Showing 30001 words to 33000 words out of 54422 words
ta hadiye wasu yawu sannan ta
furta
"kayi hakuri uncle say ka rabu dashi,wannan mutumin na tsaneshi wlhy" matsowa yayi kusa da
ita yace "Mesa nakejin matukar tsoro da yawaitar fad'uwar gaba hafsat? Gabaki daya banjin
dadin tawa rayuwar sekace nine nake ciwo,wlhy hafsat hankalina baya kwance,bawai wannan
muhammad dinba da kalamansa aa, komai ma senake ga kamar mutuwa zanyi ayanda nakejin
duniyar tanamun qunci" zare idanta tayi waje
"Haba Uncle sayyeed? Ya kake magana haka? Inshaa Allah atare zamu rayu babu abunda ze
sameka,kuma inshaa Allah atare zamu mutu" murmushi ya sakar mata yace
"Zanje gida na dawo nanba jimawa inshaa Allah" batayi magana ba haka yaja kofar ya fita, ita
dinma dai haka kawai takejin tsananin faduwar gaba me tsanani,hankalinta sam baya
jikinta,koda momy tazo bayan isha abinci kurin tabata sukayi sallah seta kwanta,say yazo sun
dan taba hira,wuraren karfe tara yamata sallama akan seda safe ze dawo,har kuma ze fita ya
dawo ya kalketa yace
"Hafsat idan har Allah yasanya wani abun yafaru dani kimin adu'a ita kadaice nake buqata
agareki" kura masa ido tayi dukta rude murya na rawa ta furta
" mesa kake irin wannan tunanin wai? Sabida kawai wannan muhammad din yayi wannan
furucin seka damu,inshaa Allah ba abunda ze iya yi maka" murmushi ya sakar mata
"Hafsa nafasan waye muhammad,sam yayi furucin dayayi ne sabida kawai ransa ya b'aci amma
mutum ne me nagarta sosai,matsalar sa d'aya kafirar zuciya da rashin human relation amma
hes a nice person" shiru ta masa kawai amma bawai danta yarda ba,tanaso ta tsani
muhammad dinnan amma zuciyarta taqi aminta da tsanar tasan......
Wuraren sha dayan dare unle say ya dawo wurin hafsat,zama yayi kusa da ita yamata a dua
lokacin tamayi bacci sannan ya kashe fitilar dakin ya fito ganin ko momy bacci ya kwashe ta
batare data kashe fitilar ba,yana barin dakin ya kula da mutumin daya wuce part din fuskarsa a
rufe da mask se suaune kansa yakeyi,harya wuce kuma seyakasa nutsuwa ya dawo baya
gaba daya,binsa yayi yaga lallai dakin ya dosa,ya murda sad'af sad'af ya shige aikam say da
sauri ya biyo bayansa shima yafada dakin,ganin yayi mutumin ya dauki filo ya danne fuskar
hafsa se shura kafa takeyi acikin duhun dakin,kuka kura yayi yayi kanshi aikam fada ya kaure
har suka tashi momy,da sauri ta haska torch light dinta tana ganin haka ta kunna fitilar dakin
kokawa suke sosai da sauri ta kwallah kara,amma kan wani ya farga kasancewar darene har
mutuminnan ya daga wuqa ya cakawa uncle say a qahon zuci har wurare biyu......ko kafin
mutane su zo wancan mutumin ya gudu,hafsat ma ta farka tuni sakkowa tayi tama manta
zancen karaya,sayyeed kuwa tuni rayuwa tayi halinta,se kuka takeyi tamkar ranta ze fita a haka
doctors dake nan sukaxo,kowa se hawaye yakeyi ana fadar mutuwarsa ....
Mom nuaiym
[2/9, 8:55 PM] Billy Galadanchi: *í ½í²…BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*í ½í²…
Love story 2018
Billy galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
Wattpadd@ 68billygaladanchi
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*
23
Ba shakka hafsat ta gama haukacewa da mutuwar uncle say,tsakani da Allah tanki tana gani
aka fita da gawarsa wanda ko ba'a gaya mata ba ta tabbatar wlhy ya mutu,ko dan ganin jinin
daya zuba ajikinsa, kasa zama tayi asibiti dole aka wuce da ita gidansu.......tunda hafsa taje
gida take kuka ba qaqqautawa shi kanshi shaam din ya girgiza da mutuwar
sayyeed,musamman da yake ko a dakin da hafsat take aka kashe shi,kuma ita bata gane
wanda ya danne mata fuska ba da filo,kasancewar acikin dubu ne farkawar momy ne ta ga
sayyeed.....
Da yamma yan sanda sukazo gunsu da tambayoyi kallon ta sukayi bayan ta momy ta gama
fadar iya abunda ta sani suka ce da hafsat
"Hafsat dukda yake munsha mamakin ance kinada matsalar ido,amma se gashi faruwar
abinnan idon naki ya bude,muna san sanin shin sanda abun ya faru kina ganine? Ko kuma aa
bayan faruwar abun kika soma gani" kallon dan sandan tayi gaba daya gani tayi ya gama raina
mata idan dai har karatun datayi na lauya harta zama qwararriya ba shirme bane a yanda ta
fahimci kalamansa zarkin nasa akanta ya fara shi
"Tun ranar danayi a hatsari na farfado komai ina ganinsa lapiya lau" gyaran zamansa yayi ya
kalleta sannan yace
"To meyasanya likitoci sukace bakya gani,kema kuma kike ta faman pretending?" kallonshi tayi
shima sanda ya razana da kallon sannan tace.."Banasan auren yaa shaam,shikuwa so yake na
aureshi sabida wata manufa tashi da ban santa ba,nakuma san ba dan Allah bane da wannan
yaje ya sanya kakanmu tace dole sena aureshi,ranar dana samu accident ranar naji doctor
yana wa su daddy bayanin cewar idan har na farfado idona ya sake tabuwa baze
gyaruba,kasancewar shine na biyu,daganan dabara tazomun ta nunawa duniya cewar bana
gani sabida nasan yaa shammaz baze aureniba ina naqasashiya,uncle say da abokinsa
Dr.shuraim sunsan ina gani tangaram dama shirine se bayan na auri zabina sannan kowa
yasan ina gani clear" nisawa kowa dake wurin yayi ganin tana fad'ar gaskiar ta kai tsaye,police
din ya sake cewa
"Menene zaki iya tuna ya faru a daren jiya?" hawayen daya gangaro mata ta saka hannunta ta
share sannan tace
" Kawai dai nasan munyi sallama da uncle say tun karfe tara na dare akan se washe
gari,daganan yana fita na kwanta nayi bacci,acikin baccin ne naji an sakamun pillow a danne
mun fuska sosai bana iya numfashi,can kuma sena ji an sakeni na sanya hannuna da ke lapiya
na janye pillow din amma sabida yanayin dakin ba wadatar haske banga komai ba seda momy
ta farka ta haska torchlight jin hayaniya,ananne naga uncle say da wannan mutumin me mask a
fuska suna kokawa,harya caka masa wukar,kuma kan momy tayi wani yunkuri mutumin ya fita
da gudu,amma fa ni naga face d'insa asanda uncle yaji azabar ya caka masa wuqa ya da
damko face mask din wacce ina saran tana hannunku" nisawa police din yayi yace
"mungode da amsoshinki kai tsaye,dakuma hadin kai,muna fatar idan muka dawo zamu samu
hadin kanki idan buqatar hakan ya taso" a fusace ta miqe tace
"Sabida yana da kudi? Ko sabida yana taqama da isa dacewar shidin wanine ze kashe mun
muji ya zauna lapiya,ku sani akwai sadakin sayyees akaina wanda yake nuni ya kuma isa hujjar
kasancewata matarsa sabida haka wlhy sena ga karshen shari'ar nan,matsayi na na cikakkiyar
lauya nice zanyi bincike me ma'ana idan har ku bazakuyi ba" cikeda rashin fahimta suka kalli
juna sannan dayan yace
"Ban gmfahim ceki ba?" atake ta zayyane musu abubuwan dasuka faru tsakanin muhammad da
sayyeed da kuma furucin muhammad ta qara da cewar "A shari'ance muhammad ya aikata
babban kuskura furta wannan kalamin kawai balanta na yakai ga aikatawa,nice zan sameshi da
nawa tuhumar nice zan bincikeshi dan kaina ina ikon tsayawa kaina nima din cikakkiyar lauya
ce meji da kanta" kallonta mutumin yakumayi yacewa
"haj amma ina ganin kamar Barrister muhammad kike magana ko?,a iya sanina dai shine
mutumin da akace ya kade ki,kuma babban lauya ne da ake fafatawa dashi a fadin kasar nan
gaba daya" tsaki taja ta sanya hannunta me lapiya ta bubbuga kirjinta
"Sabida yana taqamar shi babban lauyane seya kashe mutum? To nima babbat lauyace ta
kaina,kuma wlhy senabi jinin mijina" shiru sukayi ganin yarinyar nacikin zafin mutuwar....
*Bayan kwana uku*
Shirin ta tayi tsaf kasancewar mahaifinta yamata komai na lauya me zaman kanta bata
gwamnati ba,domin kare haqqin sayyeed daya mutu akanta,kai tsaye gidan Barrister
muhammad jalalludeen Auwal yana zaune a harabar gidansa yana kurbar lemo a hankali
cikeda yanga,dama kuma yasan da zuwanta kuma police ma sunzo sunyi nasu har sun
wuce,har a news paper an sanya tuhimarsa da yake wanda wannan ko kadan be daga masa
hankali ba sam sabida yasan meya taka hmmmm.....A yangace ta fito daga cikin motar zuwa
inda yake zaune shi kuwa tun daga nesa yake kallonta yana wani murmushin kin rainawa kanki
hankali,Tana zuwa ya miqe tsaye sinfi mintuna biyu suna kallon juna,hannu ya miqa mata,sanda
tabi hannun nashi da kallo sannan a wulaknace ta miqa masa nata yace cikin muryarsa me
tarwatsa littafinta
"Bar.muhammad j Auwal AkA j.A" murmushi tasaki me ban haushi ta furta a yangace
"Bar. Hafsat muhammad gaya AKA Miss poojah" murmushi ya sake meban dariya
"Nice meeting u young barrister"
"Nice meeting u too the oldest one" murmushin ya sakeyi tace "ina fatan kasamu labarin suing
naka damuka yi a court,ina kuma fatan ka nemi qwararren lauya macecinka" juice ya dauko ya
kurba sannan ya zauna ya kalleta ya nuna mata da hannu kujera
"Have a sit miss poojah" zama tayi ta dauki cup na juice da hannunta me lapiya ta kurba sannan
ta kai dubanta zuwa gareshi tace
"Bakace komai ba" sanda yaja numfashi sannan yace
"Hafsat lallai kin dakkowa kanki abunda bazaki iya karasawa ina so ki sani bakin rijiya fa ba
wurin wasan makaho bane,ni dinnan nafi karfin tunanin ki wlhy"Murmushi tayi har haqwaranta
suka bayyana sannan tace
"Tabbas zancenka dutse ne Br. J.A,Amma ina san ka sani wlhy bazan saurara maka ba harse
naga bayanka" cup dinshi ya dire akan table yace cikin nutsuwa batare daya kalli inda take ba
"Miss poojah courage dinki yana burgeni sosai,abinda nakeso dake shine wannan fafatwar
tamu ta zama deal" kallonshi tayi ta kauda kanta gefe batayi magana ba yace
"Idan har kikayi wining case dinnan zan karbi hukuncin kisa kuma zan mallakamiki daukacin
dukiyar dana mallaka fiye da rabinta zan baki,dukkanin abubuwan dana gada awurin mahaifina
kuwa kashi uku zan masa in baki kashi biyu in yarona daya tilo dayan kashin,idan kuwa har
nine nayi wining wannan case to kuwa ko kina so ko bakyaso sekin aureni" da sauri ta dago ta
kalleshi taga shidin ba ita yake kallo ba,sai saita kanta tayi ganin deal din ba wani babba bane
kasancewar tanada yaqinin shi yayi kisan kuma zata diddigo abun,tace
"Na amince da wannan kuma zanyi" ta miqe kallonta yayi yace
"Bakida wayo,shiyasanya nace dake bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane ai,an tab'a deal
ba'a rubuceba idan na cuceki fa? Zama zakiyi mu rubuta muyi sighning inada photocophy
machine se nabaki copy daya nima na ajiye dayan kuma ke zan baiwa orijinal ma" yafada yana
murmushi kauda kanta gefe tayi sannan ta zauna amma sam bata karayaba,sanda suka gama
komai sannan ya miqa mata hannu yace
"Deal?" murmushin yaqe ta masa tace
"Deal" daganan ta karba ta juya yace
"Semun hadu a court poor poojah" juyowa tayi ta washe masa baki sannan tayi gaba abunta ta
shige mota sukayi gaba,ya koma ya zauna yace "Smart poojah".
Toophaaa jama'a wasa farin girki yanzu ake book kam,yanzu race ya fara.
Idan kaji dadin wannan page dan Allah comment and vote.....
[2/10, 10:05 PM] Billy Galadanchi: *í ½í²…BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*í ½í²…
  Love story 2018
Billy galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
Â
Wattpadd@ 68billygaladanchi
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*
                   24
Tunda hafsat ta koma gida take nazarin abubuwan da suka shiga tsakaninta da J.A sam bata
ankare da wautar data aikata ba se yanzu,idan ya kasance shi yayi wining na case din fa? Ko
kuma ya kasance ba shi bane yayi kisan fa?" wani tsoro ne ya shigeta lokaci d'aya qirjinta ya
soma wani irin dokawa,dafe kanta tayi ta shiga rero adu'o i kala kala na tsari.....
  Brr. J.A kuwa bayan fitar hafsat a fusace shima ya fita,be tsaya ko ina ba se asibitin uduth kai
tsaye wurin masu bada katin shiga wurin ya nufa bayan sun gaisa ya nuna musu ID card d'insa
sannan yace
"Nazo bincike ne akan wani case na murder da aka samu anan asibitin kwanakin baya,ina
matukar buqatar had'in kanku domin tallafawa family d'in wannan babban rashin ba bisa haqqi
ba,nima kuma da ake zargi ku taimakamun matsayin na na baban lauya me matsayi ace ana
zargina da kisan kai" sosai suka fahimce shi dama mutane da dama sun dad'e da qaryata
zancen zargin da ake masa kasancewar mutane da dama sunsan halinsa na nagarta, babban
cikinsu yace "Wane taimakao kakeso mu maka yallab'ai?" gyaran zaman madubinsa yayi
sannan yace
"Record nakeso na dukkanin motocin dasuka shigo asibitin nan aranar 11/11/2016 tunda
shabiyun daren shigar ranar har zuwa shabiyun daren wucewar ranar,na kuma san kunada cctv
camera anan so idan ba damuwa ina buqatar video d'in" gyaran zama ogan nasu yayi sannan
yace dashi
"Dama plate number ne muke d'auka mubaka card na shiga,se kuma sunan motar da color
dinta da model number na motar,cctv kuwa yana daukar shiga da fice na kowa a asibitin
nan,sabida haka yallab'ai komai daya dace zamu baka inshaa Allah" godiya ya masa sannan
yashiga tattare muhimman informations da aka lokaci daya ya harbo bakin zaren.........
Shammaz kuwa tunda abun yafaru yakejin wani tausayin hafsat,a qasan zuciyarsa kuwa
yanajin wani iri tamkar laifin sane komai,zuwa yayi ya samu haj Innah ya sanar mata yafasa
auren hafsat baya santa kuma ta janye qudirinta,dama ita tunda taji cewar sabida auren sa da
aka ambata hafsat ta gigice harta samu hatsari ta kudurta aranta bazata qara wannan furucinba
kuma idan ma hafsat taji sauqi zatace abata zab'inta,shi kenan kuwa ta amince wa shaam akan
ya gayawa iyayensu......
*Court*
    Hafsat ce a zaune tare da lauyan me kare J.A se wasu lauyoyin guda biyu,acikin babban
court dake jihar sokoto,Justice d'inne ya rero bayanin zargin da akewa Brr. J.A tare da baiwa
masu qara damar bayyana hujjojinsu daya sanya suke zarkin sa da kashe likitan,batare da bata
lokaci ba hafsat ta zayyane komai daya faru agabanta ta qara da cewar
"Furucin sa kad'ai ya isa ya nuna mana cewar shine yayi kisannan" dayan lauya din me kare
wanda ake qara ne ya miqe yace
"Objection my load" kallon sa justice din yayi shikuwa yaci gaba
"my load be kamata lauyan wanda suke qara ya riqa alaqanta laifin kisan kai kacokam ga
wanda ake zargi ba,tunda ai zargin sa ake bawai an tabbatar ba" justice ya kalli hafsat yace "A
kiyaye" ya sake kallon Brr. Khaleed yace
" yallab'ai zamu so akara mana lokaci kadan domin gabatar da shedunmu kuma zasu so a
gayyato mana babban Abokin marigayin anan wato Dr. Shuraim" dama aka basu daganan aka
d'age zaman sena da sati d'aya.
*Bayan sati d'aya*
   Lauyan wanda ake qara ne yace fara magana kamar haka
"My load wannan gabaki d'aya record ne na motocin dasuka shiga asibitin ranar da abun ya
faru,acikin mun samu mota iri daya kirar honda civic kalar ja wacce aranar tashiga asibitin
kusan 7 times a wannan ranar cctv camera ta main gate data ward din da akayi kisan duk sun
tabbatar mana da shigar mamalakin motar so bakwai a wunin ranar, kuma duk shigar sa kai
tsaye ward d'in yake nufa wato inda sin din ya faru kuma mayannin dayayi duka ba face mask a
fuskarsa se ziyartarsa ta karshe inda har yayi nasarar hallakar da sayyeed,sannan kuma a
binciken da muka gabatar,makashin yaje kashe hafsat ne ita kadai bawai da sayyeed,sabida
sayyeed ba asibiti bane gidansa,kuma idan ma kasheshi zeyi sedai yaje gidansa ya kashesa
acan,abinda muka sani shine sayyeed taimako yaje a yanda muka gani a camera shine harya
fito ya ganshi ya shiga seya bisa a baya,abinda camera ta kasa nuna mana shine menene ya
soma faruwa acikin dakin kasancewar babu wadatuwar haske ya sanya se bayan yayi kisan ya
juya ze fita haske ya wadata kuma har fuskarsa mun gani,abunda masu qara sukace wanda
yaje kisan hafsat itace wacce yafara dosawa pillow a fuska kafin sayyeed ya cece ta,idan ko har
hakane furucin da muhammad yayi sam bashida alaqa da wannan kisan na sayyeed" shiru yayi
hafsat gaba daya kanta ya daure sabida batayi wannan tunanin ba shi kuwa yaci gaba
"Munyi nasarar cafke wanda yayi kisan,kuma munaso yazo nan da bakin sa yayi bayanin
wanda ya sakashi kisan idan har kotu ta bamu damar yin hakan" izini. Aka basu akan su
gabatar da mutumin......koda alqali ya tambayi mutumin seya fara bayani kamar haka
"Da farko dai sunana kamilu,kuma ni dan area boy ne ina zamane a unguwar iraqi dake cikin
garin sokoto,ina zama wani likita me suna shuraim yazo ya sameni akan yanaso in masa aiki
akan wata mara lapiya me suna hafsat,ni kuwa dama ba ruwana aiki ko wane irine indai na
kudine to kuwa zan yishi yabani details na komai da komai na dakin datake da time da babu
yawaitar mutane awurin yakuma ce na danneta da pillow sabida gudun zargi ganin zan samu
kudi ya sanya na amsa tayinsa naje nagama monitoring na wurin da komai,nashirya rana daya
naje,shine qaddara ya fadowa wanda yazo tare fadan na kasheshi da wuqa ta,shine wayannan
suka bi ta hanyar kotar danake hawa suka kamoni" jinjina kai kowa keyi yayinda hafsat ta rikice
tabbas wannan shine mutumin data gani kuwa,dama sun buqaci ganin shuraim shi kuwa be
karaji daga wurin wannan mutuminba so bezata hakan zata faru ba,koda aka buqaci yazo beyi
gaddama yazo a rude ,tambayar sa akayi dalilin san kashe hafsat baiwar Allah yafara magana
kamar haka
"Na kasance ina matukar san yarinyar tun tana secondry schoool amma ta wulakantani,har
kuka nake mata amma bata damu dani ba,ganin nayi nayi taqi kulani yasanya nashiga malamai
na sanya duk wani namiji idan ya kalleta zeji yana matukar tsanarta idan kuwa me riqon
addinine yafara santa semu saka masa mafarkai na tsoro akan zamu kashe duka su biyun
harse yagaji ya kyaleta,kwatsam mukazo asirinmu damuke mata ya dena tasiri bincike ya