Showing 9001 words to 12000 words out of 76927 words

Chapter 4 - Auren Hadi Book Compelet Samira Haruna

22 Jun 2026

1102


fad'a Ummi kam ba tayi wani k'ok'arin rufe jikinta ba duk da ta ganshi.

Hannunta rik'e da pillow ta kalleshi tace" malam ya dai lafiya ka shigo min wannan lokacin
haka?" da sauri ya d'auke kanshi daga kallanta bai ce k'ala ba dan haka tace" ka shigo d'aki
babu sallama, ba tapé ba excuse kawai ka shigo, yanzu idan nayi ihu nace za kamin fyade kana
ganin zaka fita?" ci gaba tayi da abinda take, ganin ba yada abin fad'a yasa ya juya ya fita,
d'akinshi ya shiga ya kwanta saman gado yana kallon sama a hankali yake rufe idonshi yana
bud'ewa wani sabon abu yake ji a tare da shi, surarta ce take dawo mashi a k'wak'walwar shi a
haka bacci yayi gaba da shi duk da yaso ya fita.
27/02/2019 à 17:34 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)��

*Page*

3⃣5⃣-3⃣6⃣

Misalin 23:30 ya farka, wanka ya farayi ya fito ya kalli agogo tsaki yayi yana fad'in" mi yarinyar
nan take nufi da ni ne da har yanzu bata kawo min Tea na ba?"wani tsakin ya k'ara saki ya fito
ya nufo k'ofarta, zai bud'e wata zuciyar ta gargad'eshi karya saké ganinta a yanda ya ganta
d'azun, ya dan jima a tsaye kafin ya zira kai cikin d'akin, ga dukkan alama tayi nisa a cikin
baccin ta har yanzu babu riga a jikinta tayi rub da ciki, sai lokacin ya kalli shatikan carbin da ke
bayanta duk ya farfashe, ga kananan kitsonta daya kwanta a bayanta kamar ya taba wata
zuciyar ta gargad'e shi, k'afarta ya kama ya fizgo a tsorace ta mik'e zaune tana murza ido tare
da kallonshi kafin tace" wai dan Allah miye haka, haka ake tada mutum daga bacci kamar a
gidan mahaukata, kai idan aka maka haka sa kaji dad'i?" ke rufe min baki ina abinda na saki?"
kallaonshi tayi ido bud'e tace" wane abu kuma?" dan 'kuwa ya mata yace" ban sani ba, Tea k'in
fa, ko ni kike so naje na dafa?" kau da kai tayi tace" nifa ba zan'iya ba, ace Tea ba za'a shashi
da safe ko da rana ba sai dare yayi kuma sai na kai har cikin d'aki haba gaskiya da saké" ganin
ya fara waige waige yana neman abun bugu yasa ta tashi da gudu ta bar d'akin ta shiga cuisine
ta fara had'awa.

Tana kammalawa ta kawo mashi har d'akinshi, kallo d'aya ya mata yaga bacci pal a idonta dan
haka ya mata tsaki yace" ba kida aiki sai bacci kamar kasa" lumshe ido tayi ta saké mik'ama
mashi faranti tace" ni ka karb'a dan Allah in tafiya ta" wata harara ya watsa mata yace" ki aza a
kaina mana tunda ba babu wurin ajewa" gefen gadon ta d'ora harta juya zata fita yace" waye zai
zuba kenan?" dawowa tayi ta zuba mashi kallonshi tayi cikin muryar bacci tace" sugar nawa
zan saka a ciki?" d'aya" ya bata amsa idonshi na kallon hannayenta da suka sha jan lalle da
bak'i abin sha'awa,tana gamawa ta mik'a mashi wani kallo ya mata yace" ki aje ko dole sai na
karb'a" ajewa tayi ta juya cikin magagin bacci ta fita, har saida ta bace ma ganinshi sannan ya
kalli faranti yanda ta k'awatashi ma kad'ai da abin birgewa ne ga kamshin da ke tashi mai dad'i,
d'auka yayi ya kurb'a har saida ya lumshe ido dan Khairat bata taba dafa mashi mai dad'in
wannan ba kuma gashi duk abinda ake sakawa a waccen nan ma an saka "to miye banbanci?"
ya tanbayi kanshi.

Yau ma da zazzab'i ta tashi tana yin sallah asuba ta nufi cuisine dan ta tuna abinda ya fad'a
mata akan girkin, gashi kuma ta d'ora mai wuya abincin da Abbanta yafi sone ya karya dashi ta
d'ora tuwon shinkafa da miyar agushi, duk da ta d'ora da wuri saida tayi late akan lokacin da ya
bata sakamakon zazzab'in daya addabeta ga kuka da tasha abunta ta k'oshi.
Tana fitowa zata aje kwanukan ta ganshi zaune ya hakimce rai a b'ace saida ta gama jera duka
kayan ta zuba mashi zata wuce d'aki yace" zonan" dawowa tayi ta tsaya sannan yace" k'arfe
nawa yanzu?" da k'yar ta gane lokacin dan jiri kawai take gani, a hankali tace" 08:22" bien" ya
fad'a yana kallonta yace" nawa mu kayi da ke na dinga samun abinci a nan" kamar za tayi kuka
tace" dan Allah kayi hakuri banji dad'i ne shiyasa, kuma kaga tuwo ne nayi" cikin tsawa yace" to
sai me, ina ruwana da abinda kika dafa, kina nufin haka zan dinga zaunawa jiranki kullum
kenan?" dafe kanta tayi saboda sarawar da yake mata gashi shi kanshi Salman k'in guda uku
uku take ganinshi dan haka tace" kayi hakuri dan Allah ka taimaka ka siyo min madara wallahi
mutuwa zanyi" wani kallo ya mata yana magana akan wani abu ita kuma tana magana akan

wani abu daban, kafin ya ankara ya jita a k'asa ta dad'i hannunta kam har yanzu a kanta ya ke
cikin bacin rai yace" ke dan Allah tashi miye haka kamar wacce tasha k'waya" ya jima yana
mata magana amma kamar bada ita yake ba, dan haka ya ka mata ta mike tsaye ya zaunar da
ita akan kujera, da k'yar take bud'a baki tana fad'in" madara yaya Salman dan Allah ka Siyo min
in sha" hararanta yayi yace" ke tafi can sai naci na k'oshi in yaso na siyo maki jarababba kawai
kin d'ora ma kanki shan madara kamar wacce saniya ta haifa" kanta a duk'e tace" kaima
miyasa ba zaka siyo min ba in yaso sai kaci tuwon, kenan duk jarabar gare mu, kuma wallahi
saina fad'ama la mamma nace ka ce mata saniya tunda ai kasan ita ta haifeni in ba kana san
cin zarafinta ba miye na had'a yar da ta haifa da saniya" maida hankalinshi yayi ga cin abincin
shi har saida ya koshi sannan ya fita ya barta a wannan halin.

Tunda ya fita bai saké tuna wata Ummi ba harkokin gabanshi kawai yake hankali kwance har
saida lokacin dawowar shi yayi da rana, kai tsaye yazo gidan yana shigowa baiga alamun girki
ba dan haka ya d'auko belt a d'akinshi ya nufi d'akin Ummi da ke kwance tun safe ga ciwon kai
ga zazzab'i ga amai da take na duk wani abinda ta ci.
Yanda ya ganta cikin bargo ya k'ara k'ona mashi rai matuk'a, bai ko tsaya Haye bargon ba ya
fara tsuga mata belt kin nan, ba tayi wata Kara ba sai kuka daya saké kubce mata mai tsanani
yana cikin dukanta amai ya taho mata haka ta fara kelayashi dole ya tsaya yana kallon ikon
Allah, duk ta b'ata gadon dan haka ta rairafa ta dawo k'asa ta rakub'e tana kuka, tsaki ya mata
ya fita daga d'akin dole ya fita nemo madara da magani da abinda zai ci.
27/02/2019 à 17:34 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

```dedecated```

```To```

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da_ _amana insha Allah)�_ �

*Page*

3⃣7⃣-3⃣8⃣


Yana dawo ya sameta in da ya barta, da kanshi ya zubo mata madara a cup da abincin ya kawo
mata mik'a mata yayi kawai sai tak'i amsar ta cup d'in sai ta cikin gorar, tana karb'a ta kafa kai
saida ta sha fiye da rabi sannan ta aje tana maida nunfashi a hankali, Salman zaune yayi yana
kallonta baki bud'e ganin zata kwanta yace" ke tashi dan Allah kici abinci" da k'yar ta koma ta
zauna ta d'auki abinci saidai ba taci sosai ba ta aje ya bata magani nan fa aka sha fama, yana
mik'a mata ta ya tsina fuska tace" a'a ban sha" kwance tayi ya fizgota yana fad'in" tashi Dallah

malama, wato magani ne ba zaki sha ba, amma abun dad'i kinci kinsha ko maza karb'i kisha
nan" ganin ba zata sha ba yasa ya d'auki cokalin da taci abinci da shi ya k'wandara mata akai
dole ta karb'a tasha tana kunkuni.

Baifi minti biyar ba bacci ya d'auketa, kujerar da ke fuskantar ta ya zauna ya fara cin abinci yana
tunani iri iri, inda wata zuciyar ke saka mashi ya horata ta hanyar yi mata wasa da madara, wata
zuciyar kuma na fada mashi kar yayi hakan tunda tana shiga matsala in bata sha ba.

Ana sallah la'asar ta farka, wanka tayi sannan tayi alwala tayi sallah ta shiga cuisine dan
gabatar da abincin dare, tana d'orawa ta shiga d'akin shi ta fara gyara masa duk da bâ wani
datti yayi ba haka ta gyara shi tayi turare sannan ta rufe d'akin taci gaba da sauran ayyukanta,
sai bayan Magriba ta kammala komai tana shiga d'akinta wanka tayi ta saka riga da wando na
bacci ana kiran sallah isha'i ta saka doguwar riga tayi sallah sannan ta kwanta saboda gajiyar
da tayi, dan tunda take bata taba aiki mai yawa kamar na yau ba.

Bacci mai dad'i ya d'auketa, amma shigowar Salman ya mata wani hargitsantsan tadi da ruwan
sanhi saboda ta fito ta zuba masa abinci, haka ta fito tana kuka tana zuba abinci, tana idawa ta
ajiye masa ta koma d'aki ta kwanta ta dinga shek'a kuka tana fad'in" shikenan haka rayuwata
zata k'are, an rabani da iyayena da yan uwana da kowa nawa ba'a barni nayi ban kwana da su
ba, gashi wannan mugun yana neman kashe ni, wallahi ba zan zauna gidan nan ba dole na
barshi in ba haka ba to zai kashe ni ko ni na kashe shi" tunda ta fara kukan Salman ya tsaya
k'ofar d'akin yana sauraranta yana jin tace ko ta kashe shi ya bud'o k'ofar da k'arfi ya shigo dab
da ita ya tsaya ya kama kunnanta yace
"Wallahi karki bari zuciyar ki ta fara raya maki ki kashe ni, dan kafin ki kashe ni ni zan kashe ki,
kuma zama daram a gidan nan babu inda zaki je kuma dolenki kiyi abinda na saki in kuma ba
haka ba" k'wafa yayi alamar tasan mi zai biyo baya.

Iya k'arfinta ta sa ta tureshi da sauri ta mik'e daga kan gadon tana k'ok'arin guduwa, yaji zafin
turar data masa dan haka yayi saurin rik'ota duk da yayi nasarar rik'o k'ugunta a tare suka fad'a
saman gadon inda Salman ya fad'a samanta da gaba d'aya nauyinshi, k'ara ta saki lokaci guda
kuma ta soma kici kicin k'waceya, d'agata yayi yana kallonta kafin ya juya ya fita daga d'akin.
Haka ta takure taci gaba da kukanta tsawon lokaci, duk da bata manta da Tea d'in shi ba amma
tayi niyar ba zata kai bâ saidai ya kasheta.

Tunda yaga 00:30 tayi ya tabbatar ba zata zo ba shi kuma yana so ya canzata dan haka ya
shigo d'akin hannunshi rik'e da belt, yana ganinta kwance duk da baccin bai jima da d'aukarta
ba haka ya ware iya k'arfinshi ya zabga mata belt d'in nan, a gigice ta mike zaune tana dube
dube tana ganinshi ta fashe da kuka lokaci guda kuma ya soma tsula mata belt d'in, duk in da ta
nufi saiya tarota ta shige cikin bargo ya yaye shi da k'yar ta samu ta rik'e belt d'in tana fad'in"
dan Allah kayi hakuri, kayi hakuri wallahi ba zan saké ba na daina daga yau, zanyi duk abinda
kace wallahi ko, dan Allah kayi hakuri."

Wata harara ya wurga mata yace" nan da minti goma ki kawo min Tea d'akina" yana fad'a ya
wuce d'akinshi ya barta nan, ita ma tashi tayi jiki na rawa ta shiga cuisine dan had'a mashi,
hak'ik'a yau ta matuk'ar tsorata da al'amarin Salman, yana dukanta ko a gida amma bai taba
mata irin dukan daya mata yau ba, dan-danan ta gama ta kai mashi d'aki, harta juyo zata fito
yace" ke saurara kiji" cak ta tsaya tare da juyawa tana kallonshi" daga gobe k'arfe 23:00 zaki
dinga kawo min Tea, idan kika wuce lokacin dana baki to jikinki zai fad'a maki" saida ta
murgud'a baki sannan ta juya da sauri yace" ke wa kike juyama baki?zo nan" tana zuwa yace"
gwiwanki k'asa" ba gardama tayi abinda yasata, ta d'auka zai fad'a mata wata magana ne
amma wasa wasa sai ga Ummi durkushe sama da awa d'aya, da tayi yin k'urin tashi zai dalla
mata harara dole ta koma, shi kuma yana ta latse latse a wayar shi yana dariya, shi kam bai
san Ummi raguwa bace daga nan ta d'ora kanta saman gadon sai bacci.

Tunda Salman yaga haka ya gyara kwanciyar shi yana fad'in" saidai ki kwana a haka
mahaukaciya kawai" Allah sarki kamar na daddab'ata ta tashi.

02:40 Ummi ta farka ta kalleshi tayi tsaki tace" mugu azzalumi wallahi kai ma sai kaji abinda
naji" cup d'in da yasha Tea ta d'auka ta zuba Tea d'in a ciki ta d'ora saman gadon ta ja
k'afafunta da sukayi nauyi ga ciwo ta fita ta bar d'akin.

Bata koma bacci ba har akayi sallah, tana idar da sallah ta fito ta shiga d'akin Salman dan ta
gaishe shi kamar yanda yace, tana shiga ta same shi akan sallaya kau da kanta tayi daga tsaye
tace" ina kwana" kallon banza ya bita da shi yace" bari na tashi sai mu gwada tsawon" ta gane
mi yake nufi dan haka ta durkusa ta saké fad'in" ina kwana" a wahalce ya amsa mata da" lafiya"
tashi tayi dan ta shiga cuisine yace" zauna" zaunawa tayi yayin da ya mik'o mata Al-Qur'ani
yace" fara daga Hizib biyar har zuwa Al-Nass" karb'a tayi ta fara rera 'kira'a, masha Allah kamar
ruwan sama ga tattausan murya Salman sai yaji kamar ya samu kullum ta dinga karanta masa,
musamman Suratul Munafiqun kai kace gabanta akayi wahayinta ko wace kalma ko wane harafi
yana fita daki daki, tana karantawa yana jin tsantsar abinda surar take magana akai, bai san
lokacin da hawaye suka fara zubo masa ba har saida ta kai Suratul K'alam ya d'aga mata hannu
yana share hawaye tana d'ago ido su ka sarke dana juna, ashe ita ma kuka ne take haka suka
share hawayensu ta tashi ta fara aikin gabanta.
27/02/2019 à 21:27 - Vous avez ajouté My Meelat
28/02/2019 à 17:02 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

```dedecated to```

```Fans```



( __Luv you my mom tu est très chers pour moi, ce toi qui m'adonner une bonne éducation

pour devenir comme ca, je te remercie beaucoup bizou😘)_

*RABBIR HAM HUMA KAMA RABBAYANI SAGIRAN.*���

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_ ��

*Page*

3⃣9⃣-4⃣0⃣


Tana cikin aiki taji yana k'walla mata kira, da k'asaita ta shigo d'akin tayi tsaye tana kallonshi,
dama ranshi a matuk'ar b'ace yake dan haka ya falleta da mari yace" wani rainin wayo ne
wannan? ina tsaye kina tsaye kina kallona da idon kinnan kamar na aljanu" k'wallan da suka
cika idonta ne ta matso su hannunta a kumatunta a hankali ta zube k'asa, shi kuma ya d'ora da
tambayar ta" ya akayi wannan Tea d'in ya zuba akan gadon nan? dan ni dai nasan ban aje ba."
kallon gadon tayi ta kalleshi tace" ni kuma ta yaya zan san lokacin da kayi fitsarin kwancen ka"
tana rufe baki ya sake d'auketa da wani wawan marin da yafi na d'azu, zafi daya kai mata kawai
sai ta mik'e tsaye cikin zafin rai ta d'auki cup d'in da ta zuba Tea d'in ta jefa masa a k'irji tana
fad'in" karka saké dukana mugu kawai azzalumi macuci" dafe k'irji yayi yace" Ummi ni kika
jefa?lallai wuyanki yayi kauri, kuma idan banyi da gaske ba to wata rana dukana za kiyi kema,
amma bari yanzu nayi maganin wannan tantirancin naki" wayar chargeur d'inshi ya d'auka a
gefen gado sai ko ya fara zabga ma Ummi ba 'kakk'autawa, haka Ummi ta dinga ihu tana
neman taimako da agaji, amma ina babu haka Salman ya daketa san ranshi ya gaji ya bari,
jefar da chargeur yayi ya shiga douche ya barta nan rakub'e da gado tana ruzgar kuka jikinta sai
rad'ad'i yake mata kamar zai cire duk jikinta ya farfashe.

Haka ya fito ya shirya saida ya harareta ya nuna ta da yatsa yace" wallahi idan har kika ce ba
za ki girmani ba, to wallahi ranki idan yayi dubu zai dinga b'aci, ya zama dole kisan abinda zai
dinga fita daga bakin ki sakarya kawai" ficewa yayi ya barta nan tana kuka.

Awa biyu ta d'auka kafin ta tashi ta fito daga d'akin, cuisine ta nufa dan tunawa da tayi tana cikin
d'ori ne ya kirata, tayi mamakin ganin gas a kashe tasan shi ya kashe dan haka ta koma
d'akinta ba tare da ta bud'a tukunyar taga abinda ke ciki ba, ko wanka ba tayi ba ta kwanta
saman gado taci gaba da kuka da k'unar zuci.
12:20 taga zaman ba zai gyarata ba ta fito ta shiga cuisine ta fara girkin rana, tsananin yunwa
da zafin jiki ga ciwon kai duk ya taru ya mata yawa, haka ta kammala girkin da k'yar kamar zata
mutu.

Tana idawa ta koma d'aki tayi sallah ko wanka ba tayi ba saboda raunikan dake jikinta, tana
kwance Salman ya shigo d'akin yace" wa kika aje da zai zuba maki abincin" fita yayi bai jira

amsarta ba tashi tayi tabi bayanshi, tsaf ta zuba masa shinkafa da miyar kayan cikin ragon da
tayi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0