Showing 21001 words to 24000 words out of 76927 words
Ummi na gani a écran d'in tasha abaya bak'a ta yane
kanta da k'aramin dan kwali, sai jan-baki ja da tasa, yana bud'e code d'in wayar nan ma pic d'in
tane ya fito inda take sanye da wandon nan, saida ya kalli pic d'in da kyau sannan ya shiga
WhatsApp saidai Ummi bata en ligne, ba yada zab'i daya wuce kiran numberta.
Ummi na ganin kiran Salman taji ranta ya b'ace gaba d'aya haushinshi ya kamata, d'aukar
wayar tayi ta kashe gaba d'aya dan karya sake damunta.
Takaici ne ya rufe Salman ganin ya kirata amma ta kashe masa waya, k'arshe tama kashe
wayar gaba d'aya, tana tunanin ko ya fara damuwa da al'amuranta ne shiyasa zata masa
wannan wulakanci, k'wafa yayi yace" ba laifinki bane, laifina ne dana damu sai nayi magana
dake, dama wannan nake gudu shiyasa nake nesanta kaina dake, amma ba komai, wallahi ba
zan saké kiranki ba harna dawo." jefar da wayar yayi ya saké mirginawa akan gadon.
Baifi minti talatin ba jawahir ta dawo gidan, ta samu Ummi kwance akan kujera tana ta kuka,
kusa da ita ta zauna ta cire hijab d'inta ta d'ago da ita k'yar ta fara tambayarta" sister lafiya,
miya faru ne haka kike kuka?"
Share hawayenta tayi tace" babu komai, ba kuka nake ba" hararanta tayi tace" karki rainamin
wayo mana, ko yaro ya ganki a haka ai yasan kuka kike, ki fad'amin abinda ke damunki kawai"
Kai ta girgiza tace" nace maki babu komai, karki damu kanki" tashi tayi ta shige d'akinta, binta
tayi da kallo tana tunanin abinda ke damunta, dan a iya saninta bata tab'a ganin Ummi na kuka
ba tunda take.
Sallah kad'ai ke fiddo Ummi waje, amma ko abinci ta kasa ci duk bata jin dad'in komai,
madararta kad'ai take kurb'awa kad'an kad'an, jawahir duk ta shiga damuwa da hakan, shiyasa
ma ta kira khamis ta tambayeshi ko akwai abinda yama Ummi ne, amma yace babu komai
sannan yace ta rabu da ita.
Har khamis ya dawo gidan baiga Ummi ba, jawahir ta rok'eshi yaje yaji abinda ke damunta har
yasa ta kuka amma yak'i, saima fad'a mata da yayi auren da Salman ke son k'arawa da zaran
ya dawo tare da nuseiba.
Cikin rashin Fahimtar jawahir tace" aure kuma, da nuseiba, nuseiba dai k'anwarka, amma
yaushe yaya Salman yayi aure har yake tunanin saké wani auren, kuma yaushe suka fara ma
soyayyar bâ tare da kowa ya sani ba.?" kallonta yayi yace" e ita, ni bama wannan ne a gaba na
ba, kinsan mamarmu tana so ta had'a rumana da Salman, shi kuma nuseiba ce tafi kwanta
masa a rai, dukansu 'yan uwana ne amma fa rumana ciki d'aya muka fito, duk inda na goyi baya
sai na shiga matsala, shiyasa nake so ya nemi k'uri'arshi da kanshi bana so na shiga cikin
maganar."
Bata sake cewa komai ba, dan a ganinta hakan bai dace ba kuma yaya Salman zaiyi hakane
dan ya nuna ma duniya baya son Ummi.
*Bayan kwana uku*
Salman ne a d'akinshi keta birgima a k'asa, duk yayi kaca-kaca da d'akin da kaya ya barbaza
komai, hatta zanin gadon ya jayoshi izuwa k'asa ya rufe jikinshi dashi.
Abu guda kawai yake fad'i a bakinshi" Allah Allah Allah na wayyo Allah" kamar mazari haka
jikinshi ke rawa, duk jijiyoyinshi sun tashi idonshi jawur kamar garwashin wuta, hak'oranshi
had'e sai hard'ewa suke.
Cikin wannan yanayin ya d'auki wayarshi ya dannan, pic d'in Ummi ne ya bayyana, kallo yake
kamar zai had'iyeta, sai gani nayi ya buga wayar da bango yana wani irin gunji kamar kuka
kamar kuwa, saidai ya kasa furta ko kalma d'aya.
Da k'yar ya iya rairafawa ya kai ga jakarshi ya d'auki magani har kala biyu ya b'alli guda bibbiyu
ya had'a.
A hankali ya fara dawowa normal kamar yanda yake, nunfashinshi ya daidaita saidai har yanzu
akwai zafi a jikinshi, hawayene ke bin fuskanshi a hankali yake fad'in" bazan yafe maki ba har
abada, shekara d'aya kenan rabon da naji irin haka, amma gashi yau na kusa mutuwa saboda
kin shigo rayuwata, kin kusa tarwatsani."
" Dole na koma gida kafin na aikata ba daidai ba, dole naje gida na samu alhaji na rok'eshi ya
auramin nuseiba kafin na mutu, wallahi ke kuma sai kinyi kuka da idonki muguwa marar imani,
ba zan saké kallonki ba daga yau harna mutu."
_Salman kuma haka abin ya zamaí ¾í´”_
*Ummi* na zaune d'aki, number naga tana danna kira tana kashewa, tun tuni haka takeyi kamar
wasan yara, d'aga kanta tayi sama tana fadin" miyake damuna, miyasa na damu da tunaninsa,
miyasa na kasa mantawa da maganar aurenshi, miyasa nake jin haushinshi dan zai k'ara
aure?"
Siraran hawayene suka biyo kuncinta, a hankali ta saké fad'in" ni dai nasan bana son yaya
Salman domin kuwa da muguntarshi ya raine ni, haka kuma ba ban tab'a jin koda k'aunarsa ba
a zuciyata ba, to miyasa?" kukan da tafe dashi ya jawo hankalin jawahir dake zaune ita da
khamis suna hira, tashi tayi ta shiga d'akin ta zauna kusa da ita ta fara magana.
"Ummi sai yanzu ne nagane wani abu, ban tab'a tunanin zaki iya b'oyemin wani abu daya
shafeki ba, na d'auka ni da ke d'aya ne zaki fad'amin komai dake damunki, kamar yanda nake
fad'a maki abinda ke damuna kuma na nemi shawarar ki, ashe ke ba haka bane a wajenki"
" Ki duba ki gani mana, yaya Salman ya amince da kizo gida na ki zauna, bayan kuma ga
k'anwarshi nan khairat, ga hafsat da nadia duka suma yan uwanshi ne amma baice kije can
ba,sai yace kizo nan, miyasa yace haka?"
Ci gaba tayi da fad'in" saboda yana ganin munfi kusa da juna shiyasa, yasan kuma babu abinda
zai dameki anan inhar muna tare, amma gashi yanzu kina cikin damuwa tsawon kwana uku, ba
kicin abinci sosai sai kuka kike amma kin 'ki fad'amin damuwar ki saboda kina ganin ban kai
nasani ba."
Kai ta girgiza mata tace" a'a jawahir ba wai baki kai bane, saidai bansan ta yanda zaki fahimce
niba, ni kaina bansan miye yake damuna ba, bansan akan mi nake damuwa, saidai nasan za
kimin dariya kuma ki fahimceni ba daidai ba idan na fad'a"
05/03/2019 à 17:28 - Mamar Latifí ½í²ƒ: í ½í²‘ AUREN HA'DI í ½í²‘
_Samira Harouna_
_My í ¼íµ±K *BILKISU Z. YA'U* murnar kammala wannan littafi naki mai sunan *SO MAHA'DIN
RAYUWA* ha'ki'ka ya fad'akar ya nishad'antar, musammam ma a wajen mu 'yan soyayya, ina
maki fatan alkairi ina rok'on maki Ubangiji da ya yafe maki kurakuran dake cikin wannan littafi,
inda ki kayi dai-dai kuma Allah ya baki ladar fad'akarwa_í ½í±�í ½í±�í ½í±�
_Sai mun jiki a novel na gaba mutuniyata 'yar hannu dama na, ina mugun sonki BK ta_
``` daga samirar ki rabin ran bloodynki```í ½í¸œ
í ¼í·¸í ¼í·¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
5⃣3⃣-5⃣4⃣
Jawahir tace" haba Ummi, ta yaya zan fahimceki ba daidai ba, ki fad'amin insha Allah zanyi
k'ok'ari na fahimta yanda kike nufi" cikin kuka ta fara mata bayanin abinda take tunani.
"Jawahir bansan miyasa nake jin haushin yaya Salman ba tunda yaya Khamis ya fad'amin zai
k'ara aure, na rasa dalilin tsanarsa nidai nasan ba kishinsa nake ba domin kuwa bana sonshi
kuma bana k'aunarshi, to amma miyasa nake damuwa bansani ba" saida ta goge hawayen da
suka zubo mata taci gaba da cewa.
" Jawahir wata'kila wannan itace 'kaddarar rayuwata, har abada bazan samu abinda nake so
ba, da farko an min AUREN HA'DI da wanda bana so ba tare dana shirya ba, a bisa d'an
k'ank'anin kuskure akamin dukan tsiya aka kawo ni gidan miji babu shiri, to yana iya dole na
hak'ura tunda banda yanda zanyi, Jawahir dama bana tsammanin cin amarci ko farin ciki a tare
da yaya Salman, saidai ina buk'atar na samu 'yanci kamar kowace mace mai ji da kanta, amma
ina na kasa samu azabtar dani kawai yake a gidansa, ya tafi ya barni ko sati banyi a gidansa
ba, shine yanzu zai k'ara aure dan yaci mutunci na, shin Jawahir kinsan mai zai faru idan ya
k'ara auren nan?"
Kai ta girgiza, ci gaba tayi da cewa" zai kawo min Nuseiba a matsayin amaryarsa, yarinyar da
bana jin ta cika shekara shabiyar a duniya, zata fini matsayi da 'yanci a gidanshi saboda ita
yana sonta, cikin k'ank'anin lokaci zata fahimci zaman da muke da shi, daga nan saita fara jin ta
fini sannan itace mowa a wajen mai gida hakan zaisa ta fara min gani-gani."
"Bayan wani d'an lokaci kuma zata samu ciki, kinga daga nan komai zai k'are, domin kuwa zata
fara min gori akan hakan shi kuma zai dinga biye mata, d'awainiyarta hidimarta rainon cikinta
zai zama duk nice, idan kuma na'ki nasha duka haka harta haihu daga nan zata fara min gorin
haihuwa lokacin shi kuma ya d'auki soyayyar duniyar ya d'ora akan d'anta da ita kanta, zai
dinga fita da su duk inda zaije koda barin garine, ni kuma zan zama 'yar gadin gida har lokacin
da tawa zata zo k'arshe." kallabinta ta kama ta rufe bakinta da shi taci gaba da rera kuka.
Da k'yar Jawahir ta rarrasheta tayi shiru, kafin ta fara magana" 'yer uwata kiyi hak'uri, insha
Allah duk abinda kika fad'a ba zai faru ba, ke da yaya Salman da Nuseiba duka 'yan uwane ku,
babu wanda zai cutar da wani, kuma ni bana tunanin auren zaiyiwu, saboda yaya Khamis
bayasan maganar gaba d'aya."
Kallonta Ummi tayi tace" dan yaya Khamis baya so, ba shi ke nufin zai fasa abinda yayi niyya
ba." kafad'arta ta dafa tace" to naji ma ace ya aureta, miye Nuseiba keda shi da har zaki tashi
hankalinki? ni kaina k'anwa take gareni, bare kuma ke da kika ban shekara d'aya, kinga kenan
k'anwarki ce kema." wani murmushin kan labb'a tayi tace"Jawahir bakisan kishiya bane shiyasa,
bata kad'an kuma bata k'arama"
Dariya jawahir tayi tace" yanzu ke harkin fara kallon nuseiba a kishiyarki? ai 'yer uwarki ce"
hararanta tayi tace" lokacin da zata shiga tsakanina da mijina ba baki sani ba"kallon mamaki ta
bita dashi tace" Ummi kece kike kiran yaya Salman mijinki, to inaga fa kamar anjima da kashe
boss" da gudu tabar d'akin saboda dukan da Ummi takai mata.
Kwance ta koma tare da d'aukar pillow dake gefenta ta rumgume, a hankali take tariyar
rayuwarta a gidan Salman da tayi.
_Tambayoyi ne ta jero ma kanta" miyasa nake damuwa, miyasa nake jin haushin shi dana
Nuseiba, miyasa nake jin zafi a zuciyata, miyasa nake so naji muryarsa, kuma miyasa na kasa
kiranshi?"_
í ½í¸œí ½í¸œí ½í¸œ ```in bata amsa, koko cikin ku akwai wanda zata bata?```
_Ma chérie ta Hakima fito mucashe, lokaci ya kusa yan bak'in cikin Salman saidai a
mutuí ½í¸‰í ½í¸œ_
05/03/2019 à 17:30 - Mamar Latifí ½í²ƒ: í ½í²‘ AUREN HA'DI í ½í²‘
_Samira Harouna_
_My seeya fatan alkairi da godiya tare da addu'ar ya fiyar Ubangiji a bisa kurakuran da ki kayi,
daidai kuma Allah ya baki ladar fad'akarwa da ki kayi, *BAMU DACE DA JUNA BA,* darasi
nishad'antarwa tare da ilimi da fad'akarwa ne a cikin shi._
í ¼í·¸í ¼í·¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
5⃣5⃣-5⃣6⃣
Tunda safe haka Ummi ta tashi sukuku jiki babu k'wari, Jawahir ce ta fad'ama Khamis halin da
take ciki, kiranta yayi tana zuwa da kanshi ya zuba mata abinci a plate ya aje mata tare da
fad'in" maza cinye ki bani plate d'in"
Kallonshi tayi tace" yaya Khamis ko zanci ba zan iya cinye wannan ba" yanda ya had'e rai yace"
Ummi ina wasa dake?" kai ta girgiza tace" kayi hak'uri yaya Khamis wallahi yamin yawa"
"Ke, ina wasa dake ne, za kici ko saina takaki?" tsawar daya mata ce tasa tayi saurin jan plate
d'in a gabanta ta fara kai loma baki, Jawahir ma 'yan cikinta ne suka kad'a, haka nima saida na
saki alk'alamin.
Tana ci tana kuka tana rok'onshi ya isa haka, amma ya tsareta saida ta cinyeshi duka ta bashi
plate d'in, tunda uwar Ummi ta haifeta bata tab'a cin abinci mai yawan haka, shiyasa Khamis na
fita Ummi ta fara tsula amai, abin ya d'aga hankalin Jawahir dan da farko tayi tunanin idan ta
amaye abinci zata daina, amma sai taci gaba da shek'ashi.
Cikin tashin hankali ta fara kiran Khamis ta fad'a mashi halin da ake ciki, cikin tashin hankali
yace da ita "gani nan zuwa saimu kaita asibiti"
suna jiranshi Salman ya kiran Jawahir dan tunda ya tashi bai fita ba, gab'a d'aya hankalinshi ya
koma gida, hakan yasa ya kira iyaye maza da mata da kakannin amma saiya ji baibar kewa da
damuwa na gidan ba, dole ya kira Jawahir ya tambayeta Ummi.
Tana d'auka cikin damuwa tace "assalama alaikum, ina kwana yaya Salman?" gabanshi yaji ya
fad'i, da k'yar ya daure yace "lafiya lau, kun tashi lafiya?"
Kamar zata fashe da kuka murya na rawa tace "yaya Salman da sauk'i dai, kaga Ummi nan
tana ta amai wallahi, nifa na fara jin tsoro" cikin d'aga sauti yace "amai kuma, miyasa meta to?"
Cikin kuka tace "yaya Salman daga taci abinci fa shine take amai "innalillahi wa'inna illaihir
raju'un, kinga bata wayar" ya fad'a tare da nuna tsantsar damuwarshi a fili.
Mik'a mata wayar tayi, wata harara ta wurga mata tare da kau da kai, maida wayar tayi a kunne
cikin sanyin murya tace "yaya tak'i karbar wayar" abun mamaki na d'auka Salman zaiji
haushine, amma sai naji yace "Jawahir karki min k'arya, ki fad'amin abinda ke damunta?"
"Yaya Salman nima bansan miyake damunta ba, amma dai jiya ta fad'amin wani abu wanda
nake tunanin kaine silar shigarta wannan halin" cikin rashin fahimta yace "bangane ni nasa
taba?"
"E yaya Salman amma kayi hak'uri nima zato ne nake, amma banda tabbaci" cikin jin haushi
Salman yace "naji ni fad'amin me ta fad'a maki?"
Duk da tana d'ard'ar dashi haka ta daure ta fad'a masa duk abinda Ummi ta fad'a mata jiya,
dariya yayi yace "Jawahir lallai yarinya ce ke, waya fad'a maki ana kishin wanda ba'a so?"
Saida ta sauke ajiyar zuciya tace "yaya Salman ai macen kenan, tsamar dake tsakaninku ba
zata hana zuciyoyinku fallasa sirrin dake cikin taba, ko bata sonka zata iya kishinka saboda
akwai aure tsakaninku, kamar yanda da zaka ganta da wani namiji za kaji zafi a zuciyarka,
amma idan aka fahimci hakan zaka iya wayancewa ta hanyar cewa kana san kare martabar
aurenka ne dake kanta, kaga kenan dan tayi kishinka ba abun mamaki bane."
Shiru yayi yana tunanin abinda ta fad'a, murmushi yayi kamar yana gabanta yace "Jawahir ban
tab'a jin alamun haka a raina ba, ko zanyi soyayya zanyine da wata daban amma ba Ummi ba,
yarinyar da idan naganta sai gabana ya fad'i saboda tunanin abinda zata min musammam idan
ina cikin mutane"
Dariya tayi cike da jin k'arfin gwiwa tace "Yaya Salman ai fad'uwar gaba alamune na so" dariya
yayi yace " ke Jawahir banasan sharri, ke har kinsan alamomin so?"
Dariya tace "na san wasu yaya Salman wanda nake ji a duk lokacin da naga yaya Khamis"
cewa yayi "to fad'amin uku daga ciki, kuma idan ki kayi ba daidai ba to idan nadawo dole kisha
rank'wasa a kai"
Hannu ta d'ora a kanta dan bâ zata manta rank'wasan daya tab'a mata ba har saida tayi ciwon
kai, cewa tayi " yaya Salman duk lokacin da kaji gabanka ya yanke ya fad'i a lokacin da gaka
wata 'ya mace, to alamune na zuk'atanku suna shirin k'ulla wata alak'a koda ku baku shirya
hakan ba.
"Sannan lokacin da kaji komai na wata 'ya mace yana burgeka, komai yana nufin dariyarta,
murmushinta, fara'arta, kai dama kukanta to shima akwai yiwuwar ka kamu da sonta ko kana
shirin kamuwa."
"Yaya Salman akwai jin tausayinta duk lokacin da wani abu ya sameta na rashin jin dad'i, haka
kuma akwai son ganinta a cikin farin ciki tare da mata fatan farin ciki mai d'orewa, son jin sautin
muryarta a koda yaushe, son ganinta a kusa da kai a kullum."
"Yaya Salman duk lokacin da kayi nesa da ita tunaninta zai iya hanaka sukuni, zaka kasa komai
burinka bai wuce ka dawo ka ganta ba, zaka ji kewarta na yawan damunka kana buk'atar
kasancewa da ita, sannan yaya Salman duk wacce kake so za kaga murmushin da kake mata
ma na dabanne, haka kallon da kukewa junanku ma zuk'atanku ne kad'ai zasu iya fassarashi,
don ko mai kallonku ba zai iya fassara maku shi ba."
"Ke" ya daka mata tsawa yana fad'in" nawa na tambayeki ni uku fa nace, waike sarauniyar
soyayya ko?" kai ta girgiza alamar a'a, tace " yaya nadai fad'a maka abinda na sani ne kawai,
amma ina so ka sani kai da Ummi koda baku son junanku, to ku sani akwai jinin 'yan uwantaka
da yake yawo a sassan jikinku wanda baku isa ku cireshi ba, ko babu so a tsakaninku akwai
k'auna, yaya Salman abune mai sauk'i samun masoyi, amma samun wanda yake k'aunarka da
gaskiya shine mai wahala, mafiyawancin soyayya tana farawane daga k'iyayya sannan ta koma
so wannan shine."
Kashe wayar yayi ba tare da sunyi sallama ba, maida kallonta tayi ga Ummi dake kwance tana
bacci, Khamis na zuwa Ummi tace taji sauk'i, dan babu abinda ta tsana kamar shan magani da
allura, dole suka k'yaleta da sukaga jikin yayi sauk'i ta daina aman.
_Wato dai 'yarta bakin Salman baki son shan magani sai abun dad'i_í ½í¸‚
05/03/2019 à 17:30 - Mamar Latifí ½í²ƒ: í ½í²‘ AUREN HA'DI í ½í²‘
_Samira Harouna_
*MEELAT*_(my meelat)_
*HEENAT*_(my heenat)_
*CHOUKRA*_(habibaty)_
*FATIMA*_(mom dady)_
*HALIMA*_(kakale ta)_
*SAFIYA*_(ma chérie)_
*AZEEMA*_(k'awata)_
*RAMATOU*_(rammess)_
*MAMAN