Showing 15001 words to 18000 words out of 54422 words

Chapter 6 - Bakin Rijiya Book Compelet Billy Galadanci

02 Aug 2026

947

jijiyar tata
me aika jini me makon saqonnin fahimta akanta aikinta ze janyo wani matsalar,kodai lalacewar
ido,kokuma ta kunne sabida haka sekun saka haquri a lamuranku" kuka shaam ya saka tamkar
wani qaramun yaro sabida shi gabadaya tunaninsa ya tsaya cak,tayaya ze kalli su abbba da
daddy da wannan zancen? Ina courage din? Menene ma mafita agareshi?" A yanda ran Abba
haris ya baci idan wani abun ya samu hafsa agarin aikinnan ai tsaf ze tsine masa wlhy kowa ya
huta,dak'yar Dr.sayyed ya rarrasheshi yabar asibitin....

*Ur vote is important also ur comment fan's,inasanjin ra'ayoyinku,i hope ur enjoying this story*

Mom Nu'aiym[1/21, 9:43 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho
bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

12
Dr.sayyed tunda yaje gida yake tunanin yanda zasu b'ullowa lamarin hafsat,haka kawai ya
tsinci kansa da tsananin tausayin yarinyar,indai har acikin halin hauka bata manta muguntar da
yake mata tokuwa lallai abun ba qaramun abu bane yana cutar da ita over,sam bayaso wani
abu ya tab'u a jikinta kuma yasani sarai chancess na rashin samun hakan ba qaramun abu
bane, yanaso ayi aikin as soon as possible amma fa sam bayaso ayi garaje a samu

matsala.......

Shaam kuwa koda yaje gida masa bacci yayi,bangaren zuciyar sa na masa zafi akan abinda
yaji da kunnensa haleemah na fad'a itada uwarta,yayinda dayan bangaren na zuciyarsa ke
masa rad'ad'i akan abunda abbansa yace dashi akan hafsat,wani dogon tsaki yaja yace a
asarari "Gaba d'aya wannan hafsat d'in ta jamun masifa wlhy,dabadan ta maqale akan seta
aureniba wlhy daban shiga wannan mugun yanayinba,ita kuma haleema yaya zatamun haka??
Ina sanki sosai haleema ko baki sani bane" a haka ya dinga sambatu shi kadai harna
shirme.......

Dr. Sayyeed da kanshi yayiwa su Abba bayanin rashin lapiyan hafsat da kuma da kuma
abinda yake hange idan har aka mata wannan aiki,fatanshi d'aya ayi aikin lapiya kuma adu'arsu
itace abun nema" Babu yanda suka iya dole su yarda da akan ayi aikin dukkuwa dayake Abba
haris yaso a fita da ita waje daddy ne yace duk inda akayi aikin nasara a wurin Allah take,da
wannan aka tsaida ranar aikin nan da sati d'aya......

Hafsat dai tana nan jiya iyau,ba abinda ya ragu har yau ba hankali akanta,yaa shaam tunda
suka yaji wannan zancen nasu haleema seya kirata yace ta zauna gidansu se bayan sati biyu
zuwa lokacin hankalinta ya kwanta dama kuma hakan takeso ya sanya ta kwantar da hankalinta
tayi gidan bokan ta....
Sati ya zago Aka shirya shiga da hafsat tiyata yaa shaam har kuka yayi abubuwa sun taru sun
masa yawa yanzu ya tabbatar wa kansa cewar abinda yaji gaskiyane,coz kwana kusan uku
baya samun number wayan haleema kuma koyaje gidansu se a ce masa wai batanan sunfita
da momy........Aiki dai anyishi cikeda nutsuwa da kuma na sara an samu damar kwashe duk
wani jini daya taruwa hafsat a kai, yanzu jira kawai akeyi ta farfad'o, a ga yanda zata tashi......

Umma da momy sunyi jigum jigum suna adu'ar farfado war hafsat lapiya,se suka jiyo
maganarta sama sama "Saro kunna mun fitilar d'akin nan kuma ki bani ruwa" kallon juna su
umma sukayi sabida su sam basusan da wani zancen wai za'a iya samun matsala ba,da sauri
suka miqe atare sukayi kanta,umma ta riqe hannunta tace
"Sannu hafsat ai ranane aikin da'aka mikine akai,inaga lallai alluran nan ne be sakeki ba
shiyasanya kike ganin duhu,sannu kinji" Shiru tayi tafara tunano abubuwan da suka faru da ita
ita dai bata jin wani jiri gashi ta tabbatar wa kanta cewar idonta abude yake yama za'ayi ace wai
allurace,amma seta kama bakinta tayi shiru kawai tana me mamakin har meyake damunta
daza'ace wai ammata aiki akai,wasa wasa hafsat haka ta wuni ta kwana bata gani zuwa
wannan lokacin har su momy sunsan halinda ake ciki kowa ya sakata agaba har Shaam tana
bacci tana farkawa tace

"momy zansha ruwa?" ruwan momy ta bata tasha sannan ta kwantar da ita gyaran kwanciya
tayi tace "Momy dan Allah wai se yaushe gari ze waye ne,ni nagaji da ganin duhu idan ma garin
be waye ba ku kunna mun fitila" D'aukacin mutanen d'akin suka saka kuka sabida tsabar

tausayi daddy ne ya qarasa gunta yace

"Hafsat nasani maganar dazan fad'a miki zaki jita wani iri kuma tabbas zata tayar miki da
hankali,amma inaso kiyi hakuri ki yarda da khaddarar Allah ya d'aura miki,khaddarace ta
sameki sakamakon dukan da yayanki yayi miki wannan ne ya sanya kanki ya samu matsala na
tab'in hankali, to agarin yi miki aikine kuma wata khaddarar ta sake samuwa gashi dai munyi
nasara hankalinki ya dawo jikinki amma an tab'a miki wata jijiya aka wacce tayi sana diyar
lalacewar idonki yasanya kika dawo makauniya bakya gani" shiru tayi kamar yanda kowa yayi
shiru tamkar bataji meyace ba secan hawaye ya fara gangara daga cikin idonta da suke abude
bazaka taba cewa basuda lapiyaba ,batayi magana ba wannan ya sanya kowa ya sanya
bakinshi ana bata baki seda taji kowa yayi shiru sannan ta sanya daya hannunta dabashida
ruwa ta dafe qirjinta tace cikin d'aga murya

"meya sanya a rayuwa nayi rashin sa'an zuwana aduniya? Meya sanya wannan baqar zuciyar
tawa takesan mutumin da yafi qaunar mutuwarsa akan ya d'aura idonshi koda akan me
ita,meya sanya a rayuwa sam na zab'i bak'in cikina akan farin cikina,meya sanya zuciyata
keson wanda bashida buri illah yaga qarshenta,lallai ina cikin tashin hankali ba adadi,lallai yaa
shaam da inada ikon raba wannan wahalalliyar zuciyar tawa da k'aunarka wlhy da nayi a
yanzu,inama ace inada ikon raba raba rayuwata da ruhina ko zan huta da wannan baqar
soyayyar da batada ci gaba ko kad'an seci baya,ina ma ace zan iya sanya hannu in lalubo inda
rad'ad'in sanka yake inyi wurgi dashi,kaico na dana zab'i abu mafi muni arayuwata,kaicona
dana zab'i mummunan k'haddara da hannuna khaicona dana siyo makancewar idona da
hannuna kaicona ni hafsatu,kaicona ni lelen daddy da Abba" wani razanannen kuka ta saka me
tsuma zuciya wanda baya misaltuwa duk kuwa cikin d'akin aka rasa me
rrrashinta.......Dr.sayyeed ya tabbatar musu da cewar matsalar bame yawa bace idonta ze iya
bud'ewa yanzu,ko gobe ko anjima ko wata ran ko wata shekara kokuma har abada,Allah shine
yabarwa kansa sani,haka hafsat tayi wata daya a asibiti gashi sam ya kasa yiwa halima komai
sabida san dayake mata kurin dai ya qaurace mata kuma sannan be nuna mata komai ba,har
aka sallami hafsat ta koma gidan Abba haris.

A gida Abba haris yayi kiran shammaz agabdan daddy da momy ya kalleshi cikeda nutsuwa
yace

"shammaz abinda yasanya nayi kiranka ba komai bane illah zancen komawan hafsat d'akinka
wato gidan auren ta" Da sauri ya d'ago ya kalli abba yace dashi "Abba nifa na rigada na saki
hafsat kuma bance zan maida ita ba wane komawa kuma zatayi,kurin dai Allah ya bata wani
mijin ta aura" cikeda mamaki kowa ya kalleshi wannan karon har daddy abba yayi karfin halin
cewa

" Ai wlhy tunda ka nakasa ta seka zauna da ita,so kakeyi ka gama lahanta mata rayuwa" cikin
bacin rai yace

" Haba abba nifa ba qaramun yaro bane,sa annan kuma zakuce zakumun dole,yarinyar ban

sota tanada lafiyaba se yanzu,dan Allah na rokeku karkuce zakumun dole kalar na farko kundai
ga ba aci nasara ba,ba alkhairi a tare da wannan auren,inshaa Allah zataji sauqi ku aura mata
wani,kuma ni ba qinta nakeyiba kurun dai ina gudun gurbacewar zumuncine sabida kunga
bawai san aure nake mata ba,kuma ma koba itaba banasan auren zumunci" Sosai da sosai
maganganun shi suka girgiza rayukan ilahirin mutanen wurin,lallai shaam baze rasa yin shaye
shaye ba,Abba haris miqewa yayi yace

" Bazan maka baki ba Shammaz amma kaje duniyace,inshaa Allah kana darai hafsat zataci
gaba kaikuwa kana bayan yan baya" yana kaiwa nan yayi waje,daddy ma waje yayi batare da
yayi magana ranshi a b'ace momy ce tace

"kaima danane shaam amma dan Allah inaso ka dubi girman zumunci ka taimaki
qanwarka,waye ze aureta tana makauniya yarinya ga qarancin shekaru ko haihuwa batayiba"
budar nakinshi se cewa yayi

"momy dan Allah kiyi hakuri wlhy bazan iyaba" aikam momy kuka ta saka cikeda takaici shikuwa
ko a jikinshi yayi waje abunshi....

Mom Nu'aiym
[1/22, 7:56 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                     13
Yaukam rayuwar daddy tayi matuqar b'aci da wulakncin shaam akan hafsat,lallai wannan yaron
yazo da salo na raini iri iri,banda haka tayaya ma agaban su kaikoma ba agabansuba zece wai
baze auri hafsat ba haryana iqirarin be sota tana da lapiyaba se yanzu data zama
nakashashiya,ba abunda zece dashi koya nuna masa zega iya gudun ruwanshi tare da jiran
matakin da Haris ze dauka.......

   Hafsat zaune tanaso taci abuncin dake gabanta amma bata saka cokalin wurin daya
kamata,har ranta takejin wani tuquqi,wannan ya sanya ta ajiye cokalin ta laluba ta gincira,duk
wannan abun datakeyi khairri na kallonta tana hawayen tsananin tausayinta,zuwa tayi ta zauna
kusa da ita ta kamo hannunta tace "Sister ya bakici abuncin da yawa ba kaddai harkin koshi?"
Murmushin yake tayi tace " Na qoshi ne wlhy"

"Nasani baki koshiba hafsat,kawai sabida bakya saka spoon din inda ya dace ne,kiyi hakuri na
baki kanki saba kuma inshaa Allah zaki warke ai haka doctor yace zakiji sauqi kinji" hawayen da
dukkaninsu ke qoqarin tarewa ya silalo musu hafsat tace "Khairiyya haryaufa yaa shaam bezo
ya duba niba,da gaske manufarshi kenan ya rabu dani har abada?" kukane ya kwace mata ta
toshe bakinta,khairiyya tama rasa me zatace mata "kiyi hakuri hafsat,amma barin kira miki shi
awaya" batace komai ba wannan ya sanya khairiyya taje waje tayi kiran shammaz akan dan
Allah yazo hafsat ta damu da rashin zuwansa,beyi musu ba yace yana nan zuwa da dare.....

    A parlor zaune hafsat take a kujera me mazaunin mutum biyu,se shaam dake zaune a me
mazaunin mutum d'aya,dak'yar ya iya bud'e bakinshi yace

"Hafsat ya jikinki"

"Naji sauqi Alhamdulillah"

"Akace kina nemana?" sadda kanta tayi qasa "Yaya dama zancen komawa nane gidanka,dan
Allah kayi hakuri abubuwan dasuka faru wlhy ko mutuwan khaleefa ba laifina bane lokacin sa
ne yayi" murmushi yayi yace

"Haba hafsat,kewai bakya fahimtar abubuwane? Ban soki nakuma zauna dakeba sanda kike
mutum me lapiya,se yanzu dakika zama nakashashiya,na dade da fad'a miki sam bakin rijiya ba
wurin wasan makaho bane saura miki yaushe ki gama iddah,idan ma banyi kuskure ba aiba
idda a kanki,saboda haka kiyi hakuri ki kalli dahir ni bazan taba dawo dake gidana ba,ina miki
ao irinna yan uwantaka matsayinki na kanwata amma bawai zancen aure ba" dukda bata gani
amma hakan be hanata duban inda take jiyo sautin muryanshiba tace tana kuka

"Yanzu yaa shaam idan kai dakake dan uwana ka gujeni akan inada matsala waye aduniya ze
aureni? Kaine sanadin lalacewar rayuwata,ka b'atamun duk wani abu danake taqama
dashi,bani ga karatuna babu labarin future na,banida d'a ko d'aya a duniya da wanne kakeso
inji?" murmushi ya kuma yi
"Hafsat wlhy kinji na rantse bazan tab'a iya zaman aure dakeba,ke ni idan ma kinamun wannan
maganar haushi kike bani wlhy,kimun magana kanki tsaye indai zaki bani matsayin yayanki to
zakiga gata na haduwa,amma zancen aurennan yarabu kenan har abada,idn bakida wani abun
fada zan wuce"......sanda ta d'anyi shiru sannan tace
" Nayi dana sanin saninka arayuwa,nayi danasanin kasancewarka d'an uwa na jini agareni,nayi
danasanin aurenka,nakuma yi danasanin aurenka,nayi danasanin kasantuwar zuciyata tawa ina
ma ace canje aka mun bisa kuskure dana roqa a sauyamun da tawan sabida na kaucewa
wannan wahalalliyar soyayyar,daga rana me kama da yau inaso ka nemo biro da takarda
kakuma rubuta ka ajiye cewar ni hafsat nakashashiya nafita arayuwarka na har abada,na yanke
duk wata alaqa dake tsakanina dakai, harta zamanka d'an uwana,ko a hanya ka ganni karka

nuna sanayya tsakanina dake,bana buqatarka arayuwata ka sani ayau d'innan wlhy na tsaneka
tsana mafi munin tunani,bazan hana zuciyana haukanta na sanka ba amma zan iya haramtawa
rayuwata koda gaisawa dakai koda hakan yana nufin zan rasa ilahirin rayuwata kuwa tunda ai
ka gama nak'asani meya ragemun,nice nan yaa shaam zan tabbatar maka da cewar bakin rijiya
sam ba wurin wasan makaho bane" Yad'anyi mintuna biyu bece komai ba secan ya nisa yace
"Hafsat me kuma ya kawo maganar tsana anan nifa d'an uwankine" miqewa tayi ta soma
doddogara sandarta tana neman hanyar waje,kasancrwar tasan tsarin gida. Yasanya tayi
amfani da basirar ta ta nufi cikin gidan zuwa dakinsu.....duk wannan zantutuukan nasu akan
kunnen abba haris tausayinta me tsananin gaske ya rufe shi,daganan ya qudiri niyyar nemawa
hafsat lapiya kota halin qaqa koda kuwa dukkanin abinda ya mallaka ze qare.....

    Hafsat tama kasa kuka,gaba d'aya wani mummunan yanayi takeji a zuciyarta game da
shaam,tabbas yau tafara jin yana fice mata arai cikin qanqanin lokaci,wayantane ya soma
ringing tashiga lalubarta tana kamowa dama wurin sazata amsa kira baze mata wuyaba ya
sanya ta d'aga ta kara a kunne
"Assalamu Alaikum" shine tajiyo am fad'a a d'ayan b'angaren tun kafin tayi magana,cikin sanyin
murya tace

"Amun wa Alaikassalam,barka da wuni"

"Hafsat ya gida ya kuma jikinki?" "Da sauqi Alhamdulillah" ta bashi amsa "Sunana Dr.sayyeed
Hameed Ali uncle d'inki" Murmushitayi tamkar yana gabanta sannan tace "Ayya Uncle say ya
aiki yakuma kwana biyu?"

"Alhamdulillah hafsat,dama Number din abban ki damuke da afile nayi tankira baya zuwa gashi
kuma emagency case ne ya taso,shiya sanya nace barin nemeki ko zaki had'ani dashi"

"Babu damuwa uncle say barin je ingaya mishi seya duba last call nawa ya kiraka,amma sekayi
hakuri ni kadaice adakin khairii batanan,idan tashigo seta rakani gun abban" sosai ta bashi
tausayi yace "Babu damuwa hafsat,nagode sosai"
"nima nagode sosau uncle say Allah ya saka ma da alkhairi" har ranshi yaji dadin adu'arta
lokaci d'aya ya tuna da matarsa margayiya data tafi ta barshi da tsananin kewa,itace take
yawan masa adu'a irin wannan tun bayan mutuwar mahaifiyarsa......
  
   Office Abba yaje ya sameshi,bayan sunyi magana awaya,da suka gaisa Dr.sayyeed ya tattara
nutsuwarsa gun Abba sannan ya gyara zaman gilashin idonsa yace da Abba

"yallab'ai Allah shine ya dasamun tsananin tausayin hafsat wanda tunda nake ban taba jin
tausayin patient kwatankwacin yanda naji akan hafsat ba,musamman yanda na kula da karacin
shekarunta, da farko dai ni haifaffen qasar India ne amma kuma d'an asalin Nigeria,mahaifina
likitane kwararre wanda gaba d'aya acn yake aiki acanne ya had'u da mahaifiyata datake
Ba'indiya kasancewarta musulma gaba da baya ya sanya basusha wahala iyayensu suka

aminta dasuyi aurensu, acan aka haifeni kuma acan nayi karatu na gaba daya,bayan
mahaifiyata ta rasune mahaifina ya dawo ainahin qasarsa wato nan Nigeria a kuma birnin
sokoto,inada qanne na mata guda biyu suna gidansu mahaifiyata dake Babban birnin indiya
wato Goa acan suke karatunsu,ni kadaine nabiyo mahaifina nayi aurena anan har Allah ya
karb'i ran matata a wurin haihuwa......Dalilin daya sanya na baka tarihin rayuwata shine sabida
inaso kaje kayi bincike kaji koda zaka da abinda zan fad'a maka yanzu,dukda yake dakai
nakesan muyi tafiyar idan ma hakan ta kama" Dukda yake Dr.say yayi magana me harshe
damo amma abba be katse shiba yace "Ina jinka sayyeed"

"Mahaifina ya mallaki qatotuwar asibiti tashi ta kanshi a k'asar india inda kusan garuruwa hudu
a fadin qasar zaka tarar akwai branches nata,zan baka komai sekayi browsing ka gani,akwai
wani qwararren likita dake aiki a asibitin na mahaifina wanda shararre ne a b'angaren k'walwa
shine nayi waya dashi sabida al'amarin hafsat yana damuna a bakin shi naji cewa inshaa Allah
indai tanada rabon gani a duniya Allah ze bashi ikon mata aiki kuma fitowar farko ta warke
sabida badashi aka haifeta ba, dama nikuma zanje india gun yan uwana dakuma kula da
asibitin ta mahaifina shine nake sha'awar zuwa tare dakai da hafsat idan bakuda damuwa,nidai
ayanda nake tausayin hafsat bana san ko sisin ku har jirgi ma nine nan zan dauki nauyi
amincewarku kawai nake buqata dakuma uwa uba adu'arku" sosai Abba haris yaji dad'in
wannan zancen yace "wannan ai babban ci gaba ne sayyeed,kuma zancen yadda tun yaushe
aina yarda zancen kuma wai kyauta duk bata taso ba nine nan zan biya komai har zancen
tafiyar ma,kuma wlhy na gode nagode maka sayyeed Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarka ya
sanya haske acikinta yakuma d'aukaka,Allah ya jib'anci lamuranka ya baka wata matar ta gari
ya ilmantar da bayanka yakuma tallafi bayanka sayyewd" godiya sayyeed din tun kafin abba
yabar asibitin yafara processing visa batare da sanin kowaba.......

     Ranar wata juma'a hafsat na kwance ta rufe idonta acewarta ba amfanin bud'asu wayanta ya
soma ringing janyowa tayi ta kara a kunenta bayan ta d'aga,jin muryanshi kad'ai ya sanar mata
waye me kiran cikin shagwaban dabata masan tana dashiba tace "Uncle say se yanzu,ni baran
ma kula kaba Allah kuwan" murmushi yayi tamkar tana gabanshi
" Beauty kefa rigimanki baya qarewa,wlhy Aikine yasha kaina matuqa kiyi hak'uri yanzu ya
jikinki ina fatar kinji sauqi?" turo baki tayi "Ni bazan kulakaba" dariya sosai tabashi amma sabida
bayasan ya b'ata ranta yace "Kiyi hakuri mana Beauty,aina sanar miki uzurina kuma fa yau zan
siya miki pop corn da ice cream plus frozen coffee amor" murmushi tayi
"Ni bazaka siye ni da wannan ba bazan ma shaba,nidai kawai ka kawomun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0