Showing 24001 words to 27000 words out of 76927 words

Chapter 9 - Auren Hadi Book Compelet Samira Haruna

22 Jun 2026

1104

LABYB*_(momy na)_
*MOMYN SULTAN*_(aunty)_
*MOMYN DEEJA*_(ma belle)_
*HAWA JAMIL*_(aunty na)_
*HAKEEMA*_(ma chérie)_

```WANNAN PAGE SADAUKARWA CE GAREKU, DAN HAKA KUYI YANDA KUKE SO DA ITA
TAKU CE KYAUTACE DAGA GARENI```


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_��

*Page*

5⃣7⃣-5⃣8⃣



Yanda Salman yaga rana haka yaga dare ba tare daya rintsa ba, kalaman Jawahir sun gigita
tunaninshi sosai ya kasa fayyace gaskiya da k'arya, indai har fad'uwar gaba yana d'aya daga
cikin alamun so, to kenan tun Ummi na matashiya yake sonta, domin ko duk lokacin daya ganta
sai gabanshi ya fad'i sannan baya jurar kallon idanunta, suna sashi yaji wani yanayi a tare
dashi, hakan ma yasa yake kiranta da mai idon aljanu kona mage wani lokacin.

Ya yanke shawarar komawa gida jibi, dan haka ya ciro ticket haka ya k'agu safiya ta waye ko ya
kama hanyar gida,yayi niyyar bankad'o gaskiyar abinda Jawahir ta fad'a masa zaiyi k'ok'arin
gano gaskiya ta hanyar lalubo kishin Ummi sannan yasan dalilin kishin nata.

08:00 na safe suka kamo hanyar zuwa niamey, banda kallon pic d'in Ummi babu abinda yake,
ko abinci baisa a bakinshi har suka sauka, duk da gobe zai wuce amma yayi niyyar bazai
fad'ama kowa ba yana so ya masu bazata, sannan yaga yanda Ummi zatayi.

Bayan ya huta sosai abu d'aya yake da buk'ata yayi wato bacci, amma ina ya kasa samuwa duk
da cewar baiyi bacci daren jiya ba, wayarshi ya d'auka yana so ya kira Ummi amma yana tuna
ya fad'i bazai k'ara kiranta ba, haka ya daure ya kirata amma abun haushin wayar kashe, haka
ya k'urama pic d'inta ido yana kallo har bacci b'arawo ya d'aukeshi.

*Washe gari* da safe Ummi ce ta fito farfajiyar gidan dan tasha iska, sanye take da doguwar
riga mai colour ja da bak'i da fari, sama a matse sai k'asa daya bud'e ba tada dan kwalli dan
haka ta d'ora na abaya ba'ka, zaune tayi akan 'yar gajerar katangar da aka kewaye rabin
harabar gidan da ita, jingina bayanta tayi ta rumgume hannayenta a k'irji tayi shiru tana kallon
'yar k'aramar bishiyar mangaro, a hankali ta tuna ranar da suka fito tare da Salman ta rakoshi
zai fita, da kuma ranar da ta fad'i saboda jiri ya d'auketa sannan ya kawo mata madara tasha.

Rayuwarsu take tunani tana murmushi ajiyar zuciya ta sauke tana mai k'ara fad'ad'a
murmushinta tace "ina ma kadawo yau, da zan zauna da kai ko dukana ne kaci gaba dayi da
wannan tattausan hannun naka"

Jawahir dake zaune gefe ita da Khamis ta kalleshi tace "mijina dubi mutuniyar murmushi take
ita kad'ai, ina ga fa tunanin yaya Mane take"

Dariya suka saka gaba d'ayansu hakan ya janyo hankalinta, mamakine ya bayyana a fuskarta
dan batayi tunanin suna nanba suma, saidai kallonsu kawai take saboda ganin k'afar Khamis a
cinyar Jawahir tana masa wankin k'afa, take ta tuna da ranar da tama Salman yankan akaifu,
wani murmushin ta koma saki tare da jin wani sanyi na lullub'eta, gaba d'aya taji kawai tana son
ganin Salman ko fad'ane ma su dinga yi zata ji dad'i.

Jawahir ce data lura ba tada niyyar magana tace "Hajia Abu tunanin me ake ne haka?" kallonta
Ummi tayi tace "ba komai"

Tab'e baki tayi tace "to naji ba komai, amma ya kamata ki shirya gobe muje muyi kitso" cikin
farin ciki tace "yawwa dama nima ina so nayi kitso"

Cewa tayi "amma ai da kin bari har yaya Salman zai dawo sai kiyi" hararanta kawai tayi ba tace
komai ba, Khamis kam cewa yayi "to nidai kamar kullum ne, indai har kina so kije to ki tabbatar
kin kira mijinki kin fad'a masa."

Ba tada zab'in daya wuce ta kira ta fad'a masa dan haka tace "to yaya Khamis zan kira, na lura
kaidai kana jin tsoron mutuminan sosai"

Hararan ta yayi yace "ke kuma baki tsoronsa ko jaruma?" dariya kawai tayi ba tace komai ba.


Ummi bata kira Salman ba saida safe sannan ta d'auki wayar ta kuna, ta danna numbershi tana
fara k'ara taji gabanta ya fara dukan uku-uku, da k'yar ta iya daurewa tana sauraran ya d'aga.


Tana jin ya d'aga taji cikinta ya d'uri ruwa take taji tana buk'atar kewayawa, amma haka ta dake

ba tare da tace komai ba, Salman dake saman hanyar dawowa yana ganin kiranta yaji farin ciki
ya mamayeshi, ba tare daya kula ba ya samu kansa yana mai kasaitancen murmushi amma
daya tuna wacece Ummi da kuma kashe wayar da tayi, kawai sai ya b'ata rai sannan ya d'aga.

"Oui je t'ecoute" ( na'am ina jinki) ya fad'a a tak'aice, cikin sanyanyen murya tace "haba ba ko
sallama?"

Cikin dakakkiyar murya yace "ki fad'i abinda yasa kika kirani da gaggawa inada abinyi?" tab'e
baki tayi tace "dama na kira ne dan na fad'a maka za muje wajen kitso nida Jawahir yanzu,
kuma yaya khamis yace dole saina fad'ama zanje shiyasa na kiraka."

Wani buhun haushi ne ya kama shi, wato badan Allah ta kirani bama kuma saida akace ta kira
sannan ta kira, ba damuwa zanyi magananinki ya fad'a a ransa.

Bud'ar bakinshi yace "baza kiba to indai nine zan bada izinin, ni dama nasan kinfi k'arfin ki kira
ni ki gasheni bare ki tambayeni ya nake saboda bakisan mi ake nufi da miji ba, amma yanzu
buk'atarki tasa kin kirani bayan kashe waya da kika yi."

Haushi taji itama cike da tsiwa tace "kaga nifa na kirane badan kamin masifa ba, sannan da
kake cewa na kashe waya, e na kashe saboda banga anfanin kirana da zaka yiba tunda kana
da wacce zaka dinga hira da ita, kuma ni ba izininka nake jira ba ina so naje kitso kuma zanje."

Cikin tattausan murya yace "to kenan kin fad'amin ne dan nasan zaki tafi, ko ko kin fad'amin ne
dan nasan kin isa da kanki, ko kuma umarni ne kike bani akan na baki izinin fitar?"

K'irjinta k'ara tsananta bugawa yake amma haka ta daure tace "ka d'auki d'aya da kaga yafi da
cewa dani saika sani a mahalin" cikin jin haushi yace "Ummi ince dai nine mijinki ko?"

Kamar tana gabanshi saida ta murgud'a baki tace "to saime mijin da baisan hakk'in matarshi ba,
zaka k'ara aure amma saidai naji a gari amma ba komai akwai Allah, dan haka ni yanzu ko ka
bani izini ko ka k'i bani izini, fitata zanyi in yaso in kamatsu ka fara bada umarni to sai ka bari
harka kawo k'waillar matar taka saika fara mulkarta, amma ba Ummi ba."
Salman daya saki baki yana sauraranta izuwa yanzu ya fara fahimtar inda zancen, wato tana jin
haushi dan zan k'ara aure, murmushi yayi yace "babu ruwanki da amayarta yarinya mai
nutsuwa da hankali, sannan na fad'a maki karki je ko ina har saina dawo"

Abinda ya fad'a shiya k'ara harzuk'ata, cikin fitina tare da k'ok'arin b'oye hawayenta tace "saina
je d'in, idan ka dawo ka kasheni." cike da izza yace "aiko idan kika fita bada izinina bâ, to zaki
rasa k'afa ko ido"

Cikin kuka mai tsanani tace "e na rasa k'afar tunda kaine ubana da zaka min baki Ya kama ni."
tana fad'a ta kashe wayar, toilet ta shiga ta wanke fuskar'ta sannan ta fito ta samu Jawahir da

Khamis suna jiranta fitowarta.

Khamis ne yace "kin kirashi?" kai ta fara girgizawa sannan tace "na kira kuma yace naje, amma
wai karna dad'e" hakan data fad'a yasa Khamis ya tabbatar data kirashi d'in.

Cikin farin ciki Khamis ya aje su gidan mai kitson, amma yace idan an ida su hau adaidaita sahu
su koma gida tunda suce sai sun biya 'yar kasuwa sunyi siyayya.

_Ummi kam akwai marar jin magana, ko baki ji maganarsa a matsayinshi na mijinki ba, ai kin ji
ko a matsayinshi na yayanki._
05/03/2019 à 17:30 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


_Samira Harouna_

```OH ALLAH KABAWA 🅱K LAFIYA ALFARMAR ANNABI MUHAMMAD S.W.A, ALLAH YASA
KAFFARA NE```


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_��

*Page*

5⃣9⃣-6⃣0⃣


Saida su kayi sallah azahar a gidan mai kitson sannan suka fito, a k'afa suka k'araso 'yar
kasuwa saboda duk bisa hanyane babu nisa sosai, sayayya su kayi sosai musammam Ummi,
duk kud'in da Salman ya bata kaf ta kashesu ga k'ananan kaya da kayan bacci da kuma kayan
kwalliya.
Ana kiran sallah la'asar suka tsaya bakin titi suka shiga adaidaita.

_Tsotsayi kenan wanda ba'a sa mashi rana, idan ya wuni tofa baya kwana_

Sun d'auki babbar hanyar da zata sadasu da gidan saiko wani mai mota daya fito daga cikin
kwana da iya k'arfinsa cikin ganganci, saiko yayi gaba da adaidaitar dasu Ummi ke ciki.

B'angaren da Ummi take nan adaidaitar ta fad'a, mai adaidaitar na fad'owa k'asa kuma wani mai
babur ya taka kanshi take ko shurawa baiyi ba yace ga garinku nan, tuni aka kewaye su ana
k'ok'arin basu agaji, wasu samari ne suka kama Jawahir ta taka adaidaitar ta fito ta sama,
sannan aka d'aga adaidaitar dan a janye Ummi.

Ana d'aukewa Ummi ta tashi zaune idonta ne suka sauka kan mai adaidaita, tana ganinshi ta
dafe kanta tare da zankad'a uwar k'ara take kuma ta saké zubewa k'asa somammiya, Jawahir
da jiki keta mata rawa ta kasa tsayawa daidai wani dattijo ne ya janyeta daga wajen, kafin aka
d'aukesu aka nufi babbar asibiti da su.


Jawahir gurjewa kawai tayi a goshi, dan haka ana gama dubata aka amshi wayarta aka kira
Khamis, Khamis bawon Allah tashin hankali ne ya shiga wanda bai tab'a shiga irinsa ba, haka
ya garzayo yazo asibitin.

Saida aka bashi tabbacin jikinsu da sauki sannan ya tafi gida ya fad'ama manyansu halin da
ake ciki.

Babu wanda yayi yink'urin zuwa ba tare daya fad'ama Alhaji ba, amma sam ya rufe ido yace a
barta can ita da halinta, ran kowa ya sosu musammam ma iyayenta sunfi kowa shiga damuwa
sai kuma Hajia Zeinabou wacce babu wanda ya kaita d'aga hankalinta.

Ganin ba zai barsu ba yasa Hajia Zeinabou ta fara rera mashi kuka tana lallab'arshi, ba zai juri
kukanta ba shiyasa ya amince duk mai so yaje ya ganta amma hakan ba yana nufin ya yafe
mata bane.

Dan-danan sai asibiti ta cika da yan uwa, an masu barka ta wani b'angaren kuma an jajanta
masu, Khamis duk ya rud'e ya rasa ta yanda zaiyi ya kira Salman ya fad'a masa, dan a ganinshi
babu dad'i ace an baka amana amma amanar ta salwanta a hannunka.

Missalin 17:20 Salman ya doko ma Khamis kira wanda yasa gabanshi tsinkewa, da k'yar ya
d'aga basu ko gaisaba Salman yace "kazo ka d'auke ni dan Allah na gaji da kiranka" kashe
wayar yayi ba tare daya jira me zaice ba.

Haka Khamis yaje gidan bus d'in ya d'aukoshi, kallo d'aya Salman yama Khamis yasan akwai
matsala amma baya cikin yanayin farin ciki shiyasa bai tanka saba, ganin sun d'auki hanya
daban yasa yace "ina kuma zaka kaini malam? ka kaini gida dan Allah yunwa nake ji" baice
masa komai ba sai cigaba da tuk'insa yake har suka kai babbar asibitin.
Tunda suka shiga gabanshi keta dukan uku-uku, yana da 'yan uwa dayawa dan haka ya rasa
wa zaiyi tunani ke asibiti, zuciyarshi na raya mashi wani ko wata mai mahimmanci sosai ne a
gareshi ke kwance anan d'in.


Ummi na zaune an gama mata dressing d'in ciwon, sai yanzu ne take jin zafin ciwon sai kukan
shagwab'a take masu Hajia dasu Mama (mahaifiyar Salman) su kuma sai rarrashi suke cike da

taussayinta, kwatsam Salman ya fad'o d'akin yana zare ido yana kallon ikon Allah.

Fad'uwar gabanshi ya k'ara tsananta duk jikinshi yayi sanyi ga wani jiri daya keji yana 'dibarshi,
kukan da Ummi keyi yasa yaji takaici ya rufeshi, wato rainawa mutane hankali zatayi ma bayan
bata ji maganarsa ba.

Sannu da zuwa su mama suka masa cike da mamakin yanda yazo bai sanar da kowa ba, tsaye
yayi kusan k'afafunta data ji ciwo k'afar dama an nad'eta da bandeji tun daga wajen ijiyar sau
har zuwa cikin tafin k'afar saboda k'arfen daya karceta har farar coka ta fito, sai k'afar hagu
kuma gurjewa ne a gwiwa amma saboda buguwa da k'afar tayi kuma adaidaitar ta tausheta
hakan yasa tayi kumburi sutum da ita, sai kuma hannun dama data fad'a samanshi ba daidai ba
ta goce.

_Hum dama 'yan magana sunce, in haka ji bari ba kaji hoho_

Da k'yar ya tambayi abinda ya faru, ana fad'a masa ya kalli Jawahir dake gefe da 'yar
gurjewarta a hannu yace

"Kingani ko Jawahir da yake ke kina jin maganar mijinki, kinga baki ji ciwo sosai ba Allah ya
k'ara kiyayewa"

Take La mama ta maida kallonta ga Ummi, Ummi kam da hannu ta mashi alamar yayi shiru, dan
inhar La mama taji to abinda zata mata sai yafi ciwon dake jikinta yi mata zafi.

Zagayowa yayi ya zauna kusa da ita, saida ta sauké ajiyar zuciya saboda shak'ar kamshin
turarenshi har cikin zuciyarta taji dad'in zaman da yayi kusa da ita, ji tayi kamar ta fad'a jikinshi
ya rumgumeta, kallonta yake sosai dan har yanzu yana mamakin abinda ta aikata, baiyi
tsammanin zata tafi ba daya hanata ashe da gaske take zata tafi.
Cikin shagwab'a tace "yaushe ka dawo?" kafin ya bata amsa La mama tace "abinda ya kamata
ki tambayeshi kenan?" k'ara kwab'e fuska tayi tace" kazo lafiya, ya hanya?"

Tsawa La mama ta mata tace "Ummi mijinki kike kira da kai, babu girmamawa a ciki ba zaki iya
cewa kunzo ba, saidai kazo?" kamar zatayi kuka amma ba tace komai ba, Hajia Zeinabou ba
zata juri ganin b'acin ranta ba dan haka tace,

"Kai kuma ka amsa mana, yarinyar dake cikin halinnan ai tayi 'ko'kari ma data iya gaishe shi."
kallon Hajia yayi yace "ba zan amsa ba Hajia saboda bakisan méta aikata ba"

Yana fad'a ya mik'e ya fita harabar asibitin, La mama tashi tayi tabi bayanshi, tsaye tayi tana
Kallonshi kafin tace,

"D'ana ka fad'amin meta maka dan Allah?" kallon La mama yayi cike da kunya sannan yace "La

mama babu komai wasa nake mata"

Murmushi La mama tayi tace "Salman yaushe ka fara b'oyema mahaifiyarka farin cikinka da
damuwarka dama sirrinka?" baya b'oyema La mama komai, idan har bai fad'a mata abinda zata
nutsu ba to ya san zata iya huce haushinta akan Ummi dan zata titsiyeta saita fad'a mata.

"A'a La mama bawai na b'oye maku bane, kawai jiya munyi wayane da ita kuma munyi akan ba
zata saké kashe waya ba, amma nayita kira tun safe bata d'auka ba sai yanzu nazo na tarar da
abinda ya faru."

Ko kad'an La mama bata yarda ba, amma bata so ta takurashi dan haka tace "shikenan ba
damuwa" ciki La mama ta dawo amma badan mutanen dake d'akin ba da sai ta tambayeta
abinda ya faru.

Salman ya jima yana jin babu dad'i yana tunani akan abinda Ummi tayi "me yasa tayi haka, me
yasa da nace ta zauna tak'i zaunawa, shin abinda ya fad'ane da wasa dan ya hanata fitar shine
ya faru da gaske, shin dama haka bakin miji keda ta siri akan matarsa, inko hakane dole nasan
me zan dinga fad'a mata tunda dai ita ba zata ji maganarshi."

"Yanzu gashi abinda ya faru da ita, yanzu da ita ce fa abinda ya faru da mai adaidaita sahun ya
faru da ita fa saime ya faru da ni?" ya tambayi kanshi.

Zunbur ya mik'e tsaye daga kan tabarmar da yayi sallah la'asar, cikin sauri ya nufi d'akin da
suke yana fad'in "ina babu abinda zai sameta insha Allah, tana nan tare da ni ba zata mutu ba
muna nan tare."

Tsaye yayi k'ofar d'akin saboda mutanen dake ciki, idonshi akan Ummi wace idonta sukayi jawur
alamar har yanzu tana kuka, juyawa yayi ya fita daga d'akin gida yasa Khamis ya kaishi.

Wanka yayi ya shirya sannan suka fito tare restaurant (maqui) ya ajeshi dan yaci abinci amma
saiya kasa, tunaninshi ya koma kan Ummi da ciwonta dan gani yake kamar shine silar
hatsarinta, haka suka dawo asibiti suna zuwa lokacin magrib yayi dan haka suka tsaya
masallaci sukayi sallah sannan suka wuce d'akin da Ummi take.
Sun samesu sun shirya suna jiransu zasu tafi gida, Hajia ce ta kalli Salman tace "kaga tunda ba
zata iya takawa ba, ka d'auketa ko"

Ido ya fiddo ya kalli kowa dake d'akin yace "haba Hajia ai k'wara na d'aukeki na goya akan
wannan b'ulleliyar, dan zata iya karyani gashi dama ina jin yunwa, kinga saimu fad'i daga ni har
ita."

"Kaga banasan rainin wayo, in zaka d'auketa ka wuce muje ka d'auketa, in kuma ba zaka

d'auka ba nasa Khamis ya d'aukarmin 'yar leleta." ta fad'a tana kashe ma Khamis ido.
05/03/2019 à 17:30 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_


```DEDECATED TO```

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_��

_Kunada karamci a gareni matsayinku da girmanku ya mafi haka, domin daga cikinku ne na
samu makusanta masu nunamin k'auna a kowane lokaci *Yan ZAMAN AMANA* ina k'aunaku
dukanku._

'KUNGIYATA ABAR ALFAHARI MAI NUNA DAMUWA GA WANDA YAKE CIKINTA


*Page*

6⃣1⃣-6⃣2⃣


Matsowa Khamis yayi kamar zai d'auki Ummi, saiko Salman ya hankad'eshi yana fad'in" dallah
malam gafara daga nan" bushewa sukayi da dariya, shi kuma sunkuyawa yayi ya zura
hannunshi ta bayanta ya tallabota, d'aya hannun kuma ta k'asanta nanma ya ciccib'ota gaba
d'aya.
Kamar zuciyarta zata fasa k'irjinta ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0