Showing 33001 words to 36000 words out of 54422 words
nuna
mata an mata magani kuma turarukan datake using ba wani aljanin daze iya rab'ar inda take
ma, da wannan naji zuciyata tanamun zafi a yanda nakesan hafsat lallai na qudurta araina idan
har ban sameta ba to kuwa bazan taba bari ta mori wata rayuwa da wani namiji ba,a wannan
karon kuwa naga bazan iya kashe abokina ba kuma asirin yaqi cinsu shine nayi amfani da
damar kwanciyar ta asibiti na aikata hakan,amma wlhy nayi nadama musamman rashi aminina
na sosai sosai" shiru aka danyi kan mutane su fara mamakin dan wannan guntun laifin ze saka
tsabar rashin imani ka kashe mace har lahira,hukuncin daya dace dashi aka yanka mai aka
tarwatse karar aka kuma gargadi muhammad akan furucinsa daya janyo masa cin zarafi.......
*Washe gari*
Tsaf J.A ya shirya yaje gidan su hafsat a parlor akai masa masauki,sannan akaje kiran
hafsat,jiki a mace ta sakko yana ganin ta ya miqe tsaye yazo suna fuskantar juna yace
"Bakin rijiya poor barrister,the youngest one,nazone in sanar miki ki gayawa iyayen ki one week
kawai na saka d'aurin auren mu,lokaci yakusa zuwa dazaki san waye muhammad,menene
kuma matsayin wanda ya tozartar dashi yakuma bata masa suna a idan duniya" wasu miyau ta
hadiya masu dacin gaske ta runtse idonta sosai ta bude su a hankali sannan tace
"Kayi hakuri muhammad" bece komai ba ya miko mata waya kirar iphone 6 yace zan miki
waya,idan buqatar hakan ya taso,yana gama fadar hakan ya juya a nan ta durqushe ta saka
kuka me tsuma zuciya.....
Mom nuaiym
  Â
[2/11, 8:52 PM] Billy Galadanchi: *í ½í²…BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*í ½í²…
Love story 2018
Billy galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
Wattpadd@ 68billygaladanchi
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*
25
Da k'yar ta iya lallasr kanta tayi ciki,tarasa wazata tunkara da wannan maganar a duniya,ganin
shirun baze amfaneta da komai ba ya sanya for the first time tun bayan rabuwarta da yaa
shaam ta d'aga waya ta kirasa,mamakin ganin sunan ta yayi amma seya dauka da sauri ya kara
a kunne tare da cewa
"Hafst ya jikinki" amaimakon ta ansa shi se kawai ta saka masa kuka,mamakin jin kukan tane ya
kamashi yace cikin rud'u
"Subhanallah hafsat meya faru? Bakida lapiyane ko kuma shari'an ne be miki ba mu d'aukaka
qara?" cikin sheshekar kuka tace
"Dan Allah idan baka komai mu hadu a season 7 park,inaso muyi wata magana dakai ne"
batare da bata lokaci ba yace "Babu damuwa in the nxt 25 mnts zan isa wurin"
"To yaa shaam nima a haka" da kanta tayi tuqi tana isa wurin ta tarar ya rigata aranta ta ayyana
wata qila yana kusa da gun dama,motarshi ta nufa kai tsaye ta bud'e gidan gaba ta
zauna,gaidashi tayi sannan ta miqa masa takarda,cikeda mamakin takardar meye ya karb'a ya
bud'e zare ido yayi bayan kammala karatun takardar sannan yace yana kallonta
"Hafsat se yaushe zakiyi hankali ne wai e? Mesa komai naki bakya san ki saka tunanin mezeje
ya dawo aranki? Yanzu gashi kin janyowa kanki sabida babu wani wanda ya isa ya watse
wannan maganar yanzu,kuma sanin kanki ne j.A babban lauya ne wanda ya shahara a fannin
iya shari'a,ni bawai auren sa bane banso kiyi sabi kowa ya masa shaidar halayya ta kwarai
kuma sosai reputation dinsa ya girgiza da faruwar wannan abun waya sani koda wata manufar
ze aureki ta cutar wa? Babban burina shine ki samu nutsuwa a gidan mijinki wannan shine
dalilin daya sanya sam kikaga na janye zancen aurenki da zanyi sabida na tabbatar wa kaina
bazaki tab'a samun nutsuwa dani ba musamman akan halima,yanzu sanar dani yaya kikeso
muyi kuma yazo miki da wata maganar ne?" Kallonshi tayi tama kasa kukan yanzu kam tace
"Yazo da yamman nan,yake cewa dani wai nagaya wa su daddy aure nan da sati daya yakeso
kuma zan fahimci ba'a cin zarafinsa a zauna lapiya,har ya bani wannan wayar akan zemun
waya idan buqatar hakan ya taso" nisawa yayi yace
"Hafsat gaskia kinyi kuskure da kika aikata wannan shirmen,babu abinda zakiyi illah kije ki
gayawansu daddy ayi masa yanda yakeso kije kiyita hakuri,danni nan matsalolin dakike
fuskanta suna daukarmun hankali bamu sani ba ko wannan auren dazakuyi dashi ya zamo
sanadiyar jin dadin na har abada ta yiyu ma adu'ar iyayen mu ne Allah ya karba zakiji dadi"
kallonshi tayi qirjinta na dokawa tace
"Baka tunanin cewar wani zargi ze iya shiga tsakani na da mutane? Baka ganin wasu ma zasu
iya cewa hadin bakine kisan da aka yiwa sayyeed nida muhammad? Baka ganin kuma idan sun
fada haka basuyi karya ba,muhammad so yake ya batan suna nima so yakeyi gaba daya nima
duniya ta zageni,idan har na yadda da zancen aurennan tofa wlhy kowa zega tamkar ban
damu da mutuwar sayyeed bane musamman lokacin nan daya diba kadan,dama ace nanda
watanni hudu yace ko biyar"
"Hafsat kije ki lallab'asa da dabarunku na mata cikeda hikima sabida ya yarda abar auren har
nan da koda watanni uku ne,kuma kije gidansu sayyeed na nan garin ki nunawa mahaifinsa
wannan takardar ta yar jejeniya ,shima mahaifin na say kizo masa da hikima ta hanyar rokarsa
akan ya nema miki alfarmar muhammad ya janye wannan agrement din ya hakura da auren
ki,ta wannan hanyar kadai zaki tsira da mutuncin ki a wurin iyayen sayyeed koda kuwa an daura
auren nanda sati daya" jinjina kanta tayi cikeda gamsuwa da bayaninsa
"Yaa shaam dan Allah mana muje gida na ajiye motana muyi sallan magrib in yaso ka rakani
gun baban sayyeed ni tsoron wannan muhammad din nakeyi wataqil idan ya aureni ma mutuwa
kawai zanyi" murmushi yayi yace "Kece mutuwan ai,sekace wani dodo".......
Bayan ta gama yiwa mahaifin sayyeed bayani yakuma ga takardar murmushi ya sake yace
"'yata wannan muhammad din yana sani ya miki haka,sabida yasan bashi bane yayi kisan so
kekuma bakida wani hujjan dazaki iya cewa aa bayan an gama shari'ar,shawarata anan shine
kije ki lallab'ashi" kallon dattijon tayi tace
"Daddy dan Allah ka bashi hakuri akan ya janye wannan zancen nidai bana sansa,kuma idan su
daddy sukaji nayi wannan shirmen bazanji da dad'i ba" kallon ta yayi shima yace "To hafat kije
gobe zan sameshi da kaina,suna kokarin barin wurin kanwar sayyeed datazo hutu daga india ta
shigo,se kallon shammaz takeyi,suna fita ta biyo bayansu da suruun ganin hafsat,a can tace da
hafsat
"T loojah waye wannan?" hafsa tayi sannan tace "Bros shaam my big bros kenan"murmushi
tayi
"hes handsome ina sansa kuwa?" zare ido hafsat tayi
"Da gaske Baby?"
"Ea mana da gaske wlhy" murmushi tamata tace "Idan zaki auresa shikenan sena gaya masa"
dariya tayi tace "Zan aure sa mana ai yafiki kyau" haka dai suka rabu baby se matsawa take da
zancen shaam,koda sukaje mota hafsat ta gaya masa dariya yayi yace
"Ina ni ina ba indiya rufamun asiri" cike da zolaya tace
"Kai yaa shaam banda boye boye fa,Allah ina ganinka se wani kallonta kake kana murmushi"
dariya yayi yace "Ina wasa dake zan mareki wlhy" seda sukaje gidan sannan ya karbi numer din
baby haka kawai yakejin yarinyar ta masa wannan zankadediyar yarinyar lolxx.
Qememe muhammad ya kafe akan lallai baze janye qudirin saba kuma nanda sati daya zeyi
auren danita,su daddy hankinsu ya tashi kowa gani yakeyi auren manufa ne na rama sunansa
da aka nemi batawa zeyi.
Waya kawai ya kira hafsat bayan magaribar ranar yace da ita ta sameshi a mota,tana zuwa ta
shiga gefen me zaman banza ta gaidashi,fitilar motar ya kunna fiskarsa ba yabo ba fallasa yakai
hannunshi ya daga hannunta dake ciwo,dan kara ta saki ya juyo ya kalleta itama d'in shi take
kallo harta soma kwallah,dauke kanshi yayi sannan yace da ita
"Har yanzu hannun nan be gama dawowa daidai bako?" batace dashi komai ba se
hawaye,tausayin kanta takeji sabida sosai take tsoron muhammad,hannu ya saka ya share
mata hawayen daya gangaro mata yace bayan ya dauke kanshi
"Mesa kike kuka hafsa? Banasan ganin saukar tsadadden hawayenki yana zuba a banza kinji"
sauke kwayar idonta tayi kasa batayi magana ba,ya sake cewa
"Yanzu sanar dani me dame kike buqata,bazakiyi shagalin biki ba,ni zanyi dinner da reception
sabida yanzu ne zanyi auren soyayya na kuma zab'ina" kallon shi tayi tana kuka tace
"yaa muhammad dan Allah kayi hakuri" dagowa yayi a karo na farko "Hakurin me kike bani"
kukan ta ne ya tsananta ta dukar da kanta taci gaba da yi,tafi minti talatin tana kuka amma bece
da ita komai ba seda dan kanta tayi shiru,kanta ne ya soma sara mata ta bud'e mitar da nufin
wucewa cikin gida yace cikin izzah
"Nine nace dake na gaji dajin wannan zazzaqar waqar da kika sakani agaba kina reramun?
Maza dawo kici gaba dayi harse ya isheni" kallonshi tayi cikeda mamaki idanta ya kad'a yayi
jajir,yakuma cewa
"Dawo mana nace ki rufe murfin" a hankali ta sako kafafunta ciki batare da tayi magana ba
"Kalli idanki hafsat,duk yayi ja sabida bakyajin magana,nace dake kukan na menene amma
kinki ji,kin zauna kina kuka sekace wacce ke rero waqa,idan ba so kike na sassab'a miki ba
karna kuma ganin hawayenki wlhy,sanar dani yanzu tsakanin ki da Allah menene kikewa
kukan?" sadda kanta tayi kasa tace "Auren ne bana so" kallonta yayi ya sakar mata murmushi
"Banida maganin wannan gaskia,so kiyita kukan,shika d'aine damuwar kodai da wata bayan
wannan?" sadda kanta tai a qasa tace
"So nakeyi ka tausayawa rayuwa ta ka agazamun ka bar aurennan har nan da wata biyu na
roqe ka yaa muhammad dan Allah" kura mata ido yayi na yan dakiku kan yace
"sekin mun alqawari guda biyu,tsakaninki da Allah" kallonshi tayi amma batace dashi komai ba
yace
"Na farko sekinmun alqawarin bazaki taba kawo matsala me kamada kin fasa auren ba idan na
qara miki lokaci,na biyu kuma sekin mun alqawarin bazaki sakeyin kukannan agaba naba
sabida gaskia banaso yana batan rai" yawu ta had'iya tace
"Abba haris ya sanar dani muhimmancin Alqwari sabida haka bazan taba fasa auren kaba,sedai
idan kaine kace ka fasa,kukan ma zan kwatanta" gyada kanshi yayi yace
"Nima ai alqawarin auren ki nayi,idan ko bazaki karya ba ni mezesa na karya, nasan
muhimmancin alqawari ai,kije na yadda nanda watanni uku idan munada rayuwa se ayi auren"
godiya ta masa ya tsare ta akan setayi dariya seda tayi dariyar kuwa sannan suka rabu,se dadi
takeji......
Shaam ba kad'an ba yake jin yana san baby,sedai be sanar da kowa zancen ba se daddy
kasance war shi abba haris har wannan lokacin fushi yake dashi,sedama hafsa ta saka baki
yake dan sake masa kadan,cikin sirri kuwa aka shirya auren sa da baby tare da nasu hafsa,sam
haleemah batasan wainar da ake toyawa ba,tunda taji hafsa zata auri wani shikenan hankalinta
ya kwanta......
Hafsa gabaki daya ta rame tayi baqi,sam wani jarababben tsoron muhammad takeyi gashi
abu mafi ban mamaki shine tunda ya tafi akan ya dage zancen aurensu be qara zuwa wurin
taba kuma gabki daya ya dena kiranta,ita kuma duk sanda tayi yunqurin kiransa se gabanta ya
fad'i, huda ce ta fad'o mata arai ta d'auki wayar ta kirata,komai da ake ciki ta sanar mata,hudan
kuwa ta bata shawaran akan lallai ta kirasa,kuma ta basa kulawa as if tana matukar
sanshi,wasan da yake so su buga idan ba ta wannan hanyarr ta biyo masa ba lallai akwai
matsala,sabida ya shirya daukar fan sane,sosai tayi wa huda godiya koda sun dade basu hadu
ba amma sosai suke hurda,huda yanzu tana germany itada mijinta.
Cikin sanyin jiki kuwa tayi kiransa a waya,kamar baze daga bama,se can taji muryarsa me
saukar mata da fad'uwar gaba yace
"Hello" sanda ta d'anyi jimm sannan tace "Yaa muhammad Barka da yamma" gyaran murya
yayi yace
"Barka dai" a ta k'aice,jikinta ne ya qarayin sanyi tace "Dafatar kana lafiya"
"Ina lafiya" itace amsar daya bata,runtse idonta tayi sannan ta kara budewa tace
"Yaa muhammad ka gane me magana kuwa" kamar baze amsata ba yace
"Na gane mana ba hafsa bace?"
"Ea nice ya kwana biyu?" tafad'a cikeda jin zafin wulakancin data janyowa kanta
"Lafiya lau,ya akayi ne?" dafe kanta tayi dayake barazanar rabe wa gida biyu tace
"Dama naga kusan watanni biyu ban jika ba,shine nace Allah ya sanya lafiya"
"Lafiya lau mana,me zan miki to? Ina auren Agreement ne zamuyi,sekace wata soyayya ke
tsakaninmu dazanta damunki,kokuma daze kasance komai nawa sekin sani?" kasa hakuri tayi
tace
"Koda na kirak bakaji na ambaci soyayya ba ai,danni a wannan zamanin banajin ma akwai
soyayya,kurin dai kamata ya sanya nayi kiranka sabida ni nasanta" sarai ya sani magana ta
gaya masa,amma seya dake yace
"Ni ai tun farko na sanar dake yanzu ne zanyi auren soyayah, kuma zab'ina bakijiba ne,kece
bakya sona so meye zesanya na nanuqe miki?" jan dogon numfashi tayi sannan ta furzar da
wani iska me zafi tace cikin wata rikitacciyar murya
"Yaa muhammad" shiru ya mata tace "Why?" cikin dakakkiyar murya yace
"Hafsatu manga yar sarki wacce maza ke rarrashi,koba haka taken yake ba?" ganin ze raina
mata hankali ya sanya tankashe wayar ta ajiye,be kuma kiraba se qarar shigowar message taji
a wayarta kamar haka
"This should the very first and last time dazaki ajiye mun waya,koda mun gama magana kuwa
lallai nine zan zama na farko da zan ajiye" jikintane ya qara macewa jin kalamansa ta daga
waya takuma kiransa yana d'agaba tace dashi
"Yaa muhammad kayi hakuri" cikin sanyin murya yace "wuyarta ka bani hakuri kai tsaye za'a
wuce wurin,dama gobe zanzo zancen kayan lefenki ki shirya zuwa dubai"
"To Allah ya kara girma na gode sosai"
"Se anjima" shine abunda ya fada a zatonta ya ajiye wayar ashe be kashe ba,ajiye tata wayar
tayi ta sanya hannunta a kirjinta ta shiga rero kuka tana sambatu ta shiga uku,ita dai batayi
sa'an zuwanta duniya yazatyi da masifan yaa muhammad,tunda tasan hankalinta take kwasar
bakin cikin d'a miji,da karfi ta furta
"Allah na tuba ka yafeni,Allah idan na aikata wani laifin ake jarabtana da wannan masifun Allah
na tuba ka yafeni,kuma ka bani ikon cinye jarawar nan daka dauramun" kuka take
sosai,muhammad dake saurarenta ma dafe kanshi yayi,ba abunda ke hanashi zuwa gun hafsa
illah wannan kukan nata,ya tsani kukan ta masifaffen tausayinta yakeji,shidai bazece yana
santa ba kuma bawai wata manufa ta cutar da ita yake da itaba kurun dai tausayinta yakeji yana
gani kamar lallai idan ta auri wani zatasha wuya ne,tunda kuwa ya binciki tarihin rayuwar ta
kaf,ya sani sarai dabe biyo mata ta wannan hanyar ba,shaam zata komawa kuma matar sa ma
masiface a wurinta,kwanciya yayi ya runtse idansa yana mejin zafin zubar hawayenta.....
Menen ra'ayoyinku game da auren hafsat da muhammad? Ina tsumayin jin comments naku.
Vote plss
Mom Nu'aiym ca
[2/12, 8:21 PM] Billy Galadanchi: *í ½í²…BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*í ½í²…
Love story 2018
Billy galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
Wattpadd@ 68billygaladanchi
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*
26
Washe gari da yamma hafsat tana kwance mero ta shigo tace da ita
"Kulele kije guest parlor muhammad yana jiranki yace wai baya samun wayanki" k'irjinta ne ya
dan doka ta dago ta kalli meron
"Ke kika ganshi da kanki?" kallon ta mero tayi,batun yauba ta fahimci ko zancen muhammad
akayi hafsat tsorata takeyi tausayin tane ya kamata tace tana dafa kafad'arta
"Inshaa Allah babu abinda ze sameki,kuma inaji ajikina tarayyarki da wannan muhammad d'in
alkhairi ne mutum ne me nagarta sosai na kula da hakan tun a yanayin gaisawar da yakeyi da
mutane,dan Allah ki saisaita nutsuwarki gu d'aya" batace komai ba ta sanya hijab dinta ta
sauka zuwa qasan......Da sallama ta shiga parlor d'in kanta a kasa,ansawa yayi batare daya
kalli inda take ba,karasowa tayi ta zauna kusa a kujerar dake fuskantar tasa tace
"Ina wuni yaa muhammad?" Amaimakon ya amsa ta seya wurgo mata tambaya
"Mesa kika kashe wayanki,bayan na sanr dake tun jiya yau zanzo?" kanta a kasa yayinda
qirjinta keci gaba da uban dokawa tace
"Banida caji ne"
"Bakuda wutane?" ya wurgo mata wannan tambayar cikin tane ya juya ta dago da sauri suka
had'a ido saurin janye nata idan tayi sannan tace
"Da Akwai wuta caja nane ya lala ce" D'an kishin gida yayi sannan yace
"Mesa baki saka layinki a wayan dana baki ba,kumama mesa bakya amfani da ita tunda na
kawo miki ita da layine a ciki"
"Kayi hakuri" shine abunda ta furta,ya tsani wannan ban haqurin na hafsat wlhy ita komai se
ban hakuri qara tubire fuskar sa yayi yace
"Zancen zuwa dubai ne had'o kayan lefe,idan ina irqawa daidai yau saura 27 day's daurin
aure,so inasan sanin keda wa kuke da intl pasport wacce ayau zaku iya tashi zuwa dubai ko
gobe a misali?" kanta a qasa tace
"Nida khairiyya ne,amma inaga anan ma za'a iya siya ai base anje dubai ba" kallonta yayi na
yan daqiqu sannan yace
"Ba zuwa nayi ki bani shawara ba umarnin tafiyar nake baki hafsat,abu d'ayane zaki riqe mu
zauna lafiya shine rashin yimun gaddama,nine da kaina zan sanarwa da Abba haris zancen
tafiyar nanda kwana biyu zakuyi tafiyar,yanzu zamuje gidan Abba haris mu karbi pasport din
nata,kema ki bani naki daga can zan masa bayanin tafiyar,akwai kayan dana saka aka kawo
daga saudi wasu daga dubai,suma zamuje ki duba ,kayan gidane abinda be miki ba ki fada a
sauya wani" kallonshi