Showing 1 words to 3000 words out of 56145 words

Chapter 1 - Bakar Izaya Complete Book Ansholy

Ansholy   

31 Jul 2026

579

Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

😭BAQAR IZAYA😭 1


Bissimillahir rahamanin rahim


sadaukarwa ga qawata maryam rimaye much love you💋💋💋


😘Ansholly😘



Rugar jalo ruwa ake kamarda bakin qwarya kowa yamaida gidanshi yakolle dan darene sosai
ruwan harda kankara gidan mlm iro

Yarinyace wacce aqastin shikarinta bazasu wuce goma ba

Zaune ruwa nadokanta sai karkarwa take kowa nacikin gidan yana daki

Amma ita tana waje acikin ruwa harta babanta yana cikin gidan

amma baidamu da itaba yana dakinshi akolle yana bacci mai dadi itako tananan

Cikin ruwa kuka tasa mai tsuma xuciyar mai saurare duk da tasaba amma ba asbd da wahala

Ba adaina ruwan nanba sai kusan asuba kana aka daina amma duk dahaka ana yaiyafi

Tananan zaune har akafara kiran sallah mahaifinta yafito

cikin dakinshi dauke da bota alamun alwallah zaiyi

Jikinshi wata irin rigar sanyice jibgegeya amma duk da haka rawar dari yake
kallo daya yaima inda take yadauke fuskarshi yakama hanyar bayi

Itadai tana zaune tana kallanshi harya fito yagama alwalla yatafi masallaci

wani irin kuka tasa maiban tausayi tana tunanin anya ita diyar mlm iro ce

dan da ita yarshice daya tausaya mata yadda yaganta cikin wannan sanyin

shikanshi babba yanajin sanyi ina ga ita wacce bata wuce shekara gomaba

nanda nan gabanta yafadi data tuno saura wata biyu tacika shekara goma

takama tunani itadai tasan tunda tatashi mutane ketsoran sura beta ciki harda mahaifinta

Wasu harkiranta suke aljana qawarta daya Hadixa
itama sadda tacika shekara tara hadixa tamutu wanda sanadin haka uwar hadixar har gida tazo
tai mata danbanxa duka dawata maganar da harta mutu bazata manta tab
[3/8, 1:04 AM] +234 703 962 5239: 😭BAQAR IZAYA😭2

😘Ansholly😘

Saudakarwa g hadixa tunau



Ta zurfafa cikin tunani kowai taji saukar ruwa ajikinta da sauri tadago

taga waye yai mata haka dan bata gama jin sanyin ruwan daya doketaba gashi anxuba mata

wasu ganin inna uwalace yasa tamaida kanta kasa cikin tsawa inna uwale tace dan ubanki
mikike

da har yanxu bakitai rafiba ibar ruwa cikin ladabi tace inna naga anyi ruwan sama kuma duk
sadda akai ruwa

Naga bana zuwa rafi juyawa inna uwaletai duk tadauko ruwan duk tamaka mata ajiki

wa yannan ruwanne kikace kin tara to bari keji xuwa rafi yaza mammaki dole

daga yau kodaza akwana ana ruwa bance kisaman kuda roba daya ki taraba

nagaji dashan ruwan tare narafi nakeso kobakiji ba

Cikin rawar murya tace naji kana ta dauki tulin tatafi rafi
yayinda tabar uwale nata xaginta dan sotai taimata mgn taimata dan banzan duka

tana fita kofar gida taga babanta dashi dawani makwabcinsu dagaji maganarta

akeyi dan taji anacewa saura wata biyu tacika shekara goma

tasan kuma da ita ake danduk cikin rugar ko yaro zaka tambaya shekarunta indai harya iya
magana zai fadama

tazo tagifta tagabansu tawuce dantasan kota gaishesu bazasu ammasa ba dan babant yace
karta qara gaisar dashi domin

shiko gaisuwa bayaso tahadashi da ita duk cikin rugarsu sarkin rugarne kawai yake mata
magana

kana yake janta ajiki kamar jikarshi zata iyacewa shika daine ke santa duk fadin duniya

hakadai taketa tunane tunane harta kai rafin saida tayi alwalla tai sallah kana tashi zata ibi
ruwan kamin

takai tulin cikin ruwa tuni wani irin bacci ya dauketa ba ita tatashiba sai yamma lis tatashi
dasaurinta

tadauko tulin dataga gefanta taibi ruwan cikin sauri tajuya xata tatafi taji kamar anriqe mata
kafa tawai wayo bataga kowaba

nantake tasa kuka dan tasan duk sadda tai irin wannan to ranar mai qwatarta gurin inna uwale
sai Allah kuma

tunda taji kafarta tariqe tasan ita da komawa gida sai anyi sallar magariba haka taita zama anan
har

aka kira sallah kana ta tashi tatafi lokacin data isa gida har anfara sallah
[3/8, 1:05 AM] +234 703 962 5239: 😭BAQAR IZAYA😭3


😘ANSHOLLY😘

Uwale nazaune wurin murhu tahassala wuta

kamar maida huwar kai ko inda innuwarta takema bata kallaba

to ita kantama tasan duk sadda tai irin wannan baqar izaya take gallaxa mata

shiyasa tana juye ruwan tatahu gurinta tadir kusa

kawai jitai tace kwanta kimiko man kafarki da sauri ta kwanta

tamiqa mata kafar dan tasaba dasalan cuta irinta inna uwale saidai

duk da tasaba tana tsoran yaukuma wace irin izaya tatana darmata tana cikin tunanin nan taji
wata

irin azaba tashiga daga cikin kafarta har cikin kanta wani irin ihu tasaki

dukda sunada taxara daga gidansu zuwa masallaci amma harcan saida sukaji wannan qara

liman da sauran mutane dama angama sallar sukayo gidan mlm iro danjin mike faruwa

kamin sukawo ankuma fasa wata qarar da sauri suka fada ciki ko jiran abasu ixinin shiga
basiba

Uwalece riqe da wuka jajjawur ahanninta taqara azamata akan kafa tana azamata tana
shedewa tasuma liman ne

yafara mgn haba uwale mi xakici jikin wannan yar yarinyar duka Hainan nawa take daxaki
taimata irin wannan baqar ixayar

yarinyar dabata wuce agoya taba uwale tadaga mashi hannu mlm dan Allah kada kataman

kasan mitaiman aikentanai tunda asuba rafi ibar ruwa tanacan tana baccin dana san

bazai zame mana alheriba duka rigarnan dan duk sadda hainan tai bacci nanda sati kajira

kaga abinda zai samu rigarnan kuma konsani baccinta ba alkairi bane

shiyasa nace kamin wani abu yasamemu ita xaifara samu dansu aljanninta insukaga anacis
guna mata sun barmu muhuta

daga liman har wa yanda suka shigo tare saida suka yabama uwale gani suke tayi abin arxiki
atunaninsu inhar ana musguna ma hainan dole abar masu rigarsu tahuta dan tunda aka haifeta
rugarsu take cikin tashin hankali

Liman yace ai uwale bansan haka bane cigaba daga inda kika tsaya dan baxan taba mance

wannan yarinyaba ranar sunanta mai dakina tamutu ranar da tacika shekara dana yamutu
ainibaima dace

nazo nacece taba kawai dan xuciyar musilinci amma yanxu ko kasheta zakiyi nagama magana

wani daga chan gefe yace wallahi dama kashetan akayi dama yafi mana kwanciyar hankali

hakadai suka juya sukatai kowa yana fadin albarkacin bakinshi



😘Ansholly😘
[3/8, 1:05 AM] +234 703 962 5239: 😭BAQAR IZAYA😭4




😘Ansholly😘






Ruwa inna uwale tadebo tawatsa mata afuska wata ajiyar zuciya Hainan

tasaki wadda dagaji bata dadi bane tai maza tatashi xaune

tana kallan inna uwale dan ubanki bari kallona shegiya

maiya toni kurwata tafi karfinki wallahi saida kicinye tawasu badai uwale ba

kuma kitashi ki maxa ga wankinan kiman cikin ladabi ta bude baki tana magana

tace dan Allah inna uwale kiyi haquri sai gobe nai maki bakiji yadda qafata takeman ciwo

aikamar jira take tarife baki taji duka ko ina ajikinta saida tai mata lilis da irin dorunar korar
rakummar da sike ta fiya da ita kiwo

kana tace kitashi kitafi kiman wankin kona qara maki mayaiya wace harta mahaifiyarta bata
bariba

haka taja jiki hartakai inda wankin yake kukanma bata iyawa dan banda zafin duka da zafin da
kafarta takeyi wata irin yunwa takeji dan yau satinta guda ko lumar tuwa batasa abakinta ba


hakadai tafara wankin cikin jiga tuwa wata tsawa taji abayanta kobata wai wayaba tasan inna
uwalece dan ubanki daga zaune zaki man wankin

dasauri hainan tatashi tsaye duk da kafarta namata azaba amma hakataita wankin harqafe
daya nadare

kowa nagidan yai bacci ahankali takejan qafarta hartaje cikin madahin gidan dan yinwa takeji
tamkar zata mutu

tacisa a ta iske tuwo kuma yanada yawa tasan uwale ta ajeshi nadimaman safe harta maida
zata rife sai wata zuciyar tace gwara kici

dan kinsan kokici kokar kici baxaki tsallake izayar uwale ba gwarama kisan laifi kikai mata
tazubo miya cikin tuwan tazauna duk yawanshi saida tacinye shi

kana tatashi taje tasha ruwa tadawo tazauna jitake kamarta yanke qafarta tayar sbd wani irin
radadi take mata haka taita kuka

har aka kira sallah asuba tanan zaune a inda yazame mata daki wani irin xaxxafan zazxabi
yarifeta sai rawar sanyi take
[3/8, 1:05 AM] +234 703 962 5239: 😭BAQAR IZAYA😭 5




😘Ansholly😘


Haka malam iro yazo yawuceta yatafi masallaci ko kallo bata isheshiba

itama tashi tayi daqel ta dauki tulu tana tafiya tana hada hanya dan batasu inna uwale

tazo ta isketa tasan dan banzan duka zata sha

tana fita gidan sarkin rugarsu tayi dan tasan shikade zai iya tai makonta

Shima bacikin gidan tashiga ba awajan gidan tatsaya dan matanshi sun hanata shiga

sunce duk ranar da taqara shigam masu gida saisun illatata tana nan zaune har aka fito
masallaci

dayake akwai hasken farin wata shiyasa yaga neta

Yace hainan mikike anan da asussuba haka tadago fuskarta daqel dumin ta gala baita iya gala
baita

wani bafa danshi yasa yadaukota ya ajiyeta acikin dakinshi kana yadauko wani magani yami
qama bafadan yace bata tasha

Ya dagata yabata maganin tasha kana yabashi wani yace ammshi kashafa mata aqafar saida
yagama duk umarnin da sarki yabashi kana yaja gefe yatsaya


Saida suka kwashe kusan minti talatin har gari yasoma haske

kana cikin ikon Allah xaxxabin yasauka kuma kafar tarage yimata zafi

Takalli sarkin tace ardo nagode murmushi kawai yai mata kana yace mikikaima uwale tai maki
wannan dukan

bata boye mashi komiba saida yayi danjim domin shikanshi yasan duk sadda hainan tai bacci

garinshi yana cikin matsala domin bata bacci daga shekara sai shekara to yanxu gashi saura
wata biyu tayi shekara goma

kenan wannan karin bazata ciki shekara goma ba abubuwa zasu faru dan bawai abu dayane ke
faruwa ba

Ita dai hainan zuba mashi ido tai tana kallanshi can dai yadago shima yakalleta yace kiyi haquri
hainan Allah zai saka maki

inda ita mahaifiyarkice aiba zatai maki hakaba

Hainan tace yauwa ardo dan Allah kabani lbrn ni wacece dan naji wasu suna cewa waini
nakashe mahaifiyata da kakanni na

dan Allah dagaske ardo taqare maganar tana kuka

ardo yakalleta cikin tausayi yace share hawayanki kinji hainan yanzu

zakisan koke wacece

*tuna baya*



😘ANSHOLLY😘

08136195038
[3/8, 1:05 AM] +234 703 962 5239: 😭BAQAR IZAYA😭 6




😘Ansholly😘


Kamar yadda kikasani rugarnan hade take da Fulani da buzaye

to haka take tun kaka da kakanni gidan mlm sule da malm amadu makwabtane kana kuma
abokaine

nasosai da sosai wanda duk rugarnan ansan yadda sukesan junansu har matansu haka suke

Yayinda malm sule yake ba fulatani shikuma mlm amadu buxune duk dare tare sukecin abinci

Yauma kamar kullin mlm sule ke sallama agidan mlm amadu da sauri yafito

Kayi haquri mlm sule kanata sallama ban amsaba wallahi

nagewaya bayan gidane yana maganar suka ida qarasawa gurin da suke xama

domin cin abinci A,a bakomi abokina kana suka faracin abincin saida suka gama suka wanko
hannunsu


Kana suka dawo suka zauna domin tattauna abinda yasha fesu mlm sulene yai gyaran murya

yafara mgn dama mlm amadu wani alfarma nake nema agurinka saidai yagyara xama

yace ina jinka mlm sule dama iro nake yima neman irin auran hadixa diyar wajanka

mlm amadu murmushi yai haba mlm sule dije yar kace kaike iko da ita inma wani kace xakaba
ba iro ba wallahi bazance komi ba

Dan dije ikon kace ballantana iro Allah dai yasa alkairi Amin inji mlm sule suduka akwai abinda
suke tunani dumin qa idar rugarnan indai maza dayawa sunasan yarinyan tu dule sai anyi shadi

tu lukacin harda dan wajena kesan dija kuma duk rugar nan ansan yafi kowa jarimta

gashi shi mlm sule antaba kashe mashi da a irin wannan shadin dama su biyune yaranshi to
yanxu saura iro anya zai iya wannan kasadar

sana tunda buxuwace saiyayi wasa da rakumi su duka sunyi zirfi cikin tunani

mlm amadu shiya katse shirun yace abokina nasan mikake tunani

Yace mixai hana da asuba inminje masallaci adaura auran kaga bawani shadin daza ai tunda
tazama matarshi

Mlm sule�kai amma abokina kakawo shawara wannan yayi Allah yabarmu tare nasan dai za
asha surutu arugarnan


ace munyi sar ranmu abinda ba ataba yiba kenan

Hmmm mlm sule inhar ana biyema mutane to subazasu fadi abin alkairiba kuda abin alkairi kayi

haka kumafa ne abokina to yanzu tashi muje mugayawa yan uwa dan sushirya

karsuce munyi gaban kanmu dan munga iyayanmu basu raye

A,a Mlm sule ba inda xamu kasan daga yan uwanka har yan uwana basanmu sukeba

zasu iya zuwa sufa dama sarki ace dole sai anyi wannan shadin gara miyi shirinmu da asubar
sunji

hakadai suka aje magana saida asubar kowa zaiji da dauri auran kowa

yashiga gidanshi cikin farin ciki iro dayaji abinda baffanshi yace yayi murna sosai dan dama
yanasan

dija sosai gani yake kamar tafi ajinshi domin jail dan sarkin rugarsu yana santa

Hakadai yakwanta cikin farin ciki yayinda dija koda mlm amadu yafada mata abinda

suka yanke shida abokinshi bata nuna wani farin cikiba kuma bata nuna bakin cikiba

yayinda iyayanta suka dauka kunyace takeji



*Asuba*



*Ansholly*
*08136195038*
[3/8, 1:05 AM] +234 703 962 5239: 😭BAQAR IZAYA😭 7




😘Ansholly😘








Asuba nayi iro yafito cikin sauri yashiga bayi yayi wanka

yafito yayi alwalla lokacin baffanshi yafito shima zaiyi alwalla kallan iro kawai yayi yagirgiza kai

Yayinda iro akashege daki akashafa mai yadauko shaddarshi tasallah yasa sai wani washe baki
yake waishi ango

Chan naga yan group din Ansholly novels sunata lekenshi wai inama yace yana sansu dan
sunga yasha kwalliya to qwalelanko loll

Haka iro yafito sai washe baki yake kamar saban kamun nan lol

tun kamin mutane suzo su malam sule suka samu liman sukaimai bayani amma yaki amin cewa

saida mlm amadu yabashi raqomi daya kana ya amince domin mlm amadu mai kudin rugar nan
ne domin kuni danake sarki zamanin dayana

raye yafini raqumma nisa bakusa shiyasa yan garinnan suke girma mashi yayinda dangin
ubanshi dana uwarshi suka tsaneshi

dan dukiyar da mahaifanshi suka mutu suka bar mashi

shikuma Allah baibashi dana mijiba yarshi daya mace itace dije

hakadai liman ya yadda dan akwaishi akwai san kudi bayan angama sallah liman yai sanarwar
daurin auran

Iro da dije cikin ikon Allah cikinmu ba wanda yai musu kamar anrife mana baki har aka daura
auran

Kana tsegwamin mutane yafara tashi sudai su mlm amadu hakuri kawai sukeba mutane duk
wanda yace basu kyautaba saisuce yayi hakuri

to andaura aure ba yadda za ace dole awarware shi saidai surutun yayinda yan uwan mlm sule
dana mlm amadu sukace sunfidda hannunsu

daga kan almuransu dan sunga basu daukesu kan iyayeba inda iyayansu nanan zasuqi gaya
masu

sudai haquri suketa basu nan suka gama surutansu suka qara gaba


da mlm sule yace abari amarya tatare jibi amma mlm amadu yace ranar zata tare tunda bawani
abu zatai mashi cikin gida ba

Kuma tanada komi nakayan daki dan kayan dakin da aka kaima dije irin nacikin yan borni ne
dan mlm amadu yanada

aboki cikin borni shiyaba kudin yaje yasawo mai kaya masu kyau wanda duk yashiga cikin dakin
dije bayasan fitowa

dan gurin kayan dakin dije mukasan miye wannan abun mai laushi katifa yake nifi

hainan tace dama ardo wannan abin mai laushi nadakin inna uwale na innata ne tabbas shine
hainan

dan tunda aka sawowa marigayiya dije har yanxu ba wanda aka kara sawuwa irinta

hakadai amarya tatare gidan mijinta suna zaman lfy dan hadixa bata da matsala yayinda jail
dana har rishin lfy yasha saboda

rashin dije dan dije ko kyanta zaisa asota dan lokacin yan matan cinsu itace tarike kambon
kyaikyawa dan duk cikin rugar saiya zammana ba wanda yakama qafarta agurin kyau



hakadai amarya da ango sukaita rayuwarsu cikin mutunta juna dije nada shekara biyu Allah
yabata ciki karkiso kiga murna wurin wa yannan bayin Allah yayinda ranar da yan gari sukasan
da cikin aranar

gonar makwabcinko tayi gobara takone kurmus kuma alokacin baza ace ga abinda ya haddasa
gobarar ba kinsan kauye da canfi

to daga nan wasu suka fara yan magan ganu dan alokacin da abin yafaru ana cikin fadin
mahaifiyarki tanada ciki kawai sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0