Showing 24001 words to 27000 words out of 54422 words

Chapter 9 - Bakin Rijiya Book Compelet Billy Galadanci

02 Aug 2026

951


yace "Na sani hafsat wlhy na sani narasa dalilin daya sanya na kasa cireta araina,kuma kullum
tunanina a duniya waye zata mayemun gurbin suhaila? Waye ze soni kamar yanda suhaila take
sona,wa zata kula dani kamar yanda suhaila take kula dani?" riqo hannunsa tayi sannan tace
tana zubar kwalla

"Nice nan zan maka dukkanin abubuwan nan daka rasa uncle say,meyasa bakasan kawa kanka
adalci ne,had'uwana dakai had'in Allah ne sabida haka tun farkon had'uwa na dakai nakeji
ajikina i meant for u and u alone,Ban tab'aji araina ina sanka ba ko kadan bantaba jin
soyayyarka araina ba,amma kullum ina tambayar kaina menene k'auna? Banida mutumin
danike matukar kewa sama dakai aduk fad'in duniyar nan,banida mutumin danike matukar
tausayi aduk fadin duniyar nan sama dakai,banida wanda nakejin damuwar sa tawace har raina
se kai kad'ai uncle say,banida wanda arayuwa nakejin tamkar zan rasa farin cikina idan yana
fushi dani sama dakai,banida wanda arayuwa banida burin daya wuce naganni kusa dashi
sama dakai,banida wanda nakejin zan iya sadaukar da dukkanin farin cikina akansa se kai
kad'ai uncle say,banida burin daya wuce farin cikinka arayuwa,babu abinda yake qayatar dani
se inganka cikin walwala,babu abu mafi soyuwa agareni se ganin farin cikinka inga kana dariya
yafi komai saukarmun da nishad'i,a iya tunani wayannan abubuwan ba soyayya bace,k'aunace
me zafin gaske,ada nayi tunanin so shine komai se yanzu danake rayuwa dakai na tabbatar wa
kaina cewan so shirmene zallah,ada nayi tsammanin cewa akan soyayyar shammaz na shige
halin da nashiga na ciwon zuciya se daga baya na fahimci cewar zallar mugunta,cin amana,cin
zarafi dakuma wulakantanin dayakene ya sakamun ciwon zuciya,sabida soyayya ruwan shayi
ce yana zubewa a qasa kuma sedai kanemi madarar ka rasa shimfidar ruwan banza kawai zaka
gani a kasa,kauna kuwa kakkauran kindirmo ce sabida zubewar sa a qasa baze tab'a zama
sanadiyar b'acewa kalarsa ba,itace nake maka zallarta,dan Allah uncle say ka
k'aunaceni,dukkaninmu muna tsananin buqatar kulawar junanmu" sosai yake kallonta harya
kasance ko qiftawa bayayi ya rasa dalilin sa najin komai tamkar a mafarki jikinsa gaba d'aya
yayi sanyi,har yanzu hafsat yarinya ce bazata tab'a fahimtar saba idan yace mata kuma bashida

hanyar daze bar zuciyarsa ta k'aunace ta sabida wasu manya manyan dalilai,batare dayace
mata qala ba ya miqe yabar parlor d'in fuska kici kicin zuciyarnan sam babu dadi a jagule......

*kome hakan yake nufi,da Alama hafsat batada farin jinin masoya a duniya,ba wanda yatab'a
cewa yana santa,sannan kuma ita sedai taso wannan taso wancan amma babu wata
nasara,Allah ya temaketa dai,muje zuwa kuci gaba da bin alqalamin mom Nu'aiym.....

          
[2/1, 8:32 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*


18

Dafe kanshi yayi bayan ya kwanta yace cikin kukan dabesan sanda ya kwace masa ba "Meya
sanya arayuwa Hafsat take shan wahala har haka,ina tsananin sanki hafsat amma bazanyi
ganganci nuna miki hakan ba,kamar yanda bazan tab'a bari soyayya ta tayi tasiri azuciyarki
ba,gwaramun haqura dake a matsayin mata akan narasa rayuwarki har abada.." kukan
yashigayi kaikace qaramun yarone,ganin wannan bazata fiddashi ba ya sanya ya shirya zuwa
gun amininsa kamal khan domin sanar masa matsalarsa......

"Kamal akwai damuwa fa babba wlhy,duk sanda na kwanta senati mugwayen mafarkai akan
lallai idan har na kuskura na auri yarinyar nan se an kasheta har lahira,ni bazasu iyamun komai
ba sabida riqon addini haka sukace amma wai itad'in alqawarine duk mesan tan daya aureta
lallai se sun ga bayanshi babu ita ba tarawa da wani d'a namiji harta bar duniya ni sosai take
ban tausayi wlhy,wama yasan ko wancan yayan nata hakance ta faru dashi,ni ina matukar san
hafsat son daban taba yiwa wata 'ya mace irin saba a duniya,rashin adalci d'aya zuciyarta
tamun na sanya ta qaunaceni,Bansan yanda zatayi da ciwon zuciya ba idan har naguje
mata,kuma ni bazan iya cewa da ita ga abunda yake faruwa ba harga Allah" nisawa khan yayi
cikin yaren india yace

" Sam karka gjjeta,karkuma ka nuna mata baka santa,wannan ba abinda zeyi illah ya wargaza
mata zuciya gaba daya,sanan ni ina abu d'aya ne cikin biyu,kodai iskokaine da ita kokuma asiri
aka mata,danni bantab'a jin hakan ba se'a irin harkar iskan nan,nifa a nawa tunanin kabata

lokaci,ka kula da ita ka nuna mata soyayyar dakake mata inyaso a hankali kana koyar da ita
girman adu'a da tsare azkhar safe rana da dare dakuma yawaita yin azumun litinin da
alhamis,kana ana yawaita yin salatin annabi ba adadi,idan ma iskane zasu bayyana kansu idan
kuma asirine lallai Allah ze taimaka kaga abun ya karye" murmushi yayi ya daura hannunshi
akan kafadar khan

"Inajin dadin shawar warinka abokina,Allah bar zumunci hakan zamuyi ai dole ma".

Tunda hafsat taga yananyin Uncle say se jikinta ya mata sanyi,dak'yar ta iya jan jikinta zuwa
bedroom nasu,har akayi magrib da ish bata fito ba,har akazo cin dinner koda aka aika kiranta
se cewa khairii tayi ta qoshi tasha fresh milk,ganin haka Uncle say ya gano damuwa tashi ga
wannan yasanya ya janyo wayarsa ya rubuta mata txt kamar haka
"My love i swer idan bakizo munci abinci ba bazan ciba nima,kuma na tabbatar bazaki so Uncle
say naki ya zauna da yunwa,plss kizo I LOVE YOU". Kasa dauke idanta tayi daga message din
tana mamakin kalamansa har ya kuma turo wani jinta shiru

"Baby na dagaske fushi kike sabida namiki shiru dazu,tsabar jin dadin kalamanki ne yake shirin
sakani kuka a dazun,kuma inajin kunyar nayi kuka a gabanki amma trust me i love you more
than words can tell,plss com and hav dinner together with ur fam" Tana murmushin jin dadi tazo
dining d'in ta zauna amma me tarasa dalilin daya sanya matukar kunya ya hanata had'ata ido
dashi har abincinma ta gagara ci se wasa takeyi da cokalin hannunta,wayarsa ya dauka ya
rubuta mata

"Meye hakan kunyan wa kike kuma? Yauba shagwab'a kenan" karayin k'asa tayi da kanta
bayan ta karanta message d'in amma batayi replyin nashi ba,murmushi yankumayi yace cikin
message

"u go and get set,we r going for a date" murmushin dake qarawa fuskarta kyau ta d'ago tana
masa cikeda qauna sannan a hankali bayan sun had'a ido ta sadda nata idon k'asa lokaci daya
taji tana masifar jin nauyinsa kuma ya mata kwarjini,miqewa yayi kakarsa ta kallesa tace

"Bakaci komaiba?" murmushi ya sakar mata

"Nida hafsat zamuje yawo ne,bamasan mu qoshi danyawa a gida,murmushin tayi itama bata
tankaba,tun dazu ta kula da yananyinsu ai yau taga sauyi sosai awurin dukkansu musamman
Sayyeed dabaya iya d'auke idanshi akanta duk wani zumud'i yake ji......

A hanya yau hafsat gaba d'aya ta kasa sakin jikinta dashi,hannunta ya janyo yace "'Yan
matan uncle say yadai niyau tsiwar nakesanji sa shagwab'ar" batayi magana kurun dai ta juyar
da kanta d'ayan gefen tana murmushi,hannunta dake had'e da nasa ya matse sosai da sauri
tashiga janye hannun ta saka wata qaramar qara,tace cikin shagwab'a "Nashiga uku Uncle say
dazafi wlhy" sake hannun yayi yace yana dariya

"gobe ma kya kuma mun banza idan ina miki magana" batace komai ba,shima shirun ya
d'anyi,se can taje bayan ya wuce wani samosa joint

"Uncle say onions samosa zanci" kallonta yayi yace "sekin cemun baby tukunna" zaro ido tayi
tace "Haba mana Uncle sayyeed" murmushi ya sakar mata yace yana kallon dayan gefen
alokacin dayake shan kwanar barin layin "Kinwa kanki sekince Baby say zan siya miki komai
ma" Turo baki sannan ta sadda kanta kasa a hankali tace "Baby" dariyar mugunta ya saki
sannan yakuma cewa "Cewa zakiyi,Baby say zanci onions samosa" Kara turo baki tayi batai
magana na yace "Bazaki fada ba na qara gudu kinwa kanki kenan??" cikin muryan kuka tace

"Baby say zanci onion samosa" parking yayi ya mayarda hankalinshi akanta,sannan yace
"kinsan Allah hafsat ba wasa a zancena akan wannan yawan koke koken wlhy semunyi fad'a ke
ko wasa aka miki se kinyi kuka,bazan ma qara miki wasa ba" D'agowa tayi tace tana share
kwallan
" Im so sorry Uncle say,bazan kara ba" cikin kuka tayi maganan ko yanzu,shi wlhy dariya ma ta
basa,itafa komai qarantar abu kukane,kannewa yayi yace "Oya call me Baby say again" tana
kukan tace "Baby say" yace "Noo cewa zakiyi I love u baby say" kallonshi takumayi sannan tace

"I love you Baby say" ta fashe da kuka" jiyayy kamar ya rungumota amma ba hali,ya tabbatar
cewar lallai jitai kamar yace ta maresa dayace setace masa baby,yasani tanajin nauyinsa amma
wannan ita kadaice damar dazeyi amfani da ita ta saki jikinta dashi mastayin saurayi seya ganar
da ita amfanin suturta jiki dakuma yawaita ibadar mahaliccii.... Da wannan yace "kiyi hakuri
dear,bazan kuma sakaki kuka ba kinji?" daga masa kai tayi tace "Tokimun matashin murmushi
mana,dariya tayi gaba daya hawaye shabe shabe a fuskarta tace " Uncle say a murmushin ma
akwai matashine?" dariya ya saki shima "Ea mana bagashi kinyi ba?" suka saka dukkansu......

Mom Nu'aiym
[2/4, 9:26 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                  19

Shammaz zaune a office d'insa duniyar habaki d'ayanta baqi take masa yarasa yazeyi akan
zancen hafsat,sam mahaifinsa yaqi ya basa fuska,gaisuwar sa ma dak'yar yake amsawa,gashi
gaba d'aya Haleemah ta gama rainashi zaman auren kawai sukeyi amma sam bajin dad'i har
qasar take bari bada izininsa ba,yama rasa tayaya zeyi gashi dai hafsat yanzu kusan shekaru
hudu da barinta qasar acewar Mommy ma takusa dawowa domin tace qasarta zata
bautawa,amma duk inda yaje da zancenta ba sauqi har wurin hajiyar su wato kakarsa......

    Sosai hafsat ta tara abubuwan burgewa ajikinta,yanzu batada wata damuwa ita da uncle say
sambarka,duk da yabar qasar ya koma Niger amma koda wane lokaci suna maqale da juna
awaya,sunyi wani sabo mara misaltuwa,kwance take acikin dakinsu tana karatun wani English
novel me suna she's with me,khairii ce tashigo ta kalleta taja tsaki
"Allah hafsa kin shiga ukunki kekam,wannan wane irin karatun jarabane kikeyi haka? Kinfasa
tafiyarmu nanda kwana ukune, amma meye naki na tsayawa karatun wani banzan novel,kofa
kayanki baki had'a ba wannan zumud'in na uncle say duk gulmane abaki kawai ya tsaya bekai
zuciba" bata kula taba,kuma sarai tasani bawai kulatan zatayiba wannan ne ya sanya taja wani
tsakin ta shiga had'a musu kayan har hafsat,se zumud'in ta takeyi ita kadai tana mitar san
banza irin na hafsat....

*NIGERIA*

      Gaba d'aya hafsat gani takeyi tamkar mutanen dake yanga akan jirgin basu san ciwon
kansu ba,sakkowa ajirki sekace wanda ya tasa tray na samosa agaba,se yanga sukeyi tamkar
basa taka qasa,tun a airport na sultan muhammadu maccido dake garin sokoto ta fahimci sauye
sauye da dama da aka samu a garin,idon tane ya sauka akan masoyinta uncle say,shekara
d'aya kenan rabon data ganshi,takowa tayi a hankali taje har gabansa ta tsaya ta sakar masa
lallau san murmushi,kankace meye wannan kuma idonta ya cicciko ta soma kwallan murnar
ganinsa,a hankali ta furta "i so much miss u Baby say" murmushin shima ya sakar mata sannan
ya ja hannunta ya riqa cikeda kulawa yace

"Rose kukan kuma na menene,daga had'uwarmu zaki fara ko Baby?" murmushinta ta fad'ad'a
batare data dena zubar wahayen ba tace "Uncle say bakada labarin akwai hawayen dadi? sune
nake zubarwa tsabar murnar ganinka" Janta yayi suka juya se mota,dama shi kadai yazo tarar
su suka shiga suka wuce gidan abba haris kai tsaye,se labarin soyayya sukeyi cikeda qauna da
tsananin murnar ganin junansu......

   Satinsu daya agarin aka tsayarda ranar auren say da hafsat nanda watanni hudu masu
zuwa,dama can tun tana india akayi tambayar auren kowa ma yasan da zancen auren.

*Bayan kwana biyar*

    Tun da hafsat ta dawo basu hadu da yaa shaam ba har yau,gwara ma matarsa sun had'u a
gidan daddy,shi kuwa yana sani yake gujewa ganinta sabida gudun karya tayarwa kanshi cutar

so da ta jima tana addabar zuciyarsa,yau dai seda ya kira qaninsa da safe ya sanar masa cewa
suna gida sannan ya shirya zuwa gidan na daddy,bashida lamarin hafsat ta dauki al'adar waje
bata fiya fitaba seda yamma,wannannya sanya ta zuro doguwar rigar jallabiya ja har qasa tasha
shape da bakin mayafi da uban qaton madubin ido,lips dinnan sunsha red lipstick,a hankali take
taunar cingam dake bakinta tana yamutsa fuska,yau sam setakeji tamkar batada lapiya driver
din na parka wa tafito a yangace zuwa cikin gidan daddy cikeda yanga, A hot na gidan ta hango
yaa shaam lokaci d'aya qirjin ta ya mugun dokawa,adu'a taci gaba da karantowa ta dauke kanta
tamkar bata ganshi ba,murya ya d'aga yace "Hafsa zo zan" qirjin ne yaci gaba da mugun
dokawa amma bata ko waigo ba, yi tayi tamkar bata jishiba, shikuwa ganin haka kuma yasan
sarai tana jinsa ya sanya yayi saurin tasowa yafara takowa zuwa inda take,ita d'inma sauri ta
qara amma ina kan ta isa kofar dazata sadata da cikin gidan ya rigata,tsayawa tayi cak ta
runtse idonta ta sauke wata nannauyan ajiyan zuciya,a hankali cikin sanyin murya yace

"Hafsat ya kwana biyu" bud'e idonta tayi a hankali batare da tayi magana ba,tana kallonshi ta
cikin gilashin idonta,ya kuma cewa

"Bazak gayarda yayan naki ba?" hannu ta saka ta zare madubin idonta sannan ta lumshe
manya manyan ida nuwanta tace "Yaa shaam ina wuni,ya kwana biyu?" murmushi yayi shima
hade da daura hannunsa saman qirjinsa yace "Lapiya qalau hafsat yaushe agarin?" murmushin
itama tayi tace
"Au baka masan zanzo ba aikuwan na cika tara,seka biya" wani dad'i ne ya xiyar cesa ganin ta
sakko,besan kuwa nan umarnin yaa say kawai take bi ba abun beyi wani damuntaba,dak'yar
ma take masa murmushin,shikuwa se dadi yake ji ya kalleta sosai

"poojan dady an girma fa sosai yanzu" murmushin takumayi tace

"yaa shaam d'in daddy kuwa ya zama tsoho tunda qanwarsa ta girma" Murmushi yayi ya shafi
gefen fuskarsa "Ki shiga ciki yan matan Yaa shaam" wata dariya tayi me cikeda ka raina kanka
ta wuce ciki kawai....

Tunda yaa shaam yaga hafsat na sakar masa fuska se kawai ya qudurta aranshi shine ze
angwance da ita,da wannan har tunaninsa ya kaishi ga zuwa ya ziyarci Innah wato kakarsu ta
wurin iyayensu maza....

Zama yayi ya saka mata uban kuka,akan wai ai asiri aka masa ada,yanzu kowa yasan yana
san matarsa Amma abba haris dasu daddy sun hanashi sun baiwa wani har an saka rana
nanda watanni hud'u,Innah kuwa tacika fam ta fusata,i da take shiga batanan take fita ba akan
za'a hanawa magaji mata,aikam tana da rai basu isaba,da wannan tayi kiran kowa da kowa a
gidan ta!!!!

Kallonsu tayi bayan kowa ga natsa yana saurarenta tace dasu "Dama akan zancen hafsat ne
da Magaji,tayaya dukkaninku kunsan airine yayi tasiri akan shi a wancan lokacin yanzu zece

yanaso amayar masa da matarsa hankalinsa ya dawo jikinsa amma tsabar bakusan
muhimmancin zumunci ba zaku rufe ido ku baiwa wani inada rai banma sani ba,to wlhy kunyi
kadan kunji na gaya muku,na baiwa shaam auren hafsat tunda dama saku d'ayane a
tsakaninsu,kuma na dawo ma da bikin wata me fita" kallonta Abba haris yayi cikin rudu yace
"Innah dan Allah karki taso da wannan maganar yarinyar nan yanzu ta samu wanda
takeso,kuma bazamu zamo qananun mutane ba munyi magana kuma mu dawo muce dasu wai
amfasa,dan Allah ki rufa mana asiri maganar nan tunkan ta tashi daga nan mu barta" kanwar
haris me binsa ma tasa baki kowa dai yayi magana tana jinsu seda duk suka gama sannan ta
kallesu tace

"Dukkaninku nan baku isa kun sauyan ra'ayi ba,sannan idan qaranta kuke gudu ni nan bana
gudunta,ku sani wlhy ko yau na mutu duk wanda ya sauya wannan maganar tsakanina dashi
Allah ya isa ban yafe ba" zaro ido sukayi dukkansu suka shiga lallami da ban baki,amma
qememe tace dasu acikinsu ma wanda ya kuma tada zancen bata yafe ba,indai ba akan
zancen bikin bane,kar wanda yazo mata dashi kuma kartaji sun sanar wa Alhj wato mahaifinsu"
ai gaba d'aya mamaki ne ya damqe ilahirin su,suka silale d'aya bayan d'aya.....

Mom Nu'aiym ce
[2/6, 9:16 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

20
Zirga zirga abba haris keyi tamkar me ynqurin naquda,sam ya kasa gayawa hafsat meke tafiya
gata durqushe a gabansa amma se gumi yake had'awa,kar yarunyar nan tayi tunanin cewar san
kai yake mata akan d'ansa,ganin yayi shiru beyi magana ba ya sanya takuma cewa

"Abbana gani" jikinsa ne yayi mugun mutuwa jin takirasa da abbanta, yasani hafsat duk gatan
da mahaifinta keyi mata gani takeyi tamkar shine ya haifeta kuma yafi santa,hannu ya sanya ya
rage zufar data tsatsafo masa a goshi sannan yace,
"jeki ki dakko mayafinki kizo mu je wani wuri" dubanshi tayi haka kurun taji qirjinta na dokawa
kuma kanta ya soma sara mata,jiki a mace ta miqe zuwa part nasu ta sako hijab a saman
doguwan rigar atamfar dake jikinta tafito......

*A parlor daddy*

Tunda hafsat ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0