Showing 21001 words to 24000 words out of 54422 words
yabi da kallo sannan a hankali ya mayarda dubansa zuwaga Dr. Hafiz
amma beyi magana,cikin dakiya hafiZ yace dashi
"Im so sorry to say we lost both the mother and the child,tunka mufara thereter d'in Allah yayi
ikonsa akansu kayi hakuri abokinaHaka Allah ya tsara"Kasa koda motsi yayi idonshi sun
qeqeshe sunyi jajir amma ba alamun ruwa acikinsu,ihun da hafsat ta kwallah ne ya dawo dashi
duniyar tunanin dayaje,da sauri sukayi kanta se gunjin kuka take wayyo ita Allah Aunty suhaila,
bata taba ganinta ba se a hoto kasancewar wancen lokacin dasukayi shiri sosai ita bata gani
kuma tunda ta warke bata zoba amma sunyi wata irin shaquwa mara misaltuwa kullum se sunyi
waya yafi a irga,ko jiya sanda sukayi waya,yauma da safe haka, sosai hafsat ta gigice dajin
zancen Dr.Hafi,say shi yama rasa me zeyi Dr.bafiz ne ya lallashinta azatansa qanwar
marigayiyar ce, A haka ya lallaba yayiwa mahaifinshi waya da kuma nata mahaifin kasancewar
dama basusan ankawota asibiti ba,mutuwar suhaila ta rikitar da Dr. Say sabida yana matukar
qaunar matar tasa,sannan be tab'a kawo mata mutuwa ba ko kan yafita da safe lapiya lau ya
barta kuka yake tayi tamkar wani qaramun yaro har akayi sadakar uku,hafsat ma gaba d'aya ji
take duniyar ta mata duhu,batajin dad'in komai,haka dai dole kowa ya haqura wanda ya fisu san
baiwarsa ya dauke abarsa gaba daya.......
*Bayan sati uku*
Yaa shaam zaune a parlor din gidansa kusa dashi haleema ce take ta faman taunar cingam
sekace abun dole, shi kuwa gaba daki daya hankalinsa baya kan kallon dasukeyi yana gun
wannan hafsat da gaba d'aya tun zuwanta ta sauya masa tunani,be tab'a zata akwai ranar da
tunanin hafsat ze hanashi sakat ba,anya kuwa bazece da abba yayi nadama ze maida itaba,kai
idan yaje gun abba baze saurareshiba wataqil gwara ma yaje gun daddy,da wannan tunanin
yaje ya kwanta....
Niko nace hmm ubanka zakaci d'anye wlhy..
"Mero ni kuwa wai in tambayeki?" kallon hafsat meron tayi "Ina jinki mana Allah yasa na sani"
gyaran zamanta tayi ta tattare nutsuwarta gun mero tace
"meyake damun yaa shaam? Naga duk yabi yayi baqi ya rame,kuma ya rage kiza kiza" kura
mata ido mero tayi na yan dak'k'u kan daga nisani bayan ta gama nazarinta ta nisa tace
" kaidin mace ke d'awainiya da shaam hafsat,wlhy haleema tagama da yaa shaam ta shanyeshi
tas,danma su momy sun tashi tsaye da adu'a,danma bazaki fahimta bane amma da kunnena
naji tana magana da qanwarta harira akan naqasashin dasukayi,ko kad'an fa baya sha'awar
mace wai sabida karya tuna abunda suka aikata,in taqaice miki dai kud'ad'e take karba a
hannunshi da kadarorinsa baji ba gani nan da kika ganshi yanzu bashi da komai se asibitinsa
shi d'inma sabida daddy yana tsaye ne akan asibitinsa da takardun wurin gaba d'aya,sedai
tayita yawon banza nabin maza,ni a ranar danaji suna zancen aunmai asiri a ranar na sanarwa
momy nanne fa aka d'an samu sauqi domin adu'o i da magungunan tsari sukayita nemar
masa,gashi baya kula da ibadunsa da addininsa seda daddy ya tashi tsaye yanzu dai yaji
sauqin rashin jin sha'awa duk nice yar rahoto akwai lokuta da dama da idan naje gidan nikan
tadfasu suna wasaninsu wasu time ma har kwanciyar aure nake fahimtar sunayi dukda ni ban
yarda da matar ba,yanzu abu daya ya gagaremu shine rabashi da matar sabida tsananin santa
yakeyi fa,gashi ita kuwa komai ya samo seta qwace shi tatas ni na rasa wane irin kaine sa yaa
shaam,gashi kumansu daddy sun saka yana adu'o i kema dai ki tayashi gaskia,yana cikin
wahalar mace" nisawa tayi sannan tace "Allah ya kyauta musu,Allah ya shiga tsakaninsa da ita"
kallon tausayi mero ta mata ganin tana kwallah tace
" Nasani hafsat har yanzu kina san shaammaz ina rokon Allah ya daidaita tsakaninku" kallonta
takumayi tana me sharar kwallan daya zubo mata tace " Mero bana fatan sake zaman aure da
shaam,ko a mafatki naganni matsayin matarshi lallai senayi adu'ar tsari daga mugun mafarki
had'eda yin sadaka, har kwanan gobe ina san yaa shaam sedai a yanda na fahimta sam
wannan bashi bane mafita agareni,so tari zakiga abubuwan damu y'an adam muke so basu
suke zamtowa mafakar alkhairi agaremu,yaa shaam ko banda asiri ba sona yakeyiba kuma
tsana ta zahiri,nidai wlhy kinji na rantse miki nidashi har gaban abada,ina dai masa fatan
alkhairi" jinjina kai mero tayi "To Allah ya kawo miki muji na gari me qaunarki" "Ameen" ta fad'a
ataqaice sannan ta kwanta ta runtse idonta......
*Bayan sati biyu*
Shaam durqushe agaban daddy da abba haris dasu momy harma hafsat wacce dominta aka
tara zaman,kasancewar wai shaam yace ze aureta kuma ze barta harseta qarasa karatunta a
india,kowa yayi shiru yana kallon ta tsuniyar daddy domin kuwa ilahirin jama'ar wurin kallon me
bada tatsuniya suke masa harya idar,hafsat dai batace qala ba kazalika bata koda girgiza da
zancen ba tunda taga yana mata bata dagawa be dena kiranba ta tabbatar cewar lallai da wata
aqasa..... Kallon su Abba yayi yayi wani malalacin murmushi sannan ya kalli hafsat yace "y'ata
nasan bazaki tab'a watsan qasa a idoba,ina sauraronki menene naki ra'ayin ni duk abunda
kikeso shi zan miki" kallon shi ta dago tayi ido cikin ido suna had'a ido abba ya gano ta shaqa,ta
nisa sannan tace idonta a qanqance
" Bazan sake fad'ar abunda zan fad'a a yanzu ba,abu d'aya nake san kusani shine,dukkanin
abinda kukaji zan ambata yanzu babu wasa kokuma wani abu makamancin raini
aciki,kuskurewa qa'idata d'aya ka iya janyo lalacewar komai musamman idan na aikata abinda
zan aikata idan aka kuskuremun qa idar" shiru ta danyi kowama yayi tsit taci gab
"Ni bazawarace ba budurwaba kuma a tsari na addinin musulunci nice dakaina nake da haqqin
zab'awa kaina mijin aure a yanzu,bazan lamuncewa zab'in kowa ba tsarin addinina zanbi, kuma
wlhy summa tallahi bazan tab'a komawa auren shammaz ba,ko gawata akayi kuskuren
daurawa aure da shaam ban yafewa wanda yayi ba koda mahaifinane kuwa, idan aka
qarabtayarmun da zancennan wlhy na sanya qafa nashiga duniya nida gida har abada,idan
dame tantama kuma ya gwada tada zancen kuga ikon Allah, ku tambayeshi kuji dalilansa naqin
zama dani idan dai basankai kuke sanyi ba ai bazaku qara cutar saba kamar yanda kukayi
abaya,da bakinsabyace dani ya tsaneni!! An cuceshi da aka had'ashi aure dani,da bakinsa
gashinan zaune ya kalli tsabar idona yace dani Babu tabinda ze zauna da mace bushashiya ni
menakedashi,mena ajiye ajikina ina fama da qasusuwa,da bakinsa ya kalli tsabar idona yace
dani na dena mafarki ze tab'a had'a shimfud'a da banza irina bushashiya,ashe nidin nan icce
ce a idonku,ashe bajini a jikina,ashe qarfeceni bansan dadin mijiba,idan har baku sani ba toku
sani yau nasha baqar wahala rayuwa da miji fanko,ina da aure an kawar dani sabida gudun
wannan yaso ya cillani gayinta banda a litttafan hausa da fina finai ina kuka tab'ajin anyi aure
shekara daya amma namiji be taba koda riqe hannun matarsa ba duk sanda kuka ga jikina da
nashi ya hadu tofa duka ne,kuma da bakin sa ya sanar mun cewar bakin rijiya ba wurin wasan
makaho bane,shine ina makauniya zan dauki kaina inkai daidai bakin rijiya,sabida bana tsoron
afkawa aciki,toku sani ina tsoro!! Na rantse da Allah kona rasa mujin aure bazan auri yaa
shaam,ninan ni kadaice na san baqar wahalar danash a hannunsa,a ranar dana samu matsala
dakaina na roqeshi akan waze aureni idan yasaken ya taimaka ya maidani gidansa,bud'ar
bakinsa se cewa yayi dani be soni sanda nake da lapiya ba se yanzu dana dawo
nakashashiya,bayan shine silar lalacewar rayuwata da quruciyana kowa namun kallon
bazawara!! Kullum zancensa d'aya ya tsananeni yana tunasar dani bakin rijiya ba wurin wasan
makaho bane,shine yanzu ze bazamo kome ya gani ajikina oho!!! Ko kuwa dai yanzu zan iya
wasa a bakin rijiyar tunda naqasa ta tafi oho!!! D'aukacin mutanen parlor dinnan ku shaideni
ranar dazaku qara zuwamun da zancen komawa gidan shaam kun rasani kenan har abada!!!!""
Jikin kowa yayi sanyi yayinda abba haris ya zabgeta da albarka,shaam kuwa ya saka kuka wiwi
wai ta taimaka masa....to phaaaa..
Zaune suke idata Uncle say a babban parlor na gidan daddy se shagwab'a takeyi wai bazata
koma india ba,shi biyeta yakeyi ya saba haka sukeyi da qannenshi sesu sakashi gaba abu beje
yazo ba su saka masa kuka
"Haba dan Allah uncle say,idan kuma na tafi bazan qara ganin kaba fa" murmushi yayi yace
"Dan Allah hafsat ki dena rigimarnan,bakya ganin khairi batayi haka ba? Ke komai se kace jin
jira,komai rigima komai kuka,na sanar miki akwai wani coirse dazanyi a india na shekara daya
kuma nxt montj zanzo,tunda kunfara school seki koma kafin nazo" turo bakinta tayi waje " Ni dai
jiranka zanyi bazan iya juran rashin ganin kaba na tsawon wata ni yanzu im used to you over,i
just cnt imagine my self with out you around" Murmushi ya sakar mata "Nima haka beauty
amma ya zamuyi yanzu idan namiki aure ya zakiyi? Sekice dani zaki tafi" B'ata fuska tayi
"Ni nace dakai zanyi wani aurene,ni bazan taba aureba aje ana dukana,maza basuda kirki wlhy"
janyo hannunta yayi shi yarigada ya saba da al'adar indiyawa yace
"Beauty banasan wannan mummunan tunanin dakika sakawa kanki,sam be dace kina cewa
bazaki qara aure ba,adu'a zakinayi Allah ya kawo miki muji na gari me qaunarki tsakani da
Allah" kallonshi tayi ido cikin ido tace
"Ni koba wannan ba bazanyi aureba,idan nayi aure mijin baze bari ina ganinka kullum
ba,nikuwa that will be d worst thing that will happen to me ever,i just cnt imagine my self living a
day with out u" murmushi ya sakar mata yana nazarin kalamanta sannan yace
"yanzu dai naji,amma ki daure ki koma school Allah zan siya miki sabon waya da sabon laptop
da sabon ipad kuma zan siya miki sabon kaya ma,na zuwa school madam gayu" tana murmushi
tace "Thank you for that,buh bana buqatar komai daka lissafa i just need u beside me,idan
wannan baze samu ba,zan haqura nace haka Allah ya tsara" sakin hannun mata yayi yace yana
miqewa "Thats very good of u gold,zancen waya kuma i already bought one for you, samsung
s8 your favorite product,yana mota muje nabaki " miqewa tayi tana ihu tamkar ta
rungumeshi,say akwai principles seyaga dama suke riqe babbar waya fa!! A hanyar fita suka
had'u da yaa shaam,uncle say ya miqa masa hannu su gaisa,dakyar ya bashi hannu sannan
yace " ke hafsat wai an sanar miki kowane mutum kika dakko secikin gida ake kaishi haka
akeyi?? Ga guest parlor can kuje amma se ciki,ba wani privacy kuma bare ma" kallon mamaki
say ya masa ita kuwa taja hannun say batare data koda kalle shiba domin kuwa ita alqawari tayi
idan yayi sallama zata amsa,ita kuma tashigo koda shi kadaine a wuri zata masa sallama amma
bazata taba yi masa magana ba,koda ze mata bazata kulashi ba, gabansu yasha sekace wani
dolo yace "ke badake nake magana ba?" say ne yace "kayi hakuri Dr. Shammaz inshaa Allah
bazan qara zuwa muku gidan bama gaba daya bare kayi fadan bare ya shiga ciki" kawai se
hafsa ta saka masa kuka
" look uncle say,lemme just go n pack my things im going back to my Abba's house,im tired of
this mesa daga zuwa hutu,Allah bazan kuma dawowa Niger ba sena gama school" hannu ya
sanya ya dauko mata mayafin daya fadi ya rufe mata kanta sannan yace " Ina sauri ne
gold,muje na baki wayanki" wani kishine ya tasowa shaam yace kai din dan iskan inane dazaka
taba ta?? Dama iskancin dakuke kenan ko?" sosai rayuwar say ta baci ya wuce su zuwa
mota,ya shige ita kuwa hafsat bakin ciki ya hanata koda motsi daga inda take se kallon say
takeyi kunyarsa dukta rufe ta,hannun ta shaam yaja ya mannata da kofar parlor din yace " Ke
wlhy ko zaki mutu sekin koma gidana wlhy ki sani wannan kayan dakika tara sena mora,bazan
bari banza ta wuce niba" kallonshi kawai takeyi harya gama ya saketa batace dashi ci kanka
ba,rayuwarata intayi dubu tota baci,haka ta zauna ta dinga kuka tana kiran uncle say yamma
yaqi dagawa gaba daya ta damu da fushin sa,tsinuwa kuwa shaam yashata cikin kwando
dubu....
Koyaya zata kaya a wannan bada qalar,gamu gani dai.....
Mom Nu'aiym ceí ½í´¨
[1/30, 8:18 PM] Billy Galadanchi: *í ½í²…BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*í ½í²…
  Love story 2018
Billy galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
Â
Wattpadd@ 68billygaladanchi
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*
                  17
Yaa shaam juyawa yayi zuwa gidansa,ransa a b'ace yarasa dalilin sha'awar hafsat da Allah ya
jarabeshi da ita,gashi sam shi har yanzu beji yana santaba,amma dai tunanin ta kullum dashi
yake kwana yake kuma tashi.......hafsat har washe gari idan takira wayar uncle say baya
d'agawa duk hankalinta ya tashi, se messages take sending mai na ban hakuri sekace ita ta
masa laifi,ganin dukta damu mero ta kalleta tace
" kulele lapiya dai?? Naga tun jiya kamar kina cikin damuwa?" lumshe idonta tayi sannan tace a
wahalce "Uncle say ne yake fushi dani mero,sam yaqi ya saurareni" kallon nutsuwa ta mata
take hankalin mero ya tashi,kaddai ace hafsat san wannan sayyeed d'in takeyi? Inko hakane
wannan yarinyar taga rayuwa ita gaba daya kullum san maso wani takeyi,kuma a yanda ta kula
koda tana san say din batamasan tana yiba,ta yiyu wannan karon da sabon salon daya zo mata
"Menene ya faru yake fushi dake har haka?" dafe kanta tayi sannan ta zayyane mata komai da
ya faru ta qara da cewar
"Amma mero kinga ya dace ace wai ya d'auki zafi dani har haka? Bafa nice namar laifi ba,taya
ma za'ayi laifin wani can ya shafan?" nisawa tayi sannan tace "Tooh hafsat kinsan wani be iya
fushi ba ta yiyu bawai fushin yake dakeba ranshi ne kurin a b'ace idan ya huce ze kiraki" kan
wani yayi magana wayan ta ya soma qara,jikinta har rawa yakeyi ganin uncle say ne,da sauri ta
d'aga ta kara a kunne,kasa magana tayi kurin ta sanya masa kuka me tsuma zuciya a hankali
yace
"Rose menene kuma na kukan,ke komai bakida wani uzuri,kizo ina parlorn qasa a gidan daddy"
zabura tayi ta suri mayafinta ta sauke da sauri,taje kusa dashi ta zauna tace tana sharar
kwallah
" Uncle say im so sorry" kallonta yayi yace "meye na bani hakuri kuma me kika mun,naga cols
dinki ne,inata fama attending patients jiya goda naje gida it was late i coul'nt col u back,yau
kuma tun asuba aka mun waya muna emergency thereter,i had to go there wlhy kina
raina,shiyasa da sauri ina gamawa da office nazo na ganki kiyi hakuri"Â share k'wallan daya
gangaro mata ta saka hannu ta share sannan ta kalleshi tace
"Ni na damu na zata fushi kakeyi dani,rabon danaci abinci tun jiya ma" zaro ido yayi yana
kallonta "Wlhy ina ganin mutane masu wawta na dad'e sosai banga irinkiba hafsat,tayaya
bakimun laifin komai ba zan soma fushi dake,maza tashi muje na siya miki abun dadi a season
7" murmushi ta masa tace "Karka damu zanyi samosa a gida" B'ata fuska yayi
"Lallai ki tashi mu tafi,banasan shashanci" ahaka taje ta sako hijab tazo suka fita,suna fita yaa
shaam na danno kan motarsa acikin gidan,qwafa yayi yace aranshi lallai dani kuke zancen sena
qulla maka sharrin dabakasan akwai irinsa a duniya ba !!!!!.....
*Bayan wata d'aya*
Tun bayan da su poojah suka koma school yaa shaan yake cikin damuwa,da kanshi ya fahimci
cewar lallai ko bayan sha'awa san poojah ya masa mummunan kamu ba kad'an ba, gaba d'aya
mantawa ma yakeyi da wata haleemah a rayuwar sa kuma sam yadena bata kud'i hasalima
baya kwanciya wuri d'aya da ita sun raba jaha ita kuwa dama ba sanshi takeba wannan ya
sanya bata damu ba neman mazan datake kawai tasaka agaba tana samun kudad'e dama abu
d'aya ya tsayar da ita shine asibitinsa daya saura ta k'wace masa,ganin kuma baya zuwa
wurinta azatonta aikin da boka yace ze koma yine na ganin sun kwace asibitin daya kuma cewa
lallai ne seya hanashi jin sha'awarta,wannan ya sanya hankalinta yake a kwance,yau shiri na
musamman yayiwa zuwa gidan daddy akan maganar auren sa da hafsat wanda yake wannan
kadaice mafita agareshi,koda yaje ga mamakinsa daddy haquri ya bashi akan lallai se idan
hafsat dince da kanta ta amincewa komawa gidan sa amma muddin ba ita kesan koma masa
ba toko lallai ya zame masa dole ya haqura,da wannan b'acin ran ya koma gidan sa.
*INDIA*
Tun bayan rasuwar matar Dr. Say yake cikin tsananin damuwa,shidai sosai ba kadan ba yake
santa over,yaji zafin mutuwar ta fiyeda tunanin me hankali,zaune yake a babban parlor ya rufe
fuskarsa da littafin dayake nazari,tunani ne fal a ranshi na suhaila wanda sam bemasan cewar
hawaye sun fara gangaro masa ba,poojah kuwa tajima tsaye akanshi tana nazarinsa wanda
shigowarta gidan kenan daga makaranta,a hankalibta sanya hannu ta janye littafin dake saman
fuskar tasa ganin hawaye ya sanya ta danja baya a d'an tsorace,k'ura mata ido yayi itama din
shi take kallo,zama tayi kusa dashi ta kalleshi cikin kulawa tace cinkin mutuwar jiki
"Uncle me kuka kuma? Meya sameka haka?" d'an juyar da kanshi yayi yace "Hafsat suhaila
na,suhaila na nake tunawa,yaushe zan samu macen da zata mayemun gurbinta arayuwa??
Wlhy ina matukar kewarta" tausayin sa ne ya kamata tace jikinta a mace "Uncle say dan Allah
ka rage damuwar nan,idan kana wannan kukan mu kuma muce me? Batun yauba na kula dakai
sosai kake damuwa da rashin ta koka manta cewar Allah wanda yafi kowa santa mahaliccin ta
shine ya karb'e abarsa,kuma arayuwa ba'a tab'a barin wani dan wani kuma Allah shi yasan
dalilinsa na dauke rayuwarta alokacin daka fi buqatarta,dan Allah kayi hakuri" kallon ta yayi