Showing 45001 words to 48000 words out of 58434 words
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITIONí ½í¶Š️
P.E.W.A
Home of perfect essential writer's together we standí ¾í´�
ESSENTIAL WRITER'Sí ½í¶Š
Pení ½í¶Š️*is migthier than the sword *í ½í·¡️
EPISODE1️⃣
PAGE32
TYPINGí ½í³²í ½í³²í ½í³²
©°••••••••••••••••••••••••••••••°©
Sallamar da akayi A dayan b'angaren ce ya amsa yana sakin murmushi,Unni yakike?ya
gida?'sunan da aj ya furtane yasanya gaban Dr.Ammar fad'uwa idanu ya tsurawa Aj dake
wayarsa da unni a tsanake cikin girmamawa cikin ladabi.A d'ayan b'angaren Unni ta tambayi Aj
ya aiki ? bayan ta amsa masa duka gaisuwarsa,Alhmdllh ta furta ya furta yana mai sake fad'in
Unni ai yanzu haka ma muna hospital d'in yau bamu tashi da wuri ba...
Ohk tau Allah yataimaka"ta furta masa,A hankali ta furta" Nur na kusa"ehh ya bata amsa
atakaice yana mai d'aga idanunsa ya kalli Dr. Ammar da ya tsuramasa idanunsa masu kaifi Ba
ko kyaftawa tunda yaji sunan Unni ya fito bakin dr aj gaban shi ke k'ara faduwa.
Unni ce ta juye harshen ta a yaren fulatanci,tana tambayarsa har yanzu Ammar yana nan kan
bakansa ne?bazai karb'i sarautar ba,fahimtar da yayi bata son Dr Ammar d'in yagane zancen
da suke yi yasanya sa shima chanja shima zuwa fulatanci,dan duk sun san Dr.Ammar baijin sa
tun suna yara akayi koya musu yaren inji kakarsu Ammie gimbiya fatima,wanda itama ga mijinta
margayi sarki Hamza ta iya sa da kuma kawar tata HAjiya,har ya" yan ta ma,shi yak'i maida
hankali ya iya ne shiyasa bai iya yaren ba.
"Amsawa unni yayi da tabbas dai kam Unni yana nan kan bakansa,Unni bata nuna komai ba
duk da amsar tasa tad'anji ba dadi ganin kafiyar yaron nata duk da tasan baizubar bane haka
mahaifinsa yake da kafiya.furta masa tayi " kyalesa kar ka k'ara masa maganar komai yazo
karshe in sha Allah.Sosai Aj yayi mamkin sosai da jin maganar da unni tayi dakuma rashin nuna
damuwa da batayi ba kamar sauran lokutta,sai dai bai tambaye ta dalili ba saboda yanajin
nauyin ya yar ta mahaifiyarsa fiye da mahaifiyartasa.Tambayar da ta masa ce ta katse tunanin
zucin nasa"•••••••••
Ranar nace ka kirani inkazama less busy Amma Aminullah shiru babu kiranka,da yake haka
take kiransa some times itada Sarki Ali ko son,shiru yayi na rashin gaskiya dan tabbas yana
sane yak'i kiran nata gudun tambayoyin nata game da Dr.Ammar d'in akan rigimarsa da
mahaifinsa,saboda kuma bayaso ya rik'a yawan yiwa Ammar maganar dan duk lokacinda ya
masa magaanar sai yaga damuwa karara akan fuskar d'an uwannasa shikuma hakanne bayaso
duk da yasan cewa yana cikin damuwar da shi kansa bazai iya boyeta ba a wasu lokuttan ba
duk da jarumtar da yakeyi,shiyasa tun ranar da suka fito meeting d'in bai kirata ba,A yanzu ma
koda yad'aga kiran yana d'ar darr ne a zuciyarsa duk da yasan unni mace ce marar daukar
zafi,sai kuma yaji akasin Abunda yake tunani,yazata yaga ta nuna damuwa ko b'acin rai ko tayi
fushi ma dasu.
A hankali ya furtama sorry unni kinsan aikin namu ne,shiyasa bansamu na kiraki ba,Murmushi
kad'ai Unni tayi dan tasan tabbas gan gan yaki kiran nata domin baison takurawa AMmar d'in
dan tana basa umurni ya tambayesa in yajanye domin ita ko takirasa shiru yake mata,DA kuma
yarika convincing nasa har yajanye ra'ayinsa duk da tassan abu ne mai wuya.Shima Aj
murmushin kad'ai yayi
dan yagane dalilin murmushin na unni akan maganarsa.
°©•••••••••••••••••••••©°
Bayan minti biyu dukkaninsu suka yi shiru,Unni ce ta takatse shirun nasu ta hanyar tambayarsa
game da mafarkin da Ammar yasabayi tun yana k'arami wanda anyi neman taimako akai Amma
ba,a dace ba kusan shekara ishirin da yan kai.
Amsa mata yayi da ehh yanayi Unni ma a wasu lokuttan kad'ai dan yasan Ammar bazai masa
karyaba in yayi saboda shak'uwar dake tsakaninsu.
labarin last mafarkinn nasa yabata wanda ya banbanta da saura duk a harshenn na fulatanci
suke maganar.
Ta B'angaren Ammar ido kad'ai ne ya zubama Aj din dan dukkanin abunda suke fad'a baya
fahimtar komai inbanda gaisuwar daga cikin yaren,kuma tabbas yaji ajikinsa duk akansa ne
suke magana sai dai bai gane kan zancenba,A hankali Ya lumshe idanunsa tare budesu
wadanda suka d'an sauya daga farin madararsu yanayin nasa kamar mai jin bacci wanda haka
kawai yake jin kasala na saukarmasa ta rashiin dalili.
'Ta B'angaren Unni ta razana sosai da jin labarin mafarkin da dr Ammar yayi,sosai hankalinta
yatashi,Kwantar mata hankali Aj Yayi yana furta "unni karki manta fa ba duka mafarki yake
zama gaskiya ba agaremu, Annabin mu muhammad saw shine kad'ai wanda yakeyin mafarki
kuma ya tabbata dan haka karkisa damuwa dan sun furta zasu dawo kansa bashi ke nuna ko
suwaye zasuyi nasara akansa ba Unni kawai kisanya duka wannan mafarkin nasa amizaninb
sharrin shaid'an (la'anannen Allah) ba abunda zai iya zama gaske ba,sannann UNNI Addu'o'in
ku natare damu mezaisa ki razana,ayanzu ya mayarda maganar sa da hausa inda duk maganar
da sukeyi yanaji rad'am akunnensa.
Ajiyar zuciya Unni ta sauke abangaren ta cikin jin dadin furucin na dr aj wanda yasanyata jin
sanyi aranta. wanda akullum take k'ara jin sa kamar ma ita ta sunb'ulosa duniya saboda kusan
halinsu guda da aj a tabangaren iya sarrafa zance na fahimta da nutsuwa, Ahankali ta furta
hakane son muna kai kam addu,a kuma kudage da Addu,a kaji,kai yad'aga mata inda takara
furta Allah ya muku Albarka yakare gabanku da bayanku,Ameeen ya amsa mata cikin jin dadi
har tamasa sallama Aj yamaza yatare ta daga shirin yanke kiran Unni pls karki sanarwa da
kowa harda Abbah,in sha Allah ta furta suna yanke kiran.
Ajiyar zuciya kad'ai yake saukewa a jere cikin kara lumshe idanunsa kansa ya dafe jin yana
juyamasa kad'an,A hankali ya bud'esu tar yakoma a mazauninsa daga d'an tsayen da yake tun
dazu wanda su bakomai bane agaresu yin irin wannna tsayin saboda yanayin aikinsu na likitota.
Idanunnsa yak'ara lumshewa dasuka k'ara yin d'an jaaa na damuwa
Mafarkin nasa ne yadawo masa akai bayan zaman nasa wanda maganar da yaji aj nayi ce
tak'ara dawo masa dashi sabo duk da yana ransa ne har yanzu baisan meyasa yake jin kashe
yarinyar da akayi a mafarkin nasa ba yake jinsa har cikin ransa idan ya tuna da sun kashe masa
ita jiyake kamar ya yi ta yin kukan da babu mai iya rarrashinsa,tambayar kansa yayi wai
dagaske ne kwa?sun kashe masa dream girl d'insa,kansa ya girgiza da karfi yana furta nooo
baki mutu ba Cikin d'aga murya irin tsawa d'in nan ta rashin tabbas Kan abu....
©°••••••••••••••••••••••••••••••°©
Ikon Allah kad'ai Aj ke kallo dan Shi Al amarin Ammar nabashi mamaki anya kuwa ba aljana ce
ta Auresa ba ko ta shiga jikinsa take zomasa a mafarki kamar yadda su unni suka zata abaya
sai dai duk iya binciken da manyan malammai sukayi masa ta hanyar yimasa rak'iya babu
alamar hakan atare dashi. Kuma yanaji ajikinsa kamar ma soyayya yakeyi da aljanar ko sonta yakeyi .Dan tabbas Alamu
ya fara nuna son yarinyar yakeyi inma ba soyayya sukeyi din ba,domin ba tun yauba yana
ganin wasu alamu agaresa duk da bai tabbatar ba.
Kallon Ammar yakeyi kallo na tausayi da mamaki,ganin kallon da yakemasa shima bayan bud'e
idanun nasa da ke
a lumshe jin yayi sub'util kalam,yasan kallo ne yake masa na tuhuma duk da yafi hango
tausayin sa acikin idanun na d'an uwansa,maganar da ke zuciyarsa ta fito fili yasan cewa sai Aj
ya tuhumesa shikuma hakanne bayaso,kauda kansa gefe yayi daga kallon da sukeyi wa juna
shida aj d'in yana mai tsuke d'an karamin bakinsa kar Dr .aj yaga damar sa har iya yimasa wata
magana kan zancen.
Dr.Aj k'aramar dariya yayi duk da ya fahimci Ammar d'in sai yayi kamar bai gane nufinsa ba,A
hankali Aj yadan duk'o da kansa yana mai furta masa anya kuwa ba son wannan aljanar kakeyi
ba domin Kuwa nikam nafi tunanin ALJANA CE (oum Amjad) yakai k'arshen maganar tasa
yana sakin karamar dariya,Dasauri Ammar yad'ago Dara Daran idanunsa yana sakarwa Aj wani
irin kallo da idanunsa da suka kara girma kallo ne wanda sai da Aj yaja baya,shima yana kallon
Ammar d'in da mamaki take zuciyarsa ta kara tabbatarwa da aljanace Ammar din yake tare da
ita.
Ran Ammar ya b'ace sosai matuka wanda har sai da labbansa suka kara yin jan wahala na
taunar da suka sha sanadin bacin ran da yasame sa na furucin Aj,Huci yake fitar wa mai zafi
wanda shikansa aj sai da yayi danasanin maganar yakara yadda tabbas aljanace ke tare da
Ammar d'in shiyasa yake wulakanta ire irensu dr malini.
Bayan kamar minti shida yafara sauka daga fushinsa A hankali ya bud'e bakinsa da kyar kamar
wanda bayason yin maganar ya furtawa aj "yanzu nizaka had'a da aljannu halittar da muke
neman tsari daga gareta,kuma wannnan baiwar Allahn itace Aljanar dude harararsa yayi yana
furta kuma ni ba sonta nakeyi ba kawai dai inajin badadi ne sannan ita ba aljana bace then
karka kara kiranta da aljana pls mutunce itama kamar kai inada yakinin tabbas mutunce duk da
bansan sunantaba har yanzu bansan a ina take ba.
Kallonsa kawai Aj keyi baki asake,Addu,a kad'ai yayi aransa Allah yabawa Ammar lafiya,domin
shi gani yake wannan Abu bana hankali bane.
Aiko insunje Nigeria zai sanarwa su Unni aljannu nan kamar ya kamata kara dubashi
agani,anema masa magani kar abun yak'arayin girma ganin irin bacin ran da Ammar ya shiga
kan furucinsa.kai kawai yak'ara kad'awa yana mai furta ohk!nagane,Amma fa dude kabani tsoro
wannnan fushi haka daga kawai na furta Al......Dr Ammar murmushin da baiyi niyyar fitomasa
ba yasaki jin aj yayi furucin Aljanna yakasa idasawa kenan bazai k'ara furta masa hakan ba,har
ransa yaji dad'i yadda d'an uwan nasa yake gudun b'acin ransa tun kuwa suna kanana.
Aj wanda yayi shiru jin zai kara sub'util kalami ya furta baki yabawa Ammar hakuri sannann ya
kara furta"nasan kaji wayar damukayi da Unni har naroketa karta sanarwa da sarki gudun
fad'awa tashin hankalinsa"kallonsa kawai Dr Ammar keyi bece dashi komai ba.
Dr aj samun kansa kawai yayi shima dayin murmushi,ganin yadda yake ta kallonsa kamar wata
sabuwar halitta.
Hadadden Rolex din dake daure akan tsintsiyar yakalla ganin lokacin sallar azahar yagabato
yasanyasa mikewa dukkanninsu suka dauro alwallah suna dan gabatar da sallar alokacin ta.
*NIGERIA*
*ZAMFARA GUSAU*
Uwar ranar da ake kwatsawa ce ta ruwa tasanya dukkanin wani mai abun nawa yake gaggawa
ya is a gida don ganin hadarin da had'u lokaci d'aya gudun shan kashin ruwa musamman masu
babura.
Baba Adee ne ke ta k'ok'arin barin babban fuel station na nnpc bayan yasha man da zai kaisa
garinsu Bungud'u,mashin d'insa ne d'ai daga cikin dankara dankaran motocin dake shigowa a
gidan man ne,ya buge mashin d'in na Baba Adee sanadin shigar da sukayi ba dai dai ba.
Fadawan dake cikin motar ne suka fito dasauri suka rik'a masa mashin d'in nasa suna masa
sannu tare da duba lafiyar mashin d'in NASA dan tabbatar lafiyar sa suna kara basa hakuri kan
d'an karamin had'arin da ya auku sanadinsu,shiko yana furta musu bakomai cikin dattako.
A lokacin ne kyakkyawan dattijon dake cikin motar da duk tafi daukar hankali tafi sauran kyau
kirar range rover fara tass new design yasauke glass a hankali dan son yin magana da Wanda
accident din ya so faruwa kansa dan yabashi taimako a lokaci nne shikuma Baba Adee ya juyo
A hankali daniyar duba bayansa yadda zai fita batare da ya buge wani ba da mashin d'in sa sai
yayi dai dai da d'ago kan maimartaba sarki Aliyu Murai da ya sauke glass d'insa gabansa ne
yayi mummunar fad'uwa ganin Wanda yahad'a ido dashi sak k'anensa Abdul rashid,sai dai d'an
yanayin manyan taka dake tare dashi bakamar lokacin da yana saurayi ba. Wanda har yau
basu San meyafaru dashi ba,sai dai kawai anwayi gari da rashinsa anyi nemansa ba,agansa
ba.
Sarki Ali kuwa ido yasakar masa ganin bai nuna alamar cewa yagane saba,sai abun yabashi
mamaki da alajabi Wanda har yasanya sa tunanin anya shine kuwa shine,kodai bashi bane mai
kama dashi ne ,har Baba Adee yayi wucewarsa baisani ba da d'aya daga cikin fadawansa ya
furta Allah yataimake sarki shin ko kasan wannan bawan Allah ne sai dai kuma gashi har ya
wuce ai,sai lokacin ne hankalinsa yadawo kansa cikin tashi hankali bafaden ne cikin rashin
hango tashin hankalinda sarki Ali yashiga ya furta Allah ya taimake ka har ma kama kuke dashi
fa,Amma sai dai shi farar Fata ne duk da zafin ranar da ya d'an k'onasa a na hango farinsa....
Ganin samu da rashin da yake shirin yi alokaci d'aya duk da baya da tabbacin cewa shi din
ne,Umurni yabawa d'ai daga cikin fadawansa cikin gaggawa da subi mutumin daya fita yanzu
Wanda suka buge wa mashin,dasauri suka ja motar d'aya suka bisa.
A MAFARKI NASANTA
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
Fa'eeh BG
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai
------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITIONí ½í¶Š️*
*P.E.W.A*
*Home of perfect essential writer's together we standí ¾í´�*
*ESSENTIAL WRITER'Sí ½í¶Š*
*Pení ½í¶Š️*is migthier than the sword *í ½í·¡️*
*Free*
EPISODE1️⃣
PAGE33
TYPINGí ½í³²í ½í³²í ½í³²
°©•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••°©
Fitowa motocin sukayi daga gidan man suka parker a gefe gwanin burgewa dama mota biyar ce
d'aya tabi mashin d'in Baba Adee,Bayan kamar mintuna goma sai gasu sundawo,sunyi rashin
sa,ar ganinsa,sarki Ali Bayan dawowarsu da wannnan mummunan labari labari hankalinsa
yak'ara tashi sosai sun sanar masa wata mota ce ta tsaya ta shiga gabansu kuma sai ta
lalace,....maimaraba sarki Ali baice musu komai ba face umurtarsu dayin reverse sukama
hanyar Gida ( fada).
Abunda yafaru Alokacin da Baba Adee yake tafiyar sa hankali cikin rashin kwanciyar hankali
ganin hadarin da ya had'u yana so ya isa gida lafiya batare da yasha kashin ruwa ba... sai dai
kuma baima lura da motar da ke bibiyarsa Abaya ba, kuma Alokacin da suka bi bayansa kad'an
saboda d'an cunkosan da akasamu sai dai suna hangosa kad'an yana tafiyarsa akan babur
d'in kasancewar sa bama gudu da abun hawa bane,wata katuwar mota ce jif bak'a wulik mai
tinted glass tashiga gaban motar fadawan atsiyace,wanda dukkaninsu sai da suka razana
yadda motar ta kutso agabansu bayan barin guraren da cunkuso yake,abun haushi kuma
wanda ke cikin motar ne yak'i fitowa duk da jin k'arar horn d'in da fadawan ke ta sakar masa,d'ai
daga cikin fadawan ya fito cikin yanayin masifa yana kwankwasa gilas d'in motar,A hankali
glass din motar yake zugewa izuwa k'asa wata matashiyar kyakkyawar budurwa ce da taji
bleaching ta bayyana a driver seat d'in wanda da alama ita kad'ai ce acikin motar yanayin ta
kamar arazane Amma bai hana ta taunar cingum d'inta ba.
'Magana bafaden yayi cikin nuna bacin ransa"meyasa zaki tare muna hanya kinsan aikin da ke
gaban mu ne,Alamun kuka ta fara cikin kissa tana furta masa motar ce fa ta kucce mata kuma
she try to control it but takasa sannan ta daura da basa hakuri,sannann kuma yanzu taki tashi
ma,Cikin d'an yanayin gamsuwa bafaden ya furta bakomai yan mata amma akara kulawa da irin
gudun sa za'ayi domin mafi yawancin haka mota ta kufcewa mutun to ta iya yuyuwa mugun
gudu yakeyi da ita ko kuma d'an koyo ne,kai ta d'aga masa cikin kara yimasa godiya,tana mai
kara gwada tada motar da farko bata tashi ba na biyu ma sai a na uku ta tashi cikin murna
tad'ago tana ma bafaden murmushi da yabata umurnin ta tada motar akaro na biyu taga ko
zata tashi,Hannu tad'aga masa cikin sakin fuska sannan ta fisgi motar tana yin gaba
abunta,suma fadawan da basu fahimci komai ba suka juya ganin tabbasa Baba Adee ya kubce
masa basu ga ko ku'rar sa ba Yasa suka koma gurin sarki domin isarda sako...
©°•••••••••••••••••••••••••••••••°©
Gudu motar tayi kamar na barin Duniya sai gata a wani tangamemen gida,Bayan wangale mata
k'aton gate d'in inda ta shiga aguje suna parker motar a inda yadace maimakon mace ta fito sai
wani saurayi ne yafito a driver seat din wanda daga ninsa dai kaga d'an hau,dariya kad'ai yake
tik'a yana furta ashe dai lawisa zaki iya sana'ar film wannan acting haka kinga yadda kikayi
kuwa wallahi kad'an yarage dariya ta tafito fili a bayan nan da nake kwance. budurwar da naji
ankira lawisa ce ta fito a extra seat itama tana ta tik'ar dariya harda rik'e ciki ashe ma itace
budurwar da tashiga gaban motar fadawan sarki...
FA'EEH BG
FIRST LADY
"Muryar tace take tashi tana furta kace kaso katona mana asiri jimmy sugane da gan gan muka
shiga gabansu takai k'arshen maganar tana dariya,tak'ara furta jimmy Amma fa nima naso in
d'an kwafsa dan namance kwata kwata inbar taunar cingum dinan tana mai kara yin wani k'aton
kwai da cingum d'in,dasauri saurayin da aka kira jimmy ya furta wallahi kuwa taunar cingum d'in
nan naki yaso yabadamu dan naga kamar bafaden nan yana miki wani kallo duk da nasan bai
fahimci komai ba,dariya tayi tana furta