Showing 27001 words to 30000 words out of 54422 words

Chapter 10 - Bakin Rijiya Book Compelet Billy Galadanci

02 Aug 2026

963

ga kowa zaune har yaa shaam jikinta ya mata sanyi,gaba ki d'aya setaji wani
iri,zama tayi yaukam ma akasan carpet ta gayar da kowa,kallonta daddy yayi yace

"Hafsat ina fatan kin san cewar mu iyayenki ne kuma mun isa mu sakaki komai a yanda muke
so muke kuma ganin ya dace?" kallon su tayi d'aya bayan d'aya sannan ta sauke idanta akan
yaa shaam dayake ta faman murmurshi a hankali hawayenda suka taru mata tun farko suka
silalo,ta gyad'a mar kai alamar gamsuwa da jawabinsa sannan yaci gaba
"kuma kinsan cewar dukda muke iyaye a wurinku muma muna da iyayen dasuke sakamu abu
adole koda bamaso se munyi shi?" nanma d'aga masa kai kurun tayi wannan lokacin kam tana
kuka sosai,ganin yaa shaam na murmushi ta gano da babbar matsala,daddy yaci gaba

"Innah ce da kanta tayi mana umarni akan lallai mu d'aura aurenki da shammaz nanda wata
d'aya me zuwa,kuma idan d'ayanmu ya sauya wannan maganar ko bayan ranta bata yafe masa
ba" qirjinta ya dad'a dokawa fiye da da,ta d'ago cikeda razani ta kalleshi,idonta ya kada yayi jajir
yanzu kam tama kasa kukan se quna da zuciyarta keyi,miqewa tayi ranta a b'ace ta qarewa
kowa kallo sannan ta kalli Abba haris tace cikin wata murya me d'aci wacce basu santa da ita
ba

"Abba na da gaske wai Innanku ne ta fad'a haka ba shiri bane wannan,na tabbatar kai kadaine
zaka sanarmun zallar gaskiya" wasu yawu ya had'aya dak'yar masu d'acin gaske sannan yace
dak'yar

"Inna ce ta bada umarnin nan jiya hafsat" hijabinta ta gyarawa zama sannan tace " To yayi" Ta
juya da gudu zuwa waje batare da tasan me yake damunta ba ko ina zataje ba,daddy da Abba
haris ne suka bi bayanta,da gudunta suma haka a haka tafito daga gate d'in gidan tana kawowa
kuwa wata motar na dannowa da gudun fanfalaqi atake tayi mata ebar karan
mahaukaciya.......dafe kai sukayi dukkansu bame abunyi haka aka cillata acikin drainage dake
gefen titin,abbah haris na kuka kamar wani yaro yaje ya fada ya cirota,sam babu alamun
numfashi a tattare ita,ta sume mamallakin motar ma daya kasance matashin saurayi dan gayu
fitowa yayi ya taya abba haris daukarta suka saka ta mota suka fada atare yaja da karfin gaske
sukayi gaba,anan suka bar abba a tsaya ya kasa koda motsi sabida rudu,dakyar ya iya komawa
ciki ya kallesu yace

"Bana tunanin hafsat ,
Zata tashi,koda kuwa ta tashin bana tsammanin mata ingantacciyar rayuwa a yanda mota tayi
mata wannan eban karan mahaukaciya ta cillata a gota" momy ce ta riga kowa miqewa jin
kalamansa ta dage qirji "A ina wannan ya faru Alhj?" kallonta yayi da rinannun idanunsa yace

"A kofar gida yanzu data fita da gudu,ina jiye mata idan ba ajali bane ya fitar da ita" zarewa
momy tayi tayi waje da gudu shi kuma ya bita, dak'yar ya samu kanta tazo aka dunguma mota

bayan sun kira abba ya sanar musu suna asibitin uduth wurin dr. Say.......

Say yana zaune a office abba haris ya shigo masaa birkice,dakyar ya iya sanar masa mota ta
kad'e hafsa tana waje,ai banke abban yayi ya fito da gudu,Trauma suka wuce kai tsaye da
ita,babban tashin hankalin say be wuce ganin pause nata yayi qasa ba sosai,sannan gashi bata
numfashi daidai abu mafi ban tsoro shine jininta dakeyin qasa sosai amaimakon ya hau,yaukam
kasa yin komai yayi ya janyewa wasu likitocin suyi,har yamma suna kanta sedai ba sa'a,Dr.
Shuraim ne yafito ya sameshi har iffice shida abba haris da daddy,suna ganin ya shigo suka
tashi tsaye,kai tsaye wurin sayyed ya nufa ya dafa kafad'arshi,hannun nashi say yafara kallo
sannan ya kalleshi da kyau,yace kafin shuraim yace wani abun

"Dr. Shuraim karkace dani abunda nake tsammani?" kallonshi shuraim yayi cikeda tausaya
wa,duk sunsan hafsat itace xe aura kuma yana matukar santa yace

"To zaka ja da ikon Allah ne sayyeed?" kafin wani yace wani abun say ya sulale wurin a sume....

Mom Nua'iym
[2/7, 9:14 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

21

Taimakon gaggawa suka bashi atake ya farfad'o,kallonshi Dr. D'in yayi yace "Haba sayyeed da
kanka en uwanta kuma suce mana me?" kallon mamaki yake masa sannan yace

"Allah yasanya mafarki nakeyi" murmushi Dr. d'in yayi yace

"Ya zakayi da ikon Allah akanta to? Arziqinmu d'aya ma karayar iya hannu ne,se buguwa datayi
aka,wanda wannan shine yake san bamu matsala sabida dama akwai wannan matsalar
damuwa na d'aya idanta" sauke ajiyar zuciya yayi sannan yace "Indai da ranta komai yazo
mana da sauqi ai,indai inada rai da yardar Allah da izininsa seta samu lapiya" ahaka suka
dunguma dunkansu dakin da take.......tunda hafsat taji likita awa su daddy bayanin cewar
idantane suke tunani adawo baya kuma idan ya samu matsala lallai wannan karon gyaruwanshi
se Allah,amma dai bazasukai karshen maganar ba seta farfad'o idan har bata gani da matsala

idan kuma tana ganin komai to wannan daidaine,hankalinta ne ya tashi amna bata nuna ta farka
ba hasalima ko motsin kirki batayi ba daga kwanciyar datake,har suka fita aka barta ita kadai,da
sauri ta bud'e idon nata tana ganin hasken fitila da komai sannan ta sauke ajiyar zuciya had'e
da tunano abinda ya faru,dukda tanajin azabar d'aurin da aka yiwa hannunta seta samu kanta
da murmushi,ita kadai tasan ma'anar sa kuwa........

Washe gari hafsa ta farka amma qememe tanuna bata gani,wannan abun ya tashi hankalin
sayyeed musamman dayake ya sani yanzu kam da matsala tunda shine na biyu,agaban su
daddy sanda yayi kuka sosai yana me mata adu'a,shaam kuwa koda Dr. Shuraim yamasa
bayani kasa cewa komai yayi gaba ki daya jikinsa ya masa sanyi,dana sanin abubuwa da dama
ya farayi ciki kuwa hadda zuwa ya ziyarci Innah,yana ganin dayabi abun a hankali da duk haka
bata zo ta faru ba,jan jikinsa yayi zuwa kofar dakin da hafsa take ciki,a hankali ya tura ya shiga
ganin ba kowa ita kuma tamkar me bacci ya sanya ya matsa kusa da ita ya kurawa fuskarta ido
dayake da tabbacin lallai dabeyi yunkurin tarwatsa farin cikinta ba da duk hakan bata faru
ba,da fuskarta bata kumbura har haka ba,da yanzu tana gani yanda kowa ke gani da yanzu
hannunta be karye ba lapiyanshi qalau,da yanzu bata kwance a wannan asibitin, dafe kanshi
yayi ya furta a sarati cikin muryar kuka

"Mesa arayuwa ni shammaz na cika san kaina da yawa? Mesa zan wulaqanta jinina kuma
yarinyar data zab'i zama dani ta sadaukar da farin cikinta akaina? Mesa zan sakaki a had'ari
hafsat? Mesa tunda kika fara girma kika san meye so kika fara dani nake kuma kan wulaqanta
miki rayuwa? Tunda kikace kina sona nake qasaki ta hanyoyi daban daban,Allah kuwan Allah
ze barni kuwa? Zan iya jin dadin rayuwa bayan haqqinki na saman kaina?" fashewa yayi da
kuka awurin cikeda ban tausayi sam sam bayasan abunda ze tashi hankalin hafsat yanzu,ita
kuwa duk wani abinda yaje fada a kunnenta yake fad'a sedai tana d'aukar kalamanshi cikeda
yaudara mara misaltuwa,sam bata yarda dashi musamman a wannan gab'ar data nemi san
datake msa ta rasa gaba d'aya........

Uncle sayyeed ne yazo dakinta da dare ba kowa se ita kad'ai,ta rufe idonta ruf tamkar me
bacci zama yayi a kusa da ita ya kura mata ido ba tare da yayi magana ba,taji kamshin
turarensa wannan ya sanya ta bud'e idanta a hankali,tabbatarwa kanta tayi da cewar shi
kadaine ya sanya ta sauke masa su,cikeda tsoro yankalleta dakyau murmushi ta sakar masa
tace

"Uncle baby,wannan ita kad'aice hanyar dazanbi in raba kaina da shammaz,na tabbatar a
yanda nake nakasasshiya baze aureni ba,nakuma sn bakada labarin cewar Innah ta sokoto ta
rantse sena auri shammaz kota tsinewa sundaddy, banje mota ya kadeni da gangan ba,amma
jin cewar idona idan na farfado yana a rufe baze taba budewa ba ya sanya naji gaba daya na
samu mafita,karka sanar da kowa se bayan aure na dakai" murmushi yayi yace a sarari

"Alhamdulillah,amma hafsat kya baiwa kanki wahala duk akaina? ,
Zama a matsayin makauniya anya ba wahalar da kanki bane" murmushi ta masa

"Uncle sayyeed banida burin daya wuce na ganni a tare dakai,babu abu mafi soyuwa agarareni
daya wuce na zamto mata agareka,babu abu mafi bani kwanciyar hankali illah in ganni kusa
dakai kusanci mafi dad'i acikin kusance kusance,dan Allah ka tayani cimma wannan burin
nawa" murmushi ya sakar mata yace
"Babu damuwa Babyn ubcle say,Allah ya baki lapiya amma kin kware a pretending" dariya tayi
sannan tace

"Kaina yana masifar yimun ciwo,da kuma hannun nan,ni samosa zanci" dariya ya kwashe dashi
jin excuse nata nasan cin samosa yace

"Madam ina zan samo miki samosa yanzu?" turo bakin tayi

"Ni koma a inane" To naji barinje season seven su dama 24hrs service sukeyi" bata ce dashi
komai ba ya miqe yayi waje.....

Shammaz kuwa ya kasa bacci,ga haleema zaune a kusa dashi amma sam yama manta
danita,ita kuwa se hotuna take faman dauka tana sakawa a snap gashi batada maraba da
tsirarara,kallonshi ta d'anyi a kaikaice tace dashi

"Shaam lapiya nka kuwa ?" dan waigowa yayi ta gefenta ya marairaice

"Hafsat ne tayi accident shekarnjiya fa,kuma idonta ya kuma rufewa gashi babu chance yanzu
sabida shine na biyu,ya kamata kije ki duba ta" tsaki taja

"Yo sabida nakasasshiya ta qara naqashewa shine kwana biyu duk ka canja,Allah ma yasanya
ta zama gurguwa a had'a mata double" kallon mamaki ya mata sannan kamar ya maketa yace

"Tsabar ba Allah a ranki zakiwa yar uwata kuma jinina mugun fata har haka?"

"mtsww aikin banza,ai inada labarin accident din biris dai na maka wai kare ya taka sisi,in
banda rainin wayau akan kanaso ka auri wannan karuwar zataje ta kara mota ya kadeta,kaji na
rantse ba inda zani,kuma ka sani wlhu idan kace zakamun kishiya sena yanka tsuliyar uban
kowa ma ya huta" tana kaiwa nan tayi waje,dama ya zama mujin hajiya se shiru yayi,shi yanzu
damuwarsa lapiyar hafsat......

Muhammad Jalalludden Auwal,shine mutumin daya kade hafsat shekarnjiya,yaune kuma
yake shirin zuwa lapiyarta domin tunda ya baro asibiti be koma ba sabida ayyuka sun sha
kanshi,sanye yake da babbar rigar farar shadda dinkin sufani yasha kyau,gabaki dayanshi
komai na jikinsa fari ne kaikace shirin zuwa qabari yakeyi, hatta hanky daya tiqe fari ne,agogon
hannunsa ma haka haka ya taka yace asibiti,hadaddiyar mercedese benz dinsa ya parka a
harabar asibitin ya fito yana tafiya irin ta manyan mutane dududu shekarunsa bazasu wuce 37
ba aduniya amma gabaki daya manyance ya masa yawa,ga uban kwarjini daya keda koda ya

fito acikin motar kowa qura masa ido yayi,a yangace ya isa kofar dakin dayake tabbacin
nanne,a hankali ya tura kofar ya shiga da sallamar sa,momy ce zaune kusa da ita tana ganinsa
ta miqe suka gaisa sedai bata shaidasa ba,sabidanita basu hadu ba ranar,murmushi yayi yace

"Mama nine wanda na kade hafsa,nazone in duba lapiyarta sabida gobe zan bar qasar,kuyi
hakuri banzoba kwana biyu ayyukane suka sha kaina" kallonsa hafsat tayi da qasan idonta ta
dauke kanta lokaci daya,gaisawa sukayi da mama sannan ta masa godiya sosai

"Mama yanzu menene matsalar hafsat?" sadda kanta tayi tashiga rero masa tundaga matsalar
farko data samu har zuwa wannan akan rashin ido,taqarashe sanar dashi cikin kuka sosai,
girgiza kanshi yayi cikeda damuwa yace bayan ya zare madubin dake fuskarsa ya shafi idonsa

"Bazan yadda cewar idon baze bude ba sedai idan basu san kan aikinsu ba,akwai likitana dake
a china,a can zamu da ita,idan mahaifanta zasu yarda zan dauki nauyin komai na aikin da
tafiyar" shiru momy tayi hafsa ce tace

"Niba inda zani,ku barni anan kawai Allah ze bani lapiya" kallonta yayi yace cikin fada

"Hafsat idan kika kuma saka bakinki amaganar manya sena sassa b'a miki wlhy" tsoronsa ne ya
darsu aranta lokaci daya,tanajin tsoron ayi tafiyar aje garin gyara ayi barna,tunda lapiya ta
qalau,amma dai bata kuma cewa komai ba" sallama ya musu akan zece wurin su daddy da
kanshi,yana fito wa ya hadu da shammaz,kallon kallo suka tsaya yiwa juna sannan ba tare da
sunwa juna magana ba suka raba kowa ya wuce


Hmmmmm toophaa ga oga muhammad ya iso

Mom Nu'aiym
[2/8, 8:47 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

22

Tunda hafsat taji zancen zuwa china se tafara tsoron tafiyar,lallai idan har ta kuskura akayi

tafiyar nan tofa se an ce za'a yi mata aikin,kuma lallai garin neman gira rashin idone ze biyo
baya,tana kwance tayi shiru uncle say ya turo kofar dakin ya shigo da sallamar sa,yunkurawa
tayi ta tashi zaune sabida yanayin hannunta da har yanzu da sauransa ta tashi zaune,kura mata
ido yayi yana murmushi sun dad'e sosai suna hirar su ta masoya kan ya mata sallama harya kai
kofa ya juyo ya kalleta,murmushi ta sakar masa tace

"Uncle say yau nakula ka nacewa kallona lafiya dai?" girgiza mata kanshi yayi "Ai dama can
kinsan ni sam bana gajiyawa da kallon kyakyawar fuskar nan taki" lumshe idanta tayi cikin
sanyin murya tace "Nima haka baby say" batare dayayi magana ba ya juya sanye da murmushi
a fuskarsa, gabaki d'aya wani tsoro ne yakeji da yawaitar fad'uwar gaba yarasa dalili seyakeji
gabaki daya duniyar tana juya masa....


Shaam zaune yana dannan wayanshi a farfajiyar shan iska dake cikin gidansa haleemah tazo
ta sameshi,cikeda rashin mutunci tace dashi

"Wai kaikam me kake nufi dani tunda qanwar ka ta qara zama naqashashiya kake wani shamun
mur sekace nice nan na nakasata?" dagowa yayi ya kalleta yace

"Me kuma ya kawo maganar hafsat anan?kuma ban sanar miki cewar kidena ce mata
naqasashiya ba?" tsaki taja

"Meye laifina danna kirata da sunan dayafi dacewa da ita? Wlhy akan hafsat zan baka mamaki"

"Kya daiji dashi,amma ki sani wlhy sena aureta a nakashen,ni tazo ma ta haifamun yara tunda
kin zama juya,narasa me kika dauki duniya dabazaki haihu ba hakanan,shasha kawai me bakin
hali" a fusace ta furta

"Kafi kowa sanin cewar niba juya bace tunda na haifa maka ya qanwarka ta kashe,kuma ka sani
wlhy koba hafsa ba indai banice zan haifa maka yara ba kaida haihuwa har gaban abada kuwa"
tsaki yaja ya miqe yabarta gun a tsaye......

Tunda haleema taji zancen auren hafsat da say zeyi seta tashi hankalinta ta sani sarai boka
ya sanar mata ba ita ba haihuwa har abada sannan kuma gashi yanzu sam asiri ya dena tasiri
akan sa,bokansu ya sanar musu sun sanar mata cewar lallai ya riqe addininsa yafi karfinsu ko
kusantar sa ma gaba daya bazasu iyaba, wurin ummansu taje ta zayyane mata komai atake
kuwa aka shirya cewan ayi airin akan hafsat gaba daya tunda itace banza.....hmmmmm

Say yana zaune tare da hafsat suna hira muhammad ya shigo cikeda taqama yaud'inma
acikin shigarsa ta shadda fara amma ba babbar riga bace, yau dinkine dai na zamani me kyau
komai nasa fari,hannu ya miqa masa suka gaisa sannan ya mayarda dubansa akan hafsat da
alokaci daya qirjinta ya soma dokawa

"Hafsat ya jikin ki?" kallon sa tayi tace

"Naji sauqi Alhamdulillah" shiru sukayi dukansu su uku can muhammad yace "Ke baki iya
gaisuwa bane,ko bakisan girman manya bane?" idon tane ya ciciko sannan tace

"Kayi hakuri yaa muhammad" dan guntun tsaki yaja sannan yace

"Mesa zakiyi karyan bakya gani kuma bayan sarai idanki lapiyanshi qalau,bayan yanzu
gashinan kina kallo na kuma kallo daya na miki na tabbatar kina gani kema kuma kina kallo na
ido cikin ido duk sanda nayi magana" shiru tayi yayinda say ya miqe tsaye yace

"Amma yallabai anya bakayi shishigi da yawa ba kuwa,baka ganin cewar mu doctors mune
mukeda haqqin komai nata bawai kaiba,kuma mun tabbatar cewar idan nata bashida lapiya kai
miye naka aciki? Kuma idan taimakonta zakayi mu bawai mun kasa bane ka barshi kawai mune
family nata zamu mata komai ma har fita wajen" shiru ne ya ratsa wurin dukkansu sun bata
dakiku suna kallon juna kafin muhammad yace

"mesa arayuwa zaka kalli girma na kace zaka kirb'a mun k'arya,zanyi magana a d'aga licence
dinka na zama likita idan dai har tsabar hauka wannan idan ne zaka ce baya gani" jin ankira
hauka ya sanya say ya dago da fuskarsa gaba daya cikeda fusata

"Kai waye? Mekake taqama dashi? Me kuma kakejin ka isa kayi da zaka kalli tsabar idona kace
dani mahaukaci,dakake iqirarin cewar zaka sanya akarbe license dina mesa kai bazaka qwace
ba idan ka isa,tunda nake ganin mahaukata bantaba ganin mara hankali irin kaba,tayaya zaka
kalli idan mutum kace masa mahaukaci beside waye ma ya baka damar yi mana iko anan?"
wani murmushin qasaita yayi sannan ya shafi gemunsa yace

"Ba license d'inka ba har abu mafi muhimmanci arayuwarka zan iya kwace wa shine
rayuwarka,kuma wlhy kaf fadin Nigeria ba wanda ya isa yamun komai,kuma zaka gani wlhy,ke
kuma karna dawo asibitin baki gayawa doctors masu hankali kina gani dakyau ba" yana gama
fad'ar hakan ya juya ya fita hafsat ta kasa koda motsi dakyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0