kafin Ummi tayi magana iska ya
taso da k'arfi, dan haka suka koma ciki nan fa aka fara ruwa kamar da bakin k'warya dan dama
an kwana biyu ba ayi ba.


21:00 aka d'auke ruwa ba jimawa kuma Salman da Khamis suka shigo gidan, Ummi ko kallon
Salman ba tayi amma ta gaishe da Khamis, haka ta shirya Islam suka tafi tare da Jawahir,
tunda Salman ya fita ya matsu ya dawo gidan dan sosai yaji haushin banzan da tayi da shi
gaban mutane.


Yana dawo har cikin d'akinta ya shiga amma abun mamaki kwance take tana hawaye, tunani
yayi ko dan Islam ta tafi ne, matsowa yayi cikin muryar fad'a yace "Ummi naga har yanzu ba kya
neman zaman lafiya da ni, ke kinfi k'arfin ki gaishe ni ko?"

Zuciyarta a wuya take dama dan haka ta harareshi sama da k'asa tare da tsaki ta kau da kanta
gefe, mamaki ne ya bayyana a fuskarshi cikin b'acin rai da zafin nama ya cabko hannunta yana
fad'in,

"Wa kike harara, ni kike wa tsaki?"

Cikin muryar kuka da fitar hayyaci Ummi tace "ka sake ni mugu kawai azzalumi, wallahi sai
Allah ya saka min kuma wallahi ka auri Nuseiba sai zaman gidan nan ya gagareta dan babu
abinda zai hana ni ci mata uwa, mugu kawai kana fad'a wai ni nama k'aramta amma kuma
shine zaka auri yarinyar dana bata shekara hud'u, dama ita kake so shi yasa zaka aure ta."
Sakinta Salman yayi dan yanzu kam ya fahimci abinda ke cikin zuciyarta ne ya fito fili, lallai har
yanzu tana kishi da shi to amma me yasa.?

D'akinshi ya koma yana tunani akan abinda ta fad'a har bacci ya d'aukeshi, ita ma bacci ne yayi
gaba da ita.

💃💃💃💃����
05/03/2019 à 17:33 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_��

*Page*

7⃣5⃣-7⃣6⃣


Tunda safe Ummi ta tashi ta had'a abin karyawa iya bakinta ta ci, tana kammalawa tayi wanka
ta komo falo ta zauna tana kallo, Salman ne ya fito daga d'akinshi singlet da dogon wando da
alama sport zai je.

Ko kallonshi Ummi ba tayi ba haka ta zauna har ya dawo saidai baiyi gumi ba saboda ansha
ruwa jiya, d'aki ya shiga kai tsaye ya shiga toilet dan yin wanka, yana fitowa ya shirya cikin
k'ananan kaya sannan ya fito falon.

Ba tare daya kalleta ba yace "tunda har yanzu ba kiyi wayon gaida mutane ba, to ki kawo min
abinci na."

Bata kalleshi itama tace "iya bakina kawai na dafa kuma na cinye."

Wani kallo ya watso mata kafin yace "Ummi karki saka ni abinda banyi niyya ba, ki kawo min
abinci na kafin ranki ya b'ace."

Saida ta watsa masa harara ta murgud'a baki sannan tace "kaji min mutum dan Allah, to
wallahi ba zai yiwu ba haka kawai ni da ciyar da kai kuma wata da morarka, kaje mana
amaryarka ta baka abincin."

Dariya ce ta sub'uce masa bai shirya ba, sosai yake dariya har da rik'e ciki yake, Ummi kam ta
gama cika dan haushi kawai sai taja dogon tsaki, shiru Salman yayi yana kallonta kafin ya
mik'e tsaye yasa hannuwa aljihu yace,

"Ok zan tafi naci a waje, amma fa karki manta Salman d'an dangi ne, iya gidansu Khamis ma
kad'ai zan iya cika ciki na har saina ture."

Yana shirin ficewa Ummi tayi karaf ta rik'e hannunshi tana fad'in "a'a dan Allah kayi hak'uri to
zan dafa maka abinda kake so."

Kallonta yayi ya kalli hannun data rik'e yace "sake min hannu malama"

"Dan Allah kayi hak'uri wallahi zan yi." ta fad'a kamar mai shirin fashewa da kuka, dawowa yayi
ya zauna bisa kujera har yanzu tana rik'e da hannunshi, kallonta yayi sosai kamar yana so ya
fahimci wani abu a tare da ita kafin yace,

"Mi amarya ta ta miki ne haka? tun jiya kike masifa a kanta."

Dama kamar jira take sai kawai ta fara kuka kamar an k'wak'wale mata ido, Salman kam shiru
yayi yana sauraranta har ta gama, kusan minti shabiyar tayi tana kuka kafin ta bawa kanta
hak'uri ta share hawaye ta kalleshi tace,

"Yaya Salman wai da gaske aure zaka k'ara?"

Cike da gamsarwa yace "e aure zanyi, miya faru?"

Shan majina ta fara tare da saukowa daga kan kujera ta zube akan gwiwoyinta biyu ta had'e
hannayenta biyu alamar rok'o tace "yaya Salman dan Allah kayi hak'uri karka k'ara aure,
wallahi ni kuma nayi maka alk'warin zan canja zan zama yanda kake so kuma zanyi duk abinda
kake so."
Hannayenshi ya d'ora akan gwiwoyinshi yana kallonta cikin mamaki yace "Ummi me yasa ba
kya so, miye matsalarki idan na k'ara aure?"

Kuka take sosai tace "ban sani ba nima yaya Salman, kawai dai bana jin dad'i idan kace zaka
k'ara aure zafi nake ji a cikin nan da k'unci." ta fad'a tare da d'ora hannu a k'irjinta b'angaren
zuciyarta.

Wani irin murmushi Salman yayi najin dad'i yayin da yake fad'a a zuciyarsa "lallai wannan so ne
kuma Ummi tayi nisa, kawai dai ta kasa fad'a kamar yanda nima na kasa fad'an komai."

Da hannu ya mata alama ta zauna kusa dashi, tana zaunawa ya kalleta yace "Ummi da gaske
kike fad'an maganar nan?"

Cikin kuka tace "wallahi da gaske nake yaya Salman, ba zan sake maka rashin kunya ba."

Shi kam kamar yayi dariya amma ya rik'e, cewa yayi "ok tunda kince haka na yarda, amma a
bisa wani sharad'i."

"Na yarda koma wane iri ne in dai zai hana ka k'ara aure."

"Ok ba zan k'ara aure ba in dai zaki dinga jin magana ta, amma ki sani duk sanda kika min ba

daidai ba to tabbas a satin nan k'anwarki zata shigo gidan nan a matsayin amaryarki."

Saida ta harareshi ta gefen ido tace "na yarda, kuma wallahi idan nayi abinda kake so kuma
kace zaka k'ara aure to wallahi...." mik'ewa tayi danta had'a mashi abin karin, da sauri ya rik'e
hannunta yace,

"Wallahi me?"

Saida ta nuna shi da yatsa tace "saina kashe ka, dan ba zan had'u ni da wata a kanka ba."
Fak'at 😳

Wucewa tayi Salman ya bita da ido "anya yarinyar nan ba zata kashe ni ba kuwa in ina
maganar auren nan?"

_Ah to koma dai miye ni dai ina daga nan_


Haka ta wuni ita d'aya a gidan jikinta yayi sauk'i sosai shi yasa ma babu wanda yazo gidan
dubata saidai kiranta a waya kawai, har dare haka ta kammala 'yan aikace aikacenta kafin
Salman ya shigo gidan, kai tsaye d'akinshi ya shiga yayi wanka yana fitowa ya shafa mai, tsaye
yayi yana kallon kayan da zaisa kafin daga bisani ya yanke wata shawara.
"Abule, Abule, wai Abu bata jine?" Salman ne fa ke kiran Ummi haka, Ummi dake zaune falo
tun kiran farko taji tasowa tayi tana fad'in "haba wallahi saina maka rashin mutunci in kana
kirana da wannan sunan."

"Gani" ta fad'a a tsaye, kallonta yayi dan bai san da shigowarta ba hankalinshi na kan sak'on
daya shigo wayarshi yanzu, ba tare daya kalleta ba yace "fiddo min kayan da zansa."

Kallon ba kada hankali ta bishi dashi har ta bud'a wadrob d'in ta d'auko wasu bleue noir rigar
kamar singlet saidai hannuwan suna da fad'i

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0