Showing 15001 words to 18000 words out of 58434 words
sun hango gate man yana
kokarin rufe k'ofa.....
Suna isowa bakin d'in suka dakata,d'aya daga cikin su ne ya furta sir bude muna gate d'in
,saboda dukansu ya girme su,shiyasa aka bashi tsaron gate...
A hankali wannan tsohon gate man din ya mayar musu da amsa cikin yaren india domin shi
baya jin turanci,ya furta Dr.yace kar wanda yabisa,jin wannnan magana tasa ta tayar musu da
Hankali,shi bai ma san yadda abun yake ba sai da suka sanar dashi,an aiki enuch da mota
yakaiwa Dr.Aj amma har yanzu bai je ba,kuma meeting din na gaggawa zaije....
Dan danan hankalin sa yatashi,dan dukkansu sun san muhimmancin wannan meeting da
uwayen gidansu zasuje,saboda meeting ne daya tara manyan likitoci na kasashe daban
daban,gashi d'ayansu bai je ba tun da in d'aya yaje a wani lokacin ya isar sai d'aya yayi
attending a system live ta hanyar comference call da ake hadawa ga wayenda basu samu
damar halarta ba..
Jimami suke atsakaninsu,d'aya daga cikin sune yayi k'arfin halin furta guys muna cikin matsala
idan wani yasamu Dr.bazamuji dad'i ba domin munyi ma gwamnati rantsuwar karemata
su,kuma munyi rantsuwa ga abun bauta shiva,dan haka dole mu daure hakan nan mubisa duk
da yayi warning namu ......Ga ra nasa fushin da wanda lord shiva zai yi damu
......Kunsan indiyawa da rikon Addini.....
Allah yakyauta,yakara tsare muna imanin muí ½í¹�
Bayan sunyi na,am da maganar ta dan uwansu sai suka nemi gate man da ya bud'e musu gate
din wanda shima yayi na,am da shawarar tasu duk da shi musulmi ne,duk da kuma ta wani
gefen yana jin shakku,wanda suma sauran duk hakance azukatansu.....
......nima dai anan alkalamina yakara k'aimi wajen dauko muku rahoto.....Ku cigaba da
bibiyata.......
Fa'eeh Bg
Ficewa sukayi atsare cikin gidan a cikin manyan2 motocinsu kirar hillux da wasu daga cikin
normal car nasu bakake wulik,bayan wangale musu gate d'in da yayi..
*************************
Suna fita ya rufe gate din yana jimamin Abinda zai biyo baya.
A bangaren Dr.Ammar kuwa bayan fitar sa bai zarce ko ina ba sai inda Dr aj sukayi parking na
motocinsu,Domin gudu ne yayi ba d'an kad'an ba, ta hanyar amfani da Gps tracking ya isa inda
suke, A hankali ya tunkari motar da Aj yake ciki duk da yaji gaisuwar da yaran suke masa
amma ba wanda ya tankama,Dr aj dake cikin mota har sakon zuwan Dr.Ammar ya iso masa ta
hanyar Babban yaronsa dake gefen motar atsaye....
A hankali yaron Dr aj dake atsaye kusada murfi motar ya bu'de masa murfin bayan motar ,mai
makon ya shiga sai yayi tsaye yana k'arewa cikin motar kallo,Bayan kamar minti biyu yasanya
yasanya k'afarsa d'aya a hankali ya zauna yana mai k'ara tamke kyakkyawar fuskarsa,A hankali
itama dayar leg dinshi ya janyeta zuwa cikin motar kamar wanda ankayiwa dole shiga,shiko
Dr.Aj duk da yasan da zuwansa kuma yaga shigowarsa bai nuna masa ba yamai da hankalinsa
kan meeting d'in da yake kallo live a yar madaidaiciyar tvn dake makale akujerar driver,wanda
ake gudanarwa ahadadden hall na garin mumbai mai suna......
( MUMBAI EXPENSIVE HALL )
wanda shine Babban hall wanda gwamnatin india ta zube mak'uddan kudade gurin
ginshi,wanda yaji kayan more rayuwa ta ko ina....
Shima Dr.Ammar baice masa uffan ba kawai yayi joining meeting din ta hanyar kunna tvn dake
bayan kujerar dake gabansa tare da makala bluthood a kunnen sa kamar yadda aj din
yayi,cigaba da kallon yadda meeting d'in ke gudana sukayi,Bayan yayi joining duk wanda ke
gurin yaga Dr ammar A hankali sukayi ta daga masa hannu alamar gaisuwa shima yana d'aga
musu .....Bayan sungama gaisawa suka ci gaba da gudanar da meeting din su kamar yadda
suka fara banbancin kawai dr.Ammar ayanzu yana musu yan gyare gyare ne,ko yayi solving
wani issue tunda duk suna ganinsa ..
Dr.Aj ba abunda yake face murmushi da alhinin halayen dan uwan nasa baiyi zaton zaiyi joining
meeting ba haka,ganin rigimar da suka sha tashi bazai je ba sai dai shi yaje ya wakilcesu,haka
dai suka gama gudanar da meeting din atsanake har suka kai matsaya sukayi conclusion suka
watse,sukuma suka kashe tvn....
Enucch ne yak'araso jiki asanyaye bayan ganin motar ta uban gidan nasa,Parkeyn yayi
agefe,ya gaiggaisa da "yan uwansa,tsaye yayi gefen da ogan nasa yake,Bayan tsayuwar da
minti biyar sai ga sauran bodyguard din sun iso gurin ta yin amfani da location,duk suka firfito
daga cikin motocin su a hargitse......
A bangaren su Dr aj kuwa bayan gama meeting din su,shiru ne yabiyo baya,Dr aj yakatse
shirun nasu ta hanyar furtawa Dr ammar wanda ke jingine da sit dinsa idanunsa alumshe,cikin
murmushi "meya ka woka nan"shiru yayi masa duk da yana jin sa,"fitar mun amota"
wannan furuci na Dr aj ne yasanya sa a hankali ware manyan idanunsa masu cike da kwarjini
da haske ga kwayar idonsa maroon mai shining,Kafe aj yayi dasu wanda har sai da Dr aj
yakara ja baya yana furta lafiya?
Shiko uban gayyar murmushi ne ya wanzu akan kyakkyawr fuskar sa,yana ficewa daga cikin
motar koda yafito enucch ya fara cin karo bawan Allah yana ta kame kame am yallab'ai sir kayi
hakuri wallahi namanta wayana a gida kuma ina tsoron komawa gida bayan nayi nisa karkaga
kamar namaka rainin wayau ko yanzu ma su joshu ne nakira da karamin wayana suka min
kwatancen gurin (dai daga cikin yaran aj).......
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Duk wannnan maganar yanayinta da indiancine saboda shina bai jin turanci,kuma duk abunda
yake fadi dr ammar najinsa sai dai bai ce masa komaiba har ya isa inda ya parka motarsa
yaren sa dake gurin duk suka taso da hannu ya dakatar dasu yana shigewar sa motarsa ......
Reverse yayi yabata wuta sai kan titi tare da shara raara gudunsa,shima dr aj umurnin ya bawa
yaransa wanda cikin minti daya suka bar wurin har yaran dr ammar din....
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Alkalamin Fa'eeh Bg mai kaifi ne kamar wuk'a,kucigaba da bibiyata dan jin karshen wannan
labari mai cike da abun tausayi,soyayya,cin amana,ta,addanci duk acikin littafin amafarki
nasanta....Nasan wasu zasuce ai haryanzu ba,a fara nuna mafarkin bato karku damu kudai
sanya hakuri duk zamu kai chan .......
Dan Allah kurka comment domin shine kwarin gwiwarmu akoda yausheí ½í¹�
A MAFARKI NASANTA
in my dream i know her
By
Pha'eezah Almstapha
Daga Alkalamin ����
Fa'eeh Bg
Dedicated to my lovely sis laila Almustapha Murai
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
P.E.W.A
Home of perfect essential writer's together we stand í ¾í´�
ESSENTIAL WRITER'Sí ½í¶Šï¸�*
pení ½í¶Šï¸� is mightier than the swordí ½í·¡ï¸�*
EPISODE1�⃣
FREE PAGE1�⃣3�⃣&1�⃣4�⃣
TYPING í ½í³²í ½í³²í ½í³²
---------------------------------------------------------------
Lokacin da Dr.ammar yatashi motar Sa har ya hau kan titi duk akan idon Dr aj murmushi kad'ai
yayi yana girgiza kansa....
A b'angaren Dr .ammar kuwa yana kawowa bakin gate d'in gidan ya dannan horn sai ga k'aton
gate din yana wangalewa,Wanda dama gate man din yana kusa da controller din gate din ya
bude masa.
Yasanya hancin motar cikin katafaren gidan nasu yana dosar parking space,bayan yayi parking
dinta a inda yadace
Ya fito da had'addiyar kafar sa mai sanye da wasu rufaffun takalma boot masu kyau milk colour
sannan a ahankali yasanyo dayar waje tare da gangar jikinsa,mik'a yayi sai kuma a hankali
yafara takawa bayan rufe motar tahanyar danna key din dake hannunsa,katon falon nasu ya
nufa zama yayi daya daga cikin cusion dake d'akin yana sauke nannauyiyar ajiyar zuciya,sai
kuma ahankali ya lumshe idanunsa....
Motocin su Dr.Aj ne suka shararo harabar gidan bayan bude musu gate da akayi,A hankali
suke diddirowa daga motocinsu,wanda shima dr aj yafito daga motar tasa bayan bude mishi
kofar da bodyguard dinsa yayi.
Kofar shiga falon yadosa,sukuma sauran yaran suka gyara parking nasu...Sallamar da yayi ce
tadawo dr ammar tunanin zucin daya kasance masa dole akullum inyayi mafarkin nan nasa to
duk yinin ranar zai kasance acikin tunanin sa ne,badai natsuwar zuciya,
A hankali ya bud'e manyan idanunsa da suka dan fara sauyawa na damuwa,ya dora su akan,Dr
al amin aj,dake gefen sa wanda har yazauna ma,A hankali kuma yadauke idanunsa kan aj din
wanda shima kallonsa nasa yake yi dan ya fahimci kamar akwai damuwa a fuskar dan uwan
nasa.......
A hankali dr.Aj yafurta masa meye matsalar dude,shirun daya masa shi yakara tabbatar masa
da zarginsa na cewa tunanin dake kezo masa arai bazasu wuce mafarkinsa ba da kuma
mahaifinsa, sai mahaifiyar wadda ke yawan yin fushi dashi akan sarautar da baida ra,ayi
kanta... Bayan ya k'ara k'are masa kallo sai kuma yadafashi ahankali yana furta calm down man
anything will be fine ohk!yakai karshen maganar cikin tausayin dan uwan nasa....
-----------------------------------------------------------
A hankali kuwa Dr.Ammar yaware manyan idanunsa kan dr aj sannan yacire hannunsa da ke
kan kafadarsa ya mik'e a hankali ya doshi upstair har yafara taka step na daya na biyu sai ya
juyo a hankali yadan kalli aj dake zaune kan rugs yana kallonsa,A hankali kamar bai son yin
maganar irin an masa dole cikin zazzakar muryar sa mai yanayin natsuwa ya furta wa dr aj
thanks,wanda koshi dan saboda hankalin sa nagaresa ne da bazai ji abunda ya furta ba da iya
labbansa ....
Yana gama maganar ya cigaba da tafiyarsa,shiko dr aj murmushi kad'ai yayi yana girgiza
kansa,dan hangosa da yayi ya lakaci tsinin hancin wanda alamace dake nuna yana cikin yanayi
mai dad'i,Shigar sa haddadden falon nasa wanda yake ko ina tsaf ank'ara gyarashi bayan
fitarshi,takalmin sa ya fara cire da safarsa bayan yazauna akan rugs dake dakin masu taushi
bayan kamar minti biyar ya bude idanunsa dake alumshe bayansa najingine da kujerar ya mike
ahankali ya wuce yashige had'adden bedroom nasa,yana maida takalimin a inda suke,Kayan
jikin sa ya fara cirewa a hankali komai yana yinsa atsare kamar wata mace yana gamawa
yajawo d'ai daga cikin towel nashi dake cikin sip sabbin kal yad'aura nan take hadaddiyar surar
shi takara bayyanar da kanta ga lallausar cholcolate skin din sa sai kyalli takeyi....
Toilet yayi shigewar sa cikin takun kasaita,kansa yasakarwa shower ruwan masu dan dimi suna
dukan sa atsaye idanunsa alumshe,bayan ruwan sun duke sa sosai sai yadannan wani abu
take shower din yatsaya,kan hadadden katon bahon wankansa na kwalba wanda kana iya
hango na waje daga ciki amma shi bazai iya ganin ka ba,yashige bayan ya cire towel nasa
yajefa shi a cikin haddaden washing machine na cikin toilet din..
ya dade acikin bahon wanka inda yayi nutse,sannna ya dauro wanka sa da turarrukansa da
shower gel mai kamshi,a natse yafito yana takawa in da jerin towel din sa suke da
bathrobe,wata farar batherobe yajawo fara kar gwanin burgewa domin shi Allah yamishi son
farar kala shiyasa zaka mafi yawan komai nasa farine,bayan yasanya ta ne yajawo dai daga
cikin kananan towel dake wurin ya daura akansa bayan yagoge kansa dashi,kansa yake karewa
kallo amadubi dake cikin toilet din....
Ficewa yayi ahankali cikin toilet din bayan yagama tsayuwar sa abakin mirror din yana karema
kansa kallo...
Stool din dake gaban kamfacecen madubinsa dake shake da kayan gyara jere gwanin
burgewa...
Cigaba da goge gashin kansa yayi mai taushi da walkiya,bayan yazauna,bayan kamar minti uku
ya goge gashin kan nasa da sauran danshin ruwan dake jikinsa,yafara murza mansa na fata
mai sanyayyen kamshi kamar turare lungu da sako haka yake murza man nasa akan fatar
sa,bayan yagama neyajawo hair cream nasa mai kyau mai kara ma gashin sa sheki ya murzasa
tare da taje sa,dan danan kyawon sa yakara bayyana sumar kansa sai sheki takeyi,lipsbalm
din sa yashafa akan kyakkyawan labban sa pink colour masu laushi,turarukkansa ya fesa tunda
kan body spray oud masu kamshi,kala kala wanada akalla zasu kai guda biyar,kan sipdinsa
yakoma inda yadan thumprint take kuwa sipdin ya shiga bude kansa,sashen da yake na under
wears da short trouser yamatsa,jawo dai daga cikin short trousers din yayi sky blue color da
short fari da kuma best fara sai yakoma sashen armless yazaro mai layin blue ajikin yana
gamawa yadanna abun rufewa take ta rufe ruf,cikin natsuwa yafara shirinsa.
Fa'eeh Bg
A b'angaren dr. aj shima bayan wucewar dr ammar ya wuce shi dake kusa da na Ammar din
daga gefen damar shi dakin yaji komai na more rayuwa,banbancin dakin shine cusion shi nashi
maroon color ne dan shi kalar na matukar burgesa da fari kamar dr ammar din.....
-----------------------------------------------------------------
* Nikam ban ga laifin ku ba domin farar kala tayi,ko mala'ku kagani masu farin kaya tokai
kawuce wurin,a kabarin mu ma sune suturar mu domin sune suturar mu takarshe a
duniya,Annabi muhammad s a w farin kaya yake sakawa duk ranar idi,haka ma ranar juma,a
wannan yana dai daga cikin sunnoninsa...Allah yasa mudace yasa muyi kyakkyawan
karshe,Yasa da mu da mala'kun rahamaí ½í¹�í ½í¹�*
------------------------------------------------------------------
shima dai yashityawr sa tsaf cikin irin kayan dr ammar.
A hankali yake taka step step din da wayar sa a hannusa dayan hannun kuma acikin aljihun
wandonsa yana tafiya dai dai cikin izza daga yanayin tafiyar kasan ta zaratan maza ce wadanda
suka da mulki iko...
Kamshin turarensa ne yasanya dr aj dagowa daga kan wayar sa dayake kan preesing,wanda ke
zaune akan dining table wanda shima bai dade da fitowa ba....
A hankali yatako izuwa kan dining har ya iso inda aj yake,cikin sanyin murya ta gwarazan maza
ya furtawa aj lafiya?yana mai jan kujerar dake facing dr aj,ganin ya tsare sa da idanu,zama yayi
yana ajiye wayar tasa agefensa.
Murmushi kawai dr aj yayi yana furta dude dole dr malini ta zauce wannan madarar kyau
haka,ya k'une kyakkyawar fuskar sa yayi jin furucin dr aj din yana sakin karamar tsuka wadda aj
kadai yajita shida yake kusa dashi " mts",murmushi kawai aj yayi yana aje wayar tasa agefe...
kukunsu ne sajid khan yakaraso yana fadin afternoon sir yana mai kokarin yin serve na dr
ammar,dakatar dashi yayi,da hannu,sai kuma ahankali yajawo dai daga cikin haddadun filet din
dake kan dining din yafara saving kanshi,farar shimkafa da miyar da taji na man sa yadiba
sannan yajawo wani filet din ya debi hadadden farfesun kaji wanda yaji hadi sai tashin kamshi
yake yi.
A hankali cin abincinsa dan shi kam ingurin ci ne bai wasa da cikin...
Aj dayake ganin duk abunda ke faruwa murmusawa kadai yayi dan dama yasan abunda zai faru
kenan,kusan kullum haka suke shida sajidkhan indai yazo zai zuba masa abinci cewa yakeyi
baiso duk da zaman kukun nasu musulmi,dan shi mutun ne mai bakar tsandar tsiya,ansha
chanja musu masu dafa abinci saboda shi,sai akan wannan ne haryanzu baiyi complain ba,shi
abun ma dariya yake basa da haushi mutun ya girka abinci amma kace baka son yayi serve
naka saboda bak'ar rigima,kara girgiza kansa yayi yana cigaba da cin abincinsa da sajidkhan ya
zuba masa....
Motsin chokulla kadai ke tashi a falon sai karar ac,dr aj ne yayi ma kukun alama da ya wuce
kawai,a hankali ya dago kansa ya kallesu duk su biyun cikin second guda yamayar da kansa
kasa yacigaba da cin abincinsa.....
Bayan wucewar sajidkhan kitchen suka cigaba da cin abincinsu hankali kwance.
Karar shigowar sako ne a wayan dr ammar yasaka dr aj dago kansa yakallesa,a lokacin shima
yadagi nasa,ido daya dr aj yakashe masa yana sakin kayataccen murmushi dan tabbas yasan
sak'on wayene yashigo wayar ammar din,shikam dr ammar duk da yaga abunda Aj din yamasa
bai nuna ba sai ma cigaba da cin abincinsa da yayi hankali kwance yana mai kara tamke fuskar
sa.
Aj yana gama cin abincinsa ya mike tare da daukar wayar yana barin kan dining table din
...............................
A hankli dr ammar shima ya mike yabar kan dining a hankali fuskar nan a tamke,a falo shima
yazauna kan 3 sitter wanda shikuma aj yana kan 2sitter yana pressing phonedinsa.
kyawawan kafafunsa ya mike yana mai daura hadadden throwpillow akan dan shafafen cikin
sa,har yakwanta kuma meya tuna sai ya mike zaune yana jawo wayarsa dake gefen
kafens,thumprint yadanna wanda take takawo haske har yayi niyyar ya wuce sakon da yaga
anturo da private number ,sai kuma yaji yana kwad'ayin bud'esa,abunda yaci karo dashi ne
ybasa mamaki dan shi baiji alamar shigowar sakon ba dan yaga sako biyu ne suka bayyana na
biyunne wanda yaji shigowar sa shine na dr malini nafarkon baiji shigowar sa ba,ya karanta
sakon ya fi akirga har private number din yake karantawa,inda na leka kan wayar dan ganin
abunda aka basa mamaki dan shi baiji alamar shigowar sakon ba dan yaga sako biyu ne suka
bayyana na biyun ne wanda yaji shigowar sa shine na dr. malini na farkon baiji shigowar sa
ba,ya karanta sakon ya fi akirga har private number din Da yabayyana yake karantawa,inda na
lek'a kan wayar dan ganin abunda sakon ya k'unsa nan naci karo da rubutu kamar haka da
manyan haruffa da yaren mu na hausa "¿KA NEMI YAR UWARKA TANA RAYE¿?" ..............Tambayar kansa yake yi waya turo sak'on ?…ba amsa ¿
Nima dai kaina yad'aure kowa cece wannan yar uwartasa oho?kuma a waya turo sak'on
????????nima dai ana n alkalamina ya fadi......,kucigaba da bibiyar akalamin���� Fa'eeh
Bgdomin warware muku duk wani abun da yashige muku duhu acikin littafin a mafarki
nasanta........... Kuyi hakuri da rashin samun update jiya hakan yazo sanadiyyar rashin chaji da banida.......
Shiyasa ma na had'a muku page biyu..
Comment kadai nake bukata ko like
Sannan plskutayani sharingí ½í¹�
inayin ku í ½í²¯ percent a mafarki nasanta fansí ½í²‹í ½í²‹ over Allah yabark kauna