Showing 15001 words to 18000 words out of 76927 words
za kayi da duka" rigar baccin da ta saka ta
tub'e da k'arfi tana nunawa Salman jikinta da fuskarta tana fad'in" ka duba ka gani yaya Salman
jikina duk shatin bulala ne, dukan da Alhaji yasa aka min a gaban mahaifana da kuma wanda
kai kamin, wallahi ba zan iya zama a gidanka ba yaya Salman saboda bâ kada imani ko kad'an
k'eta kawai ka iya" fad'awa tayi jikinshi tana kuka da k'yar Salman yasa hannu ya fara shafar
bayanta amma da ya ji laushi sai ya fara mata wani salon shafa har yana 'ko'karin kaiwa a
k'irjinta dan haka ta d'agashi ta kwanta akan gado taci gaba da kukanta, a kasalance Salman ya
koma d'akinshi ya kwanta gaba d'aya ta rikita mashi lissafi ko kad'an bai iya tuna abinda ta fad'a
ba, shauk'in da ya ji lokacin da ta rumgume shi kawai ya keji, da k'yar bacci ya d'aukeshi cikin
wannan mawuyacin halin da bai taba jin irin sa ba a rayuwar shi.
23:00 Ummi ta shigo d'akin cikin sallama da muryarta data dakushe wajen kuka, har ta aje
faranti ta zuba mashi duk yana bacci bai san ta shigo ba, saida ta daddab'a pilow da yake
kwance sannan ya tashi aje masa tayi ta ta koma d'akinta.
Tun 07:30 Ummi ta kammala had'a abun karyawa amma bata ji d'uriyar Salman ba haka ta
zauna tana jiran taga fitowar shi, 09:20 ya fito da dogon wando sai singlet fara k'al kallonshi
Ummi tayi ganin ba wani shiri bane yayi amma ya yi masifar had'uwa a cikin zuciyarta tace(na
tabbata yaya Salman bâ yada burin auren mace irina, shi ma zaiso ace ya auri kyakyawa kamar
shi amma Alhaji ya masa yankan k'auna).
Zaunawa yayi ya karya dan Ummi har tayi nata break d'in, yana idawa yace mata" ki fito min da
kujera waje" yana wucewa ta mik'e ta d'auki d'aya daga cikin na dinning ta kai masa zata juya ta
tafi yace" zauna nan" jujjuyawa tayi ganin babu wata kujerar yasa tace" bara na d'auko kujera"
kallon daya mata yasa ta cire takalminta ta zauna in da ya nuna mata, k'afa ya d'ora mata a
cinyarta tare da mik'a mata abin yankar akaifu kallonshi tayi baki bud'e tace" wannan kuma fa,
miye haka?" bai tanka taba hakan yasa ganin babu wasa a al'amarin yasa ta fara masa gyaran
akaifun, kuma abin takaicin ma babu wani abinda za'a cire haka kawai tayi iya yinta ta cire na
cirewa tana idawa dana k'afa ya mik'o hannu, nan ma Kallon shi tayi tace" yaya Salman wai
miya samu hannayen naka?" Hararan ta yayi yace" wallahi zan zubar maki da hak'ori" turo baki
tayi ta rik'e hannun, Kallonta yayi ya kalli hannunta saboda wani sanyi da ya ji tattausan
hannun Ummi ma'abocin zufa a kowane yanayi zafi da sanyi, haka hannunta yake cikin zufa
kowane lokaci, sab'anin nashi mai cikakkar tsoka da dogayan yatsu da santsi haka Ummi ta
gama masa gyaran tsaf tana idawa yace" to maza kije d'akina ki d'auki d'aya daga cikin
jakunkuna da ke da kwai ki shiryamin k'ananan kayana a ciki da duk wani abu da mutum zai
buk'ata idan yayi tafiya." kai ta dafe cike da nuna damuwa kafin tayi magana yace" ba zaki yi ba
ko?" kai ta girgiza sannan ta wuce jiki a sanyaye, Saïda ta b'ace ma ganinshi sannan ya kau da
kanshi.
Tsaf Ummi ta had'a mashi kayanshi tare da duk abinda zai buk'ata, kama daga turare maclean
brush mai zanin rufa kayan bacci ect...., tana idawa ta shiga cuisine dan had'a abincin rana dan
12:50 tayi, tana cikin aiki ya lek'o yana fad'in" ina aikin dana saki?" cikin sauri tace" na kammala
suna d'aki" hararanta yayi yace" amma ba kisan ki ce kin gama aiki ba idan an saki?" turo baki
tayi tace" kayi ha'kuri"wucewa yayi ya barta, d'akinshi ya shiga ya bud'a kayan sosai ya ji dad'in
ganin yanda ta had'a masa kayan ba tare da ya nuna mata ba harda ma abinda shi kanshi bai
taba tunanin d'aukaba duk lokacin da zaiyi tafiya wato maclean da brush, duk lokacin da yayi
tafiya saidai ya siyi sabbi idan zai taho kuma ya baro su dan sun gama mashi aiki, wanka yayi
ya shirya cikin dogayen kaya da hula yayi kyau sosai yana fitowa ya k'walla kiran Ummi har
tuntub'e take wajen sauri tana zuwa ta zube k'asa tana fad'in
"Gani"d'auko min sallaya" mik'ewa tayi ta d'auko mik'a masa tayi, hararanta yayi yace" bara na
sunkuya saina karb'a ko?" turo baki tayi sannan ta sunkuya ta mik'a masa, yana karb'a yace"
wuce muje " binshi tayi tana guna-guni har saïda ya shiga mota sannan yace" oya, kimin Addu'a
zan fita" dalala ta kalleshi tace" yau dai da alama bokan naka ce maka yayi saina maka addu'a
sannan harkokin zasu tafi yanda ya kamata ko?" cikin zafin rai ya bud'e k'ofar mota yana shirin
fitowa, da sauri ta maida k'ofar ta rufe tana fad'in" sai ka dawo to" juyawa tayi zata wuce yace"
ke wannan ce addu'a, haka ake a garin ku?" murgud'a baki tayi tace" in dai sai na maka addu'a
zaka tafi, to ka kwana anan" da gudu ta shige d'aki, shi kuma k'wafa yayi yaja mota yana fad'in"
lallai da sauranki har yanzu, amma zanyi maganinki nan ba da d'ad'ewa ba."
Tana gama aikinta tayi sallah tana idawa ta shiga gyaran d'akinshi tana kammalawa ya dawo
gidan, saïda yaci abinci sannan ya shiga d'aki ya tattaro mata kayanshi k'anana yace ta wanke,
saida tasha mari sakamakon cewa da tayi" haba dan Allah wannan wane irin rashin imani ne?
wannan kayan ina zan iya wanke su, nifa ko a gidan mu bana wanki bare kuma nan" bakinta ya
murd'e yace" nan ai ba gidan ku bane gidan mijinki ne, kuma daga yau karna saké jin kince min
mara Imani, in kuma ba haka ba wallahi saina sauke maki Kafad'a" tsaki tayi tace" wai miji, ina
mijin yake anan? saidai muna maza" ji kake Tasssss, ya kasheta da mari tare da fad'in" ke har
kin isa ki fad'amin haka, wallahi ko Sa'ada dake gaba dake bata isa ta fad'amin haka ba, bare
kuma ke da aka haïfa a gabanta" haka ta fara wanki tana kuka tana fad'a, bata gama ba sai
misalin 17:40,saboda ko a gida ita ma kayan da suka zama wajibi ne a gareta ta wanke da
kanta take wankewa, amma manyan kaya mai wanki ake bawa ya wanke mata, amma yau
gashi tana ma k'aton gardi wanki( inji Ummi fa).
Tana idawa ko wanka bata yiba ta d'ora girkin dare, a gajiye ta kammala aiki bayan sallah isha'i,
tana gamawa ta aje Kwanukan a dinning tayi alwala tayi sallah tana sallamewa daga nan bacci
ya d'auketa ko shafa'i da witri bata yiba, Salman na lek'awa yaga tana bacci ya fito yana cewa"
raguwar banza, ai dama da gangan nake saka ki aikin dan babu tsiyar da kuke a gida ke da su
Khairat da jawahir sai iskanci da zuwa gidajen juna ana d'aukar photo" da kanshi ya zuba
abincin yaci ya koma d'akinshi yana latse latse a ordinateur d'in shi, jin an fara kad'a iska ga
walk'iya da ake ana cikin haka aka fara yayyafi har ruwa suka fara k'arfi, ganin an d'auke wuta
yasa ya kunna wutar wayar shi ya tashi ya nufi d'akin Ummi dan yasan yanzu zata fara neman
taimako, k'aro yayi da Ummi k'ofar d'akin tana shirin fitowa daga ita sai towel d'in dake d'aure a
k'ugunta tana shafa turare aka d'auke wutar, kallon juna su kayi sum sum Ummi ta haye saman
gadon ta kwanta, Salman ma zaune yayi gefenta tsawon lokaci ya d'auka a zaune, ganin ba
ada niyyar maido wutar ya gyara kwancinshi shi ma bacci ya d'aukeshi.
Salman ne ya fara farkawa da k'yar ya bud'a idonshi saboda haske an maido wuta suna bacci,
addu'ar tashi daga bacci yayi( Alhamdu lillahi lazhi ahayana ba'ada ma amatana wa ilaihin
nushur).
Maida kallonshi yayi wajen da Ummi ke kwance, wani irin fad'uwar gaba ne ya ziyarce shi ganin
Ummi zigidir babu komai a jikinta komai ya fito waje, towel d'in da ta kwanta da shi ya kama
gabanshi saboda gigin bacci kuma ba tasan ma an yiba, wasu irin yawune ya dinga had'iya da
k'yar ga wata irin fitinanniyar sha'awa da ta taso mashi lokaci d'aya ji yake kamar ya abka mata,
saidai wata zuciyar na gargad'inshi akan hakan, rufe fuskarshi yayi da hannayenshi yana fadin"
a'a Salman ka zama namiji mana, kar kayi haka karka zubar ma kanka mutunci mana" maida
kallonshi yayi amma ina saida zuciyar shi ce ta fizge shi ya kai hannushi a k'irjinta ya shafa,
lumshe ido yayi tare da sauke numfashi a hankali yace" ya salam, Allah ka kare ni" zunbur
Ummi ta mik'e tare da yayumo zanin rufa ta rufe jikinta tana kallonshi tace" miye haka kuma, kai
da kanka, ashe haka kake bansani ba "?" basarwa yayi kamar ba shi ba ya tashi ya fita duk
takaici ya ishe shi da kunya, sallah ya fara yi sannan yayi wanka ya shirya, yana fitowa dai-dai
da fitowar Ummi da hijabinta ta idar da sallah, cike da raini tace" ina kwana" kallonta yayi yace"
bara na duk'a saina gaishe ki ni" durk'usawa tayi ta saké gaishe shi amma bai amsa mata ba,
mik'ewa tayi zata shiga cuisine yace
" ki had'a iya bakinki, ni yanzu zan tafi" cike da mamaki tace" ina kenan?" baiyi tsammanin
tambayar daga gareta ba shiyasa yace" balaguro zanyi" cikin ladabi tace" balaguro zuwa ina
kenan?" Cotonou " ya bata amsa baki bud'e ta kalleshi tace" Cotonou fa yaya Salman,to idan ka
tafi ni da wa zan zauna a gidan?" Kallo ta yayi yace"kamar ya,mi zai cinye ki a gidan to?" kawai
sai tasa kukan shagwab'a tace" wallahi ni ba zan yarda ba, haka kawai ka tafi ka barni ni kadai
cikin gida kamar manya" abu kamar wasa Ummi ta dinga tsala kuka, amma rashin imani na
Salman ya ki damuwa saida ya wuce yace" idan kin zauna ke kad'ai mugun abu ya jima bai
cinye ki ba"sai kud'in daya fiddo ya jefa mata a k'irji ya wuce ya barta nan, da gudu ta fito k'ofar
d'akin ta tsaya tace" kaga kazo ka d'auki kud'inka, bana so tsiyar me zanyi dasu, tunda dai kai
bâ kada imani zalinci kawai ka iya mugu kawai" takalmanshi ya ciro ya jefo mata, da sauri ta
shige d'akin tare da rufewa da key, d'aukar takalmanshi yayi yana fadin" zan dawo ai bacan zan
zauna ba, sai kinsan kin fad'amin haka, mai kama da mage kawai marar kunya"yana fita
Khamis yana jiranshi dama ya d'aukeshi suka wuce suna gaisawa, Ummi kam kuka kamar ranta
zai fita.
```muje zuwa dai mutane na```
28/02/2019 à 17:02 - Mamar Latifí ½í²ƒ: í ½í²‘ AUREN HA'DI í ½í²‘
_Samira Harouna_
```wannan soyayya na yarda had'in allah ce, sai dai in ce allah ya bar k'aunaí ½í¸˜```
```-My Meelat```
```-My Heenat```
```Ku na Musammam ne ku nada karamci sosai a gare ni.
```
í ¼í·¸í ¼í·¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
4⃣5⃣-4⃣6⃣
Khamis ne yace" wai ni ban tambayeka ba da wa kabar mutuniyar ne a gida?"uhumm to ita da
wa kake so na barota to, ko kaima kana nufin na samo mata wanda zai taya ta kwana kafin na
dawo kamar yanda take fad'a?" gyad'a kai Khamis yayi yace" sosai kam, kai da a tunaninka
zaka barta ita kad'ai ne ba tare da kowa ba?ai kaima kasan hakan ba zai yiwuba ka bar yarinyar
mutane a gida ko sati ba tayi a gidanka ba kace zaka k'yaleta ita kad'ai, dan ma kasamu ta
barka ka tafi" wata irin dariya Salman ya shek'e da ita kafin yace" lallai kam akwai mahaukata
da dama a garin nan, kai yanzu kana tunanin wannan yarinyar zata iya hanani yin abinda naga
dama? to bâ ita ba ko wacce ta fita ma bana jin ta isa bare kuma ita" haushi Khamis ya ji yace"
kai kaga wallahi da gaske nake fad'a maka, bai dace ba ace ka barta ita kad'ai a wannan sabon
gidan, kai kan kafa bak'one a gidan bare ita sannan babu wanda ta sani a unguwar kaga
hakk'inka ne kareta da kula da ita, idan wani abu ya sameta mi zaka fad'ama iyayenmu?" shiru
yayi yana tunani kafin yace" to malam Khamis yanzu fad'amin ya kake so ayi?" to yanzu dai
kaga wannan tsohon mai ran k'arfe ya hanata zuwa wajensu bare ta koma can gida, haka kuma
ya hana kowa zuwa wajenta bare a d'auko ko yara akai mata can kasanta ko da wasa da yara,
kenan ni ina ganin in har zaka amince to yanzu idan na aje ka zanje sai na d'aukota na kaita
can gidana sai su zauna tare da Jawahir nasan za tayi farin ciki da hakan." kallonshi Salman
yayi yace" kana ganin hakan babu wata matsala?ni fa bana son abinda zai raba ni da dangina"
kai ya girgiza yace" insha Allah babu abinda zai faru da yardar Ubangiji zan kula sosai" d'aga
kafad'a yayi yace" OK ba damuwa ka d'aukotan kawai, amma kafin ka d'aukota ka biya ka siya
mata yar k'aramar waya wacce zata dinga kunna tocila da dare idan an d'auke wuta, dan karta
takura maku kuna tsaka da hutawa" dariya Khamis yayi yace" saboda ta kunna tocila za'a siya
mata wayar? badan ka dinga kiranta kana jin halin da take ciki ba? kumafa karka manta kai ka
amsar mata waya kuma babbar waya ka amsa amma sai kace a siyo mata yar k'arama, wato ka
siyar da ta-ta kud'in kuma k'arfi ya cinye ko?" dariya kawai Salman ke yi tunda Khamis ya fara
magana kafin yace" e mana na cinye dan na nuna ma duniya da kai da kaya duk mallakar wuya
ne." gira Khamis ya had'e tare da d'agata sama yace" eyee,lallai mutumin nan, ai banyi tunanin
zaka fara irin wannan tunanin akan Ummi ba kaga kuma idan kana jin irin haka a ranka to fa
wata rana za muga yar k'anwar tamu da juna biyu" yana k'arashe maganar ya fashe da dariya
yana kallon Salman, shi kuma photon Ummi ne ya dawo masa cikin 'kwa'kwalwa lokacin da ya
ganta babu kaya a jikinta da irin sanyin da ya ji lokacin da ya tab'a k'irjinta lumshe ido kawai yayi
ya jingina kansa a kujera yana murmushi, ina ma ace hakan zata sake faruwa ko da tab'awa ne
yayi, Khamis ne ya katse shi yana fad'in" to malam kawo kud'in ko?" hararanshi yayi yace" kai
gafara can dallah k'anwarka d'in dan zaka siya mata abu saina baka kud'i? to bâ zan bayar ba."
dariya Khamis ya ci gaba da yi yace" kaji mutum kai, baka ji ance gwamnati ta hana aikin banza
ba? ka kawo kud'i matarka ta samu waya ka dinga kiranta kuna gaisawa, ka k'i bada kud'i kuma
kaje ka dawo ba tare da kayi magana da matarka ba." to sai me? na fad'a maka ina san jin
muryarta ne, ni bata dameni ba" wani Kallo Khamis ya watsa mashi yace" malam manu kenan
har yanzu baka san mace ba amma, daga ranar da zaka san wacece Ummi to fa a lokacin zaka
fara damuwa da tunani a kanta." tsaki Salman yaja yace" kar Allah ya kawo ranar da zan santa
ko, yarinyar da nake Addu'a naga tsorona a idonta sai gashi yanzu d'an zaman da mukayi na
fara ganin wannan tsoron, haka kawai lokaci d'aya saina b'arar dashi,Allah karya nufeni da
ganin ranar da zan tub'e kayana a gaban wannan k'azamar yarinyar harna
kusanceta."murmushi Khamis yayi yace" banda fariya manu, kai yaro ne baka san tasirin mace
a wajen namiji ba shiyasa, amma tunda Allah ya had'aku zama a inuwa d'aya to ina tabbatar
maka zaka sani lokacin zai zo, s'il plaît a Dieu."
Tsaki Salman yayi yace" insha Allah haka ba zata faru ba" shiru su kayi babu wanda ya saké
magana har ya aje shi gidan Bus Sonef su kayi ban kwana, kamar yanda tun jiya yayi ban
kwana dà iyayensu suka masa Addu'a sannan ya juya, saïda ya tsaya ya siya mata waya tare
da sabon puce( sim card) sannan ya wuce gidan.
Tunda Salman ya fita Ummi ta zauna saman kujera ta fara kuka, Sallamar Khamis ne da taji ya
sata saurin goge hawayenta tana amsa sallamar, tunda ya shigo ya fahimci kuka take amma da
yake mutum ne shi wanda bai san shiga rayuwar kowa dan haka koda suka gaisa yace"
k'anwata ko dai dan ya tafi ya barki kike kuka?" kai ta girgiza ba tace komai ba dan haka shima
yace" to kinga tashi ki had'o kayanki zan tafi da ke can gidana ki zauna tare da yar uwarki har
lokacin da zai dawo" kai Ummi ta girgiza tace" a'a yaya Khamis ka barni anan idan yaji na tafi
can bada izininshi ba zai min fad'a ko ma ya daké ni, kawai ka barni zan zauna ni kad'ai Allah
zai kareni" tausayinta yaji ya kama shi sosai amma sai yace" haba hajia Zeinabou karki damu
fa, shi yace nazo na d'aukeki" da sauri ta d'aga kai tace" da gaske yaya Khamis ? " k'warai
Kuwa tashi ki had'o kayanki mu wuce" tashi tayi da gudu tana farin ciki Khamis kuma a zuciyar
shi cewa yayi,lallai duniya ta kusan tashi wai yau Ummi ce take tsoron fad'an Salman ha'ki'ka
yayi gaskiya da yace ya fara ganin tsoronshi
a idon Ummi kuma ga dukkan alama labarin Salman da Ummi ya kusa canzawa.
Tsaf ta had'o duk wani abun buk'atarta ta rufe gidan suka tafi bakinta har kunne.
Suna shiga gidan suka fashe da k'ara ita da Jawahir suna ta tsalle kamar yara tsabar farin ciki,
Khamis