Showing 36001 words to 39000 words out of 54422 words

Chapter 13 - Bakin Rijiya Book Compelet Billy Galadanci

02 Aug 2026

939

tayi taso tace dashi ai su daddy zasu siya mata kayan daki,amma tunawa
da tayi yace bayasan gaddama ya sanya taja bakinta ta guntse....
Abba haris bayan ya gama jin bayanin muhammad tare dajin cewar wannan tsarin sane kana
yanaso ma aqara sati biyu akan ranar daurin auren kasancewar bayaso a samo matsala tunda
tafiya na Allah ne,be masa gaddama ba sedai yace sedai suyi tafiyar tare da babbar Aunty
d'insu Aunty surayya,sabida zamanto warsu mata qananun yara,zuwan na surayya kuwa shine
ze dauki nauyin sa,idan har mijinta ya Aminta,kara kallon abban yayi yace

"Abba zancen kaya gida kuma,dan Allah karkuga kamar na raina iyawar ku kawai dai tsarinane
nine nake siyan kayan gidana da komai,matana ta farko ma nina mata, sabida haka hafsat ma
na riga na siya komai,kayan kitchen ne kawai bana siya,amma komai nine nakeyi" nisawa Abba
yayi
"Bazamu hanaka yiwa matarka alkhairi ba,sedai muma haqqin mune muyiwa hafsat, gyaran
daki sabida haka zamu bata kud'inta tsaba,shawarar yanda zatayi dasu kuwa ze shiga tsakanin
kai da ita ne,sabida kaine mijinta" Godiya yayi sosai sannan yamasa sallama,waya yawa hafsat
tafito suka kama hanyar zuwa ganin kaya,kallonta yayi sosai ya furta
"Hafsat karki qara yimun karya daga yau,a ina kika samu cajin yanzu? Kuma naga wayar kusan
full ma? Bakida labarin karya ba kyau,kuma batada kad'an?" sosai taji kunya wannan ya sanya
ta sauke kanta qasa tace "Insha Allah bazan kara ba kayi hakuri" murmushi yayi

"Mesa kika kashe wayar ki?" murya a kasa tace

"Nima dai yau sena tashi banso a kirani,shiyasa kawai amma ba komai" be kara cewa komai ba
ita mad'in shiru tayi sanda suka isa wani qayataccen gida me kyawun gaske,tun a gaban gidan
zakaga had'uwarsa da qayatuwarsa ba karya...Gate din automatic ne wannan ya sanya ya
bud'e kanshi yana ganin dosowar motar, a wani farfajiyar ajiye motoci ya ajiye motarsa wanda
had'uwars ba'a ma maganarta, kallon ta yayi yace "Bismillah muje ciki" Batayi musu ba kawai ta
bishi suka wuce,ta bayanshi take se kallon cikar halittarsa takeyi yanayin halinsa yanayin
maganarsa da uban ikon sa,wata kofa taga ya sakawa wani card lokaci d'aya ta wangale,kai
tsaye ciki suka shiga tun a parlor ta raina dukiyar datake taqamar wai suna da ita,gabaki dayan
parlor din komai na ciki gold ne se daukar ido yakeyi,dakuna guda biyar ne acikin gidan kuma
flate ne me masifar kyau se paluka guda uku da fankacecen ktchn wanda ya gama hadewa da
tsadaddiyar carbinet,gas cooker ne kawai aciki se freezer ta kwance da double door,a bed
rooms din kuwa duka english bed's ne aciki,dayan dakin red and white,dayan blue wanda shi
kuma akwai parlor aciki da lubby me kyau ga coffee chairs a walk way na zuwa barin,kuma
komai light blue ne da white,dayan dakin purple dayan kuma pink $ white se thee green wanda
aciki duk shine yafi burgeta,ko wane daki da toilet nashi,wanda a iya Bathrooms din idan aka
barka zaka kwana kana kallon abubuwan ban mamaki,gidan ya hadu over bayan sun dawo

parlor ne ya kalleta yace

"Hafsatu manga,sanar dani tsakani da Allah ina kike buqatar a sauya miki?inda bakyso,ma'ana
abun be miki ba?" kallon shi ta d'anyi sannan tace

"Ni ko ina ma yamun ko ince yamun yawa ma,wancen corridor dinne kawai za'a saka mun
console,se dining shelf dababu awurin dining,shima kuma zanwa daddy magana,nagode sosai
Allah ya qara girma yakuma kara budi,Allah jikan iyaye kuma ya biya bukatocinka na alkhairi"
har cikin ranshi yaji dad'in adu'arta tunawa yayi da Zainab wacce sam bata taba cewa dashi ci
kanka ba duk girman alkhairin daze mata kuwa,murmushi ya sakar mata yace

"Kinsan ni kwangila na bayar bansan wai ya kamata su zauna awurin ba,yanzu kawai muje
shops asiya choice naki,ba wani su daddy" kallonshi tayi
"To ai yaa muham......shhhhhh yafada hade da daura hannunsa asaman lips nashi,tunawa tayi
da gargad'insa na rashin son gaddama ya sanya tayi gum da bakin nata,koda suka fito kasa
hakura tayi dama hafsa akwai surutu tace dashi

"Yaa muhammad gidannan yayi kyau sosai wlhy" Bece da ita komai ba kurun murmushi ya
mata......

*Bayan kwana uku*

Hakan kuwa Akayi,da hafsat da khairii da Aunty surayya suka dauki hanyar dubai a ranar wata
wednesday,har suka isa suka kwana suna mamakin hali irin na muhammad,be basu ko sisin
siyayyar lefenba,illah kawai tunkan su isa ya sanar dasu akwai driver daze kaisu masauki daga
airport,kuma suna cin abincin wurin wanda menu kawai ake kawo wa su selecting,haushi duk
ya gama kama hafsat kusamman ya da Aunty surayyah ke faman masifa akan ya rainawa
mutane hankali,ko cewa akayi dashi basuda aikin yi,Wayan hafsa ne tayi qara tana dubawa
taga number dinshi,a dake ta daga wayar sabida ba shakka ta shaqa yau kam,yace da ita

"Hafsat ki fito idan kina masauki ina reception na hotel din" da mamaki ta kalli Aunty surayya
dake gefenta tana uban mita,sannan tace dashi "A dubai din?" tsaki yaja yace

"Noo a india,danla malama kizo ina reception ma wurin nace dake ko mun fara wasan banza ne
haka?" cikin jin zafin gwasaletan da yayi tace "Kayi hakuri ganinan zuwa" kallonta surayya ta

"Keda waye kuma Ina zakije?"

"Muhammad ne wai yana wajen reception ashe yazo,kuma shi da number shi yake amfani
niban sani ba" kallon ta tayi "Au dama shima zezo kika barni ina surfa mar ashar?"

"wlhy Aunty bansan zezo ba,ni kawai zancen dan rakiya yamun" jinjina kai Aunty tayi

"Wannan shegen muhammad din anyi miskilin masifa,ko wa yakewa iya shegen oho,jeki kiji"
batace komai ba ta zari dan mitsitin mayafi tafito ga rigar irin straight gown din nan ne na roba
ya kameta over, tun daga nesa tana ganin fuskarsa tasan akwai magana a d'an tsorace ta
karaso wurin da yake,zama tayi kusa dashi a kujerar da yake tace
"Sannu da zuwa yaa muhammad ya hanya?" kallonta yayi fuskarnan a daure yace "Banasan ya
hanyar ki sabida jirgi daya muka zo daku ai,sannan wlhy mintuna goma na baki ki sako sutura
dan wannan bakida banbanci tsirara,idan kuma na kuma ganinki da makaman ciyar wannan
shigan wlhy sena sassab'a miki,sekace ba 'yar musulmi ba" kallonshi tayi se a lokacin ta tuna
yanayinta,waifa ita tayi shigar ne a zuwan tazo garin farar fata kartayi qauyanci, jiki a mace ta
miqe,zuwa tayi ta cire kayan ta sako abaya baqa har qasa tayi talha ta fito,surayya na ganin
yanayinta tasan shigarta yayiwa masifa amma dai vata dameta da tambaya ba,koda tazo baya
nan,wayarta ta daga takirashi amma be dauka ba,anan ta zauna tafi 30 mnt be dawo ba ta qara
wayar tashi gaba daya ma tajita a kashe,gwiwa a sace ta koma dakin tace da Aunty surayya
wai yace gobe zasuyi magana,kallo daya surayya ta mata kuwa ta fahimci da babbar
matsala.......

Washe gari tun asuba ta koma parlor tayi kiransa a waya,yana kallonta harta tsinke be daga
ba, kusan 3 msd col,kawai seta fara hawaye tama rasa dalilin daya sanya take damuwa dashi
zuciyarta sam batayi adalciba,data saka masa wannan tsoron na muhammad,tana cikin wannan
tunanin taji qarar shigowar message
"Room no 10,2nd floor" shine abinda ya aiko mata sarai tabgane nufinsa ta sameshi
acan,miqewa tayi ta saka hijab dinta tayi hanyar daze sadata da wurin....knockin tayi yazo ya
bude fuskarsa a hade,gaidashi tayi sannan ya janye mata ta shige a daya daga cikin kujerun
parlor din ta zauna,ta qura masa ido,shima din ita yake kallo,yaukam seda tagaji da kallon nashi
ido cikin ido sannan tace "Kayi hakuri bazan qaraba inshaa Allah" amaimakon ya baiwa
maganarta muhimmanci se cewa yayi da ita "Meya faru kike kirana daga yin sallan asuba?"
tama rasa mezata ce masa,se kawai ta miqe "zan koma bacci zanyi" tazaci ze dakatar da ita
amma bece mata komai ba harta fice,a ranta kuwa taji zafin sa sosai....

*Nigeria*

Sun dawo lapiya dauke da lefe da ban mamaki, har masifa su daddy sukayi,amma surayya
tace dasu tamasa magana yace hafsa matar sace,babu kuwa wanda ze qayyade masa yawan
suturun dayake buqatar wadata su da ita,kuma ya jibgo dogwayen riguna da qananun kaya
over.......Aikam rana daya akayi daurin auren muhammad da hafsat,se kuma Shammaz da
maryam,kuma aranar aka kai amaren biyu,wanda sam koda ma akayi auren hajia halima
batada labari tana wurin gantalen ta dubai,acewarta taje saro kaya shikuwa da gayya ya
ganta,yan uwanta kuwa dasuka ga pictures na ebar hankali da ba indiya se hankalinsu ya
mugun tashi,amma sam basu sanar mata wai shaam yayi sabuwar amarya ba.......

Hafsat kuwa tunda yan kai Amarya suka watse wuraren karfe goma na dare seta soma jin

tsoron zaman gidan ita kadai, shi kuwa be leqo bama se sha daya da rabi, Abinci ya kawo mata
sannan ya sanya hannu ya yane mayafin dake jikinta ya ajiye gefe ya kalleta, "Kina bazawara
wani kunya zakiji,zaki wani lullub'e fuska" sosai maganar sa ya doki qirjinta amma bata nuna
masa komai ba kurun dai murmushi tayi masa,ganin haka ya sanya yace "Kici abinci kazane da
drinks ga youghurt da ice cream idan zaki sha" kallon su tayi tace "Gaskia Alhamdulillah na
koshi,sedai zuwa safiya" miqewa yayi be wani damuba,kizo ki kulle kofofin gidan ni zan tafi
seda safe" ko motsawa batayi ba daga inda take sabida mamakin daya bata,to gidan uban wa
ze kwana?" ta tambayi kanta,ganin fa tsorone ze hallakata ya sanya harya kai parlor ta rugo ta
riqe masa hannu,da mamaki ya kalleta tace dashi

"Yaa muhammad zan bika dan Allah" juyowa yayi yabfuskance ta gaba daya "Ina zaki bini
hafsat?"

"Inda zakaje mana"

"Ba inda zani fa, gidan zainab zanje na kwana,kishiyarki" tafi minti uku tana kallanshi, juyawa
yayi ze fita ta riqe masa hannu again "Bazan iya kwana anan ni kadai ba,tsoro nakeji" murmushi
yayi

"Ni ban aureki danna tayaki kwana ba hajiya,ko mun rubuta haka acikin agreement namu?"
gaba ki daya tsoro ne ya taso mata ta kalleshi sosai tace cikin dakiya idanta yayi ja sosai amma
batasan tayi kuka "Na tuna kuwa babu wannan acikin rubutaccen auren mu,na manta bayan
signing takardar yarjejeniya da mukayi ta aure,wurin daurin auren ma mun rubuta cewar kalar
auren namu na dabanne ba wanda musulunci ya tsara ba,Kaje amma karka qara kawomun
komai daya shafi rayuwar aure,idan bazamu kwana a tare ba babu wani abu dazakamun na
aure,na yarda haka tsarin namu auren yake,kaje plss" tafad'a tana me d'addage hannayenta
duka biyu alamar naci ka fam, matsowa yayi daf da ita ya sanya hannunsa asaman waist nata
yamatse ta sosai da jikinsa yace "Ni kike gayawa magana hafsa? Sabida kin samu sake ko?
Yanzu ma idanta ta dago sukayi kaura dana juna tace cikin jin haushin sa

"So nake muyi sighning wani yarjejeniya kanka tafi" sakinta yayi yace yana murmushi muje
gayamun wane iri ne?" zama sukayi a kujerun parlor tace

"Sona ke mu kwana a roof daya,muci abinci atare,mu sake wa juna soyayya,mu aminta mudin
masoya ne,idan har akayi watanni shida kaci cewar baka buqatar tarawa dani,kuma bakaji sona
ko daya a ranka ba,to ka rabu dani,kuma tsakani da Allah zamuyi" kallonta yayi ya kwashe da
dariya ya sani yanajin tausayinta amma sam baya santa wlhy, yakuma san baze taba san
taba,da wannan ya aminta suka rubuta suka ajiye.....

Hafsat ta kuma yin wauta a karo na biyu,yaya kuke zanin wannan zaman? Ze dore kuwa?" anya
hafsat bata kirawa kanta zawarci na biyu ba bayan shaam ya aure fara me gashi abinshi? Muje
zuwa dai.....

Votes pls
[2/13, 9:28 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*


27

Muhammad a d'akinsa ya kwana yayinda hafsa ta kwana a nata d'akin,wata hatsabibiyar rigar
bacci ta saka iya cinya,da saninta ta cire bra,pant kawai ne ajikinta se wannan rigar,sumar
kanta datasha gyara ta gama barbajewa har saman goshinta daga bed room nata tafito zuwa
kitchen,a parlor ta hangoshi zaune duk da zuciyarta takad'a qirjinta se dokawa yakeyi amma
haka ta daure,tasani idan bata koyawa kanta rashin tsoron shiba akwai matsala,kallon ta yayi
sosai ya raya aranshi so take taja ra'ayinshi wanda baze tab'a faruwa ba har gaban abada, bata
ko kalli inda yake ba tayi gaba abinta zuwa kitchen,d'an guntun tsaki yaja ya mayarda dubanshi
zuwaga film dayake kalla, Ha d'adden break fast tabshirya musu,finger sandwichs da chocolate
sandwich,se kuma coffee amor da vegetable potatoe, tun yana daure wa har qamshin yasoma
jan hankalinsa,ogar bata baro ktchn ba sanda ta hada samosa, jere komai tayi a fankacecen
dining table,ta bude dining shelf ta baje komai da komai da ake buqata,bata wani kalleshiba
sabida sam ma yi tayi tamkar bata kula dashi ba,dakinta ta wuce tasha wanka da wata doguwar
rigar dress maroon color ta tufke gashin kanta da farin ribon,se flat shoe data saka shima fari
qal, har tsakiyar falon ta sameshi kusa dashi sosai ta zauna ta kalleshi dauke da fara'a sosai a
fuskarta,tana bude bakinta qamshi alawar datakesha ya daki hancin sa dauke kanshi yayi gefe
d'aya

"Barka da safiya yaa muhammad da fatar ka tashi lapiya?" dan juyar da kanshi yayi gefe daya
sannan yace

"Barka dai,kin tashi lapiya" Murmushi tayi

"Breakfast kai kadai yake jira oga muhammad kose kayi wanka ne?" dagowa yayi dukda beso
ba kasancewar tunda yayi aure da zainab,be taba tashi tabgayar dashi ba kuma yauce rana ta
farko da mace ta gabatar masa da abinci,sedai kuku ne yake dafa masa,miqewa yayi yace muje
dining d'in" kai tsaye tayi kokarin shiga gabanshi dauke da tafiya me daukar hankali gabaki daya
gogan seya shagala da kallon mazaunan ta,susucewa yayi ya wani zama tamkar wani

soko,sanda tace dashi "ka zauna plss" zama yayi yaga irin abubuwan data girka acikin lokaci
qanqanin,yakuma san be rigada ya kawo cook a gidan ba dama niyyanshi yau da rana ze
gabatar mata dashi "Mezan saka maka?" ta katse masa tunani da wannan tambayar

"finger sandwich and veg potatoe zansha wancan abun kuma" batayi musu ba ta zuba masa
komai da yace ta matso kusa dashi sosai wai bashi zatayi,kallon ta yayi ya d'an had'e fuska
"Meye hakan hafsat?" kafe shi tayi da idanta "Yaa muhammad da kaina zan baka mana" a
yanayin yanda tayi magana seya ganta kamar wata yar sha biyu kasa cewa komai yayi se bude
bakin dayayi ta aika masa sanwch din ya gutsura,sosai yaji dadin abuncin yama manta inda
yake har samosa seda yaci yasha coffee Amor dinshi sosai sannan ya daga mata hannu a
lamar ya qoshi,kallon shagwab'a ta masa

"Saura ni ka bani" dan mur ya qara sha "Na baki kuma me kenan?" Take ta hado
shagwababbiyar fuska "Abuncin mana" tsaki yaja ya miqe kawai tashi tayi ta bi ta gabanshi tana
doddoka kafa wanda ilahirin jikinta motsi yake tana kuma qunquni akan bazata maci abuncin ba
yau gaba daya...bin bayanta yayi da kallo harta wuce ned room nata,girgiza kanshi yayi ya
dawo parlor ya zauna ganin tafi 1 hour bata fito ba ya sanya ya bita ciki da kanshi, a kwance ya
taddata rubda ciki takalmin kafarta kurin ta cire da zata kwanta amma komai najikinta
nanan,mazaunan ta sun qara bajewa a yananyin kwanciyar datayi ji yayi tamkar ya sanya
hannun sa ya taba wata zuciyar ta haneshi gyaran murya yayi yace

"Hafsa mesa bazakiyi breakfast ba?" tana daga kwancen bata juyo ba tace "Bakai bane kace
wai baraka feeding na da kanka ba,ni Allah bazan ciba idan baraka bani ba" shiru ya danyi
kanyace

"Naji muje zan baki" mirginowa tayi ta kiqa masa hannun ta waiya dagata,badan yaso ba ya
miqa nasa hannun ya dagota,laushin hannunta kawai ya sanyashi runtse idansa cikeda
kasala,a parlor kuwa seda ta koshi sannan tace dashi wai ita atabau seya dagata zuwa cikin
parlor cikinta ya mata nauyi bazata iya tafiya ba, kallonta yayi yanaso yace kin cika rigima
amma ya kasa,dagatan yayi ta wani lafe jikinsa har sukaje parlo ya direta ya zauna saman 3
siter zuwa tayi ta kwanta ta daura kanta saman cinyar sa tace dashi "Ka sosamun kaina zanyi
bacci" bece da ita komai ba,aka soma knockin na gidan,dagata yayi yaje ya bude,kukun da
yake jirane,koda aka nuna wa hafsat shi masifa ta saka akan itace da kanta zatana girka
abunci,dole kuwa ya kyaleta ya sallami kukun, kallon ta yayi bayan fitar kukin yace da ita

"Hafsat mesa kin cika rigima ne? Idan ma bakya buqatar sa mesa zakimun haka a gabansa?
Seki bari idan ya tafi ko? Karki qara mun haka nan kina jina ko?" dan kallonshi tayi sekuma ta
dake "Idan kayi hakuri kome zanyi ai na 6 month ne ka jira idan matar daba ta yarjejeniya ba
tazo ka murza mata iko" sororo yayi yana kallonta ita harta wuce part dinsa, gyara masa dakin
tayi ta kwashe kayansa ta wurga a loundry basket sannan ta yaye boxers nashi da singlet data
ga ya cire ta wanke su ta shanya a toilet nasa, towel dinsa ta daura tayi wanka,tana fito wa ta
ganshi asaman gadon dauke kanta tayi daga dubansa,tazo tana rawar sanyi, kusa dashi ta
zauna ta rungumoshi gaba d'aya ta gabanshi "Yaa muhammad ka rufeni da jikinka akwai sanyi

wlhy" gabaki daya ta gama da matsalar malam muhammadu,kasa ko motsin kirki yayi sanda taji
daidai sannan ta miqe bayanta ya qurawa ido,taje mirror ta dakko wani mai tazo ta zauna,shidai
yau ta gama rufe masa baki,shafa manta ta zauna tayi kamar kuma wacce aka tsikara ta laquto
man ta janyo hannunshi ta saka aciki,juyawa tayi ta rage towel nata zuwa tsarar ta tace
"Hannuna baze kaiba nika shafamun" shiru yayi dole ya murza man ya shiga shafe bayanta
dashi,se wani lumshe ido yakeyi soft skin nata na daukar masa hankali sosai.....

Da yamma yace da ita tazo su shiga bangaren zainab,ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0