Showing 6001 words to 9000 words out of 54422 words

Chapter 3 - Bakin Rijiya Book Compelet Billy Galadanci

02 Aug 2026

940

sena riqajin zuciya na yana tafarfasa
yaa shaam wlhy banasan kayi aurennan kaga nan? Ta nuna zuciyar ta da hannunta "zafi
yakemun zogi nakeji tamkar zan mutu,tun saura wata daya aurenka na rasa nutsuwata duk
sanda na tuna ko abinci bana iya ci bansan meyake damuna ba anya yaa shaam baka ganin
aljanaine suka shafeni?? Mesa ada ba ruwana dakai? Mesa ban damu da rashinka ba akusa
dani? Mesa ada bana leqen shige da ficenka ta window? Meyasa ko maima yaa shaam,a yanda
nakeji gameda zancen aurennan idn akayishi mutuwa zanyi" k'ura mata ido kurin yayi harta kai
aya,mamakin kalamanta ne yake shirin birkita masa k'walwa sam yakasa saisaita tunanin shi
idan har abinda zuciyar ke sanar masa gaskiya ne lallai kuwa da babbar matsala a gaba,sabida
sam shi wannan yarinyar kallon qanwa yake mata uwa daya uba daya,kai koda ba haka ba
shisam idan ba leeman shiba se rijiya,gaba daya hankalinshi ya tashi cikeda dabara ya kalleta
yace mata

"Lallai kam hafsat se aljanai sabida kin taba ganin inda qanwar mutum uwa daya uba daya tayi
kishi kotaji haushi akan zeyi aure,ki sani su e sukeso su shiga a tsakaninmu sam basa san suga
muna qaunar junanmu,kuma ta Allah ba tasu ba sabida haka kiyi hakuri ki dinga adua
kinji,inshaa Allah zasu rabu dake,kuma karki sake ki fadawa kowa wannan maganar" kai kurun
ta gyad'a masa yayi da mero dake jikin k'ofa a lab'e ta dafe qirji tana salallami domin kuwa tun
ba yauba ta fahimci sarai hafsat san shaam takeyi,inkuwa hakane iska tana wahalar dame
kayan kara domin kodajin wannan zancen dayaa shaam yayi ta kula baya ma buqa tar ta
sanarwa wani atilastashi aurenta yafi san son nashi ya kasheta kenan,aranta ta kudirta gayawa
momy gaskiya sedai ya kashe ta......

Bayan isha mero taje ta samu momy a d'aki bayan ta gaidata ta zauna ta fuskanceta sannan
tace

"Momy wata muhimmiyar magana nakeso muyi dangane da hafsat domin kuwa akwai matsala
akasa" kallonta momy tayi batare da bawa maganar muhimmanciba tace "Ina jinki"

"Momy na sani bani kadaiba dukkan nin mutanen gidannan sun kula cewar Kulele bata cikin
nutsuwarta da walwala sam,sa'annan ko abinci bataci gashi batama koda kallon data sabayi"
gyada kai kurun mony tayi taci gaba "To wannan kukan dakikaga tanayi a d'azu ba komai bane
illah kishin zancen auren yaa shaam datakeyi domin kuwa da bakinta naji tana sanar masa,take
ta kwashe komai ta sanar mata har sanda taji tana baiwa qawarta labari da abinda qawar tace
mata har tambayar data mata akan zancen yayanta ne kuwa uwa daya uba daya?" shiru momy
tayi tana nazarin kalaman mero tabbas idan basanshi takeyiba ba abunda ze sanya taji
hakan,inko hakane to wlhy da sake domin kuwa so sone amma sankai yafi komai,da wannan
tamiqe zuwa b'angaren daddy......ita kuwa Hafsat a daidai wannan lokacin ta shirya zuwa roqar
daddy akan ya barta taje gidan abba haris batasan yan biki su cika gidan ana hayaniya,zama
momy tayi ta zayyanewa daddy komai shi kuwa cikin fada yace

"Haba Nasara!!! Ina nidake muka zauna muka roqi dangi akan su rufe zancen cewa shaamaz
da Hafsat ba uwarsu daya ubansu daya ba har abada,tayaya ma yarinya zata so yayanta inama
hafsat ina sanin meye so?? Meta tauna vare ta had'a arayuwa?? " cikin fusata momyn tace

"Haba Alhj mesanya agaban duniya ka nuna kanasan gmhafsat amma a bad'ini ba haka
bane,karfa ma manta tsakaninta da shaam waka haifa da cikinka?? Itace 'ya daya tilo da Allah
ya baka,tayaya akan abunda bekai ya kawo ba seka dau zafi haka,tunda har tana sanshi mezai
hana a hadasu susu biyu a aura masa kowa ya huta" hara daddy ya wurga mata yace
"wlhy kinji na rantse kobada shaam ba bazan wa hafsat aure yanzu ba,tsabar mata bakuda
hankali,ke kinga karma ki nuna mata kinsan tana sanshi ki barta tayita haukanta,amma ba
zancen auren a tsakaninsu yana da wacce yakeso ita kuwa taji dashi karna kuma jin wannan
maganar wlhy" hafsat dake a waje kuma taji komai dafe qirjinta tayi tace "Ba daddynmu daya
dakai ba yaa shaam to waye babanka?? Menene ma dangar takarmj dakai?? SO SO kuma
tayaya meye mashi? Wannan shine abunda nakejin friend kullum tana mun magana akanshi
game da saurayinta da gaske san yaa shaam nakeyi? Anya ban dakkowa kaina wahala ba
kuwa? Lallai kuwa da babban aiki jaaa ma agabana.

Mom Nua'iym

            
[1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

Wattpad@galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                  06
Jiki ba k'wari ta juya zuwa d'akinta,sam hankalin hafsat beyi yawan dazatayi zurfin tunaniba ta
kasa tariyo komai,wayarta ta ciro daga k'asan filo ta kira huda,d'agawar farko tace

"Huda dan Allah kina ina yanzu??" da mamaki hudan tace "Ina kan hanyar zuwa gun Ashraf
tela" to yayi nima ganinan zuwa da maganar danike so muyi" kan huda tayi magana ta katse
wayan,da sauri ta zari hijab tayi k'asa a hanya tayi karo da yaa shaam ko kallonshi batayiba
sabida hankalinta sam baya jikinta,driver din momy ta gani tayi kiranshi da hannu,ta fada mota
sukayi gaba....a shagon janyo hannun huda tayi suka dawo mota ta kalleta bayan tayiwa driver
din umarni daya fita waje tace

"Huda wai da gaske sosai ni Hafsat ina san yaa shammaz??" kallon ta huda tayi cikeda
nutsuwa tace

"Ban fahimce kiba?" kwashe komai tayi dataji su momy na fada ta gayawa huda ta qara da
cewan "ke kadaine zaki iya fadamun gaskia dan Allah waida gaske wannan abun danaketaji
gameda yaa shaam shine so? Kuma shi din suwaye iyayenshi??" sosai huda ta gano hafsat
kuruciya ya mata yawa, banda haka ina zatasan su waye iyayen shaam,ni sawa tayi tace
"poojah ki nutsu mana,zancen gaskiya ko shakka banayi kina san yayanki kuma sosai bawai
kadanba,amma abunda nakeso dake shine kibi komai a hankali sabida kinga already an kusa
aurenshi kuma tunda su momy basusan kinji maganar suba karki fadawa kowa karkuma ki nuna
musu,wannan abun dakikeji idan yana waya da wacce ze aura da kuma idan ana zancen
aurenshi shi ake kira kishi,kuma kishin ya miki yawa ina tausaya miki sabida tunkan kisan meye
so da kishi kika fara kinsan kuwa illan kishi a tattare dake? Kishi masifane kamar yanda yake
halittane na Allah ajikin d'an adam sedai da yake na wani yafi na wani zafin,dan Allah hafsat ki
daure ki yakice sanshi a ranki,a yanda na fahimta da kika masa bayanin abinda kikeji game
dashi sarai ya gano sanshi kike sabida baya muradin ki yasanya yace karki sanar wa kowa,ki
manta dashi kici gaba da kallonshi a matsayin yayanki uwa d'aya uba d'aya" hawayen daketa
faman tarewane suka gangaro mata tace

"Huda lallai so masifa ne kuma kishi fitinane,indai haka so yake to a gaskiya da matsala,ni
bansan sanda na fara sanshiba tayaya zakice in cire sanshi a raina? Nida bansan yanda ya
shiga ba ya zansan yanda zan cire?? Wlhy bazan iyaba" tausayinta huda taji ta janyota ta
rungume tana bubbuga bayanta a hankali,a haka suka rabu jiki ba k'wari.....
*Bayan sati biyu*

Sosai aka cashe wurin bikin yaa shaam kuma acikin part d'inshi dake gidan anan aka kawo
amarya Haleematu,yau sati daya kenan da tariyarta,kullum hafsat ke zuwa tayata
aiki,kasancewar ba abinda takeyi agidan,ta d'auki shawarar qawarta ta dena nuna komai a idon
mutane harma momy ta soma qaryata zancen cewar hafsat tana san yayan nata....yauma
kamar kullum tana kitchen din Aunty haleema tana tayata aiki,suna d'an tab'a hira yaa shaam

ya shigo,ba kunya suka rungume juna har tana manna masa sumba a wuya

" Baby yadai? Bana hanaki yawan aikinnan ba? Kije ki huta mana tunda ga Hafsat ta iya komai"
kallon shi tai cikeda kissa tace

"Haba honey yaya daga zuwan yarinya tayani aiki seka wani ce na barta tayi,nooo ni banasan
small oga ta tasha wahala" hancinta ya danja ta saka qara yace "Kinga Baby da gaske ki rage
yawan aikinnan ita wannan sakaryar yarinyar shagwab'abb'iyan yarinyane yanzu take koyan aiki
ki barta ta koya kekuwa semu huta abunmu" wani langwabe kai tayi tace "Haba shaam meye
hakannan wai,nika tafi idan muka gama zanzo" hannu biyu ya saka dukda zaman ta katuwa ya
dauketa yabar kitchen din da ita,ita kuwa dama gulmane haka takeso ya sanya bata wani musa
masa ba, hannu hafsat ta sanya ta share k'wallan daya kwaranyo mata

"Yaa Allah ka yayemun wannan masifar,Allah ka rabani da k'aunar yaa shaam,Allah ka ciremun
kishinsa,Allah ka kawomun agaji" wannan itace adu'ar datakeyi a sarari cikin kuka,tafi mintuna
biyar a haka,kanta barwa Allah taci gaba da aikinta.....haka rayuwa taci gaba wa hafsat kullum
itace da bauta agidan yaa shaam sekace wata yar aiki,shi kuwa kullum kwanan duniya qara
tsanarta yakeyi yakuma rasa dalilin tsanar dayake wa kanwar tashi wanda a sanda tana qarama
bashida wacce takeso sama da ita,amma yanzu tun sanda yagano sanshi takeyi seya dauki
hakan a matsayin raini ya d'auki karan tsana ya d'aura mata kullum acikin bautawa gidanshi
take ita kuwa yi hawai takeyi domin ta faranta masa,momy kuwa komai akan idonta take tafiya
yanda ake takurawa yarta ba karamun damunta yakeba,duk kuma sanda tayi magana sekaga
fuskar daddy ta sauya akan hakan.
Hafsat da huda sun samu admsn a Usman d'an fodiyo university dake sokoto,inda dukkansu
suke karantar English,dabadan hafsat tanada kokari ba dabazata gane komai ba a makaranta
kasancewar gaba daya hankalinta yana kan yaa shaam kullum kwanann duniya da begensa
take kwana kuma take tashi,shekarunta goma sha shida yanzu yakamata ace ta qara girma
irinna tashen balagan nan amma sam damuwa ya hana ta,tanaso ta yakice wa kanta soyayyar
yaa shaam amma ta kasa,ganin rayuwar gidan yamata k'unci ya sanya tabar sama road gaba
daya ta tattare kayanta tace gidan Abba haris zataje gun khairiyyah dayake itace tsarar
haihuwarta,momy bata hanataba kasancewar tasani sarai 'yar tata tana cikin damuwa,gwara
ma tane candin kota samu sassaucin abinda yayan nata kemata wannan kenan.

Tunda hafsat takoma gidan Abba haris se kewar shaam ya taso mata,shaam seyayi sati biyu
bezo wurinsu abba haris ba,dukkuwa dayake sune iyayensa na ainahi,sabida kawaici,lokacin da
yayan abban haris yayi aure wato mahaifin hafsat yajima be haihuba kai har haris yayi aure
suka haifi shaam,shine fa suka baiwa yayanshi shi na har abada ganin yana matukar san y'ay'a
amma Allah be kawo masa ba shiya sanya hafsat datazo sanda ba'a zataba bata gane cewar
ba mahaifansu daya ba na haihuwa se daga bisani,domin kuwa an cire rai kamar daga sama
Allah ya kawowa haj nasara cikinta samun hafsat be sauya komai ba na dangane dankaunar
dasu momy da daddy kewa shaam ba......duk tabi ta qara yamutsewa batada kiza kiza,har Abba
haris ya fahimci haka,kuma yayi juyin duniyarnan amma sam tace ita ba abunda ike
damunta,da wannan yayi kiran khairiyya yace lallai tabi yar uwarta taji meke damunta cikin

hikima domin ya kula ko wannan dawowan da tayi da dalili. Da dare hafsat ta tashi kukan data
sama na rashin yayanta,wayanta ta dauko ta qurawa hotonsa ido a sarari kuwa tana kuka tace

"yaa Allah ina rokonka,ya ubangijin sammai da kassai,ya Allah ka ceceni Allah ka cire mun san
yaa shaam a zuciyana,Allah ka rabani da kaunarshi,Allah ka ceci rayuwata karna mutu"" kuka
me tsanani ya kwace mata khairiyya da ke kwance tana kallonta tana kuma saurarenta da
mamaki tazo ta dafa tace
"Hafsat yaa shaam kuma? So? So naji kina ambata,shine zaki bari san dan uwanki ya hallakaki
har haka? Kinga kuwa yanda kika dawo sekace ba poojah kulelen daddy ba? Meyasa zakiyi
shiru kibar abu aranki bayan kuma kinada gatan da za'a miki abinda kikeso?" tana kuka ta kasa
magana dakyar khairrii ta rarrasheta tayi shiru sannan ta kalleta tace
"Anya khairiyyah yaa shaam ze tab'a sona kuwa? Baze taba sona ba shekaru biyu kenan da
yasan i a sanshi amma banda tsana ba abunda yake qara nunamun kullum,ina kyautata zaton a
duk fadin duniyarnan a zuciyar yaa shaam wanda ya tsana ni kebin shedan,nikuwa bansan
mesaba nayi rashin sa'an zuwana duniya wlhy inaga san yaa shaam ne zeyi ajalina amma dan
Allah karki sanarwa kowa kinji?" hannunta ta kama tace

"Wlhy bazan barki cikin azaba bayan inada maganinta,wlhy sena gayawa Abba gobe da safe
tayaya poojah?? Tayaya san dan uwanki ze illataki bayan kinada gatanki? Ni gaskiya sena
fad'a" kwanciya tayi ajikin khairiyya tama kasa magana......washe gari khairii ko breakfast
batayiba taje ta kwashe komai ta sanarwa Abba,aikam ya hau bambami yace
"Amma shine kulelen tayi shiru,shekaru biyu tun lokacin aurenshi fa kenan,lallai wannan
yarinyar tasha wahala wlhy bazata sab'uba dole dan ubanshi seya aureta shi kuwa kodan
halaccin ubanta akanshi,maza tashi kije anjima zan nemeku" tana barin wurin ya daga waya ya
kira yayanshi da shaam akan zezo gidan ya samesu akwai magana,da khairii da Hafsat
dakuma umman su khairri aka je.....bayan an gaggaisa ya kalki yayan nashi yace

"Yaya wannan ramar da damuwar da hafsat ke kici duk akan tanasan yayanta ne shaam
aurenshi take sanyi ni kuwa na yanke hukuncin ayi auren tunda yanada halin yin hakan" tamkar
saukar aradu haka yaa shaam yaji wani maganar da sauri ya d'ago ya kalli abba haris,daddy ne
yace
"Haris ai ita kace tana sanshi shifa bamuji ta bakinsa ba,kai shammaz menene ra'ayinka?" k'asa
yayi da kanshi kan yace "Daddy ni bawai bana san hafsat bane ba amma dama tun farko ita na
fara aura amma sam ni ba tsarin mata biyu a ra'ayina tayi hakuri kawai ta nemi wani" umma ce
ta yanka masa wani mari dabesan da zuwansa ba "Kai mara hankalin inane dazaka taramu
anan ka gaya mana wani tsari to bari kaji wallahil azeem ko yanzu na mutu indai ba hafsat ce
tace bata sankaba bazata aure kaba kaine kaqi wlhy Allah ya isa ban yafe maka ba indai kaine
ka kuma cewa bazaka auretaba" se huci take abba haris ma yace "Lallai wannan anyi dan
banzan yaro,toka sani ninan na yanke hukunci kuma wlhy koda wasa kakuma furta bakaso na

sallamawa duniya kai aure kuma nanda sati biyu masu zuwa zan daura idan muka kaima ita ka
dawo mana da gawarta washe gari tsabar rashin san rugura tsari" shidai bece komai ba yayinda
hafsat se kuka takeyi daddy yace

"haris ina darai zaka yankewa shaam hukunci? Ina nine ubansa? To baza ai masa auren dole
ba indai ina numfashi" ran abba haris ya baci ya kalli yayanshi yace

"yaya iya tsawon zamana dakai ban taba maka musu ba amma wlhy wannan karon bazan
lamunta a cutar mun da 'ya ba,wlhy indai har ina numfashi nanda sati biyu zan daura aurensu
sannan kuma idan yace yafasa Allah ya isa tsakanina dashi" jikin daddy ne yayi sanyi kuma
harga Allah shima yanasan auren,momy ma dadi fal aranta sabida tasani hafsat nasan shaam
sosai......bayan sun watse hafsat na d'akinta yayinda kahirri ke toilet shaam ya shigo tamkar
wani mayunwacin zaki,tana ganin ta mike a tsorace,Da baya da baya take tafiya har suka isa
bango,ya sanya hannunshi ya matse hannunta sosai yace "Kika zab'i aurena bayan kinsan na
tsaneki ko? Kika zab'i aurena bayan kinsan zakisha uquba a hannuna? Kika zab'i had'ani da
iyayena sabida tsabar san zuciya ko?? Wlhy ki sani se kin gwammace kid'a da karatu indai
muddin kika yarda kika shigo hannuna,sekin gwammace da bakizo duniyaba sekin kasa
tantance nine kuwa kobani bane,shawara nake baki ki janye inba haka ba ko hmmm wlhy senci
qaniyarki da mai da yaji,k'aramar yarinya se iskanci banza tambad'addi'ya....yana kaiwa nan ya
saketa ya juya,ita yauma ta kasa koda kukanne sabida bakin ciki,gashi sam bazata fasa
aurenshiba koda ze yanakatane gida biyu idan anyi auren......hmmm hafsat kenan anya baki
daukowa kanki masifa ba kuwa??....

Mon Nua'iym
[1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

Wannan shafin nakine kyauta Aunty me jiddah musa,Allahu ya wadata ki da hasken rayuwa ya
sanyaki a aljannarsa madaukakiya

08
Mamakine ya kama hafsat sanda ta farka taga har qarfe tara ta gota sauqinta daya tana fashin
sallah,jiki ba kwari ta tashi ta shige toilet tayi wanka ta sanya rigarta mara nauyi pink color
doguwace har qasa ta sanya kula bayan ta tufke kanta a tsakiya sannan ta fito zuwa ktchn
indomie da kwai ta dafa ta dawo parlor tad'an tsakura kad'an ita har yanzu ta kasa gane
meyene yake damunta wasu lokutan tanaso tayi kuka amma fir se hawayen suqi zuwa tama

kasa tunanin komai gaba d'aya,ta kunna uban fankacecen tvn dake cikin parlor din amma
takasa fahimtar me akeyi abinda yafi bata mamaki shine batasan tunanin me takeyiba idan za'a
yankata batasn me take tunaniba abu daya ta sani shine wani zafi na musamman zuciyarta ke
azabtar da ita dashi wanda kuruciyarta ta sanya ta kasa gane dalilin zugin....a haka yaa shaam
ya shigo ya sameta bayan yayi amfani da key dinshi yashigo gidan kasancewar yayita faman
knocking bata bude ba,kallon tsana ya wurga mata sannan yace " ke hafsat dama tsabar rainin
hankaline ya sanya kina jina ina knocking kikamun banza?" gani ko motsi batayiba ya sanya ya
matsa kusa da ita ya doddoki kafad'arta firgigit ta dawo daga duniyar tunanin dataje,da sauri ta
miqe tsaye tace cikin tsoro "Na'am yaa shaam" harara da kallo me nuna tsananin tsana ya
rabita dashi

"kina nufin duk wannan knocking dana jima inayi bakijiba,tsabar zamanki sokuwa,kinzo kin tasa
tv

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0