Showing 42001 words to 45000 words out of 58434 words

Chapter 15 - A Mafarki Na santa By Faeeh First Lady

25 Jun 2026

464

tana furta har kun iso kenan,Macece kyakkyawa kamar Unni
fara tass komai nasu iri d'aya har muryar ma tasu identical twins kenan kafin ka shaida d'aya sai
ka d'anyi dogon nazari.
Cikin murmushi dukkaninsu suka rungumeta itama murmushin tasaki tana furta sannun ku da
zuwa "ya "yana shine ba sanarwa sai kukayi gidaan Unninku kuka turo mun driver kawai.
Dariua sukayi dukkansu har Ummin.
Nisa na bud'a baki zata furta ai yya mahir....Sumy ta mintsileta gudun karta sakammata
layi,fahimtar hakan da Nisa tayi sai tace Ummi yaya mahir yace agaisheki,ina amsawa ta furta
tana raba jikinta da nasu itama sumy ta furta Ummi yya Abdallah ma yce agaisheki duka ina
amsawa tace duk da sun gujeni kwana biyu...
cigaba da magana tayi yau Ina cikin farinciki yayan Unni da Ummi duk sai suka had'a baki gurin
tambayar mene ne yasanki farinciki haka Ummi ko dadyyadawo ne bamu sani ba duk da
bamuga motarsa ba acompound girgiza musu kai tayi cikin murmushi tana furta aah,BAi dawo
ba Amma karku damu zakuji komai nan gaba,Tana wucewar ta kitchen.
Wanka tace suje suyi suci abinci toh suka ce suna takawa upstair d'in ...

Wata kyakkyawar yarinyace fara kamar ta sak da Alamin da sumy sai dai batayi hasken su
ba,da gudu ta taho ta rungume yayyen nata bayan sun idasa take kan step din tana furta shine
kuka je gidan Unni yau badani ba koh'tana maganar tana neman bare musu baki tasaka
kuka,Nisa ce tajawo ta ta na furta kinason zuwa wurin Unni koh,kai tad'aga mata, toh kibari
juma'a tayi sai muje koh har Ummi,ai kinga juma'ar takusa zagayowa koh kai takara d'aga
mata,yawwa An Husna ta muje kema inmiki wanka ko,suna wuce wa ta sashen da rooms nasu
yake.


*HOSPITALISED*
-----------------------------------------------------------------
*INDIA*

*Maharastra 24hrs Hospital mumbai*
Zaune yake akan chair dinsa mai juyawa acikin kayataccen office d'insa mai kyau bayan ya
cire labcoat dinsa yasargafe ta a had'addiyar hangern office din nasa, bayan yagama duba
outpatient.
Katon office ne kamar wani falo guda komai yaji komai na kawa, windows dinsa gaba daya gilas
ne ga katuwar lockern sa ta ajiyar takardu da document,da haddaen fridge d'an karami wanda
yakarawa office din ado, sai d'an madaidaicin gado na duba marar lafiya tareda sauran kayan
amfani irin su spring cover d.S,sai kofar toilet da wata kofa danake tunanin bedroom ne,komai
masha Allah ba wani tarkace.

,,,,,,game Yake bugawa a had'addiyar wayartasa kirara 15promax( iphone) sanyin A.C na
office d'in yahad'e da k'amshin turaren sa mai dadi BETTER MAN na kamfanin "yosen"domin
kowa yasan dr Ammar ma'abocin sanya turare ne.
Had'adden table din dake gaban sa yana dauke da wani tambarin na kwalbar zinari kamar na
award an rubuta Dr.Abdul rashid Aliyu Ahmad,cikin tsari mai kyau,ga kayan aikinan masu
quality da kyau na aikin su irin su Bp apparatus,spygmanometer...Thermometer abun awon
pulse da dai sauransu sai wasu yan d'ai d'ai kun takardu na amfani wayenda bukatar su kan
taso ga patient...

K'arar door bell ce tasanyasa Ahankali cikin tak'ama ya furta come in,Kyakkyawr budurwace
tabayyana acikin office din nasa,Dr.Malini kenan kyakkyawar ba indiya ruwa biyu jinin larabawa
da indiyawa,kykkywace ajin karshe sanye take da sari ja da labcoat ajikin ta inda naga anrubuta
dr malini arorah,takowa tayi Ahankali tazauna akujerar da taje gefen table din tana mai furta
masa barka cikin harshen india tare k'awata fuskarta da murmushi....

kamar bazai tanka ba sai kuma ya furta yawwa Atakaice cikin yaren idia shima, yana cigaba da
buga game dinshi,tun shigowarta da yamata kallo d'aya yani itace bai ka'ara kallon taba,koda
sashen datake.

A hankali ta k'ara furta masa cikin harshne nasu,yazo sufita cin abinci suje bakin ruwa,,,,Bakin
ruwan da furta ne yasanya gabansa muguwar fad'uwa daya tunano mafarkinsa da yayi jiya
wanda har yau baisanarwa da kowa ba.

A hankali cikin tak'ama da izza irinta jinin sarauta masu ji da ita ajikinsu Bayan tsai da tunaninsa
akan mafarkinda yatsaya masa arai,ya mayar mata da Amsa ''I am not interested"
atakaice maganar ta kona wa dr malini zuciya sai dai sanin halinsa sai ta basar bata k'ara furta
masa komai ba domin inda sabo tasaba da irin cin kashin da yake mata,wanda ita taja wa
kanta,wanda su achan kasar su ba komai bane is nrml thing.
*daMa mazan yanzu ya aka kare koshi yace yana sonki bare ke kika kai kanki,abun sai anrika
had'awa da Addua,inkin zurfafa yar uwa,sannan karki bayyanar da soyyayr nan har yagane kina
iya vada ranki saboda shi,domin wasun su suna amfani da wannan damar su cutar da mu,Allah
yabamu masoya nagari*�

Ganin da yayi bata k'ara yin magana ba kuma bta fice ba yasanyasa d'ago dara daran idanunsa
yayi duba na second daya agareta,yana dauke kansa cikin cije leb'ensa na kasa,yayi danasanin
d'agowa yakalleta harsuka had'a ido,domin hawayene yagani suna a idanunta wasu na
turereniya da wasu,D'an karamin bakinsa yakara tsukewa dan yatsani ganin hawayen mace
domin take yake rikicewa,Tabbas a wannan gab'ar dr malini tayi nasara domin zata janye
hankalinsa in har tagano lagon.

Ayanzu haka ma yakar zuciyarsa yakeyi data fara darsa tausayin Dr malini wanda kuma shi
haknne bayaso yafaru.....

Karaamar tsuka yaja wadda iyakarta kan labbansa yana ajiye wayartasa akan
desk,handkerchief dinsa fari k'ar dora mata agefen da ta kife kanta tun bayan had'a idon da
sukayi tana cigaba da kukan ta kasa kasa,Saurin Dagowa tayi A hankli ta kallesa cikin wani
yanayi ganin ya ajiye mata hanky kallonsa take da mamaki da alajabi domin yauce rana ta farko
da yafara nuna mata kulawa,take ta tsinci kanta acikin farin ciki marar misaltuwa ita a tunanin ta
yafara sonta,tunda su dab'iar su ce in har saurayi yabawa budurwa handky tashare hawayenta
kamar alamar soyayya ce tunda shima wannan kulawa ce.....
Hmmmm Nikam nace DR.MALINI Kenan.



�A MAFARKI NASANTA�
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin����
�Fa'eeh BG�

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai�
------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION�🖊�

�P.E.W.A�

Home of perfect essential writer's together we stand�

ESSENTIAL WRITER'S�🖊

Pen🖊�*is migthier than the sword *🗡�

EPISODE1�⃣
FREE PAGE31

TYPING📲📲📲


"Sorry" ya furta mata ayangance,duk da yadda Kalmar kemasa nauyi ahankali ganin tana share
hawayenta Wanda har fuskarta tad'anyi jaa fuskar ta chanza alamar kuka abunka da farar
Fata.kai kad'ai Dr.malini tad'aga masa,Bayan share hawayenta da kyakkyawan handkerchief
Nasa fari kar mai kamshi. A hankali ya buda bakin sa dakyar cikin tattausan lafazi da muryarsa mai sanyi da nuna izzarsa
ya furta mata acikin harshen turanci, I have a lot of appointment today,so thats why I tell u I can't
go with you,ya furta mata hakan ne kawai ganin hawayenta yanaso tasaki fuskarta bazai so
ace kullum cikin kuntata mata yakeyi ba yasan cewa soyayyar gaskiya take masa sai dai shi
bata cikin Ra,ayinsa har yanzu.
Shiru yayi bayan gama maganar jin bata CE komai ba yakara furta i'am sorry ohk!

D'aga masa kanta tayi tana tashi tsaye da lab coat d'inta da tacire kafin ta zauna,hanky d'insa ta
ajiyemasa No,
Ya furta da ita "you can go with it"murmushi tayi har cikin ranta jin furucinsa taji dad'in kulawar
da ya bata yau kad'ai akaro na farko wadda tadauke ta amatsayin wata nasara ta ta.
Bye tamasa Tana takonta d'ai d'ai na big ladies masu ji da Kansu tako wanne fanni k'arar high
hill dinta ne kad'ai yake tashi duk inda ta wulga sai an mata kallo uku saboda haduwarta.

Dr.Am dayaga wucewar Dr malini tana ta faman sakin murmushi ne abunta,kansa yad'aure
masa kai,dama ga office d'insa ganasa,yana bud'o k'ofa yaga wulgawar ta sai dai bata lura
dashi ba. ida rufe kofar tasa yayi ya doshi kofar ta Dr.Ammar ko neman iso baiyi ba ya bud'e
door d'in yashiga ciki,ko ba,a fad'a ba yasan Al amin ne yashigo saboda shi kad'aine Wanda
baya tsayawa Neman iso ta hanyar danna door bell.

Idanunsa a rufe ya furta wai lafiya kamun tsaye akai, Dr.Am bai ce masa komai ba duk da yaji
furucinsa,sai ma kara gyara tsayuwarsa da yayi yana mai rungume hannyensa akirji,tsawuyar
minti uku yayi babu Wanda ya furta k'ala ga dan uwansa,Dr aj sai ma karantarsa da yake yi.Aj
ne yakatse Shirun nasu ta hanyar furta ma Dr.ammar" meye damuwarka na fahimce ka tun
safe kamar kawai Abunda ke damunka azuciya,kuma inada yakinin bazai wuce mafarkin da
kasaba yine kayi sai dai ban sani ba,ko wannan ya chanza daga Wanda suka sani ganin kamar
yana kokarin boyesa ne.


Shiru Dr.Ammar yayi kamar baiji Abunda da Dr aj yafad'a ba saima kara tsumewarsa da yayi
akan had'addiyar kujerar tasa mai rotating ,ganin baida niyyar magana yasanya Dr aj kawar da
shirun ta hanyar furta...
"Mekasanar wa Dr.malini ne naga ta fita tana tasakin murmushi kodai kabar hak'ar ta ta cimma
ruwa ne duk suna maganar ne da yaren India din.

Murmushin da bai shirya yinsa bane ya subuce masa akan kyakkyawar fuskarsa jin abunda Dr
aj ya furta idanunsa ya bud'e ahankali tar akan Dr aj yana kallonsa da murmushi a fuskarshi,sai
kuma yakawar da idanun nasa masu kaifi ganin Dr aj ya daure fuska ta Yar dariyar da ta fito
masa ta rainin hankali duk da bai tsawaita ba.

A hankali ya mike daga zaunen da yake yatako A hankali dai dai inda aj yake tsaye nan ya
tsaya suka jera gwanin burgewa sunsha fararen riguna da maroon colour trouser kowa ya tsuke
da belt maroon sai kuma hadaddun boat dinsu masu kyau far are kar dagani dai sunji naira,yau
anko sukayi dama mafiyawancin lokutta anko sukayi domin duka Rabin kayansu iri daya ne da
juna sai dai kala CE wani lokacin take banbanta,tsayuwarsa data Dr.Aj gwanin burgewa ne
Daya yafi daya tsawo,Dr ammar shine mai tsawon,duk sun saka hannayensu a aljihu Wanda ke
facing bangon da yake na gilas Wanda dukkan abun hawan dake wuce wa a express way dama
mutane suna gani tar.


Tsayuwarsa da minti ya juyo ya dafa aj akafad'a Wanda har yanzu fuskar nan take mur,tsulum
yayi yakoma gaban sa suna fuskantar juna, cikin izza da yanga.


Wani killer smile yake ta sakarmasa Wanda ke iya haddasa gubar soyayyarsa acikin second
daya acikin zuciyar yan mata,shiko aj ganin sa a gabansa yasanyasa ja da baya yana
sakarmasa katuwar harara wadda tasanya Dr.ammar sakin kayataccen murmushi Wanda har
sai da fararen tass jerararrun hakoransa suka bayyana.Aj ne ya furta Dan iska kawai haka
kakayi wa yan yayan mutane suna fad'awa daga kallon daya cikin kara sakar masa harara.Dr
ammar kuwa murmushin sa yakara fad'ad'awa jin abunda aj ya furta masa.


Ahankali ya mayar masa da amsa cikin kasallaliyar muryasa ta gwarazan maza,kar damu likita
yanzu duk zan baka amsar tambayoyinka duk da bayanzu naso kaji wasu daga amsoshinka
ba,yana mai kara gyara tsayuwarsa,Kwantacciyar sumar kansa yashafo sannan ya cigaba da
magana a hankali "tabbas mafarki na ya chanza kamar yadda kayi hasashe ......labari yabasa
na yadda mafarkin ya wakana domin dama tin asali basa boyewa juna sirri duk da dama shi aj
yasan mafarkin saboda some time lokacin suna kwana daki d'aya yakan ji shi yana magana
k'asa kasa cikin baccinsa,Wanda dama yasan yana yin wannan mafarkin.


Ta gwayen ajiyar zuciya yake sauke wa,Wanda har sai da Aj yaji,bayan yagama basa labarin.

Tausayinsa ne Yakama Aj ruwan sanyi yadauko a fridge dake a office din tsiya ya masa yayi
acikin glass cup mai kyau dake jere awata locker daga gafen fridge din.

Ahankali yakai cup din saiti dan karami bakinsa kurb'a d'aya yayi yasauke gilas d'in ya rike a
ahnnunsa yana sakin nannauyar ajiyar zuciya cikin wani yanayi marar fassaruwa, jin yadda
sanyin ruwan ya ratsa Dukkanin sassa na jikinsa,Bayan kamar minti Uku yacigaba da
maganarsa yana furtawa Aj" Dr.malini Arorah bata isa tasamu gurbi acikin kirjina ba ko yanzu
kawai Dan tausayi tabani ne ganin hawayenta na zuba abanza,saboda ni kai kanka kasan bana
son ganin hawayen mace bare ma ace ta sanadi na suke zuba.

*wato abanza Dr�😢*.Hmmm maza
wasu wallahi tausayinsu ragagge ne *baiwar Allah nata wahala shekaru araru amma ayanzu
hawayenta ma na banza nesabd haba dr.Namu,*
*Dr.AMMAR FANS nidai gaskiya mutumenku yafara wuce gona da iri dan bazan dauki
wulakanci ga miss malini ba baiwar Allah😢Allah karabamu da son maso wani,da soyyayar
bangare d'aya.*��

"Tabbas da badan kwallar da nagani ba babu abunda zaisa inkula ta har inbata abunda zatay
wiping na tears nata,saboda bata cikin tsarin matan da nakeso and kuma she's too young for
me yana kai karshen maganars da yatsinar fuska yana kara furta bama kuma Aladun mu d'aya
kuma ba Addinin mu d'aya nasan kasan da haka maganar hak'ar ta ta cimma ruwa har abada
yana lumshe idanunsa s ai kuma a hankali ya na bude su.
Dr Aj ikon Allah kad'ai yake kallo atare Dr Ammar yana mai yana mai mamakin hali da da taurin
zuciyh irin na d'an uwansa ace mutun kaifi d'aya ne ba chanji domin yakamata ace yanzu ya
fara kula al amarin Dr.Malini saboda shekarun da tadauka tana bibiyarsa da soyayyarta,.''kaji
tsoron Allah Dude,bayan yagma maganar zucinsa, na jin zantukan Dr Ammar d'in. yar karamar
harara yasakar masa yana mai kau da kansa gefe,Aj ne yaci gaba da magana yanzu ita Dr
malini d'ince yarinya just bai wuce kabata shekaru uku ba fa domin bazan manta ba when last
birthday nata danaje ishirin da biyar tayi celebrating Amma shine kake kiranta da yarinya
sannan bata cikin tsarin matan da kake so kake iya aure koh !!! hmm Dude kenan inbanda so
yana haka me Dr.Malini zatayi dakai dubeka skin dinka kamar zumar dataji wuta ta kone,yakai
karshen maganar cikin dan yin dariyar mugunta domin yasan Ammar yatsani wannan furucin.

Karamar harara Ammmar yasakar wa dr aj dan dagaske yatsani kalmar nan dan aj nayawan
furtamasa ita duk da yasan wasa yakeyi masa fatarsa normal take kuma ahakan mugun sonta
yakeyi.
Murmushi Dr.AJ yayi yana cigaba da maganar sa,"ga mace har mace Amma so na walagigiya
da ita gaskiya Dude da zakaji shawarata da ka karb'i Dr.Malini saboda kaima shaida ne tayi
maka son gaskiya kuma bugu da kari ta had'a duKkanin Abunda Daaa namiji zai bukata ga
mace,kuma duk jarabarka nasan malini zata iya dauka domin nasan halinka inaga ka raina
girmanta ne,ina kara baka shawara karkayi watsi da damarka toh!!!!!!yakai karshen maganar
tasa yana dariya tare da kanne masa ido d'aya.

Dr.Ammar da ke kallonsa k'uri da ido ne Yayi D'an murmushin gefen baki sai kuma ya murtuke
kyakyawar fuskarsa jin furucin aj d'in na karshe domin nafarkon bai bashi haushi ba face ma

mere baki da yayi.

"cikin tsuke fuska ya furta Wai yaushe ka koma hakane bansani ba naga alamar idanunka sun
bud'e fa,murmushi ne ya subuce masa tuna furucin wai malini zata iya daukar sa abu na kayan
wanki,dakuma amsar datazo kansa kan maganar malinin wadda zai mayarwa da aj d'in wadda
zaiji zafin ta domin tabbas yaji haushin furucinsa na karshe wai zata iya d....Kasa ida karasa
tunanin yayi ta sanadiyyar zuciyarsa da tafara hasaso masa yadda komai na malini yake duk da
ba wani kallon tsaf yakemata,subhanallah ya furta azuciyarsa yana lumshe idanunsa tare da
bud'esu

yana cigaba da magana kace Dr.Malini Dr.Malini tacika mace ;Am nace ko zaka gwada sa,a ba
ko zaka samu cikakkiyar macen tunda naga har ka hango cikarta yakai karshen maganar tasa
cikin yana kanne ma Dr.Aj ido Daya kamar yadda yamasa,tare da sakin wani killer smile, aj
wqnda daga farkon maganar ta Dr.Ammar murmushi yakeyi sai wannan furucin na karshe
yasanyasa turb'ene fuska wata katuwar harara Dr.Aj yasakar masa wadda sai da tasanya Dr .A
murmushi wanda yasanya two side dimple dinsa bayyana gwanin burgewa,tsinin hancinsa ya
lakata yana mai k'ara sakin murmushi ganin shan tokar da Aj d'in.


A bangaren aj maganar ta bashi haushi matuka domin yadda suke da ammar soyayyar dayake
masa bazai iya son abunda yakeson dr .Ammar dinba koda shi bayaso kamar dr malini haka..
Ya bud'a baki da niyyar yin magana sai yayi shiru, karar wayarsa da yaji tadakatar dashi daga
abunda abunda yake niyyar furtawa,cirota yayi daga aljihun wandonsa na baya dan ganin
wanda ke kiran nasa wanda alokacin har wani sabon kiran yashigo nafarkon yakatse saurin
d'agawa kiran yayi Bayan duba sunan mai kiran nasa UNNI sunan da ya fito baro baro da manyan rubutu.......


�A MAFARKI NASANTA�
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin����
�Fa'eeh BG�

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai�

�A MAFARKI NASANTA�

YAZAMA FREE BOOK
Nama mayar muku dashi free book akan wani dalili nawa inason duk Wanda yaji dad'i yamun
Addu'a,Allah ya biya mini da dukkanin buk'atuna�

Ina godiya da hakurin da kukayi dani har na tsawon sati biyu koma fiye�
Ina alfahari daku masoyan Amafarki nasanta,kud'in na daban ne agareni💋


------------------------------------------------------------------

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0