Showing 3001 words to 6000 words out of 58434 words

Chapter 2 - A Mafarki Na santa By Faeeh First Lady

25 Jun 2026

451

WRITER'S ASSOCIATION
�P.E.W.A�
Home of perfect Writer's together we stand�


ESSENTIAL WRITER'S� 🖊�*
pen 🖊� is migthier than the sword🗡�*

EPISODE 1�⃣
FREE PAGE4�⃣

Typing📲📲📲

Bata ce musu kala ba har suka shige dakin tsaki taja mtssw tana furta yarinya sai kace mayya
da shegen taurin ran tsiya ace duk wahalar da nake gana mata bata sanya ta guduwa daga
gidan nan ba mtssw takara jan wani tsakin tana furta mayya kawai tun randa tazo gidan nan
Baban Hadiza samun shi ya ragu gashi komai shi shalelensa dan naman miyar ma da muke
samu da yawa ya ragu ada daga ni sai hadizata yanzu kuwa takai karshen maganar cikin jan
dogon tsaki wanda Yafi nadazu tayi shigewar ta daki tana cigaba da masifarta ita kadai

Nikam nace Baba Asabe shi naman miyar halan dai bakisan sauyin ubangiji ba 😇

�fa'eeh bungudu�

Halee da Khady shigar su daki keda wuya dukkaninsu suka samu guri suka zauna kowa rai ba
dadi musamman khady wadda take jin haushin abun da mahaifiyarta keyiwa Haleen.
Matsowa Khady tayi inda Halee ke shingide gefen katifarsu data sha gyara kamar gadon
Amare🤩

Zama kusa da ita tayi tare da kamo Hannunta daya ta furta cikin tausayin Haleen kiyi hakuri
kibarwa Allah komai ninasan Babata bata taba kin kiba har cikin ranta kawai dai shaidan ne
ke zugata da kuma sharrin wani yanki na zuciyarta dan yin shiru tayi kafin tacigaba da magana
Halee! dago kyakkyawar fuskarta tayi ta kalli Khady ....banason Son ina ganin damuwa abisa
kyakkaywar fuskar nan taki,Mai sanya samarin zamfara hadarin titi�

Tunda Khady tafara magana bata tanka mata ba amma maganar ta takarshe sai da tasaka ta
yin wani kayataccen murmushi wanda har sai da two side dimple dinta dana kasan gemun ta
suka lob'a gwanin burgewa.

Itama Khady Murmushinta tasaki mai kyau wanda har cikin ranta yake nuna tsantsar farin
cikinta naganin murmushin yar uwar tata Halee wanda yake ba kullum take yinsa ba duk da
fuskarta irin ma,abociyar yalwar murmushi ce kamar ta junaid Abban sojoji😄Amma damuwa ta
hana ta bayyanar da asalin annurin Fuskarta.
�Fa'eeh Bungudu�

Dama Khady tasan tabbas ta furta mata irin wannan kalmar sai ta yi murmushi,ita abunda ke
sakata yin murmushin gani take bawani kyau ne da ita ba kamar yadda Khady ke yawan fada
mata da kuma classmate nasu,saboda ba kullum take samun damar duba fuskar ta ta ba
Amadubi dan cewa take bashine agabanta ba,ita gani take kyawon da duk ake fada tana dashi
nabanza ne saboda kyawu ba asali baida amafani acewarta,ita yanzu sanin asalinta ya fiye
mata kyawun komai agareta a cikin duniyar nan.


So dayawa in Khady ta matsamata da cewar tana da kyau na fitar hankali takan cemata
"kyawu ba asali babu amfani" kuma da ta fadi wannan kalmar sai ta fashe da kuka Khady tayi
ta aikin lallashinta Yanzu ma khady bata matsa mata da wata maganar ba dan gudun
karamata damuwa.....
Wash hannu nah wallahi typing wahala 🥹
kuyi manage da wannan ba yawa

Mu hadu a next page domin kara warware muku matsayin Halee agidan Baba Adee

Kuyi hakuri da sauyin dakuka gani�

Masu comment da like ina godiya�🥰

khadseen🥰
Halimatu B Auki🥰

�fa'eeh bungudu�
Pls like share & comment



�A MAFARKI NASANTA�
in my dream i know her
By
Pha'eezah almustapha
Daga Alkalamin����
�fa'eeh bungudu�

Dedicated to my lovely sis laila Almustapha murai�

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
�P.E.W.A�
Home of perfect Writer's together we stand �

ESSENTIAL WRITER'S
�🖊�*
Pen🖊�is mightier than the sword 🗡�*

Proud of my first my novel👌

*JIN JINA TA�� MUSAMMAN ZUWA GA BABBAR KUNGIYAR MU*
�P.E.W.A�
Ina alfahari daku musamman uwayen gidana🏢

*MHIZ BAREEMAH* (marubuciyar yan biyu macizai ne) the twins snake��

*OUM AMJAD* (marubuciyar yan biyu)the twins👭



EPISODE1�⃣
FREE PAGE5�⃣

TYPING📲📲📲


Kawar da shirun nasu tayi ta hangar ta hanyar furtawa Halee kitashi ki watsa ruwa bari indebo
muna ruwan zafi tana gama fadar haka ta cire hijabin uniform dinta tayi waje.

Bayan fitar ta daga dakin Halee ta tashi daga kishingid'en datake tacire hijabinta ta nad'esa Sa
tasanya acikin acikin sip dinsu wadda Khady bata ya mutsa ba,sannan ta jawo zanen da take
wanka dashi tayi tadaura bayan ta cire kayan jikinta tasanya acikin basket na Tara datti Dan
karamin hijabinta Wanda take wanka dashi tasanya ta cigaba da gyara kayan da duk suke
ahargitse acikin sip dintasu Wanda Khady ce ta ya mutsa su dazu da zataje makaranta..

Tana cikin gyaran sip d'in ne sai ga khady tadawo da ruwan acikin small bucket bayan ta amsa
mata sallama ne
Ta Tsinkayi Muryar Khady Tana Furta nidai Halee kibar gyara kayan nan kinga baki da lafiya
duk da naga yau jikin naki da sauk'i nazata sai munje asibiti ~takai karshen maganar fuskarta
da alamar damuwa

Hararar wasa wasa Halee tasakar mata tana idasa lankafe hijab daya daya rage saura ta
gama,Ahankali ta juyo ta dauki ruwan zafin da Khady ta ajiye mata tare da furtawa Khady
karki damu Sisi nah nafara zama strong women tayi maganar ne cikin sanyin muryarta da
yazame mata jiki takai karshen maganar tana sakar mata kayataccen murmushinta mai Sa
maza👨 had'ari atiti�
----------------------------- �fa'eeh bungudu�

Itama Khady murmushin ta mayar mata dashi bata k'ara cewa komai ba ta kama hangar da
zata sadata da d'an madaidaicin toilet dinsu dake cikin dakin har ta kusa isa ta tsinkayi
muryar Khady na furta "Halee kibari inzo in had'a miki ruwan tunda naga baki da karfin jiki
tafiyar taki takara. Zama slowly" Ko ayanzun ma murmushin Halee tasakar mata Wanda har kyawawan hakora ranta farare Tass
suka bayyana gwanin burgewa,itama Khady Murmushin tayi tana furta ohh! Yau su Anty Halee
yan sarautar sun motsa kenan girgiza kanta tayi tana kara sakin murmushi na mamakin halin
Yar uwarta na rashin son yin magana.
Itama cire uniform din nata tayi tadaura zanen da wankanta tayafa katon mayafi tana ficewa
daga dakin
-------------

Tun akofar dakin nasu tafara magana cikin farin ciki take furtawa Baba Adee sannu da zuwa
saboda tajiyo muryar shi lokacin suna magana da Khady.

A bangaren Halee kuwa tana shiga toilet din ta fara gudanar da wankanta cikin natsuwarta
da tazame mata jiki duk da yadda ranta yake ba dadi....

"Dady sannu da zuwa" ya hanya?Muryar Khady ce ta ratsa tsakar gidan nasu har zuwa
barandar da wannan dattijo yake azaune.
Murmushi wannan dattijon yi har takara so inda yake dattijon kirki Wanda sunan shi yake Abdul
rashid Amma anfi saninsa da Baba Adee Wanda akalla zai kai shekara hamsin aduniya.
(wannan suna Khady ce tafara sanya masa shi alokacin tana karama bata iya fadin Dady
kamar yadda Halee ke fadi sai ta mayar dashi Adee Wanda ganin haka yasa itama Halee ta
mayar dashi Adee jin Yar uwar ta na kiransa haka)
Sai kuma sunan yabisa har na waje suka kara masa da Baba wannan kenan..

Har ta durkusa agabansa Murmushi ne kwance akan fuskar Sa ganin yadda ta turo baki gaba
nak'in amsa mata sannu da zuwan da ta masa,Baba Asabe ce dake tahowa da amadaidaicin
kofin silver domin kawo masa yasha ta furta kekam dai Hadiza meyake damunki ehhh!daga
dawowar Sa sai fara turar masa baki kamar wadda aka daka tana magana tana tsiyaya masa
ruwa akaramin cup shima na silver mai kyau

Kurb'a ruwan da Baba Asabe ta mikamasa kurba guda yace rabu da ita kinji dije,aiko ida rufe
bakinsa baiyi ba Khady takara turekke bakin nan gaba....

Dariya yayi wadda take fitar da suffar shi ta magidantan kirki yace ke koh:khadija Dan Ankiraki
da dije ai bawani abu bane suna ne mai dadi koh! yakai karshen maganar yana Dan yin
murmushi,ganin tayi shiru batace komai ba,yace nasan fushin da like yi nafarko ban karba miki
sannu da zuwan ki ba na biyu na kiraki da sunan tsofaffi yakai karshen maganar yasa cikin yin
Yar karamar dariya wadda har far in hakorinsa na Makkah ya bayyana sannan yacigaba da
magana kin san Khadija nace kibar yimin sannu da zuwa tundaga nesa shiyasa na kyaleki na
biyu kuma ayi hakuri laifi nane shalelen Laure....yana murmushi
Baba Asabe dake gefe itama murmushinta yi,Itama Khady murmushin ta saki jin ankira ta da
shalelen Babarta cikin dariya ta furta hard a ta dadynta dukan su dariya suka sanya.
Maganar Baba Adee ce ta dakatar da da riyar su Wanda maganar bata yima Baba Asabe dadi
har fuskanta ya nuna,inda yake furta "yake cewa ina Shalele ".................

Yawan likes dinku da comment shahizai Sa Ku samu page biyu arana

*A mafarki nasanta *📒
Daga Alkalamin
�fa'eeh bungudu�


Mu hadu next page✌✌
Dan jin cigaban maganar ta Baba Adee
Dakuma jin Amsar da Khady zata bashi, nasan kun matsu kuji asalin Halee
------------------
Kucigaba da bibiyata ahankali zan warware muku duk wani sashe na littafina....

WASAN YANZU AKA FARA�

Kuyi hakuri ba editing domin dazu sai da nagama wahalar typing gaba daya ya goge.

Pls like share and comment.

�A MAFARKI
NASANTA�
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin���
�Fa'eeh Bg �

Dedicated to my lovely sis Laila Almustapha
Murai�

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
�P.E.W.A�
Home of perfect essential writer's together we stand�

ESSENTIAL WRITER'S�🖊�*
Pen 🖊�is mightier than the sword🗡�*


EPISODE1�⃣
FREE PAGE6�⃣


dama na fada muku page dinku na friday sai yau to ga alkawarinku nan na cika✌�✌�

TYPING📲📲📲

Khady cikin murmushi ta furta tana daki na barota ta shiga wanka kai yad'a ga mata alamar
gamsuwa,firarsa ya cigaba da yi da yarsa cikin lumana yana tambayar ta ya karatunsu na
islamiyya da na boko tana bashi amsa da alhamdullillah, masha Allah sai akara dagewa kinji Ya
furta cikin jin dadi,kai Khady ta d'aga masa tana furta in sha Allah Anan take sanar masa da
Halee bata je ba yau,Assha!Assha! meya hanata zuwa injin dai ba ciwon kanne nata yatashi
ba...Yakai karshen maganar cikin nuna tausayinta kara furta wa Khady yayi tun yaushe yatashi
?tun dazu da asuba,tashi ki kira mun ita in ta fito tau tace sannan ta tashi ta wuce dakin nasu
domin kiran Halee.

�Fa'eeh Bg�

Kanshi ya juyo dashi gefen da Baba Asabe take Yana furta Laure shine baki gayamun ba tunda
nashigo,Baba Asabe da tun da tun dazu take cike da jin haushin shi nakiran Halee da yayi da
shalelensa duk da bayanzu ne tafara jin yana kiranta haka ba tun tana karama,Dan bata son
yana nuna wa Halee soyayya fiye da Khady duk da yana kamantawa Acewar ta yar tsintuwa ba
"ya bace,dakyar ta bud'a bakinta tabashi amsa saboda haushi ga tsoron ta nuna mishi taji
zafin maganar da yayi mata dakuma Kiran Halee Shalelensa,Haba Baban Hadiza yanzu fa ka
dawo,ruwa kadai kasha ni dama yanzu nake niyyar sanar maka takai karshen maganar cikin
danne wani kololon bakin ciki da yataso mata,niyya ya maimata abayyane yana gyad'a kansa
cikin alhini ya nagayamiki duk randa ciwon shalelena yatashi ki rika kirana awaya in ba nanan
sai inturo nurse kamal ya duba ta Amma da yake ita ba Khadija bace sai kike yin biriss da
lafiyarta,ace kullum sai na maimaita miki maganar cewa ita din amana ce ta Allah agare
mu,Amma na fahimci bakya ganewa kuma na fahimci har yanzu na baki dauke ta amatsayin
yarki ba dan ina da tabbacin da Khadija ce keda wannan lalura haka da kin kasance mai
kulawa nasan da gudu zaki sanar mini in ya tashi amma dan rashin Amma ni kike shaida ma
wai yanzu kike da niyyar sanar mini,nasan kuma da khadijan ce da tun da asuban nan kinkira
kinsanar mini,nasan kin sani keda kanki kika karbi amanar yainyar nan ba wani ba dan haka kiji
tsoron Allah ki kara riketa da Amana.
Duk wannan maganar dayake kanta nakasa dan tasan yau ta dan ballo wani yanki na
fad'ansa,ita inbanda tasan duk randa Halee bataje makaranta ba ciwon ta yatashi da bazata
san bata da lafiya ba,tunda kosu yaran sun sani ko sungayamata babu abunda take iya yi face
ma tabi Haleen da zagi ko gwacine,batun yau ba Halee na rashin lafiya Amma Baba Asabe
bata kiransa tasanar masa in baya gida da yake ba,a garin yake aiki ba in yatafi yana kwana
biyar ko sati kafin yadawo shiyasa wasu lokuttan har ta gama jinyarta bai sani ba.
Maganar shi tadawo da ita daga maganar zucin da takeyi....Yana furta wallahi Laure ki guji
b'acin raina izuwa wannan lokaci ransa yakara baci ya hasala jin saoboda shirun da
tamasa,Cikin danyin kasa da kai Baba Asabe ta furta Baban Hadiza Allah yabaka Hakuri,bai
tanka mata ba sai ma cigaba da maganar sa da yayi yana furta baki san girman Amana ba
Laure ba shiyasa Amma zanyi maganinkin dan bana son kikawo mini shirme cikin gidana dan
haka kikiyayi b'acin raina karki kai ni baango ...........
Sallamar su Halee ce ta dakarar shi daga sake yin magana,Assalamu alaikun dady nah
Halee ce ke ke maganar da murmushi kwance abisa kyakkyawar fuskarta kyau da annuri
wanda ke nuna farin cikinta na dawowarsa gidan,cikin shigarta ta wata doguwar riga yadi pink
mai taushi da d'an madaidaicin hijab dinta fari wanda yakara haska farar fatar ta wanda har
kashe ido take yi kamar zinari acikin azurfa,inka kalle ta kyakkyawar fuskarnan sai sheki take
yi kamar wankakken gold gwanin burgewa kai bazaka ce tana da daamuwa....

�Fa'eeh Bg�

Wslm Halimatu Sadiya mai tagwayen suna kuma shalelena inji cewar Baba Adee cikin
farincikin ganin ta yake furucin murmushi kwance afuskar shi shima.
"sannu da dawowa ya hanya" ? inji Halee tana kara sakin kayataccen murmushinta jin yakira
cikakken sunanta wanda kamar ga bakinsa aka rada sa,kuma tana jin dadi yakira ta da

hakan,Alhmdllh lafiya qlau hanya yakarfin jikin ki ance baki ji dad'i ba, cewar Baba Adee,ehhh
naji sauki alhmdllh ai har nasha magani na yanzu kafin in fito,d'anyin shiru tayi tuna yadda
tasha maganin wanda sai da Khady tace zata hada ta da dady ne sannan tasha shi dakyar
kamar tayi kuka dan ta tsani magani ko allura,Dan kallon khady tayi wadda itama ita take kallo
jin yadda take bayani kamar ba sai da ta tilasta mata ba,kawar dakanta tayi daga kallon Khady
tana maida hankalinta ga Baba Adee wanda ke furta masha Allah haka ake so ai har ina
maganar akira likita ko muje asibiti
Murmushi tayi tana yin kasa da kanta wanda har kyawawan hakoranta farare tass suka
bayyana gwanin burgewa tace Naji sauki dady kuma sosai,murmushi ya karayi yana furta to
madalla Allah yakara Afuwa,Ameen Halee da Khady suka amsa, yakaratun su da makaranta
ya tambayeta kaamar yadda yatambayi Khady,Alhmdllh ta furta,kara furta mata yayi ya gidan
kuma dan shiru tayi sai kuma cikin yanayin sanyinta ta furta lafiya lau kai yajinjina kawai
batare da yakara furta komai,Baba Asabe ce da tagama girkinta na jallof din taliya da taji
alayyahu,Ahankali tasauke wanda ta zubowa Baba Adee agaban sa cikin wani filet na tangaram
irin na da mai kyau tana furta Baba Hadiza ga abincinka nan tayi maganar fuskar ta sai sa sai
sa ba fushi ba murmushi dan bataso tana wani abu yakara hawa,wadda tun lokacin da ta
samu su Khady sukazo gurin ta bar wurin tare da kayansa ta kai masa daki sannan ta wuce
kitchen.
Bayan ta aje abincin ne ta koma ta debo masa ruwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0