Showing 3001 words to 6000 words out of 46966 words
Chapter 2 - Mafiya Book Compelet By Mrs Sadauki
na fara sai dai babu ita sai shi ɗin dai,kamar ƙyaftawar ido yarinyar ta dawo
normal ta soma magana amma muryar oga ce ke fita.
“ Tun da na soma meeting ɗin yau hankalina yake kanka,wato a fuskar kowa na lura da
damuwa saɓanin kai.HAROON ka fara soyayya faɗa mini wace ce ita?” yana gama faɗa sai ya
ɗauki siffarsa ta namijin kayan yarinyar nan suka zube a ƙasa sai nasa kayan jajaye masu
kamar jini. Kasa furta komai na yi,don in na ce in yi magana ƙarya ce zan faɗa kuma tsaf zai gane.To mene
ne ma abin yi wa mutumen da yake da ƙarfin power ɗaukar siffar mace? Shirun dai ne ya fi
alkhairi a gare ni.
Kafaɗata ya dafa sai na ji wani zuuut,sai muka ɓace daga cikin toilet zuwa daularsa wacce
kusan a can muke taro masu muhimmancin sosai ko kuma in wani sabon members ya
shigo.Ban fita daga wannan mamakin ba na ji na yi sama cikin iska kafin kuma in ji ni
gammm,bayana ya bugu da bango yayin da hannuwana kuma aka banƙare su tare da ɗaure su
da kacar tsafi.
“Babu soyayya a tsarin ƙungiyarmu,amma kai ka karya doka! Zaɓi biyu zan baka ko dai ka
sadaukar da budurwar da kake so,ko kuma na aika ka ɓoyayyar duniya yanzu nan tun kafin
wa'adin shekarunka su cika”
Ido na rumtse gam,a cikin zaɓin biyu babu mai sauƙi a gare ni.Shekara biyar ta rage mini a
doron duniya kamar yadda muka yi yarjejeniya a ranar da zan sayar da ruhina,an bani shekaru
goma na rayuwa a wannan duniya kafin na isa ɗayar,a cikin goman kuma na yi biyar saura biyar
suka rage mini.‘Wane zaɓi zan ɗauka?’ na tambayi kaina a zuci....... [16/11 à 09:04] MRS SADAUKI : *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
04
“Wato soyayyar da kake yi mata har ta kai ka kasa sadaukar da ita kai tsaye shi ne ka tsaya
shawara? Hahaha! Ōgāfōr̃!” Oga yayi lafazin ƙarshe cikin Yaren matsafa a nan take kuma na ga
tile ɗin ɗakin na darewa wata jar turɓaya na bayyana kuma sai girrrr kake shi tamkar ƙatuwar
tirelar ɗan danƙarau mai yin gina.
A inda nake can sama ɗaure a jikin bango nake kallon duk abin da ke faru,gidan ƙasa ne ya
bayyana sai a lokacin kuma kacocin hannuna suka kwance kansu yayin da na soma yawo cikin
iska ina kaɗawa kamar wata leda.
Wasu ɗalasiman tsafi Oga ya soma kafin ya ce “ je ka ɓoyayyar duniya ka yi ziyara na tsawon
kwana uku,in ka fito daga ciki sai ka bani zaɓin ka” rufe bakinsa ke da wuya na soma ji na ina
yin ƙasa har na shiga dogon ramen mai ɗauke da wata daular .
Ina shiga ciki komai ya soma komawa normal ya ɗinke,sai da na ja wani numfashi sa'ilin da na ji
ƙafafuna sun dogane da ƙasa.
Baƙar ƙofar na kalla ta gabana wacce nake da tabbacin ita ce za ta sada ni da ainahin abin da
ake kira da ɓoyayyar duniyar.Na shagala sosai ina kallon ƙofar tare da tunanin da na san ba zai
fishe ni dare ba,kawai sai na ji ƙiiiiii ƙofar ta buɗe da kanta.
Ido na tsura ina jiran ganin wanda zai fito,amma sai na ji wata murya na cewa “ Barka da zuwa
duniyar Ruhaniya ” ban amsa ba haka ban gusa daga inda nake ba .
Sai na ji an kamo dukkan hannuwana biyu ana jana amma ban ganin masu jan nawa,a dole na
soma taka ƙafata har muka bi ta ƙofar nan a take kuma ta rufe ji kake gammm.Duhu ne ya
turniƙe wurin,sai a lokacin kuma na ga inuwar masu jaye da ni saboda wani jan haske da
goshinsu ke fitar wa kamar wuta.
Ci gaba suka yi da ja na izuwa ciki,matakala muka soma takawa muna daɗa yin can ƙasa.Har
muka ainahin duniyar,nan ɗin ko ina da haske tamkar goshin azahar haka.
Duk masu bi suna wuce wa na soma duba,dayansu siffar mutane ce da su yayin da sauran
kuma suke ɗauke da sifofin dabbobi iri-iri.
Irin inuwar nan gani ta waɗanda suka yi min iso,a zuci na ce ‘ ko su waye su?’
“Dōr̃ānī! Masu kula da shige da ficen duk al'ummar nahiyar nan.Ko da wasa wani ya tsaya
hutawa dangane da aikin da yake yi za su hukunta shi ne” na ji muryar ɗazu ta faɗa wacce ta
tarbo ni tun a bakin ƙofa.
Saitin inda murya ta fito na duba,sai na ga yanzu ana ganinsa da kyau sai dai muninsa ma ba
zai bari ka ci gaba da kallonsa ba.
“Amma kuma ƴan Adam ne?” na tambaya.
“Duk faɗin nan babu mai ruhin bil'adama sai kai ,duk waɗanda ka gani da irin siffarka to mutum
ne da rigar aljan.Bima'ana gangar jikin ce ta mutum amma ruhin aljani ne a ciki”
“To ya ake hakan tana faruwa?” na sake jefo masa tambayar.
“Mutanen da suka sayar da ruhinsu ga MAFIYA ,bayan wa'adin shekarun da aka ɗibar musu ya
cika za a aiko da su izuwa nan.Ruhikansu za su dinga yin bauta ,yayin da gangar jikinsu kuma
aljanai za su ɗauke ta su dinga amfani da ita.” yana kawo wa nan sai yayi shiru yayin da ɗaya
abokin aikin nasa ya ɗora da cewa “ dayawan jinnu na son ganin kansu a duniyar bil'adama sai
dai babu damar yin haka don ba za su iya bayyana da siffarsu ba,wannan ya sa suka ƙulla
yarjejeniya da manyan masu ƙungiyoyin asiri da su dinga sayar musa da gangar jiki”
“To mi za su yi da ita?” na yi tambayar cikin zaƙuwa zuciyata na bugawa jin ni ma abin da ke
shirin faruwa da ni kenan nan da wasu shekaru.Sai da suka ƙyalƙyace da dariya kafin su yi
haɗin baki wurin cewa “ duk wanda ya sayi gangar jikinka in yana so zai iya shiga duniya yayi
yawo,wasu ma har auren bil'adama suke yi ”
Tsoro ne ya kama ni,sai nake ganin tamkar in na dawo da zama a duniyar nan aljanin da ya sayi
gangar jikina zai iya zuwa ya cutar da Ammyna.
“Amma wanda ya sayar da ruhinsa ga MAFIYA shin zai iya karɓe shi kuwa? Ina nufin akwai
wata hanya da mutum zai bi ya rushe waccan yarjejeniyar ta farko sai a kafa masa ta biyu?” duk
shiru suka yi suna kallona,na gyara tsayuwa tare da matsawa can gaba ta yadda za mu yi
facing juna na ce “please ku sanar da ni”
“Eh to ba za a rasa ba,sai dai sharuɗan suna da tsauri sosai”
Duk da ban ji su ba haka na ji raina ya ɗan sanyaya har sai da na sauke ajiyar zuciya da kuma
ɗan guntun murmushi ko ba komai zan samu damar da zan yi rayuwa da abar ƙaunata.
Muna nan tsaye wata rundunar wasu inuwoyi ta zo wuce wa,inuwar siffar mutum ce da ita
amma babu gangar jiki.
“Ka ga wannan shine ruhi! ” ya faɗa.
“Amma suna jin magana?” na tambaya,babu wanda ya bani amsa sai yin gaba suka yi har na
soma take musu baya suka ce “ kar ka biyo mu,tuni mun gama aikinmu yi maka iso da kuma
amsa tambayoyinka”
“To amma ina zan je?” na yi tambayar cikin ɗaga murya,ko juyo wa ba su yi ba ballantana su
bani amsa a haka suka ɓacewa ganina.Sai a yanzu ma ne na ji mugun tsoro ya shige ni fiye da
na farko,haka na soma bulaye a ƙatuwar duniyar ina kallon abubuwan ban mamaki har na isa
wani wuri inda ake yi wa wani aski.Duk suka ɗago suna dubana kafin su fara ƴar
kallon-kallon,ɗaya daga cikinsu ya ce “ wane ne kai?”
Ba tare da wani tunani ba na basa amsa da “ Ni bil'adama ne!” ko ida rufe baki ban yi ba suka yi
min caaaa kowa na faɗar ra'ayinsa“ a'a ni zan ɗauka! ” “A'a wannan fa gangar jikin tawa ce! ” “
kai kana da wajen biyu fa ka bar min kawai”
Ido kawai na rumtse ina rawar jiki,jin ana rigima akan gangar jikina wacce Allah ne ya halitta
min ita amma saboda wata buƙatata na butulce wa rahamarsa na sayar.Ina cikin haka ne sai na
soma jin canjin yanayi,ina ware idona sai na koma fanko wato ruhi babu gangar jiki.Da ido nake
kallon yadda ake faɗan shiga gangar jikina wacce ta zama tamkar riga mai haɗe da
wando............
Talla! Talla! Talla!!!!
Set d'in gyaran gashinmu na dauke da
* Shampoing don wanke gashi
* Man ganshi da zai taimakawa gashin wajen k'ara tsayi
* Man gashi wanda zai cire miki kwarkwashi/dandruff/Pellicules
* Garin ambunu da zai hana karyewar gashi
* Man karkar da zai taimakawa gashi wajen k'ara bak'i
* Garim amrfit don sakawa a hamata ta kasance cikin kamshi
* Man coco na asali don gyaran fata
+22780416252
[17/11 à 15:36] MRS SADAUKI : *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
05
Ni da gangar jikina amma banda iko da ita wannan lokaci,ban ma san taƙamaimai ya zan yi na
mayar da ruhina a cikinta ba ko kuwa sun maido min ita.A yanzu da nake gantali cikin iskan
ɓoyayyar duniya sai na fahimci a cikin MAFIYA ni ba kowa ne ba fa ce ɗan ƙaramin jinjiri ashe
ban san komai a kanta ba.
Dōr̃ānī kamar yadda aka sanar da ni sunansu tun shigowa ta nan,irinsu ne su biyu suka zo suka
ƙwace gangar jikina daga hannun aljanan kafin su miƙo min .
“Ka shiga gangar jikinka sannan ka koma duniyarku tun da wa'adin da aka ɗebar ma ya cika,ka
yi kwana uku cicif ”
Tsakanin furucinsa na cewa na yi kwana uku alhalin ni dai a lissafina ba zai wuce na yi minti
talatin ba,da kuma tunanin yadda zan mayar da gangar jikin nawa a ciki sai na rasa wane zan
yi.
“Ka mayar mana za mu mayar da kai” ya ƙara faɗa .
“Ban san ya zan yi na mayar da ruhina a ciki ba” na basa amsa.
Suka kalli juna kafin kuma su haɗin baki wurin cewa “ kai ɗin ba ahalin MAFIYA ba ne?”
Na jinjina kai na ce “sosai ni ɗin ɗana ga Mafiya amma ban san ya ake yin duk abubuwan nan
ba” ban rufe bakina ba na ji sun soma karanta wasu ɗalasima wanda na yi imani na tsafi
ne.Wani girrrr na soma ji,gangar jikina na haɗe wa da ruhina ban san ta yaya hakan ta faru ba
amma tabbas yanzu na dawo HAROON ɗina.
Na ja ajiyar zuciya lokacin da suka ja ni izuwa can wajen ƙofar fita,na kasa haƙuri na ce “ amma
ɗazu kamar na ji ka ce wai har na yi kwana uku a nan,sai nake ganin kamar minti talatin ne ko
zuwa da biyar haka”
“Lokacin nan ba iri ɗaya ba ne da na duniyarku,duk minti goma ɗin ku matsayin kwana ɗaya
yake a nan” ban kai ga ƙara yi masa wata tambayar ba suka cillo ni waje.
Ta hanyar da na bi na shigo nan ta haka na koma,a gaban idona yanzu ma can saman ya tsage
kamar wata leda marar nauyi haka na tashi cikin iska na fito har tsakar fadar Oga ,tile ɗin ya
koma ya ɗinke kansa.
Ɗaya bayan ɗaya nake kallon members ɗin ƙungiyar tamu,da dukkan alamu sun shirya wa
fitowar tawa kamar yadda nake tsammanin Oga ya sanar da su komai.
A cikin abin da bai fi minti biyu ba na ga wani sabon abu wanda can farko ban taɓa ganinsa
ba,ba komai ne bai sai shatin Cross a goshin kowa na member ƙungiyar sannan a ƙasan Cross
ɗin kowanne daga cikinsu yana da alamun lamba,wasu 9,wasu 18 da dai sauransu.Ban yi
nauyin baki ba wurin cewa “ Oga lambobin mene ne nake gani a goshi mutane?”
Bai bani amsa ba sai jin shuuu na yi,wani ɗan madaidaicin madubi ne ya zo yayi tsaye a
gabana,ba wai wani ya riƙe shi ba a'a shi ke riƙe da kansa.A ta cikin madubin na hango hoton
fuskata,wannan karon da tsokarta irin ta ƴan adam ba ƙwarangwal ce ba.Lamba ɗaya(01) na
gani a tsakiyar goshina kuma ni ma ina da zanen Cross ɗin,ina gama gani madubin ya ɓace
daga gabana.
Sai a lokacin Oga ya soma magana,“ Barka da shigowa wani level daga cikin MAFIYA! A can
farko ba kowa ne kai ba face costumer mu,amma a yanzu kana level 1 sannan kamar yadda ka
nemi alfarmar janye yarjejeniyar mu ta farko domin kawo wata sabuwa,mun karɓi kokenka.Sai
dai kamar tun can farko yanzu ma zan sake jaddada maka cewa kowanne tasiri yana da
farashi,ina nufin yanzu shekaru biyar ɗin da suka rage maka a duniya za ka iya ƙara su domin
yin doguwar rayuwa” yana kawo wa nan sai yayi shiru tare da nuna mini kujera na je na zauna
kamar sauran.
Zamana kan kujerar sai na ji tamkar ba normal kujera ba ce amma na dai yi shiru kawai ina jiran
ƙarin bayani.
“ HAROON ?” Oga ya kira sunana,na ɗaga kai na kalle shi sai kuma na je zan mayar da shi
ƙasa amma ya hana ni ta hanyar ce mini “ tsakiyar ido za ka kalle ni sannan ka sanar da ni ka
gani a ciki”
Har sai da na ɗan ƙanƙance idona don ƙara samun tabbacin abin da nake gani shin gaskiya ne
ko kuwa?
“Mi kake gani?” ya jefo mini tambayar.
“ Maƙabarta!” na basa amsa.
“Ka san me ake yi a can?”
“Eh na sani Oga!”
“Yawwa madallah da kai HAROON tabbas alamu sun nuna kana yunwar ƙara tsawon rai” cewar
Oga kafin ya nufi allon da yake yi mana rubutu ko nace darasi.Wani suna ne ya rubuta mai
harafi bakwai wanda tuni na soma tambayar kaina ‘ mene ne kuma alaƙarmu da sunan?’ ashe
kuwa amsar na kusa.
“ HAROON ko tashi ka karanta mana abin da ke rubuce a nan” Oga ya umarce ni.
Na tashi tsaye kamar yadda ya buƙata kafin na karanta “ likafani ”
“Ƙwarai kuwa likafani ne kamar yadda ka karanta ɗin,ka yi daidai ina fatan kuma aikin da za ka
yi da shi shi ma ɗin ya zama daidai”
“Aiki kuma Oga?” na tambaya cike da tsoro,duk kowa ya kwashe da dariya sai da suka yi son
ransu kafin Oga ya umarci kowa yayi shiru.Fuskarsa babu alamun wasa ya dube ni yana cewa
“daga lokacin da wa'adin shekaru biyar ɗinka ya cika to za ka dinga farautar likafanin sabuwar
gawa domin luluɓa shi a jikinka ka kwana da shi,ta wannan hanyar ce kawai za ka ci gaba da
rayuwa a wannan duniyar akasin haka kuma za ka koma inda ka fito yanzu.Na sanar da kai ne
tun yanzu don ka zamana cikin shiri,abu na biyu kuma da ƙungiya ke buƙata a wurinka shine
tsofin takalmi na yara ƙanana.Kowa zai iya tafiya meeting ya ida” yana gama faɗa ya bi wata
hanya ya shige yayin da kowa ya watse ya bar ni cikin zullumi.
Dole dangin na ƙi ce ta saka ni fitowa ni ma,sai yanzu na tuna inda na bar motata wato can
tsohon gidana.Taxi na shiga aka kai ni can amma abun mamaki babu motar a nan,a dole na
ƙara shiga wata taxi ɗin na nufi gida.
Tun a bakin ƙofa na ga kallon da direbana ke yi mini,kamar zai yi shiru sai kuma ya kasa ya ce
“yalaɓai yanzu ko minti ɗaya ba a yi ba na ganka da baƙaƙen suite fa kuma ga shi har ka canza
kaya”
Na haɗe rai na ce “wato sa ido kake yi min?”
“Yi haƙuri yalaɓai” ya faɗa yana rusunawa.
Ina shiga cikin falo na ci karo da Ammy ita ma idon ta waro tana cewa “ HAROON canje-canjen
kayan na mene ne? Ko don ka burge Malama Zainab ne? Hahaha! Wannan kayan fa kamar ma
sun yi datti,waɗancan ɗin dai sun fi yi maka kyau”
Murmushi kawai na sakar mata ina cewa “ina zuwa” sai kuma na haye can sama,ina buɗe
ɗakina na hangi irina sak yana ƙoƙarin shiga madubina.
“Dakata!” na faɗa da sauri,ya juyo muka haɗa ido amma bai saurare ni ba yayi wata suka cikin
madubin tamkar wanda ya shiga ruwa haka ya nitse ciki tun ina ganin inuwarsa har madubin ya
dawo normal........
Assalamu alaikum,mata da ƴan matan garin Agadas.CHAFA'ATU MAKE-UP fitacciyar kuma
jajirtaciya mai koyar da kwalliya iri-iri.Ta yi tattaki tun daga Nigeria ta zo nan Nijar a garin
Agadas domin horar da masu buƙatar koyon kwalliya,ɗaurin kallabi.Wannan horar wa da za a yi
za ta kwashi kimanin sati biyu ,kuɗin koyo jika ashirin ne (20.000f).Ga masu buƙatar ƙarin
bayanin za su iya kiranmu kai tsaye ta wannan lambar 88584336 ,ko kuma ku tuntuɓe mu
lambarmu ta WhatsApp 09041604348 .
[19/11 à 07:55] MRS SADAUKI : *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
06
Gaban madubin na je na soma shafa shi tamkar wasu ruwan Teku haka na ji hannuna ya