Showing 1 words to 3000 words out of 76927 words

Chapter 1 - Auren Hadi Book Compelet Samira Haruna

22 Jun 2026

1112

24/10/2018 à 22:00 - Vous avez créé le groupe “👸PRINCESSE👸�
27/02/2019 à 17:29 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI💑

_Samira Harouna_

*Wannan labari ne da na yishi a farkon fara rubutu na, amma abisa wasu kura kurai da ke cikin
waccen rubutu sabida rashin sanin miye rubutu a waccen lokacin, hakan yasa zan sabinta
maku shi ta hanyar canza Salan rubutun da ingantashi fiye da na baya tare da canza wasu
abubuwa daga ciki dan jin dad'in ku*
💗💗💗💗💗💗
Bismillahi Rahaman Rahim
💗💗💗💗💗💗

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da_ _amana insha Allah)_ ��

*Page*

1⃣-5⃣

Duk girman gidan bai hana shi cika ba sabida hidimar bikin da ake, kowa cikin farin ciki ya ke
babu bakin ciki a nata hayaniya, shagalin biki kenan na auren da za'a d'aura nan da Minti
Ashirin, Amare ne guda hud'u da angayen su.

ban an kara ba naji an bige ni har saida alkalamina ya fad'i k'asa, daga kai nayi naga ko wace
shedaniyar ce, wata kosansan Budurwa na gani sai gudu take tana waiwayen bayanta kafin na
kula naga wani 'Kakk'arfan Saurayi da gudu yana biyar ta da belt a hannu, bin bayan su nayi
har cikin katon falon da ta shiga in da taci k'aro da wata kyakyawar tsohuwa ta b'oye bayanta
tana fad'in,

"Dan Allah hajia ki taimake ni kice karya dake ni" tsaye yayi yana huci, cikin zafin ray ya kai
mata duka da belt kin hannunshi yanda ya sauka a bayanta ne yasa ta saki k'ara tana Ihu,
tsohuwar ce da ranta ya b'ace tace" kai SALMAN ashe ba kada hankali wai miyasa kuke
hakane kamar wasu Kananan yara?" juyawa tayi ga yarinyar ta jawo ta tace" mi kika mashi
nasan dai haka kawai baya biyo ki ba tunda ba mahaukaci bane shi?" cikin kuka ta fara mata
bayani" wallahi hajia kawai muguntar sace ta tashi, daga naje karb'ar charger ta wajen yaya
MUBARAK shine fa kawai yake kallo na daga nace ya kama bakin shine wai ya biyo ni" tana
rufe baki ya kama kunnanta cikin masifa yace" kinji ko hajia dan ta raina ni ni zata ce wai na
kama baki na, ina abin kallo a jikin ta yake, wallahi sai na karyaki in kika k'ara shiga harkata
shedaniya kawai" fizge kunnen''ta tayi cikin zafin nama ta mike tsaye zatayi magana kuma sai ta
ruga a guje sabida d'aga belt kin yayi zai buga mata, juyawa yayi shi ma yabar wajen.

Saïda tabi kowannen su da kallo kafin tace" na samu hanyar da zanyi Maganin ku tak'adaran
yara kawai, kuna yan uwa amma kun zama kamar b'era da mage, Insha Allah Komai ya zo
k'arshe daga yaou, idan kuka zama d'aya zaku daina duk, wannan shirmen" wuce wa tayi d'akin
kakan yaran inda bata gushe'ba har saida burin ta ya cika.
09:00 aka d'aura auren Amare guda hud'u gami da wadanda aka kara suka zama biyar.

*to yan uwa ya zata kasance idan aka d'aura auren wadanda babu su a cikin jadawalin d'aurin
auren yaou?*

Yan Uwa kuna san labarin in'ci gaba?


~Sai naji daga gare ku.~
27/02/2019 à 17:29 - Mamar Latif💃: 💑AUREN HA'DI💑

_Samira Harouna_

*page*

0⃣6⃣-1⃣0⃣

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da_ _amana insha Allah)_ ��

Sank'ira ne ya fara fadin"(masha Allah, Allah ya nuna mana an d'aura wannan aure na amare
da angaye, aure na farko shine tsakanin,Mubarak Siraj Manu da Nadiya Yahaya Manu, na biyu
tsakanin Khamis Yahaya Manu da Jawahir Suleiman Manu, na uku shine tsakanin Shamsudeen
Suleiman Manu da Hafsat Siraj Manu,sai na hud'u tsakanin Nouradeen Salihu Manu da Khairat
Yunus Manu, sai na biyar tsakanin Salman Yunus Manu da amaryar shi Zeinab Abdul-Hamid
Manu wato (Ummi)."

Shiru ne ya ratsa illahirin mutanen da ke wurin dan jin aure na biyar,Kallan kallo kawai a keyi
saida kowa ya tabbatar sannan aka fara farin ciki, wasu da hukuncin bai masu ba kamar zasu
fashe dan bakin ciki Hajara uwar gidan baba yahaya taso ace an had'a Salman da Rumana dan
taci buri akan auren su, Ummi da ke d'aki ta nata tsokanar su Jawahir tana masu shegantaka, yayarta SA'ADATOU da RUKAYYA yayar Jawahir suka shigo
suna Bud'a suna murna a nanfa suka fad'a masu halin da ake ciki, Ummi da tak'i yarda fitowa
tayi tsakar gida tana tambayar Mahaifiyar ta wato HAWATAN(Hawaou) kasancewar ta buzuwa
yasa ake kiranta da Hawatan, tin'da tace" eh Ummi da gaske an d'aura aurenki kema" cikin
nuna rashin yarda tace" haba la mamma ta yaya za'a d'aura aure na haka kwatsam ai ba haka
ake ma kowa ba sai ni za'a fara kai na?" hannunta ta d'ora a kafad'unta tace" kinga kiyi hak'uri
kinji wannan hukuncin kakan kune, kuma ai ba yaou zaki tare ba ke" jaye jikin ta tayi tana fad'in"

a'a la mamma hakan ba zaiyiwu ba miyasa sai yaya Salman za'a aura min"? da gudu ta koma
d'akin da amare suke ta kwanta ta fara ai kin kuka kamar ranta zai fita, k'awayenta kuma yan
uwanta sunyi ban hak'urin amma ina sun kasa dan haka suka rabu da ita.

tunda a kace Ummi na kuka hajia Babba tace a k'yaleta zata ji da ita, d'akin ta shigo ta tayar da
ita zaune saïda tasa ta daina kukan sannan ta fara magana cikin nutsuwa da dubun hankali"
Zeinab ki nutsu ki saurare ni kiji abinda zan fad'a maki kinji shaleleta"Ummi shi aure da kuke
gani darajar shi ce tasa Ubangiji ya hallata shi a tsakanin bayin'sa, darajar aure da kuke gani
tafi Karfin tinanin ki sabida daraja da matsayin shine yasa hatta bishiya zakiga an mata aure
kafin ta fara toho, sannan aure sunna ce mai k'arfi daga sunnonin Manzo ( S A W ) kuma duk
wanda ya raya ta to ha'ki'ka zai samu babban rabo, sannan aure ya nada matuk'ar mahimmanci
a rayuwar mu wanda idan da babu shi da Ummi bana jin da yanzu akwai Duniya dan bad'alar
da za ayi ba kad'an bace a Sakamakon haka kuma Allah Zai iya kifar da duniyar ma Baki d'aya"

" Ummi wani abun farin ciki anan shine duniyar nan munacin Albarkacin Annabi Muhammad (S
A W) ne sannan yara ma suna taka rawa a cikin rangwamen da Allah ya keyi mana, to yanzu
Ummi in har hakane mi zaisa ki k'i aure har ki tsaya kina bata lokacin ki wajen kuka, ke da zaki
samu wannan manyan mayan rabon, Bugu da k'ari kuma Salman dan uwanki ne kinfi kowa
sanin tsakaninki da shi, nice nan na haifi iyayen'ku maza da ke da shi to miye matsala a ciki,
nasan dai za kice sabida ba bakwa shiri ne da shi, wannan kuma mai sauki ne In har ki kayi
abinda zan fad'a maki" share Hawaye tayi tace"hajia a gaskiya ba'amin Adalci ba, ta yaya za'a
d'aura min aure da mutumin da Kusan tsakani na da shi kunsan mugu ne shi ko kad'an ba yada
tausayi" kai ta girgiza tace" kash, Ummi ina baki kina rok'o, Salman fa ba kamar yanda kika
d'auka bane kece kawai kike masa Kallan mugu shi ma kuma ke kike ja ma kan ki sabida
kinsan abinda baya so amma se kika maida wannan abu kamar 'dabi'arki duk lokacin da kika
gan shi sai kinyi" amma hajia to miyasa za'a aura min shi ni gaskiya bana san shi?" Ummi kiyi
Hak'uri kamar yanda nafad'a maki, idan har kika yi hak'uri kika bi Umarnin mu to basai na fad'a
maki ba kisan za kifi kowa jin dad'in Alhaji, amma in kika ki kika bijere tofa kinfi kowa sani
wallahi zaki shiga matsala" Ummi ke da Salman duka jikoki na ne naji dad'in wannan HAD'IN
AUREN dan ba'ataba irin Shi, ki kwantar da kanki ki zauna lafiya da dan uwanki kiyi masa
biyayya domin yanzu shine k'ofar shigar ki Aljanna, kiyi duk abinda yace in dai kina so ki
rabauta Duniya da Lahira, ki kyautata mashi idan kina so Allah ya yarda da ke ya saki a cikin
bayinsa mafifita, ki zama mace ta gari a wajan Mijinta ki zama mace mai biyayyar aure ki zama
yar Aljanna" bayanin da Hajia tayi gaba d'aya amaren sun k'aru da shi kuma sun d'auka saidai a
wajan Ummi ba haka abin yake ba.


Tunda Salman yaji sunan sa ya fito a cikin wannan résult wanda shi a wajan shi kamar an kafe
sunan yan wuta ne kuma sunan shi ya fito, rud'ewa da kid'imewa da tashin hankali ya ma rasa
wanne ne a ciki ya shiga, zai iyya zama da kowace irin yarinya a duniya daga ciki har da
karuwa amma banda Ummi dan kuwa yarinyar ta mugun raina shi hakan yasa ya tsane ta duk
da suna yan uwa kuma makotan juna yana wuni gidan su tana wuni gidan su amma hakan bai
sa suka jitu ba, Hakuri da rarrashin da Abokan shi da sauran angayen ne suka fara bashi ganin

ba zai'iya ba dan bâ abu bane mai yi yuwa yasa ya shiga motar shi ya kama gaban shi ko ya ji
Sauki a ran shi.

Yan Uwa dai bakin su suke sha babu kama hannun yaro, har lokacin da aka gama kintsa amare
izuwa gidan mazajen su, a lokacin ne Alhaji USMANE( Manu) ya tara su a Babban falon su ya
masu Nasiha mai ratsa jiki tare da gargad'in su anan Kowane ya kula da Hakkin da Allah ya
d'ora mashi akan shi na dab Abokin zaman shi, sannan ya maida akalar akan Ummi da Salman,
wanda ya kwadaitar da su akan in dai sun zauna lafiya to za suji dad'in zama da shi in kuma
aka samu akasin haka to akwai matsala.

Mahaifiyar Ummi ta nemi Alfarma wajen Alhaji akan ya amince Ummi ta zauna har nanda sati
biyu sai ta tare,amma yace sam baiga dalilin da zata zauna gida ba da aure a kanta dan haka
sati 'daya ya basu akan sun gama duk yan tsirfe tsirfen su kafin nan.


*To Allah ya kai mu ranar Tariyar nan muga mi zai faru*
27/02/2019 à 17:29 - Mamar Latif💃: 💑AUREN HA'DI💑


_Samira Harouna_


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_ ��

*Page*

1⃣1⃣-1⃣5⃣


An nufi da amare gidan mazajensu inda Ummi kuma suka tafi gidan su tare da Mahaifiyar ta,
dama gidajen suna kusa ne, suna shiga d'akin ta ta shiga ta soma wani sabon kuka har saida
bacci ya d'auke ta duk da La mamma najinta amma ta kyaleta dan yanda ta d'auki Salman bata
d'auki Ummi haka ba shiyasa bataga abin daga hankali a ciki ba.
Cikin dare Ummi ta farka ta fito falo ta bud'a frige ta d'auki madarar shanunta wanda Mahaifin ta
ya sabar mata shan ta tin tana karama yanzu haka in bata shaba har kan ta ke ciwo, tana sha
takoma d'aki tayo alwala tayi Sallah Isha'i da bata yiba ta d'auki AlQur'ani tayi karatu sannan ta
kwanta. tana tashi da safe La mamma tasa aka fara mata gyaran jiki mai zafi dan ba suda lokaci wanda
aka basu kad'an ne.

kwana uku aka kwashe har yanzu Basu had'u da Salman ba, Abba ne kad'ai ke rarrashinta da

su hajia idan suka zo gidan sai kuma Mamar Salman kin wato Hajia HALIMA, yaou kam
Mahaifiyar Salman ta tiso shi gaba akan yazo yaga matar shi ba karamin d'aci yake ji ba idan
yaji sun kira Ummi da matar shi haka ya daure ya zo gidan, tin'da tayi Sallah Magriba bata saké
fitowa ba sabida kiran da JAMAL ya mata, bud'e k'ofar da taji yasa ta saurin aje wayar tana
muzurai duk alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita, Kallan tuhuma Salman ya ke mata
har ya k'araso in da take cikin rashin yarda yace,

"mi ki keyi da wa kike waya?" wata harara ta dalla mashi tace" to ina ruwanka da ni miye
matsala ka?" hannunta ya fizgo da k'arfi ya karbi wayar ya duba number ce babu suna dan haka
yace" da wa kike waya?" cikin b'acin rai tace" a'ah Malam wai miye haka ina ruwanka da ni to?"
cikin hassala ya matse mata kumatu yana fad'in" bana ciki da iskanci kar ki d'auke ni sakarai, ni
yanzu mijinki ne dole nasan mi kike ai katawa" duk da tayi 'kok'arin fizge hannunta amma ta
kasa dole tace" aw kenan kai ka d'auka da gaske ni matar kace, to wannan kishi ne ko mi?"
sakinta yayi yace" Allah ya tsareni nayi kishi a kan ki, wallahi ke kinsani in banda darajar aure
ke baki isa ba kira ki da matar aure na ba" nunata yayi da wayar yace" daga yaou babu ke babu
waya har lokacin da naga damar ki rik'e" wucewa yayi zai fita da sauri ta sauko daga gadon ta
tare gaban shi tace" kaga Malam dan Allah bani waya ta sai kace wani kai ka siya min" nuna
mata wayar yayi yace" ki k'wata mana idan kina da k'arfi" shiru tayi tana k'are mashi kallo tasan
bazai bata ba dan haka tana ganin yasa ta cikin aljihun rigar shi sai ko tasa hannu, cabke
hannun yayi ya murd'e mata yan yatsu yana fad'in" marar kunyar banza, sai ki saka ma mutum
hannu a cikin aljihu wannan salan halin b'era kenan" duk da tana jin zafin murd'ar da yake ma
hannunta bai hana tace" b'eraye dai ai kai ne ma babban b'era gashi kamin gaba da waya" tsaki
yayi ya gitta ta ya wuce ya bar gidan.
su Abba ne zaune suna cin abinci kallan La mamma yayi yace" wai ina Ummi take ne?" tab'e
baki tayi tace" tana d'aki mana tunda ta d'ora ma kan ta larura" girgiza kai yayi yace" ki dinga
hakuri mana kema, kiyi la'akari da yanda nata auren ya kasance ba kamar na kowa ba, itace ta
farko a famille nan da aka mata aure babu saka rana bare raba goro sai ki mata uziri ko" k'ara
tab'e baki tayi tace" amma miye na damuwa a ciki Salman fa dan uwanta ne tasan shi tunda
tare suka tashi to miye saban abu a ciki?" hakane amma kuma kinfi kowa sanin tsakanin ta da
shi, ba shiri suke ba" to ai auren da aka had'a su kaga sai su fara shirin watakila ma su so
junansu nan gaba kad'an" to Allah yasa haka, idan haka ta faru ai za mufi kowa jin dad'i"
gaskiya ne Allah ya tabbatar da Alkairi, ya basu zaman lafiya" Ameen Inji Abba.

haka aka k'ara wani kwana ukun ana gobe Ummi zata tare an gama kimtsata yanda ya kamata
kama daga kunshi kitso gyaran jiki har dama gyaran d'aki, gobe ake jira tayi saidai duk abinda
Allah ya tsara zai faru to babu makawa, Ummi ce da kewa da damuwa ta mata yawa ta d'auki
wayar La mamma ta kira Jamal sabida irin soyayyar da yake mata tana jin dad'i dan shine na
farko da ta fara soyayya da shi, hira sukayi sosai har saida yace mata" kinsan wani abu a
gaskiya ina so na saké ganinki?" gabanta taji ya fad'i amma sai ta dake tace" um a gaskiya
bazai yiwuba" da sauri yace" miyasa Ummi baki san gani na ne?" cikin i'ina tace" ba haka bane
kawai dai akwai matsala ne" matsala kuma ta mi?" rasa abinda zata fad'a mashi tayi dan haka
yace" kinga Ummi zan zo gidan ku yanzu ruwan kine ki fito ko ki 'ki fitowa amma kisani idan ma
baki fitoba to ni har cikin gidan zan shiga in da na ajeki a ranar da muka fara had'uwa da ke"

kashe wayar yayi yabar Ummi baki bud'e gabanta ya tsananta fad'uwa.

Minti talatin kenan Jamal ya kira Ummi yace gashi nan K'ofar gida ta fito ko ya shigo tunda shi
da aure yake santa, cewa tayi ya jira ta a bayan gidan su tana zuwa, duk da tace mashi tana
zuwa amma ta d'auki Kusan minti sha biyar kafin ta fito ba tare da kowa yaga fitar taba, tana so
ta fad'a mashi Komai akanta da auren da aka d'aura mata dan taba shi hakuri suyi sallama.
*To Allah ya kauda b'acin rana*😞�
27/02/2019 à 17:30 - Mamar Latif💃: 💑AUREN HA'DI💑

_Samira Harouna_

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)��_


*page*

1⃣6⃣-2⃣0⃣


zaune ta same shi cikin mota k'afafun shi a waje, yana ganin ta ya fito ya rufe k'ofar bakin shi
har kunne, gaissawa sukayi a gurguje Ummi tace" am Jamal na fito ne dan na fad'a maka ko
wacece ni, muna cikin halaka Jamal" cike da mamaki yace" halaka kuma wace irin halaka
Ummi?" kanta k'asa tace" Jamal ni fa ba yanda ka d'auka b'ace, a yanzu haka ina da aure a kai
na kuma na fito dan na fad'a maka haka, Dan Allah muyi hakuri da juna kaje ka nemi wata
wacce ta fini,watakila ita ce mafi alkairi a gare ka" cikin wani irin yanayi yace" a'a Ummi dan
Allah karki min haka, wallahi ina sonki, kuma na fad'a maki Komai a game da ni kinsan koni
waye kinsan labaran soyayyata har guda hud'u, Dan Allah Ummi ki amince ki aure ni ko zaki
canza wannan labaran nawa marasa dad'in ji, idan kuma baki so na ne basai kin b'ullo min ta
wannan hanyar ba"
"A'a Jamal ba haka bane, wallahi an d'aura min aure yanzu haka gobe zan tare idan Allah ya
kai mu" haba Ummi kar ki raina min Wayo mana, ki fito ki fad'amin gaskiya kawai" cikin kossawa
tace" kaga Jamal na fad'ama gaskiya ina da aure dan Allah kar ka saké

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0