Showing 30001 words to 33000 words out of 76927 words
saka kenan?"
"To ai basai na fad'a maka ba, babu wanda ya kaika samun mata a b'agas, tunda gashi za'a kai
mata Lefe tana d'auke da juna biyu, aiko kaga kai dan baiwa ne, dan haka tuwon girma miyarsa
nama kayi bajinta kawai."
Cike da damuwa ya kalli Mama yace "Mamaa, bana so kina cewa tana da cikin nan, ba tada
komai fa"
Tab'e baki tayi tace "kaidai kasa ni, ni dai ka hanzarta kawo kud'in dan a samu akai kayan da
wuri"
Mik'ewa yayi yasa hannu a cikin aljihu ya ciro kud'i masu yawa ya bawa Mama, karb'a tayi tana
kallon kud'in kafin tace "wannan kud'in haka har nawa ne?"
Dariya yayi yace "Mama kuda gasunan a hannunku, ku irga mana"
"Kai bazan iya ba, idan ma na fara ba'cewa zanyi ka fad'amin kawai"
" Mama kenan, to d'ari biyar ne (500.000F CFA)"
Baki Mama ta washe tace "kai amma naji dad'i, yanzu ka tabbatarmin da kai mai yaba kyauta
ne, gaskiya naji dad'i Allah ya maku albarka, Allah ya albarkaci aurenku, Allah ya bata lafiya ya
rabata da abinda yake cikinta lafiya."
Ganin Mama tak'i fahimtarshi yasa sukayi sallama a haka, ya d'auki abinci ya kama hanyar gida
zuciyarshi cike da wasi-wasi.
Yana zuwa da kanshi ya zuba mata abinci a plate ya mik'a mata tare da zaunawa kusa ita yana
k'are mata kallo, wai mai ciki "to cikin wa?" ya tambayi kanshi.
Ummi kam dan danan ta cije leb'e saboda ciwon da mararta keyi, saida ta malmalo lomar
fankasu daya sha jar miya zata kai bakinta, cak ta tsaya tare da kallon Salman.
Tunawa tayi jiya yace yana jin yunwa da Hajia tace ya d'auketa, kuma a iya saninta bata ga
sanda yaci wani abu ba da idonta, dan haka ta mik'a masa plate d'in tace "ci"
Cike da mamakin abinda tayi ya girgiza mata kai yace "kici kawai"
Shagwab'ewa tayi tace "dan Allah kaci nasan kana jin yunwa, tun jiya baka ci komai ba."
Kallonta kawai yake kafin yace "ki fara ci, idan kin ida zanci"
Kai ta girgiza masa tace "bazan iya ciba yaya Salman"
Idonshi akan tv yace "parce que (saboda)?"
A ranta kam cewa tayi "saboda kana jin yunwa" amma a fili sai tace "saboda bazan iya ci ba
alhalin kai baka ci ba."
K'yar idon Salman a kanta kamar zai had'iyeta, mamakin furcinta yake sosai da k'yar yace
"Ummi miyasa kika damu da sai naci, bayan kema nasan kina buk'atarsa.?"
Shiru tayi tana tunani, ba zata iya fad'a masa haka kawai taji tana so ya fara cika cikinsa kafin
ita ba, a hankali ta d'ora hannunta akan mararta tana matse fuska, karb'a yayi ya yanko loma
mai kyau, a hankali ya nufi bakin Ummi da ita tare da cewa "haa."
Bud'a baki tayi ya saka mata, kallon junansu kawai suke, Salman ya had'a ido da ita ne saboda
yana so ya gano wani abu a tare da ita, kallon ne yayi yawa yasa Ummi k'asa da idonta, amma
duk da haka bai bar bata abincin ba shima kuma yana sawa nashi bakin, haka har suka gama.
Suna idawa ya maida kwanukan ya aje ya d'auko mata madara daga nan zaune tana kurb'a, shi
kuma ya fita ya bar gidan zuciyar shi nata tunanin juna biyun da Mama ta fad'a masa wai Ummi
tana da.
Gidan Ummi ko kad'an bai tsagaita ba saboda tururuwar da 'yan uwa suka dinga yi a gidan
kamar ana biki, Ummi tsabar farin ciki kamar ta k'urma ihu, bayan hana 'yan uwanta da Alhaji
yayi zuwa gidanta, yau gashi dangi sun cika gidanta saboda zuwa ganinta.
Sai misalin 22:30 kad'ai gidan yayi shiru ya rage Ummi kad'ai a gidan, sai lokacin ta fara jin
ciwon mararta yana dad'a taso mata, haka tayi ta murk'ususu har bacci ya d'auketa daga nan
kan kujera.
23:40 Salman ya shigo gidan, saida ya k'are mata kallo daga sama har k'asa, durk'usawa yayi
yana kallon cikinta daya lafe a mararta, tsintar kansa yayi yana murmushi kafin ya mik'e tsaye
yana fad'in "ta yaya za ace akwai ajiyar yaro anan wurin, bayan a shafe yake."
Tsaf ya d'auketa ya direta akan gado tare da ja mata zanin rufa, sannan ya tofeta da addu'a ya
shafa kanta yace "saida safe".kamar tana jinshi.
Ciwon mara ne ya tayar da Ummi daga bacci, yarfa hannu kawai take gashi ba lafiya bare ta
samu damar murk'usawa da kyau, haka ta dinga cizar leb'e har taji Salman na k'ok'arin shigowa
d'akin, da sauri ta kwanta ta rufe ido kamar mai bacci.
Kallo d'aya Salman ya mata ya gane idonta biyu, dan daga yanda take sauke numfashinta da
sauri sauri,tsaye yayi a kanta yace " tashi ko malama"
Da k'yar ta tashi ba tare data kalleshi ba, zaune yayi kusa da k'afafunta yace "miyake damunki
wai"
Ko kad'an ba zata iya fad'a masa tana ciwon marar jinin al'ada bane, dan haka tace "ciwona ne
kemin ciwo"
Kallonta yayi kamar mai son gano wani abu a tare da ita, ajiyar zuciya ya sauké yace "kinsha
maganinki?"
"Bansha na dare ba gaskiya"
Harara ya dalla mata yace "zan d'auko maki yanzu kisha, amma wallahi idan kika k'isha to ranki
zai mugun b'aci a daren nan." fita yayi falo ya d'auko ledar magungunan tare da ruwa.
B'allowa yayi ya mik'a mata, karb'a tayi ta rik'e a hannu tana shirin kuka, zaro ido yayi yace
"wallahi zanci gidanku kinji na fad'a maki"
Turo baki tayi tana kunkuni haka ta jefa maganin a cikin baki ta kora da ruwa, ganin tasha yasa
ya mik'e zai fita daga d'akin, motsa k'afafunta tayi amma taji su gam kamar ba'a jikinta suke ba,
da sauri tace,
"Yallab'ai" cak ya tsaya ya juyo yana fad'i a ransa "wato akwai abinda kike so shiyasa na samu
wannan sunan."
Kar kace kai tayi tace "dan Allah taimako nake nema?"
Ba murmushi a fuskar nan yace "ina jinki"
Da hannu ta masa alama da drower tace "dan Allah ka mik'o min coton a ciki"
Saida ya gama hararanta sannan ya nufi drower ya bud'e, coton Vania ya gani dan haka ya
d'auko ya nuna mata tare da fad'in "wannan kike nufi?"
D'aga masa kai tayi alamar eh, k'arasowa yayi yace "yanzu kema kinfi so kiyi anfani da wannan,
a maimakon kiyi anfani da abinda zaki wanke da hannayenki bayan kin kammala saboda k'iwa
ko?"
"Shin ko kinsan darajar wannan jinin, Allah ne fa ya halinceku dashi saboda dacewarku dashi
d'in, yafi daraja da mutunci mace tasa hannayenta tâ wanke da kanta, duk da yana k'azanta
amma kuma ta wani b'angare cuta kuke fitarwa, sannan shed'anun aljanu suna samun damar
sauk'in shiga jikinki a lokacin da kuka jefar dashi cikin shara dama duk wani mai son cutar daku
ta hanyar samun jinin hailarku."
Girgiza kai tayi tace "a'a yaya Salman wallahi bana aiki dashi haka kawai, sai inhar zan fita
unguwa saboda gudun kar jikina ya b'ace ban sani ba da kuma canzawa idan buk'atar hakan ta
tashi,dan shi d'in yafi k'yale wani lokacin, amma tun lokacin dana fara Mama ta fad'amin komai
akanshi,harma da mahimmancin wankewa da hannuna."
Ya gamsu da maganarta sosai dan haka ya bud'e ya ciro d'aya ya mik'a mata, tana karb'a yace
"yaushe bak'on naki yazo?"
Baki bud'e ta kalleshi kafin ta kawar da kanta gefe, jin tayi shiru yasa yace "dake fa nake
magana?"
Ba tare data kalleshi ba tace "yanzu"
Juyawa yayi danya mayar da coton d'in yace "yaushe zai tafi?"
Dam!taji gabanta ya fad'i, a ranta kuma cewa tayi "wannan jaraba har yaushe da irin ta, ko ina
ruwanshi kuma."
Kamar daga sama taji yace "ba jaraba bace, kawai dai inaso in sani ne dan nasan kwana nawa
kike bakya sallah"
Kallonshi tayi k'asa k'asa yanda ba zaiji ba tace "ashe yaji"
Nan ma ji tayi yace "a'a banji ba, nasan dai abinda zaki fad'a kenan"
Hanyar k'ofa ya nufa zai fita tace "to yallabai" juyowa yayi cike da jin haushi yace "miye kuma
yanzu? bacci fa nake so nayi"
Cike da shagwab'a tace "kayi hak'uri naga baka d'aukomin pants bane kuma zaka fita"
Rik'e k'ugu yayi "ke wai d'an aikinki kina mayar dani ko me?" jin tayi shiru yasa ya nufi wadrob
d'in ya bud'e, da hannu ta masa ishara inda take aje k'ananan kayan, haushi yaji ya kama shi
dan ganinsu gasunan masu yawan kuma duk sabbi, gashi ya riga ya siyo mata masu yawo
shima.
Wasu jajaye ya d'auko mata a had'e da bras d'in yake, jefo mata yayi tare da fad'in "size nawa
kike sakawa?"
Ta gefen ido ta harareshi tace "to waini wannan wace irin tambayar k'wak'wafi ce haka?"
Bata rai yayi yace " ke in zaki fad'amin ki fad'a, dan naga kamar kina saka wanda suka fi k'arfin
ki"
Kallon raini ta masa cike da masifa tace "wacece, ni d'in, wallahi sai tayi, kaji in fad'a maka
number 40 nake sakawa na bras haka ma pants,ashe ma kallon tsoro kake min bakasan
babbar macece ni d'in ba."
Saida ya k'are mata kallo ya juya zai fita, cikin kunkuni tace "haba bakasan niba ne, kai kullum
tunaninka bai wuce an haifeni a gabanka ba, amma muna nan da kai akwai lokacin da ni
d'innan zan d'aukeka tsaf wallahi."
Cak Salman ya tsaya tare da juyowa saida yazo gabanta ya rusuna kamar zai sumbace ta
sannan yace "karki saké tunanin haka ko a mafarki, nafi k'arfinki ko kad'an ba zaki iya dani ba,
kafin abinda kike tunani ya faru sai an had'a kamar ki guda goma, dan ke kad'ai kinmin kad'an,
tamilon wofi."ya fad'a tare da dan gware mata kai.
Yana fita tayi wata doguwar k'wafa tare da cewa " aiko zaka san ka fad'amin haka, dan wallahi
sai nasa ka gane kurenka, kuma wallahi saika d'and'ani kud'arka dani kake zancen, kai har
yanzu bakasan Annabi ya faku ba, ba komai ne shekaru keyi ba amma zaka fahimci haka ranar
da ka zubar da hawayenka a kaina."
Daga zaune ta gyara ta saké pants d'in tasa coton, sannan ta gyara kwanciyarta sai bacci.
_To Allah yaba mai Rabo sa'a_
```Muje zuwa```
05/03/2019 à 17:31 - Mamar Latifí ½í²ƒ: í ½í²‘ AUREN HA'DI í ½í²‘
_Samira Harouna_
í ¼í·¸í ¼í·¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
6⃣5⃣-6⃣6⃣
Cikin dare Ummi ta farka bayan tayi fitsari tayi brush ta dawo ta kwanta taci gaba da baccinta.
Haka ma Salman koda yayi alwala masallaci ya nufa tunda yasan Ummi bata sallah, yana
dawowa kuma shima kwance yayi yaci gaba da bacci.
*Safiya*nayi Salman ya shigo d'akin Ummi dake bacci har yanzu, pillonta ya girgiza dan haka ta
bud'a ido tare da tashi zaune tana addu'a, kallonshi tayi lokaci d'aya kuma ta kawar da kanta
gefe saboda fad'uwar da gabanta yayi, bak'ar singlet ce a jikinshi ta kamashi sosai duk surarshi
ta k'akk'arfa ta fito, sai dogon wando shima bak'i murya k'asa k'asa tace "wannan ba k'aramin
k'ato bane gaskiya a daren farko zai kasheni, dan haka na hak'ura da d'aukar fansa ta"
Wani shu'umin murmushi yayi yace "aiba ma zan fara ba, dan kuwa kin min kad'an sai an har
had'a irinki guda goma sannan zaki isheni kallo."
Kalllonshi tayi tace "ni d'in, wallahi nasan na isa harna wuce, waya fad'a maka mace nawa
namiji kad'an , hasalima kune kukewa yaran mutane fyaa..." saurin kame bakinta tayi, kallonta
yayi yace,
"Ki fada mana, nasan za kice maza kewa yara fyade, amma ki sani ba irina bane su dan ni bake
ba wacce tafi kima tamin k'arama bare kuma ke, sannan ki sani mace nawa namiji kad'an
amma namiji bayawa mace kad'an."
"Ki fito falo ni zanje gida." ya fara ya dak'ile
Juyawa yayi zai fita ummi tace "to wa zai fidda ni?"
Tsaye yayi yana kallonta kafin ya matso yace "d'an aiki kika mayar dani ko me?"
Shirun da tayi yasa ya matso yana shirin d'aukarta, da k'arfi ta d'aga murya tace "a'a ni bana
san d'auka goyo nake so"
Cikin b'acin rai yayi k'wafa sannan ya juya ya sunkuya, Ummi kam tintsirewa tayi da dariya
kafin tace "to yaya Salman taya zan hau nan?ai sai an aza min tsani ko kai bakasan dogo
bane?"
Juyowa yayi yana nunata da yatsa yace "wallahi karki b'atamin rai da safiyar nan kinji na fad'a
maki."
Turo baki tayi tare da d'aga hannu cikin shagwab'a tace "pardon"
Tsaye tayi akan gadon tare da d'anewa bayanshi, amma ko kad'an tak'i yarda jikinsu ya had'u ta
mashi wani zok'ok'o kamar ya d'auko buhun k'aya, cikin masifa Salman yace,
"Ke wannan wane irin iskanci ne, kinsan bakya son had'a jiki dani miyasa kika ce saidai na
goyaki, munafuka kawai."
Tunda ya fara magana take ta murgudar baki kamar ta cireshi, a hankali tace "to haka kawai
saina had'a jiki da kai"
Haushi ne yasa Salman finciko hannunta ya manna ta a bayanshi da k'arfi, wani numfashi ta
sauke jinta a bayanshi kwance, Salman kam mutuwar tsaye yayi jin gaba d'aya albarkatun
k'irjkinta sun sauka akan bayanshi da k'arfi.
_í ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£ waya aike ka dama?_
Kunya ce tasa Ummi ida narkewa a jikinshi ta kasa d'agawa, da 'kyar Salman yayi k'arfin d'aga
k'afarshi ya doshi hanyar fita idonshi lumshe, tunda yake bai tab'a jin abinda yake jiba a yanzu a
haka suka kai falo ya direta kwance kamar yarinya, juyawa yayi ya mata runfa da faffad'an
kirjinshi kamshin turarenta ne ya fara tafiya da imaninshi, duk da ba sosai ake jinshi ba sai kana
gaf da ita.
Kallon fuskarta kawai yake wani abu na fizgarshi da k'arfi, ganin Ummi tak'i had'a ido dashi yasa
ya cusa kanshi tsakanin kafad'arta da fuskarta ma'ana a wuyanta yana shak'ar kamshinta yana
sauke shed'a sannu sannu.
Ummi duk bata jin dad'i saboda ganinta yau kwananta biyu ba tayi wanka ba saboda ciwo, duk
da dai tasan akwai turare a jikinta wanda ko zatayi sati tofa zai zauna a jikinta.
D'ago ido yayi harsun canja kala cikin wata irin murya k'asa k'asa yace "sunan turarenki ma?
gaskiya yana da dad'i."
Murmushi Ummi tayi jin wata irin tambaya a jirkice kafin tace " *ARABIAN OUD*"
D'agowa ya sake ya kalleta saidai, baisan lokacin da ya had'a bakinshi dana taba ya fara tsutsa
kamar mai shan sweet, tun yana abun a hankali harya fara mata cikin sauri da son aika sak'on
cikin gaggawa.
Ummi najin hannun Salman na shirin shiga cikin rigarta tayi saurin rik'e hannun tare da tureshi
daga kanta, zaune ya fad'a akan kujerar har yana shirin danne mata k'afa, kanshi kasa idonshi
rufe yake sauke numfashi da sauri sauri ya kasa tuna komai, haka ya tashi ya shiga d'akinshi ya
saka rigarshi yayi tsaye yana k'are ma kanshi kallo.
Yana fitowa ko kallonta baiyi ba ya wuce, yana shiga mota ya kifa kansa a stiyari ya jima kafin
d'ago kanshi yana fad'in "pourquoi, pourquoi je fais ça, pourquoi je fais ça de cette idiot fille? "
"Pourquoi je envis de cette pagaille fille? oh mon Dieu aide moi."
Ya jima kafin ya tayar da motar ya nufi gida, tunda yaje gida babu walwala a tare dashi haka ya
karb'i abincin ya fito, saida ya aje abincin a mota sannan ya shiga gidansu Ummi dan su gaisa
dasu La Mama.
Yana shiga dole ya saki ransa saboda ganin su Inna Hajara (kakar Ummi) da Tanti Fateema
(k'anwar La Mama), gaisawa sukayi sosai kafin Inna ta shaida masa sunzo ganin Ummi ne, cike
da jimami yace "haba Inna aida ba kuyi wahalar zuwa bama wallahi tunda da sauk'i"
Dariya Inna tayi tace "ai dama nasan da kunsan zanzo da ba zaku bari ba"
La Mama ma haka tace "nima saida na fada masu da sunyi zamansu tunda da sauk'i."
Koda Salman zai wuce yace su tashi ya tafi dasu, haka suka tafi tare saidai tun a hanya Inna ta
fahimci damuwa a tare da Salman, dan haka tace "d'ana shin da matsala ne zaman naku kai da
k'anwar taka?"
Cike da san basarwa yace "a'a Inna babu wata matsala ko kad'an"
Bata yarda dan haka ma taci alwashin gano matsalar idan taje gidan, dan tasan kuruciyar Ummi
dama Salman d'in, ta kuma san yanda aurensu ya kasance dan haka ita a nata ganin babu wani
dalilin da zaisa Ummi tabar mijinta cikin damuwa koda kuwa ba itace silar shigarsa damuwar ba.
Suna zuwa kuwa Ummi ta taresu da murna tana masu sannu da zuwa, Salman ne ya aje mata
abincin a gabanta ya juya zai fita, cikin b'acin rai Inna tace "kaga d'ana zo zauna nan"
Tun kafin ya zauna Inna tace "kace babu matsala amma gashi daga zuwana na hango babbar
matsala a tsakaninku"
Maida kallonta tayi ga Ummi dake kallon Salman, saiko saukar mari a fuskar Ummi a kid'ime ta
dafe kunci tana hawaye, Inna kuwa d'orawa tayi da fad'in " 'yar iska marar mutunci, ashe baki
canja halinki ba?"
"Ummi sai yaushe zakiyi hankali? mijinki na sunna kina kallo ya shigo daga fitar da nasan kece
sanadi amma ko kallon fuskarsa baki yiba bare yasa ran samun sannu da zuwa daga wajenki,
kuma abin haushi kina kallonshi da kaya amma kinfi k'arfin ki amsa koda daga zaune."
"Sannan kuma kina kallo ya juya zai fita ba tare daya ci abincin ba,amma ke ko a jikinki kuma
kinsan baici komai ba, haka kika bishi da ido ba tare da addu'a