Showing 57001 words to 58434 words out of 58434 words
MINI WANI B'ANGARE NA LITTAFI BA.INKUMA KIKAYI MINI GANGANCI
NABARKI DA RABBA....
BAN YARDA A KARANTA MINI SHI AYOUTUBE BA SAI DA IZINI NA.
MASU TAMBAYAR COMPLETE BAN KAMMALA LABARIN BA YANZU NAKE TYPING....
------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITIONí ½í¶Šï¸�*
*P.E.W.A*
*Home of perfect essential writer's together we standí ¾í´�*
*ESSENTIAL WRITER'Sí ½í¶Š*
*Pení ½í¶Šï¸�*is migthier than the sword *í ½í·¡ï¸�*
*Free book*
EPISODE1�⃣
PAGE37
TYPINGí ½í³²í ½í³²í ½í³²
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
.....Bayan nabaroka cikin shoprite din na fito in yi picking call bayan nagama amsa call din injuyo
kawai sai naci karo da yarinya tsaye abaya na tana ta sakar mini murmushi,ida juyo wa ta
kenan A hankali yarinyar ta furta mun cikin bayya! cikin murmushi ganin yanayin yarinyar
yasaka nima nasaki fuskata wanda har zuwa lokacin mamaki da alajabi bai sake ni ba naganin
kamannin yarinyar da nake yawan mafarkinta..
"Yaya zaka kaini gurin didin mu yanzu koh" da ta furta shine yasanya ni k'ara saita natsuwa
ta.Kai kad'ai na d'aga mata badan nasan wacece yayar tasu ba,muna nan tsaye tana zuba mini
surutu sai ga wasu samari mace da namiji inaga dai twins ne su sun doso inda muke suma
kuma baka ga yadda suke kallo na ba kamar ydda nake kallonsu wanda ninasan kalllon rashin
sani ne suke mini ganin na tare da kanwar ta su da ko sunan ta bansani na dan suna kama da
yarinyar Sosai.
Gaisawa mukayi dasu Sannan suka nemi in basu kanwar tasu A hankali nazare hannu na dake
cikin nata wanda ta rike gamm,rigima suka sha da ita dan tadage sai tabini nakaita gurin didin ta
harda kuka sai da na lallasheta sannan nace taje zamu hadu gobe in kaita Amma duk da haka
sai da namijin ya fisgi hannun ta tana kuka tana waige na harsuka sanyata bayan seat suka
tada motar su,d'an nisawa yayi sannan ya furta a hankali cikin wani kalar sanyi "kaina ne ya
daure shiyasa nakasa komawa cikin shoprite din
Yakai karshen maganar cikin sauke katuwar ajiyar zuciya na doguwar maganar da yayi.
Kallonsa kawai Aj keyi har yadauki ruwa ya tsiyaya yakai abakinsa,yau nakara shaida son da
kakeyiwa wannan yarinyar mai yawa ne,ace har ka iya kallon yarinya yar shekara goma siffarta
to ko dai yar shekarar goman zaka Aura yakai karshen maganar cikin kanne ido d'aya "kaga sai
muyi rainota...Yakai karshen maganar yana sakin karamar dariyar shakiyyanci.
Harararsa Ammar yayi sai kuma yasaki dan karamin murmushi yana girgiza kansa na furucin
Dr.Aj yana mai yankar tandori chiken A hankali yake taunar naman kazar bayan ya saka
bakinsa Tare da lumshe manyan idanunsa da yake jin sun dan masa nauyi kasancewar rashin
samun isasshen bacci da baisamu ba jiya a asibiti.
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
MUJE ZUWAí ½í±“
Tun alokacin kusan kullum sai Dr.Ammar ya tsiri zuwa shoprite din ko zai ga mai kama da su
lubna sai da yashare kwana goma bai hadu dasu ba sai arana ta sha d'aya ne ya hangi lubna
itada ziyadah hannunsu rike da juna amma ita sai waige waige takeyi kamar tana neman wani
abu kamar ance ta waigo daga gefen da yake tsaye ya rungume hannayensa.
'cikin masifaffen gudu ta zare hannunta cikin na ziyadah tana zuwa ta fad'a jikinsa ta rungume
sa sai kuma tasaki kuka itakam ziyada sai ikon Allah take kallo,Ajiyar zuciya yasauke a hankali
kamar wanda yaron da yake neman uwarsa sai da yaci wuya yaganta sannan ahankali
yacigaba da lallashinta yana shafa sumar kanta."Bayya"ta furta cikin sanyi da dariya mai nuna
farin cikinta.dama lubna tasha wa Kowa kai gidan su na rashin kara had'uwa dashi da batayi ba
kusan kwana uku kenan duk aka tadosu makaranta sai sun kawota gurin Amma sai dai har su
bar gurin basa ganinsa saboda suna shan ban ban wurin wani lokaci da rana yake zuwa
sometimes kuma da dare su kuma da bayan anataso skull ne.
A hankali cikin kara kawata fuskarsa da murmushi ya furta your Name cikin harshen india suke
maganar "LUBNA BABY " ta furta aunty nace mini haka Appah ma nace mini yaya ziyad ne da
ziyadah kadai basa cemun baby murmushi yakarayi sannan yashafa kanta yana dagota daga
rungumar da yayi mata ayanzu kan kafadarsa.
Itama ziyada zuwa tayi suka gaisa dashi cikin sakin fuska a hankali tunda yaji sunanta gurin
lubna yafurtawa ziyada ya schl Lafiya lau ta amsa mishi cikin girmamawa duk da mamakin jin
sunanta abakinsa.
Tattakawa yayi dasu har inda rantsasiyar motar tasa take dan bai fitowa da ko daya daga
yaransu inzai zo nan,front seat yayi yajawo wata katuwar teddy pink colour da tacika extra seat
na motar an rubuta mata baby Akan hular dake kan ta da ruwan gold.Mikawa lubna yayi,Ba
lubna ba hatta ziyadah da ziyad da fitowar su harabar wurin yahango su shine ya shima yafito
a motar da yake zaune teddyn ta burgesu ko ni mai kwaso rahoto ta burgeni matuka.
Farincikin lubna yakasa boyuwa tsalle kadai takeyi a wurin bayan takara rungumesa.
Bayan motar yakara budewa ahankali ya fiddo da wasu big bags na shoprite din masu kyau
dauke da hoton chocolate,wanda kusan kullum sai yasayesu sai dai yakyautar inbai ga su lubna
ba teddyn ce dai guda tun da yasaye ta saboda tamasa kyau sai ya ajiyewa lubna.Mikawa
ziyadah ledodin yayi yana furta keda twins broth naki daya, daya kuma na lubna baby ne ita
kadai tsalle ta kara dakawa cikin farin cikin wannan kyautar da tasamu ga trddyn ta rungume
ajikin ta,Sai ma tamanta da maganar kaita gun didinta.
Godiya ziyadah yamasa sosai bayan sun gaiisa sannan sukayi sallama dashi har inda motarsu
take Har suka shiga mota tana waigen sa tana daga masa hannu shima yana daga maata har
ziyad yatada mota ta dakatar dashi da gudu ta fito da tap dinta ta buga game da karatu kirar
samsung ahannu inda ake saka numbers tashiga duk da wayan ba mai simcard bace ta furta
"Bayya sanya mun numbanka kar ka kara guduwa baka kaini gurin didi bah"
Murmushi kadai yayi yakarb'i tap din rubuta mata nine digit nasa sannan tayi saving da bayya
tana rugawa da gudu tashiga mota ta rufe tana d'aga masa hannu har kanta ta ke leko wa ta
glass ta sakar masa murmushi...
Sai da yabar ganin kurarsu sannan yayi murmushi yanajin kansa cikin farin ciki marar misaltuwa
naganin lubna hardasu ziyad ma akaro na biyu..
Shima daukar motar sa yayi sai gida dama ga abunda yakawo sa kuma yasamu.
yau Aj yaga farin cikin kan fuskar Ammar kuma yana da tabbacin cewa ya hadu da yarinyar.
FIRSTLADY
shigowarsa baiyi tsinke ko ina ba sai akan dinning table a hankali yasanya hannunsa ya wanke
akan sink,sannan yazauna a d'ai daga cikin dining chairs din dake dinning area din masu kyau
••Butter chichken yajawo dake daure da raping sheet mai kyalli ya bud'e a hankali kamshin
hadin hadaddiyar kazar da taji hadi na musamman yabugi hancinsa ne yasanya sa lumshe
manyan idanunsa masu haske,A hankali ya yago kazar da pock da knife yakai bakinsa ya tauna
a hankali harda kad'a kai saboda yadda d'and'anon da yagame bakinsa,Bhulpuri yajawo dake
cikin katuwar food flask mai kyau ya zuba bakinsa yasanya yana taunawa ahankali Dr Aj da
yanzu yazauna kan dinning din ne ya furta acicin banza tun d'azu ina nan ina jiranka shine daga
zuwan ka kazame nan maimakon kaje kakirani ko kasanya sabirkhan shiru bai tanka masa ba
har sai da yaji cikin sa ya dauka domin Ammar bai wasa da cikinsa ko kad'an,ruwa yasha da
lemu sannan yayi hamdala tare da mikewa yana furta cikin arrogant voice nasa" kanka akeji
uban mita"yakai karshen maganar yana sakin kayataccen murmushinsa irin wanda ke kular da
aj domin smiling ne mai ma,anoni da yawa aciki harda rainin hankali upstair ya wucewar sa dan
yin wanka.
yau aj ya ga farin ciki akan fuskar Dr. Ammar kuma yana da tabbacin cewa ya had'u da yarinyar
da yake ta zagayen fita yasake gani,murmushi shima yayi kawai yana cigaba da cin abincinsa.
*NIGERIA ZAMFARA*
*GUSAU*
Ta sambo!!!!