Showing 9001 words to 12000 words out of 54422 words

Chapter 4 - Bakin Rijiya Book Compelet Billy Galadanci

02 Aug 2026

949

a gaba kina kallo,Dabadan gidanmu daya ba kuma nasan acikin daula kika taso danace ke
dinnan anyi daqiqiyar yar qauye,zuwa nayi inji meyene ya hanaki zuwa ki taya haleemah ku
hada breakfast kokuma harkin fara tunanin cewar kishiyar kice kin fara kishi da ita?? Sadda
kanta tayi kasa tanaso tayi hawaye koda wannan gululun bakin cikin datakejin ya tasomata ze
kwanta amma ina sam ta kasa takuma rasa dalili,abin se yawo yakeyi yana mata sintiri tsakanin
maqoshinta zuwa cikin yayan hanjinta dakyar ta iya furta kalmar

"kayi hakuri na makarane" tsaki yaja "ki tabbatar kinje yanzu kun daura girkin rana da ita sabida
ba baiwar gidan uban kowa bace dazata girka abinci agidan,kuma ni bazanci abuncin yar aiki
ba" Batace komai ba ta juya da siririyar halittarta zuwa ciki domin dauko hijabi,wani tsakin taji
yaja a sarari ya furta " Sabida ansan ba wanda ze daukeki da wannan bushashen kunkurun
tamkar na marainiyar kaza shine za'a cinnamun,mace se kace allo samb'al haka" sarai ta jiyoshi
wani azababben baqin cikine ya dunqule ya sake taso mata mara misaltuwa fatanta daya
tasamu tayi hawaye koda ta samu salama amma sam abun yaci tura ta kasa,da wannan ta
dauko hijab dinta tafito,bayanshi tabi har sashen haleema ba wani nisa a tsakaninsu kofa
kawaice part din kofofinsu suna kallon juna,suna shiga parlor din haleemah ta taso ta rungume
shaam,shi kuwa ya manna mata sumba a goshi bayan ya sauke hannayenshi a saman faffad'an
kuib'inta ya sauke yana me shafar manya manyan mazaunanta,wani shagwab'ewa tayi tace

" Boo mie banfa karyaba" hannunshi ya kuma saqalawa a kugunta " Bazaki iya girka komai
bane da kanki sweetest?" gyad'a masa kanta tayi cikeda shagwab'ar da sam bata karb'eta ba
tace " Ni kasanfa jiya baka wani barni bacci ba na gaji kuma chips nake sanci with liver sauce"
kallonsa ya maida kan Hafsat "kulele kije ki hada mata breakfast dinnan datakeso sannan
bayan kin kammala ki daura lunch kinsan kuma banaso ya wuce 1:00" murmushin yaqe tayi
batare datayi magana ba ta wuce su zuwa inda take saaran nanne kitchen din sabida kula da
tayi komai na tsarin gidan irine dayane da nata kayane dai ta kula kowannensu da irin nashi,taje
ta had'o breakfast din ta kawo dinig ta ajiye sannan ta juya zuwa daura na rana,zuciyarta tana
mata suya sosai a daddafe ta kammala girka musu chinese rice da veg pepper chicken and
mock champagne drink,a dining ta jere su bayan ta kammala had'a colslow sannan batare data
d'ibi komai aciki ba,ta juya zuwa part d'inta,wanka tayi ta sauya kaya sannan tayi kiran umman
yaa shaam ta asali akan a aiko mata abinci,da wannan umman ta kira shaam akan yazo ya

karb'a wa hafsat abinci,da mamaki yafito parkor din gidanshi ganin kayan abinci a jere ya
sanyashi mamaki amma batare da wani dogon nazariba yafita yaje ya karbo ya dawo, da iya
karfinsa ya banko kofar gidan ya shigo a parlor ya sameta kwance ta daura wayarta asamn flat
tommy d'inta tana tunanin data saba wannan shigowar da yayi a haka be sanya tako motsa ba
sabida ta shiryawa kanta tarb'ar duk wani bakin ciki dazezo mata bama yanzu ba har nan
gaba,a kanta ya tsaya "Wane munafuncinne ya sanya dakika girka abunci baki ebi naki ba
sekika kira sabida ke ba Allah aranki burinki kawai kiga kin had'ani da mahaifiyata,shegiyar
yarinya me munafuncin tsiya wlhy kika kuma mun haka sena illata miki fatar jikinki kuma inji
zancen nan gidan agidan daddy ko gidan Abba ko hmmm rahbb wlhy nida kene,kuma zanyi
baqi da dare kiyi girki a nan part d'in" Harya gama fadan shi ko motsi batayiba a haka ya juya be
jima da fitaba sega su huda lokacin kuwa har 3 ta gota ba karamun sanyi tajiba atake huda ta
tayata suka hada girki me yawan gaske basu suka zauna ba se 6, wanka hafsat ta sakeyi
sukayi sallah sannan suka kule d'akin hafsat kallon ta huda tayi tace "Qawata nasani kina cikin
damuwa me tsananin yawa kuma na fahimci hakan tun zuwana,nasani bakyaso ki tattauna
matsalolinki da kowa amma ki sani hafsat kin burgeni matuka lallai kinyi hankalin da ban zata
kuma inaso naja hankalinki akan abu d'aya,karki kuskura ki sanar wa iyayenki irin zaman da
kike acikin gidannan,ke bama suba kowa harni,duk sanda kikeda wani matsala kimun matsal ki
gayamun sabida yawan barin abu a zuci yana sanya ciwon zuciya,karki yadda da kowa se
kanki,kuma bawai rashin fad'a ba hadda nuna wa dan Allah yar uwata kina daure wa kuma kina
jure duk wani wulaknci da shammaz ze miki,kiyi zaman aure me kyau kindaiga ke qaramar
yarinyace idan kika biyewa waccen tsohuwar matar wlhy wahala zakiyi sosai sabida nisam ban
yarda da ita sabida haka ki kiyaye kinji" se a sannan taji wani kuka ya qwace mata rungume
huda tayi ta dinga kuka seda ya isheta sannan ta sake huda ta mata suka yi sallama akan
washe gari zasu dawo.......

Mom Nu'aiym
[1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

09
Da darema haka ta zauna zaman jiran yaa shaam amma shiru kakeji tamkar an aiki bawa
garinsu,haka ta kwana ranar kam tana rusar uban kuka,tana idarda sallan asuba wayanta ya
soma ringing tana dubawa tagan sunanshi gabanta ya fadi, jiki ba kwari ta d'aga kiran,yace da
ita "Karfe 9 zanyi baqi saga abuja zasu sauka a lodge su uku ne ki hada break fast before 8

sabida nafiso su taradda shi suna zuwa" to kawai tace ta ajiye wayan tana sharar kwallah,ga
ciwon kai sabida kuka da rashin bacci ga azabar aiki sekace jaka,a daddafe ta hada musu
finger sandwitches da sultan chips fried chicken and jello,se 8:15 ta kammala,tana shirin fitowa
kitchen d'in ya shigo da sauri taja baya ta durqusa har qasa "yaa shaam barka da kwana"
harara ya wurga mata

"ke jakar gidan uban waye wai? Bance dake before 8 ki kammala ba yanzu karfe nawa?" sadda
kanta tayi kasa wani qututun bakin ciki ya tasoma mata ta kuma rasa dalilin daya sanya sam
bata iya kuka idan yaci zarafinta sedai zuciyarta ta dinga wata suya me azababben rad'ad'i,da
k'yar ta lalubo kalmar "kayi hakuri" tsaki yaja "Dama mana kullum kece ayi hakuri,idan kin isa
gobema na sakaki aiki na baki lokaci ki wuce time d'in wlhy zaki d'and'ana kud'arki a hannu"
batace kanzil ba taje ta dauko warmers d'in data zuba abinci aciki ta sakosu acikin wasu cute
baskets guda biyu ta ajiye a gabanshi ta juya zuwa d'akinta cikeda qunci,tana zuwa tayi kiran
umma akan zancen yarinyar dasukace zasu kawo mata me tayata aiki,sabida a yanda ta gaji
yanzu bataji zata iya girka lunch and dinner kuma taga har haleemah tafara fita aiki tun
jiya,bayani umman ta mata akan an kawo yar aikin khairiyya zatazo ta kawota anjima kadan......

*Bayan wata biyu*

Rayuwa a haka taci gaba wa hafsat cikeda qunci da wahala,gashi duk k'wak'war mutum be
isa yasan abunda ke damunta sabida dama batada jiki balanta na kace tayi rama,sannan kuma
bazaka gane a fuskarta,tana zuwa school yanzu 200l suke kullum huda cikin bata shawarwari
na kwarai take akan tayi hakuri kasancewar itace kadai aduniya tasan meyake damun
hafsat,kuma har wannan lokacin shammaz baya kwana gidan hafsat indai abubuwan more
rayuwane da kudade sedai ta baiwa wani amma sam ba magana me dadi a tsakaninsu wasu
lokutan sam ko gayar dashi tayi baya amsawa,yau agajiye ta dawo daga skul tana fitowa wanka
wayanta ya soma ringing,d'agawa tayi ganin sunanshi yace " Yanzunnan ki kawomun abinci
yunwa nakeji" cikin takaici tamkar zatayi kuka tace

"yaya yau ba abunda naci wlhy yanzunnan na dawo daga skul ko sallah banyiba dan Allah kace
Aunty haleemah ta baka mana" wani mirmurshin mugunta yayi da har tana jiyo sautinsa yace "
Ita d'inma yunwa takeji kuma yauma agajiye ta dawo ke muke jira ki bamu abinci kuma 1 hour
kawai na baki" yana kaiwa nan ya ajiye wayar,cikeda takaici taje kitchen ta dafa musu sphagetty
bolognese da orange juice tafita kaimu su haushi tamkar ta had'iye zuciya ta mutu,da sallama
tashiga parlor din amma abun mamaki se numfarfashi take jiyowa juyawan dazatayi tagansu
akwance suna kissing junansu shaam se shashafa leemah yakeyi yana mamatsa breast dinta
kai abubuwan data gani sam bazasu fad'uba,wani takaicine ya taso ya tarnaqeta a wannan
lokacin ji hafsat keyi tamkar ga kashe kanta har lahira,da kyar tayi karfin halin zuwa dininga
tabajiye kayan ta juya,abunda yafi bqanta ranta shine yanda sukayi tammar basu ganta ba
kuma sarai ta sani dukkaninsu ba wanda be sanda zuwanta ba wani abin ma har da gayya suke
yinshi,wanda sosai ta kula Aunty haleema wannan surutun datakeyi danta gantane,a wannan
ranar kuka hafsat ta kwanayi ko abunci bata iyaci,Allah sarki qaramar yarinya akace ana wata
ga wata domin kuwa tun daga sanda hafsat ta gansu a haka se wani azababben sha'awa yake

taso mata gashi wannan lokacin ne tashen balagarta seta rasa yanda zatayi a haka take danne
zuciyarta tana adu'a Allah ya kawo mata d'auki...

Ranar wata juma'a bayan sallan isha tashiga part din haleemah sabida tanasan ganin yaa
shaam akan zancen bikin huda dayake wani satin za'ayi tana zuwa kofar d'kin tajuyosu suna
iskancin nasu dasuke ihu sekace wasu maguna,juyowa tayi cikeda takaici anan taci karo da
abinda tangamemen tv n dake parlor din ke haskawa wato BF,gabanta ne ya fad'i ganin me
akeyi take taja baya se kuma wata zuciyar tace kindaiji ana labari amma yaune ganinki na
farko,jeki ki kalla...da wannan ta tsaya ta kurawa tvn idon tana kalon masha'an da ake tafkawa
rashin kunya iri iri,dakyar ta dakatar ta juya zuwa part d'inta jikinta har rawa yakeyi wasu
abubuwa takeji suna mata yawo kasa haqura tayi da tambayoyin da zuciyar ta ta gaya mata ta
zari key na motarta zuwa gidansu huda......kallon huda tayi bayan sun zauna a d'akinta tace
bayan ta tattare nutsuwarta zuwaga hudan

" friend mene ne sha'awa? Yaya kakeji idan kanajin sha'awa?" kallon mamaki hudan ta mata
tace "Ban fahimcekiba?" sosa kanta tayi ta labarto mata tun farkon ganinta dasu shaam dakuma
abu da ta gani ayau,ta qara da cewar "Huda wasu lokutan sena kasa bacci kinga har kuka
nakeyi sena ringajin ina matukar sanjin abinda Aunty leemah keji tana sambatu idan yaa shaam
yana mata wannan abun,kuma kinga yau danaga turawannan suna wannan abun sena ringa jin
dadi sosai nima inaso kuma naji na rage yawan sha'awa shine nakesan siya nakuma ana
yawan cewa haramun ne kallon wayannan abubuwan kuma yana saurin kashe ido?" cikeda
tsoro huda tace

"kinga hafsat wlhy ki kama kanki,inake ina kallon wannan abun?? Masu siyarwa ma karuwai
kad'ai suka san inda suke masu browsing a waya kuma wlhy duniya tana kallonsu sosai da
sosai,sa'annan na kula kinada karfin sha'awa sabida haka wlhy kine ki samu mijinki kice dashi
kina buqatarsa inba haka ba wahala tana ganinji,kuma wlhy idan nakuma jin wai zaki siya
wayannan mugayen films senaje na fadawa momy,ki barsu yaa shaam matarshi batada maraba
da karuwa wlhy ni sunaso su b'atamun ke,wainikam ma tukunna tsaya sanar dani kina yawan
adu'a da tsayuwar dare?? Kuma kina azkhar?" dan sosa kanta tayi tace "Gaskia bana,wani yi
ina dai adu'a"

"Toki riqayi akan mijinki da duk wata damuwarki kinji huda,adua yana da kyau da kyautata ibadu
yawan yin azumin nafila da sallar nafila dakuma azkhar,kina yiwa qananan yara sadaka tunda
baki rasa ba kinji,ki cire ranki da wannan mugun kallon indai ba wuta tsundum kikeso kije
ba,kuma masu san kalllon wannan ma idan suka saba basa iya denawa,sekiga idan ba namiji a
tare dasu suna yiwa kansu abubuwa da hannu kuma wlhy masifa ne Allah ma yayi alkawari.
Azabtar da masu irin wannan mugun aikin,seki kiyaye kinji qawata" gyada kanta tayi alamar
gamsuwa sannan tamata sallama tabar gidan,huda se tausayinta takeji matuka.......hafsat se
tunanin rayuwarta takeyi da abubuwan ban mamaki datake ta faman gani arayuwa,a haka ta isa
gidan cikeda damuwa,a harabar ajiye motocin gidan taci karo da yaa shaam tamkar
bashiba,bashida niyyan koda kallonta ne balantana yamata magana,da sauri ta qarasa gunshi

"yaa shaam ina wuni?" "Lapiya" ya amsa a taqaice yana shirin shigewa motarsa takuma
kallonshi tace " yaa shaam magana nakeso muyi" batare daya kalletaba yace "Enhmm"

"Dama nikam wai yaya banida wani haqqi a gidannan ne koda na kwana a part dinane yanzu
kusan watannina biyar agidannan amma koso daya baka taba kwana bangarena ba atare dani"
wani kallo ya wurgo mata ya murtuke fuska sannan yace

"Idan tunanin kike kinada wani haqqi a kaina to kuwa kinyi babban kuskure domin nidai,ni
shaam wlhy nafi kardinki sam *Bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane* bakida wani abu
ajikinki ko a fuska daze gayyaceni kwana sashen ki,sa annan kuma bakida wani diri na ya mace
dage gayyaceni zuwa shimfidarki,wlhy Hafsat bakida banbanci da namiji awurina,iyayenki sun
cuceki domin nidai bazan taba iya furta kalmar saki agarekiba kamar yanda bazan taba iya
makwanci dakeba sabida haka idan ma mafarki toki farka samni kam bana san mace sekace
tsinken stintsiya se dare kamar wani daren yunwa,kuma me harma kinyi girman dazaki tareni da
wani haqqinki wlhy kika kuma mun irin wannan maganar sena tattaki mara kunya fitsararriya
haqqin uban wahe dake a hannuna sekace da yunwa take kwana a gidan" batare datace komai
ba tayi ciki aranta tace "Nice ma bankai mace ba,nice ma ban isa yasoni ba,nice banida
banbanci da tsinken tsintsiya" ko wannan daren hafsat kasa bacci tayi kuma se zazzab'i me zafi
ya rufeta Allah ya taimaketa ta kammala exams nata gaba d'aya........washe gari yayi kiranta wai
tasan haleemah nada juna biyu bata iyacin abinda ta girka ta kawo mata abunci,tace dashi "yaa
shaam nima a kwance nake ko bacci banyiba wlhy banida lapiya" tsaki yaja yace wai mintuna
talatin yabata ta kawo kalacin....

Mom Nu'aiym
[1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

    *Wannan shafin nakine maryam Abdullahi gumel,nagode da qaunarki agareni*

10
Tunda hafsat tashiga gida take rusar uban kuka daganan tayi alqawarin ficewa sha'anin yaa
shaam koda kuwa soyayyar sa zata hallakar da ita har abada.....da wannan ta mayarda
hankalinta akan karatunta matsalar fa d'aya tsananin sha'awar dake damunta kullum ba dare ba
rana,ta rasa yanda zatayi da kanta kuma tayi alqawarin koda huda bazata sake sanarwa da duk
wata matsala tata ba zata qalubalanci rayuwarta ita daya, amma fa sam bata acikin
walwala.....yau dai shirin zuwa gidan momy tayi sabida sunday ne ba school,harta shiga mota

yaa shaam ya tsaidata "Kije ki dafa mana abinci sabida Babyn shaam bata da lapiya kin kuma
sani sarai tanada juna biyu bata iya cin abinda ta girka" tamkar zata yi kuka haka ta ji amma
seta daure batace komai ba tafito zuwa cikin gidan,a bangarenta ta girka komai sannan ta
shirya ta dauka takai bangaren haleemah,tana zuwa ta ajiye a dining ta sanar musu,seda
haleemah ta kalleta sannan tace,cikeda sigar rarrashi "Dan Allah hafsat kiyi hakuri wlhy bazan
iya cin komai ba se indomie,ki daure ki taimaka ki girkamun" kallon mamaki tabita dashi sannan
batare datace komai ba ta juya zuwa ktchn din a gurguje gani karfe uku ta gota momy se waya
take mata akan bata zoba ta dafa ta kawo mata,har takai kofar barin parlor din tajiyo karar daya
bata mamaki "Nashiga ukuna ni haleemah,wlhy boo me baran iya ciba yaji ne aciki sosai ga
kuma magi yamun yawa" wani mugun kallo shaam ya wurgawa hafsat

"muguwar yarinya dawo nan ai kinsan muguntar da kika kullah me baqar zuciya,dan ubanki da
dakikasan bazaki iyaba meya hanaki kanki tsaye kice bazakiyiba,wato wannan cikin na jikinta
shi kikeso ki kashe ko? Muguwar banza muguwar wofi wlhy yau bama inda zaki,kin dinga girka
mata indomie kenan se sanda kika girka mata kalan wanda tace ya mata" kan tayi magana
kuka ya kwace mata se kuma wayanta ya soma ringing,dagawa tayi tana me hadiye kukan
lokaci daya ta qaqalo murmushin daya baiwa shaam mamaki takuma saisaita muryanta

"Momy dan Allah kiyi hakuri,wlhy Aunty Haleema ne batada lapiya inaga kamar bazan samu
damar shigowa ba yau,kinga ita kadaice bazan barta haka ba" murmushi momyn tayi tace
"Eyyah Allah sarki Allah ya bata lapiya ki gaida ta kinji,yanzu se yaushe??"

"gobe sha biyu nake qare lectures inshaa Allah daga school se gidanki momy karki damu" "To
Allah ya kaimu hafsat Allah ya miki albarka kinji" Ameen kawai tace ta ajiye wayan sannan ta
juya zuwa kitchn din,dafa wani tayi bata saka yaji ba ta kawo,ai loman farko ta zubar aqasa ta
kalli yaa shaam fuskar nan harta soma kawo ruwa "Yaa shaam kaci kaji wlhy ba taste yanzu fa
ko d'an green pepper ta saka man amma haka tayishi,Allah ni bazan ciba kuma" Tsaki hafsat
taja bada shirinta,dama fa hafsat gwanar rashin kunya ce kurin tsoron yaa shaam ne ke
durqusar da ita,yau kam ta cika fam

"Gaskiya Aunty haleema bansan ya kikeso na miki ba na dafa wancan kince bazakiciba na dafa
wannan indomie kince yaji,na kuma dafa wani kince ba yaji ni kije ki dafa da kanki,ko aikin
bauta nazo na muku wlhy ko zaku kasheni bazan dafa muku wani ba" kallon mamaki shaam ya
mata domin shi har tasoma bashi tausayi ya matso kusa da ita yace "Jeki kitchen ki dafa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0